← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 15

Sashe 5

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai Tabawa! Ni da ke ba wanda ya san gawan fari, har yau ba za ki rage kishi ba. Yarinyar nan dai naga ƙarama ce, ba ruwanta, bata san komai ba. Don Allah ki sassauta kishin nan naki a kanta, kinga Lami kam ko a jikinta, bata wani nuna damuwar ta ba."
Gyara zama ta yi ta ce,  "Lami daban Tabawa daban. Yo ita dama ɗaga hankalin me za ta yi? Taga jiya taga yau, abu tun zamanin ƙuruciya kuke tare, tun auren saurayi da budurwa, ta riga ta ci lokacinta ai, tunda ko ni nan ma ta haifeni few da aniya, balle kuma wata can wai ita Abuwa. Har ka ke wani ƙirinta da yarinya, ƙarshen yarinta inga Inno ta sanya majanyi ta goyata a baya, ta kuma ɗauki bulumboti ta liƙa mata a baki sai in yarda."

Ganin da gaske take, zancen nata ba na ƙare ba, yasa ya miƙe yana gyara zaman rawaninshi ya saiti hanyar fita yana faɗin,
"Ni dai na faɗa miki, ki sa ma ranki salama ki yi fatan a zauna lafiya kawai don kin san bani son fitina a gidana."  Yana kaiwa nan yasa kai ya fice.

Tana huci tana faÉ—in,
"Za ma ka dawo ne ka samen, da rawani kamar an naÉ—a gammo."

Yana fita Indo ta faÉ—o É—akin kamar wacce aka hankaÉ—o.

Gallamata harara Tabawa ta yi tana faÉ—in, "Ba ki iya tafiya a hankali ba ko? Kin wani faÉ—omin É—aki kamar wacce kare ya biyo."
"Yi haƙuri Tabawa! Mutane ne suka ishen a gari, wai me yasa za a bar Baba ya auri waccar yarinyar? Wasu sunce don yana mai unguwa ne ya sa zai yi musu fin ƙarfi, wasu suce sayen ta yi yi, wasu ma cewa suke wa..."

Tsawa ta daka mata, "Koma me suka ce, ba ke kike jajiɓo ta ba? Inda ba ki talla mishi ita ba ina zai ganta? Na ji kuma ance saurayinta da suka daɗe tare ya yi ƙaura ya dawo wajenki, kinga da ta tashi huce haushin ta sai ta huce kan mahaifinki. Kinga nan da kwanaki goma ta zama kihiyar uwarki kenan. Sai ki shirya tarbar sabuwar uwa."
Ranta ɓace ta ce, "Allah ya satura! Ko rabin-rabin uwata ba ta kai ba, na san kuma kwaɗayin hinkahwa ne zai kawo ta Yasin za ta ga walaƙanci."

Masifa ta rufeta da shi har bakin da ya gama rinewa da goro yana fidda kumfa, inda ana bada aron baki, da ba abun da zai hana Tabawa ta yo aro yau.

Haushin kaza kenan.

Ummyn Yusrah
[9/22, 3:52 PM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
       *(HWA)*

_UMMYN YUSRAH_

_A ƙara haƙuri dai._

_10_

"Yi maza ki je gidan Goshi ta baki daddawar nan, kafin ki dawo na gama daka kukar sai a haɗa musu waje guda ki tafi, kinga rana na tafiya, kada dare ya riskeku, ga hanyar ba kyau ne da ita ba."  Cewar Inno da take ta tiƙar busheshshen ganyen kukan da ta zuba a turmi, babban burin ta ta mai dashi gari.

"To Inno!"
Ta fice daga gidan ta nufi gidan Goshi mai Daddawa.

"Abulle! Abulle!! Abulle!!!"

Tun daga nesa yake ta ƙwala mata ƙira, sosai ta jishi ta ƙi juyawa  Ganin ƙiran nashi ba na ƙare ba ne, yasa ta juyo a fusace tana hararar shi.

"Wai lafiya kake yi min irin wannan ƙira kamar wani tsohon makaho ko wacce ta sace maka ɗan taure?"

Ƙarasowa ya yi yana dariya ya ce,
"Yo Abulle don na ƙwala miƙi ƙira haka ai ba laifi ba ne, tun ranar nake so mu haɗu mu tattauna amma kin ƙi kulani."

Kallonshi take mai haÉ—e da harara,
"Kam me zan saurareka? Cemaka aka yi ina da lokacinka? Ka dai san ni ba sa arka ba ce ko?"

Cike da mamaki ya hangame baki kamar wani gaɓo yana kallonta kafin ya ce,
"Nine fa"
Ta yatsina fuska tana faÉ—in"Kaine wa?"

"Hamusu rabun ran Abulle."
Ya ƙarashe maganar cikin yanayin shauƙin so, har yana wani jijjiga jiki irin na jin daɗin nan.

"Hamusun Indo dai! Ai ni yanzu na wuci saninka."

"Ni É—in?"

"Kai É—in fa."

Ta juya ta fara tafiya, ko mai ta tuno sai kuma ta juyo ta yi mishi kallon sama da ƙasa.

"A je a bi wani sarkin, ba da ni ba, auren talaka."

Ta juya ta yi gaba.

"Dakata! Kada ki yi ƙoƙarin jifana da duwatsu, ina mai shawartarki da ki adanasu ki gina gida da su domin nasan duk daren daɗewa zai yi miki amfani. Sannan kada ki yi kuskuren ƙonani da wuta domin da shi muke kunna fitilun da ke haskaka duk wani gida da ke faɗin kyauyen nan. Duk ranar da ki ka kuskura ki ka yi wannan gangancin ina mai tabbatar miki da cewar za ki dawwama cikin duhu."

Yana kaiwa nan ya juya cikin ɓacin rai,
"Matsalar ka ce wannan kuma, mayaudari kawai."
Ta ja dogon tsaki ta wuce aikanta.

"Kinsan da tafiya a gabanki amma ki ka sami waje ki ka zauna ko Abulle?"

"Inno da na same ta a gida ai ba zan zauna ba, hegiyar yawo ne da Goshin nan kamar wacce ta ci ƙafar kare."

"Ni tafi ki je ki shirya, shegen iyayin tsiya, kin san hanyar Mai Rangwangwan ba kyau ne da shi ba. Idan ku ka yi dare ku kuka sani, don ma mai babur ɗin ɗan garin ne da ya sauƙeki gida zai wuce da sai dai ki zauna sai gobe kuma."

"Inno to a bari mana gobon na tafi."

"Ungo nan."

Ta watso mata yatsun hannunta biyar.
  "An ƙi a barwa goben. Dududu bikin saura kwana goma ne, idan kin je gidan Kawun naku Talle ki ka dawo Jinjin za mu tafi can gidan Kawun ku na burni, nan ma ki kwana biyu ki zo ki bi gidajen dangi na kurkusa suma ki musu sallama."

Murna ne ya rufeta da ta ji batun tafiya Jinjin, itama za ta je burni ta ga yadda yake.

Ruwa ta dauka a bokiti ta je ta watsa, tana fitowa ta sa kaya, yau ba batun kwalliya, kayanta kulle a cikin ɗankwali, sai wani ƙaramin buhu da aka sa mata dankalin hausa, kuka da daddawa.

Sallama ta yi ma Inno, bayan ta gargaÉ—eta ta kuma ja mata kunnen ta kula ta kuma dawo akan lokaci.

Muntari ya É—aukar mata buhun kukan, suka nufi tasha wajen mai mashin É—in da aka jima da yi mishi magana.

Tana isa ba ɓata lokaci ya suri Abulle da wata mata suka ɗau hanya.

Gam Abulle ta riƙe ƙarfen jikin mashin ɗin, domin idan ba haka ba a yadda suke cafke a kan hanyar nan za a iya tsintota a ƙasa idan aka daka wani tsallen.

Taimakon ta É—aya a tsakiya take, ba don haka ba, abun ba dama ne.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

     *HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_11_

Kwananta biyu a Mai Rangwangwan ta dawo, cike da ɗoki da murnar zuwa birni.  Har gida ta je ta sanar ma Sarai itama za ta birni gidan Baffanta Jafaru don haka gara a daina yi musu yanga, don ba a fi su tsumma ba, balle a baɗa musu ƙwarƙwata.

Kwananta É—aya a Mai ludaya washe gari suka É—au haramar barin gari zuwa babban birnin Jinjin.

Tsarabar 'yan Maraya daban da ta ƙauye, domin su ba daddawa ba kuka.
Kabeji ce da kayan miya, sai kuma manyan kaji guda biyu.

"Inno! Su mutanen Jinjin É—in ba su cin kuka da daddawa ne? Naga nasu tsarabar daban da ta Mai Rangwangwan."
Abulle ta tambayi Inno, ganin yadda aka bambanta tsarabarsu

"Ke, tuwon girma ai miyarsa nama. Su can me za su yi da wani kuka da daddawa? Tuwon ma ai sai su shafe mako huÉ—u ma ko fiye da hakan ba su yi shi ba."

Cikin mamaki da sakin baki ta ce,
"To Inno me suke ci kuma?"

"Ohho! Idan mun je kya gani."

Tsuke bakinta ta yi har suka tattari shirginsu suka É—au wanya.

Kalle-kalle kam Abulle ta yi shi, mussaman ma da suka fara shigowa cikin birnin, ga kwalta shimfiɗe kamar tabarma, ƙarafunan wutar layi a tsaye kan hanya, jere reras kamar an dasa bishiyoyi.

"Ikon Allah! Kayan burni daban da na ƙauye."
Abulle ta faÉ—a a bayyane.

Kallo wasu daga cikin mutanen cikin motan suka bita da shi, don daga dukkan alamu ita É—in sabon shiga ce a zuwa Maraya.

Amai ko ta yi shi yafi sau biyar, tun tana wanke jikinta da shi har aka bata tallafin leda.

Har cikin tasha aka sauƙesu, anan ne fa taga tarin jama a, sai kaiwa da komowa a ke yi, kowa na sabgar gabanshi. Abulle kam banda kallo ba abun da ta sa a gaba.

Idan Inno ta yi gaba, sai ta sake dawowa baya ta jawo hannun Abulle idan ta ga wani abun. Wani lokacin ma tuntuɓe take yi ko ta yi karo da wani abun tsabar kallo. Haka dai har suka tsare adaidaita zuwa unguwar su Baffa Jafarun.

Nan ma dai mamakin ne cike da Abulle ganin mashin mai ƙafa uku, ga kuma gidaje harda masu hawa-hawa.
Wani akan wani.

'Ikon Allah! Na zaune bai ga gari ba.'

Zancen da Abulle ta yi a zuciyarta kenan.

Tafiya dai-tafiya dai, har suka iso inda za su, suka biya mai adaidaita, ya ƙara wuta.

Buga get ɗin ƙofar gidan suka yi, da sauri mai gadin ya zo ya buɗe musu ƙofar. Ganin Inno da ya yi ne yasa shi wangale baki yana faɗin,
"Maraba lale da mutanen Mai ludaya. Yau kune a garin namu?"

"Maraba dai ÆŠayyabu! Gamu kamar an jefomu."

"Sannunku, ku shiga mana."

Ya faÉ—a yana É—aukar wasu daga cikin kayan da suka zo da shi ya yi gaba.

"Inno kin san shi ne?"

"Farin sani ma kuwa, a Mai ludaya yake shima, É—an gidan Malam Datta mai katako."

"Au! Na É—auka ai tsabar zuwan da kike ne ya sanki."

"Yo ni yaushe ma nake zuwa? Rabon da garin nan tun ina goyon Muntari da muka zo yi ma Baffanku barka da dawowa daga Makka."
Chapter 5 · 0% Book details