Sashe 10
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abinci a yanzu ƙarfe takwas da rabi? Ai da sauran lokaci 'yannan, da yake yau duk suna gida sai ƙarfe goma ko sha ɗaya za su fito karyawa. Ki koma ki kwanta ko ki je ɗakin girki ki samu wani abun ki ɗan taɓa."
Langwabar da kai ta yi, ta kwantar kan hannun kujerar tana faÉ—in,
"Na shiga uku! Wallahi zan iya mutuwa da yunwa idan na kai wannan lokacin."
Kallo Lantana ta bita da shi, ta ce,
"Ki shiga ki sami Saude mai girki ta baki ko ruwan shayi mana."
To, kawai ta ce, ta miƙe jiki ba ƙarfi.
"Sannu da aiki Inna!"
Juyowa ta yi ta kalli mai yi mata sannun.
"A'a! Baƙuwarmu har kin tashi ne?"
"Uhmmm! Ina kwana."
"Lafiya, yaya jikinki?"
"Da sauƙi. Dan Allah akwai abinci? Yunwa nake ji."
Ta faÉ—a kamar zata yi kuka.
"Wai! Gashi yanzu nake É—aurawa. Ko in haÉ—a miki shayi ne?"
"Eh."
Ta amsa da sauri.
Tana tsaye a wajen ta haɗa mata a wani ƙaramin kofi ta miƙo mata.
Karɓa ta yi tana godiya a fili, a zuciyarta kuma haushi ne ya gama rufeta.
'Wannan ne wai abunda zai riƙe ni har wani lokaci? Alƙur'an fitsari ɗaya zan yi in zubar da shi.'
Kafa kai ta yi ta kurɓe.
'Da wannan gara ruwa ma wallahi, ban ji komai ba nikam.'
"Ga kofin na gode."
Ta fito tana tunano É—umamen tuwon dawa da kokon Inno! Da yanzu a gida take da ta manta da ta karya, da yanzu a gidansu ne miyar tuwon rana ne a kan wuta.
Amma anan wai yanzu ne ma ake É—aura girkin safe, ba za ta iya ba.
Gara ma goben ta yi ta koma gida, kafin yunwa ya mata illah.
Falon ta koma ta zauna ta fara kallo, sai dai sam bata jin daÉ—in kallon.
ÆŠaki ta nufa, ta tarar da Lubna har ta yi barci.
Tsaki ta ja a hankali, a zuci kuma ta ce.
'Barcin asara.'
Ganin ba abunda za ta yi yasa ta koma kan kujerar cikin ɗakin ta kwanta, hannunta riƙe da ciki.
Juyi kawai take na rashin sabo da kwanciyar, ga kuma uwar yunwa.
Ji take kamar ta ƙwala ihu ko duk mutanen gidan zasu tashi.
Idan ba iskanci ba, ace duk barcin da aka yi da dare bai ishe mutum ba, sai ya sake komawa.
Ba ta fatan ma tayi dogon zama a irin wannan wajen da yunwa zai yi ajalinta.
Turo ƙofar ɗakin aka yi, Hajiya ce ta sha ado kamar zata gidan biki.
Jin buɗe ƙofar yasa Abulle ɗagowa.
"A'a! Ashe É—iyar tawa ta tashi? Yaya jikin naki?"
"Na jima da tashi, na ji sauƙi. Ina kwana?"
"Lafiya, yaya ƙarfin jikin naki?"
"Da sauƙi." Ta bata amsa a fili.
A zuci kuma ta ce,
'Ina wani ƙarfin jiki, ban sanya ma ciki komai ba.'
"Allah ya ƙara sauƙi."
"Amin."
Har ta juya zata fita, ta juyo ta ce,
"Ki tashi Auntynki ku zo ku ci abinci, ga Babanki ma ki zo ku gaisa, jiya mun je asibiti da shi kina barci."
"To."
Ta bata amsa, ta je har gaban gadon ta miƙa hannu ta bubbuga ƙafafunta.
Idanuwanta ta buɗe, ganin ta tashi yasa ta faɗa mata saƙon Hajiya.
"Na ji ta. Ki je sai na yi wanka."
'Sannu kifi.'
Ta miƙe tabar ɗakin.
Fitowarta ma ba kowa a falon.
Tunani take ina shi mai gidan yake da zata gaisheshi? Ita ba ko ina ta sani a cikin gidan ba.
Kicin ta shiga ta tambayi su Lantana, ita ta fito ta nuna mata wani ƙofa da zai kaita har ɓangaren Alhajin.
Dogon lungune da ya sha sumuntin bature, (Tayis) samɓal ta miƙe ta fara tafiya tana kalle-kalle zuciyarta fal tunanin irin kayan more rayuwa da ke gidan, su kuma suna can cikin karmami.
Ba tayi aune ba, sai ji ta yi santsi ya kwasheta ya timata da kasa, take ta baje a wajen ta yi zaman 'yan biri, sakamakon goge wajen da aka yi bai gama bushewa ba.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
   _Ummyn Yusrah_
_21_
Rintse idanunta ta yi, har da É—an guntun hawaye,ta shiga shashshafa kunkuminta da ta buge a da jikin garu.
Sai da ta É—au tsawon mintuna goma a zaune kafin ta shiga yin rarrafe zuwa wajen su Hajiyar.
Bata yarda ta miƙe ba, sai da ta isa wani babban ƙofa sannan ta tashi tsaye,
'Aljannar duniya! Gida a cikin gida.'
Shine abunda ta faÉ—a a zuciyarta lokacin da ta kutsa kai cikin babban falon, sallama ta yi gami da kalle-kalle.
"Shigo mana Zainab."
Hajiya dake zaune kan daya daga cikin kujerun falon ta faɗa bayan ta amsa sallamar.
A hankali take tafiya don gudun sake afkawa gidan jiya.
Tana jefa ƙafarta kan tattausan kafet ɗin da ke baje tsakiyar kujerun ta yi saurin janyewa, don laushin ya yi yawa, tsore take kada ta kuma jefa kafar ya lume da ita.
Da sauri ta tsugunna a wajen, tana faÉ—in,
"Ina kwana Baffa!"
"Lafiya lau, ɗiyata ashe ta jirma. Taso a ƙasa ki hau kujera ki zauna."
Yaƙe ta yi, ta ce,
"A'a! Nan ma ya yi."
"Ki saki jikinki, nan ma gidanku ne, maza taso."
Kamar ta kurma ihu haka ta ke ji, gani take kamar lumewa ƙasa za ta yi idan ta sake hawa kan wannan abu mai gashin.
Ƙara matsowa ta yi, ba tare da ta hau kan kafet ɗin ba.
"Ke dai Zainab akwai ƙauyanci! Ace mutum da gidansu ya riƙa abu kamar wani baƙo."
Cewar Hajiya.
Dariya Alhajin ya yi, ya ce,
"Za ta ware ne ai, sai a hankali. Yaya jikin naki?Kin ci abinci dai ko?"
"A'a, yanzu zamu ci."
"To, maza a je a karya, kafin a zo a bani labarin Mai Ludaya."
Da sauri ta miƙe, ta fita.
Tana fitowa ta gurfana ta hau rarrafe.
"Ke! Meye haka?"
Taji tambaya daga sama, ba tare da ta ji tahowar mai tambayar ba, da yake kanta na sunkuye a ƙasa.
Ganin Afreen yasa ta magana.
"Sulewa na yi É—azu."
Dariya ya saka, ya ce,
"Sai ki riƙa tafiya kina kula." Ya wuce ya barta.
'Ji mugu! Ba ma sannu zai min ba sai wani in kula! Kulo.'
Ta ci gaba da rarrafawa har ta baro wajen, ta iso babban falo.
Tana zuwa ƙofar wajen ta miƙe, ta shiga.
Wajen da suka ci abinci jiya ta wuce ta tarar an ajiye musu komai na karyawa, sai dai ba kowa a wajen.
Daga zamanta zuwa yanzu ta yi tsaki ya fi a ƙirga.
Ga dai kwanukan abinci, amma ba masu cin.
Ga yunwa, ga takaicin rashin zuwan masu gidan.
Ganin ta ɗau lokaci tana jiransu ba su zo ba, yasa ta fara kokuwa da kula. Duk wani dabara da za ta yi don ya buɗu ta yi, amma ya ƙi buɗewa.
Ganin haka yasa ta haƙura ta koma ta cigaba da zaman jira.
A tare suka fito daga gefen Baffan suna kwasar dariya.
Kallonsu Abulle ta yi, take ta ji wani takaici ya ƙara rufeta.
Ji ta yi kamar ta je ta shaƙesu.
Har suka iso wajen suna dariya.
"Ba ki ci abincin ba?"
Afreen ya tambayeta.
Kallon takaici ta yi mishi,
'Banci ba É—an rainin hankali, da uwar kai kamar Umarun kiyashi.'
A fili kuma ta ce,
"Uhmmm!"
"Me yasa?"
A kufule ta ce,
"Ban iya buÉ—e kwanukan ba."
Buɗe mata ya yi, ya bata faranti ta ɗibi dankali da ƙwan.
'Ikon Allah! Wannan uwar mai ai sai yasa mutum ya yi lisu.'
Jida tayi yanda zai isheta, ya haɗa mata shayi ya miƙo mata da biredi.
Godiya ta yi mishi.
Ta kalli Lubna da tun zamanta a wajen take danne-dannen waya.
'Albasa dai ba tai halin ruwa ba. A haka dai za a ƙare.'
Ledan burodin ta buɗe ta yagoshi, ta dunƙule ta dauko kofin da ya haɗa mata shayin ta danna a ciki.
Hannu ta sa ta kwaso jiƙaƙƙen burodin, ta hangame baki za ta tura, hakan ya yi daidai da sauƙe kofin shayin da Lubna ta yi daga bakinta.
Kamar ance É—aga kanki! Sai ko ta yi ido biyu da kwamacalan Abulle.
Furzo da ruwan shayin ta yi, tana faÉ—in.
"A uzu billahi! Wannan wani irin azanta ne don Allah."
Ta miƙe da shirin barin wajen.
"Sista ba dai kin ƙoshi ba?"
Afreen ya tambayeta.
Juyowa ta yi tana faÉ—in,
"So kake in yi amai ne? Dubi wani gwale fa da yarinyar nan ke yi."
Ta juya ta bar wajen.
Gallamata harara Abulle ta yi.
'Har da wani korar A'uzun ta, irin ga sheÉ—aniyar nan. Idan kin ga dama har yauma ta nannaÉ—e kada ki kuma cin abinci. Har wani Sitta ko sittin ne kai ka ji wajen.'
Ta ci gaba da ba cikinta hakkinshi.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_22_
Afreen ruwan shayi kawai ya haɗa ya sha da wainar ƙai ya miƙe ya bar wajen.
Kallo ta bishi da shi mai cike da mamaki, har yaushe wannan ɗan ruwan shayin zai ɗauki mutum? Ga abinci nan a wadace ba za su sake su ci ba sai a dangwala a tashi. Shi ya sa ko kaɗan ma ba su da wani ƙiba, wannan kyakykyawar iska aka yi zai iya awon gaba da su.
Juyowa ta yi ta ci gaba da cin abincinta, tana mamakin yawan abincin da aka ajiye ba masu ci.
Wannan kam almubazzaranci ne. Wataƙila don ba su san wahalar noma ba ne shi ya sa suke haka.
Tattaro sauran sayyayyen dankali da ƙwan da ya rage akan farantin ta yi, ta haɗe waje guda ta dunƙule ta kai baki, tana tauna daɗi na shigarta.
Bakinta cike, ta ce,
"U'uhum! Garin daÉ—i na nesa, wani ya zo Jinjin bai ga moto ba. Su Inno ana can ana gwagwarmaya da É—umame."
Ta kurɓi ruwan shayin.
Ba ta bar wajen ba, sai da ta tabbatar da cikinta ya gama cika gaba da baya.
Juyi kawai ta ke yi a kujerar falon, tun tana iya zama har ta gaji ta kwanta, gashi kwanciyar ma duk ya isheta.
Wannan wani irin gida ne haka? Ba fita ba aikin komai, duk jikin mutum ya yi ta ciwo. Sai aikin zuba ma kwalba ido kana ganin masu jajayen kunnuwa na ta gwalaɓen magana.