← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na shiga uku! Wannan wani irin hauka ne? Kin gama ƙwaɓa fuskarki wai ke kin yi ado, kuma kina nufin a haka za ki bimu? Gara ma ki koma banɗaki ki je ki wanke fuskar nan wallahi idan ba haka ba sai dai ki zauna." Lubna ta faɗa lokacin da ta fito daga wanka.

Kallo ta yi mata, irin mai nuna amar kin taƙura min ɗin nan, 'Ba ke aka ce ki fita da ni ba, kama albarkacin Hajiya ne ta ce ki shirya ku je gidan barkar haihuwa.'

"Afirij zan bi ai! Ke kuma Hajiya za ki bi."

ÆŠagowa ta yi daga shafa man da ta fara, ta yi mata kallo na sakan biyu, kafin ta ce,

"Owo! Shine baza ki goge fuskar ba kenan? Ki barshi to don Allah, zamu ga wa za ki bi. Mara kunya kawai. Ana magana kina ba mutane amsa."

Cike da haushi ta nufi bayan gidan ta wanke fuskarta. Tana fitowa ta nufi hanyar fita.

"Zo nan."

Lubna ta ce da ita, har ta kara gaba sai kuma ta juyo ta dawo.

Kaya ta miƙo mata ta ce,

"Ki cire na jikinki, ki sa wannan."

Murmushin takaici ta yi, zuciyarta na faÉ—in

'A rashin sani, baƙo ya sha ruwan wanka. Ki bi a hankali, idan na bauɗe sai kin raina kanki Labano, sai kin san Abullen Inno ba baya bane.'

Karɓar kayan ta yi, ta cire nata ta sa. Doguwar riga ne, da ɗan mayafinshi. Ta rasa yadda zata yi da mayafin, don santsi ne da shi, kawai sai ta tattaro ta ɗaure a wuya. Ta yi waje.

****

"Kai! Na aikatu sosai yau, amma na fanshe gumina fa."

Hamisu ya faɗa lokacin da suke zaune a ƙarƙashin biya.

"Gaskiya kam! Nima da na gama zagawa, na je gurin Goshi na ci abinci na jima sosai a wajen kafin ka zo."

"Bari ka gani ÆŠalliti!"

Ya faÉ—a yana ciro kuÉ—in da ke cikin aljihun rigarshi.

"Ka gansu."

Ya nuna mishi É—ari biyar-biyar guda uku.

"Dubu ɗaya da ɗari biyar ya bani, da abinci mai yawa. Ya kuma ce duk bayan kwana biyu in rinƙa zuwa ina zubar da shara da share musu harabar gidan sabida furannin da ke zuba." Ya kare maganar yana kunce wani baƙin leda da ya taho da shi.

"Ga naka abincin, ni na ci na ƙoshi a can."

"Kai mutumina!"
Cewar Ɗalliti, lokacin da yake miƙa ma Hamisu hannu suka tafa, fuskarshi cike da annuri ya ci gaba da faɗin.

"Ka ce dai mun shiga wannan layin a sa a?"
"Ba laifi, mun taki babbar sa a. Ya kasuwar taka?"
"Ba laifi, na ɗan taɓa ciniki."
"Mun gode Allah!"
Janyo ledar abincin ya yi, ya wurga wani ƙaton yankin nama a bakinshi, sannan ya ce,
"Niko Hamisu me zai hana mu kama ɗaki a gidan Malam Bukar, zai fi mana sauƙi da kwanan ƙofar shagunan mutane ko cikin rumfar kasuwa ko? Kaga kullum Da u, cikin kai mana hari suke, sai ka yi nisa cikin barci wani ƙaton ya mirginaka ya kwashe abunda da wuni kana nema."

Ajiyar zuciya Hamisu ya yi, da godiya ga Allah da ya haɗashi da abokin ƙwarai, mai son ci gabanshi. Bai da ƙyashi ko hassada.

"Kuma fa ka kawo shawara mai kyau wallahi. Amma kana ga zamu iya biyan kuÉ—in?"

"In Allah ya yarda zamu iya. Dubu huÉ—u ne fa a wata guda, kasan É—akunan ba wani fasali ne da su ba."

Dariya Hamisu ya yi, ya ce,
"Allah na tuba! Wa ke duba wani fasali ÆŠanliti? In dai asiri ya rufu ai shi ke nan."

"Haka ne kuma."

Ya faÉ—a yana ciro kuÉ—i daga cikin ramin zariyar wandonshi.

"Ga dubu biyu nan, ka kawo na wajenka mu haÉ—a sai ya bimu bashin É—ari biyar ko?"

"Kawo dubu guda a wajenka ka gani."

Ya karɓa, ya haɗa da na aikinshi, ya ciro wata tsohuwar dubu ɗaya a ramin zariyar shi shima ya haɗa.

"Kaga sun cika dubu uku da É—ari biyar, ka adana dubun kaga tafiya ce jibi a gabanka, ba lallai ka sake samun wasu kuÉ—aÉ—en kamar wannan a gobe ba."

"Ikon Allah! To, ai na gama shirye-shiryena, na sai musu omo, sabulu, manshafawa, da farin magi. Burodi kawai dama ya rage in saya."

"To, ka gani ai. Ko mu hakura har ka je ka dawo?"

"A a! Daga yanzu ai duk aikin da ya samu yi za mu yi. Kaga tanan zamu riƙa samun wasu kuɗaɗen."

"Allah ya taimakemu, yanzu ina muka dosa?"

" 'Yan kura za mu, mu yi haya kagani mu ɗebi ruwa mu shigar unguwannin da suke da ƙarancin ruwa ka gani."

"Hhhhhh! 'Yan Garuwa kenan?"

"Ƙwarai!"

Ya faÉ—a yana wanke hannunshi da guntun fiya watan da ya sha.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_27_

Kai tsaye fallo ta dawo ta zauna, zuciyarta sai ƙuna yake yi mata. Walaƙanci na ɗaya daga cikin abinda ta tsana, sai dai ta lura wannan Lubnar mutuwar 'yar walaƙanci ne. Amma, ba komai. Gobe i yanzu ma ta yi nisa da garin.

" 'Yammatan mai ludaya an sha kyau."
Bata ɗago kai ba, murmushi kawai ta yi. Sai dai idan ka dubeta zaka iya hango ɓacin rai maƙale a fuskarta."

"Yaya ba ki yafa mayafin ba, kika tukuikuyeshi a wuya?" Afreen dake tsaye ya sake tambayarta.

"Ƙauyanci mana. Kasan ko yaya baƙauye yake sai ya nuna halin nashi."
Lubna ta faÉ—a lokacin da ta iso falon tana É—aura É—ankwali.

Kallon takaici bita da shi. Yanzu kam ta gama gano tsanarta ce ƙarara a fuskar Lubna.
"Hummm! Na gode Allah ina da tushe ba a kwararo aka tsintoni ba. Ki sani ko yaya mutum yake daraja ce da shi. Ɗan adam ba abun walaƙantawa bane. Idan ma kin yi haƙuri, gobe iyanzu babu ni a gidan nan."
Harzuƙowa ta yi, ta nufota gadan-gadan tana faɗin,

"Iye! Ashe rashin kunyar naki har ya kai haka ne? Har kin kai ki faÉ—amin magana?" Afreen da ya tare ta ne ya ce,
"Haba Anti Lubna! Abin da kike yi mata bai dace ba wallahi."

Kallonshi ta yi rai ɓace ta ce,
"To, mara kunya! Sai ka koyamin abin da ya dace." Tana kaiwa nan ta ja tsaki kan kujera ta zauna.

Ya juya da niyyar yi ma Abulle magana yaga bata nan. Da sauri ya nufi É—akin Lubna.

Ji alamar motsin tafiyar mutum yasa ta yi saurin sanya bayan hannunta ta goge hawayen da ya wanke mata fuska.

Shigowa É—akin ya yi, ganin ta canza kaya yasa shi tambayarta.
"Ya naga kin canza kaya kuma mu da zamu fita?" Ba tare da ta É—ago kai ta kalleshi ba ta ce,
"Ku je kawai."
"Me ya sa?
Ya sake tambayarta
"Akwai abin da zan yi ne."
"Ban yarda ba! Abin da Anti Lubna ta yi miki ne ya ɓata miki rai ko? Ki yi haƙuri kada abun ya dameki, rashin fahimtar juna yasa hakan da zarar kun kun fahimci juna komai zai daidaita ki yi..." Bai kai ga ƙarashe maganar ba muryar Lubna ta katseshi tana faɗin,

"Kai! Dallah ka zo, ka bar mutane tsaye a waje suna jiranka ka zo nan ka yi zamanka. Idan ba za ka kai mu ba ka bani makullin."

Tana kaiwa nan ta juya.

"Ki yi haƙuri kin ji? ki sako mayafinki ki zo mu tafi. Muna jiranki."
Ya fita.

Yana fita ta yamutsa fuska, ta ce
"Ko maton ubana Ilu ne, ba zuwa zan yi ba. Idan kun gaji da jira sai ku yi gaba."
Jakar kayanta ta janyo ta zazzage kayan ciki duka, ta shiga É—aukarsu da É—ai-É—ai tana sake naÉ—esu, duk da a naÉ—en suke.

"Wallahi Mommy mu tafi, ta sanfa ita muke jira don iskanci ta je ta yi zamanta. Sama da minti goma muna zaman jiranta." Lubna dake zaune a bayan moto kusa da Hajiya ta faÉ—a.

"Fita ki je ki dubota. Meyuwa wani abun ya tsaida ita ko batasan mun fito ba." Cikin yanayin shagwaɓa Lubna ta kalli Hajiyar ta ce, "Mommy!"

Itama kallonta ta yi, fuskarta ba alamar wasa ta ce, "Eh!"
Ganin yanayin Hajiyar yasa ta fita da sauri badon ta so ba. A sonta a aiki Afreen.

Tana zaune a ƙasa, ta jingina bayanta da gado. Ta gama naɗe kayanta ta mayar cikin jaka, hotunan da ta ciro take kallo, wasu da ƙawaye, wasu 'yan uwa, wasu kuma ita da Hamusu. Jin motsin tafiya yasa ta yi saurin turasu ƙasan gadon ta rarumo jakarta tana ƙoƙarin jan zif ɗin ne aka buɗo ƙofar.

Fuskarta ba annuri ta leƙo ta ce,
"Malama ke fa muke jira, kin wani nemi waje kin zauna."
"Ku je, ba zani ba." Ta bata amsa
"Ya fi miki." Ta juya ta fita, ita kuma ta janyo hutunanta ta mayar cikin jaka ta zuge zif ɗin ta ɗauka ta koma ɗakin da tun farko aka yi musu masauƙi ita da Inno.

"Ina Zainab ɗin?" Hajiya ta tambayeta ganin ta shigo tana jan ƙofa zata rufe
Fuskarta a sake ta ce,
"Kanta ke ciwo ashe, na ce ta zo mu tafi, ta ce ba zata iya ba, shine na bata magani ta sha ta kwanta."
"Subhanallah! Ta sha maganin ta kwanta dai ko?"
"Eh!"
"Mu je mu dawo da wuri sai in dubata."
"Gaskiya kam, ta riga ta kwanta kada ki je yanzu ta tashi ciwon kan ya ƙaru."

Hannu ta miƙa daga baya ta zare abin sauraron sautin da Afreen ya toshe kunnuwanshi da shi, ta ce
"Mu je ko?" Ta faÉ—a tana É—aga mishi gira
"Ina Zainab É—in kuma?"
Ya tambaya lokacin da ya juyo.
Harara ta zabga mishi,
"Kanta ke ciwo ta sha magani ta kwanta."
Kai kawai ya gyaÉ—a, don yasan kwanan zancen, sai dai bai É—auka yarinyar na da zuciya har haka ba.
Zama ya gyara, sannan ya ja suka tafi.

*Ummyn Yusrah*

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_
Chapter 13 · 0% Book details