← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 15

Sashe 4

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inno! Shima fa cin nan lafiya ne aradu, idan mutum ba ya lafiya ina ya ga wani bakin cikin abinci, Allah duk randa aka kai ni gidan da ba abinci kullum gida zan riƙa turo da ƙwarya ta ana yi mun zubi, gara ma tun da wuri kada ku cire ƙwaryata ku barni a layi." Tana maganar ne tana lashe hannunta da ta gama damalmale shi da miya, tana gamawa ta kuma rarumo kwanon tuwon ta hau suɗewa.

Inno ta ce, "Wannan ai an yi, ba a yi ba kenan. An sai da akuya, ta dawo kuma tana ci mana danga."
Ba ta kula ta ba sai ma ci gaba da ta yi da suɗe kwanon, wanda baya buƙatar wani ruwa da omo wajen wanke shi, domin yawun Abullen ya wanke shi tas.

"Ko da yake shi gwanin naki ma Hamusu rago ne, tunda tun zamanin ƙuruciya da aka bashi gwaji a kan kaza ya gaza riƙe ta, duk da yake ita ɗin dabba ce, ina kuma ga an bashi ɗan mutum?"

"Taɓ! To ni me ruwana da wani Hamusu kuma? Can, su ƙarata da Indo ƴar gidan mai unguwa ni na wuce ajinsa"

"Iyee! Zamani. Kukam dai yaran yau sai dai abarku, kina gabana ko kunya ba ki ji."

"Yo, to Inno naga dai zancen nan ke ki ka fara yowa ita, ni ko na É—ora."

"Uhmmm! Haka ne."

"Inno shi kiwon kazar kuma ta me cece ne da na ji kin ce an ba shi Hamusun ya kasa riƙon ta?"

Kallon ta ta yi, kafin ta ce,  "Ita wannan kazar da ki ka ga ana ba duk wani ɗa namiji da ke wannan ƙauyen kiwo, ana bashi ne don gwajin yadda zai iya riƙe iyali. Idan aka ga yana kula da ita wannan kazar sosai, to a hankali za a bashi tunkiya, kinsan ita tunkiya uwar tamɓele ce, idan nan ma aka ga ba laifi, sai a yi mishi canji zuwa rago, da haka dai har zuwa kan saniya, idan aka ga ya iya kiwo to anan ne za a bashi mata. Idan kuma shiririta ya sa a gaba to sai dai a wurgashi gona kuma ya yi ta fama."

Baki ta saki tana jin jawabin Inno har ta dire, ita ma ta jefo mata tambaya da faɗin, " Kuma Inno shi wannan gwagwarmayar duk mutum ɗin na ƙarami ne zai yi shi? Kuma dama ba su noma ne sai sun gaza riƙon dabba?"

Ummyn yusrah
[9/13, 4:57 PM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

*9*

"Suna yi mana, idan yaro ya kai munzali kuma sai a yi mishi auren ladan noma." Cewar Inno.
Keɓe baki Abullen ta yi ta ce,
"Hu'umm! Sun ji daÉ—insu."

Shigowa gidan ya yi, ba ko sallama sai ma bambamin faÉ—a da ya ke ta yi har ya iso inda suke zaune, ya ja ya tsaya.
Bayan shi ya yi ma masauƙi da garun ginin jar ƙasar da ke bayan shi, yana huci da huro iska daga cikin bakin shi, ya harɗe hannayeshi bisa ƙirjinshi yayin da ya ɗago ƙafarshi ɗaya ya dogare ta jikin garun, ɗayar kuma tana ajiye a ƙasa.

"Barka da shigowa Malam! Yanzu na ke neman Muntari ya kai muku abincinku waje, baya nan, ina ga ya fita dandali wasa ne."

Tsaki ya ja, ya ce, "Wa ke batun abinci kuma."
   "To, mai kuma ya faru? Na ji ka shigo kana ta bambamin faɗa."
   "Sarkin fada ne ya bi duk ya matsamin da zancen auren nan wallahi, ba dama ya ganni, duk  ya bi ya hanani sukuni."
  Jin an ambaci Sarkin fada yasa Abulle ta zaburo tana faɗin,  "Walle ɗazu ma ya aikoni, wai ko yana maka tuni ko me na dai manta."

Inno ta galla mata harara, "Ina kuka haÉ—u da shi? Ko binshi fadar ki ka yi?"
Zaro ido ta yi alamar tsoro, "Walle Inno a hanya muka haÉ—u, da na je sayo rama a kasuwa ina dawowa."

"To, dama da kin ganshi kafin ya hangoki, ki maza ki sake hanya, kin ji na faÉ—a miki."
   "Inno!"
      "Innon gidanku." Ta yi mata daƙuwa da yatsunta biyar.

"To, Malam yanzu meye abun yi?"
Ƙarasowa ya yi, ya zauna a gefen tabarmar da Abullen ke zaune.
  Da sauri ta tashi ta koma ƙasa ta zauna.

"Ni kaina na rasa ta cewa, da ina tunanin in ce mata cikin manemanta ta fidda gwani kawai, idan na je sai in sanar musu tana da gwaninta dama a hannu."
  Cewar Ilun mahaifin Abulle.

"Hakan ma ya yi, ke cikin maneman naki waye gwaninki?" Ta jefa ma Abulle tambayar.

    "Ni... Ni... Ba kowa."

"Ba kowa ki kace?"
    "Ba kowa Inno."
          "Umm! To kaji Malam. Da alama rabon mai unguwar ne."

"Ke Inno! Hauka nake zan É—au Abulle in ba sa ar kakana?"
     "To Malam, idan rabon shi ce fa?"
           "Bama rabon shi ba ne."
      "U um fa Malam! Kasan fa rabo ajali ne, ba mu san me Allah ke nufi kan hakan ba. Idan dai ita Abullen tana so ai shikennan."

Jinjina kai ya yi, kafin ya ce,  "Kuma fa kin kashen jiki, kince Allah a lamarin dole in saduda tunda ita ɗin ma bata da wani tsayayye."

"Ke Abulle! Mai Unguwa ne ya turo Sarkin fada cewar yana son aurenki, me kika ce?"

Sai yanzu ta gane kan wa suke zancen su, domin da duk a baibai take fuskantar zancen nasu.

'Wai yau ni Mai Unguwa ke son aure? Lallai ina da sa a.'
    Zancen zuciyarta kenan, kafin ta sake dulmuya wata duniyar tunanin.

Hangota ta yi a gidan Mai Unguwa, an dire mata wani ƙaton kwanon kaya shaƙe da dafaffiyar shinkafa 'yar gwamnati mai santsi da miyar ja, ga kuma ƙatuwar kaza a kai, gefe kuma ga babban kwanon sha cike da sassanyar ruwan ranar ƙasa.
 
Sake kallon ƙeta ta yi ma hinkahwar a karo na ba adadi, tana kuma tuna irin cin walaƙancin da  za ta yi mishi.
  Sake ware ɗaurin zaninta ta yi don yayi sako-sako gudun kada cikin nata ya yi saurin cika, ta kalmashe ƙafafunta waje guda, ta zura hannunta ciki ta gauraya gefe guda, ta ciko hannunta ta kai shi zuwa bakinta.

"Kingani ko Inno! Na gaya miki yarinyar nan ba son auren nan za ta yi ba, gashi ko amsa bata bamu ba."

Maganar da mahaifinta ya yi, shi ya hanata jin ɗanɗanon hinkahwar da ta shaƙe hannunta da shi, maganar ce kuma ta yi silar dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.
  Ta ji takaicin rashin ɗanɗana girkin, sai dai duk ranar da Allah ya kai damo ga harawa ba ƙaramin ɓarna za ta tafka ba, cin huce haushi za ta yi mishi.

Murmushi ta yi, wanda sautinshi ya fito,  "Kin gani ko Inno? Kuka fa ta ke yi, gara a janye maganar nan idan yaso a jira har ta samu gwani."
  Cewar Malam Ilu.

Salallami Inno ta sanya tare da tafa hannayenta, ta iza ɗaya a haɓarta ɗayan kuma ta ɗago fitilar dake ajiye ta haska fuskar Abullen da shi.
   Kallo suka bita da shi, fuskokinsu fal mamaki.

Madadin suga hawaye ya wanke fuskarta, murmushi ne ke ta bayyana a fuskarta, idanunta kuma a rufe.

"Ke Abulle! Lafiyar ki kuwa?"
Inno ta tambayeta.
Da sauri ta buÉ—e idon ta sunkuyar da kai alamar kunya ganin yadda iyayen nata suka tsatstsareta da ido.
A guje ta bar wajen ta nufi É—akin kwananta, zuciyarta cike da farin cikin nesa ta kusan zuwa kusa.

"Shikennan ai Malam, abu ya zo gidan sauƙi, alamu sun nuna ta yi na am da zancen. Sai ka yi maza ka sanar da su kai ma ka sami lafiya."
  "Ai kamar yanzu ma kuwa ba sai an kai gobe ba."
  "Sai kuma mu toshe kunnuwanmu, don za mu sha surutu gurin jama ar garin nan."
  "Yo Inno! Idan sun yi ma ai za su bari, da yardar yarinya ai aka yi, ba dole aka yi mata ba."
  "Haka ne kam."

Ya miƙe yana faɗin, "Barin je in sanar ma Sarkin fadan."
   "To, a dawo lafiya."

Tunda aka sanar ma Sarkin fada bai yi wata-wata ba, a daren ya isar ma Mai Unguwa.
   Washegari Mai Unguwa ya turo wakilanshi neman auren Abulle, da sadakinta dubu ɗari. Take aka  sallama musu aka kuma sanya musu mako biyu mai zuwa aure.

Kafin kyaftu da Bismillah, zance ya karaɗe illahirin unguwar su Abulle, ya karaɗe garin mai ludaya da ƙauyukan dake maƙwaftaka da su.

  Tsegumi ne kawai ke yawo ta ko ina, ga uwar Indo ma ta ɗaga hankali a gidan Mai Unguwa.

"Kai  dai ba ka taɓa rabo da abun kunya, ka rasa wacce za ka aura sai ɗiyar cikinka. Allah wadai wallahi, girma dai ya faɗi."
Cewar Tabawa.

Kallo Mai Unguwa ya bita da shi, kafin ya ce  "Abun kunya? Ai mu gaba muka bashi ba baya ba, in dai ta nan hanyar ne. Yaya ina ƙoƙarin raya sunnar Ma aiki Rasulullahi, kuma ki ke neman jifata da wasu kalaman da basu dace ba?"

Harara ta zabga mishi,
"Wani raya sunnar? Ka rasa lokacin da zaka rayar sai da duk furfura ta gama baibaye ka, mutuwa  yau ko gobe, amma ka ke wani ƙiran raya sunna."
Chapter 4 · 0% Book details