← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka ƙarasa har cikin gidan Inno na yi mata bayani, ita kam inda za a shaƙeta ma ba ta san ɓaɓatun da Inno take yi ba, don gaba ɗaya hankalinta ya tafi ga kallon tsari da haɗuwar da gidan ya yi.

Zuciyarta ke yi mata tambayar,
'Wai dama suna da dangi masu kuɗi kuma 'yan burni shine ba su taɓa zuwa ba?'

Ita dai a saninta da wayonta sau biyu ma ta taɓa ganin Baffan nata a ƙauyensu, sai dai Babanta ya zo ko kuma ya yi musu aike daga nan.

Suna ƙoƙarin shiga falon, Ɗayyabu kuma na fitowa. Ya ce,
"Inno wannan kamar Abuwa?"

"Ita ce."
"Ikon Allah! Girma dai ba wuya, ta girma abunta."
Ya faɗa yana riƙe haɓa.
"Girma kam ai ba wuya ÆŠayyabu, musamman ma na 'ya mace. Yanzu ma sallamar Baffanni take zata gidan aure."
"Ikon Allah! Ashe dai zamu Mai ludaya kwanan nan."

Ya wuce yane 'yan zantuttuka, su kuma suka shiga.

Sanyi da ƙamhi ne ya ziyarci sassan jikinsu da hancinsu.

Abu guda ne ya faɗo ma Abulle, tunowa da ta yi da ɗakin Inno mai tsamin ƙuli.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_12_

Tunowa da tayi da ɗakin Inno mai ɗankaren tsamin ƙuli da wasu tarkace.

Da sallama suka ƙarasa cikin falon, Hajiya da yaranta biyu suna zaune kan kujera suna kallo.

Da fara a Hajiya Sabuwa ke yi musu Maraba da zuwa, a ƙasa ƙaramar kafet ɗin da aka ɗaura kan tayis ɗin falon suka zube. Inno na amsa maraban da take yi musu yayin da imanin Abulle ya gama tafiya ga kallon kayan alantun da ke falon.

'Yan gaishe-gaishe suka yi, nan Hajiya Sabuwa ta shiga tambayar jama ar gida.

Dungurin Abulle ta yi tana faÉ—in,
"Kekam mene ne haka? Saki iya gaisuwa ba ne?"

A firgice ta dawo hayyacinta, tana faÉ—in,
"Ina kwana?"

"Ita kika gani ma, ai ga manyan masu hankalin da suka fita ma basu iya gaisuwar ba balle kuma ita."

Kallon su Inno suka yi suna mai daÉ—in,
"Sannunku da zuwa. Kun zo lafiya?"

Daga nan basu kuma ɗorawa ba, suka cigaba da abun da suke yi. Don su a zatonsu irin baƙi masu zuwa neman aikin nanne ne suka zo.

"Ke Lubna! Tafi ki kawo ma baƙi ruwa, Kai kuma Afreen ka ɗauko musu lemo."

Kowa ya tafi É—auko abun da aka aike shi.

'Lubina! Ji wani suna kamar na makarai don Allah, ga wani ma wai a firij. Idan kana raye a duniya dai kaga abu.'

Zancen zucin Abulle.

"Inno ina fatan dai anan za a bar min É—iyata ta kwana biyu ko?"
Hajiya Sabuwa ta tambaya.

"Hajiya ai itace silar zuwan tawa ma, nan zan barta ta kwana biyu, ni yau zan koma. Bikinta ya zo saura mako guda tazo yi muku sallama."

"Amma ko kin kyauta wallahi, dama ba ta taɓa zuwa nan ba."

"Hajiya, kuma ai ba zuwan kuke yi ba, ko yaran nan ma ku ɗan riƙa kai su suga dangi abun ya gagara, tayaya za su yi zumunci a tsakansu?"

"Wallahi ni kaina ina son su je, sai dai makaranta ba su da lokaci, ga kuma halin Alhaji bayaso su matsa ko ina."

"Makaranta ko ai ba zai hana su zumunci ba, naga ai suna ɗan samun hutu, ko mako guda suka je suka yi ai za su ga danginsu. Alhaji kam kada a yi mishi sharri, don kin san halin mazan namu idan ba ke mace kin sasu a hanya ba ba yadda za a yi su ce miki jeki, ke mace ke ya kamata ki riƙa yi masa nuni da hakan tunda ki ga shi ba mazauni ba ne."

"Haka ne kam wallahi, don idan ka biye tasu zumuncin ma ba za a yi shi ba."

"A to, gara dai a riƙa ƙoƙartawa. Kada wataran a haɗu a hanya ba a san juna ba."

Dariya suka sa.

"Inno ai ba za a yi haka ba ma, ga biki ya zo, sati za muyi a Mai ludaya da yaddar Allah."

"Allah ya yaddar mana."

"Amin dan na biyur Rahmanti."

Ruwan gora mai sanyi aka kawo musu da kofi, ga kuma lemon kwalba, guda biyu mai ja da baƙi.

"Ke Lubna zo ki zuba musu mana kin ja kin zauna, wannan ƙanwarki ce Zainab 'yar gidan Baffanku Ilu da mahaifiyarta."

Hajiya ta ke gabatar ma yaran nata da su Abuwa.

Kallo yarinyar ta bisu da shi, tana mai taɓe baki, na ganin yadda suke a jigace kuma wai ace danginsu, danginma na kut da kut! Ƙanin mahaifinta."

Ruwan ta zuba musu a kofi, lemon kuma ta buÉ—e musu murafen ta koma ta zauna.

Tunda aka dire musu, Abulle ke Allah-Allah lemon kwalbar nan ya ziyarci bakinta ya gangara maƙoshinta har ya zuwa tumbinta, don tana ganin mutane ranar kasuwan garinsu suna sha da burodi ko da bisko ko fanke.

Ana buɗewa kuwa ta kai ma baƙin nan sura, kai kawai ta kafa ta fara kwanƙwaɗa.

Zirrrr! Shine sautin da ta ji a kan harshenta, da sauri ta cire a bakin nata, sai da ta É—an tsaya kafin ta kuma kwankwaÉ—a, ai ke ta cire a bakinta.

Wani gyatsane ya taho mai haÉ—e da iska, gaba É—aya ta yamutse fuska tamkar tsohuwar da ta shekara dari a duniya.

Idanunta ya ciko da ƙwalla, azabar gas ya ratsa har cikin ƙwaƙwalwar kanta.

"Wayyo Allah na shiga uku! Inno kaina, hancina."

Shine abunda Abulle ke faÉ—i.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

  *HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
                      *(HWA)*

       _Ummyn Yusrah_

_13_

"Sannu Zainab! Ai coke gas ce da ita, ba a yi mata shan garaje."
Faɗin Hajiya Sabuwa, lokacin da ta taso tana riƙe Abuwar.

Sauran yaran kuwa dariya suke ta zabga mata, Inno dake gefe sai jero mata sannu take.

Wani sabon gyatsa ta sake yi mai tafe da hawaye, ta ce,
"Yau naga bone! Inno wannan ko ba itace giyar nan da ake faÉ—a ba kuwa?"

Gaba ɗaya suka sake sa dariya, idan ka ɗauke Inno daga cikin masu dariyar, don ita ta taɓa shan jar sau biyu a rayuwarta.

"Ke wa ya faÉ—amiki wannan ne giyar? Tataccen lemo ne aka haÉ—a shi da wasu sinadaran."
Lubna ta bata amsa.

"Taɓ! To nikam ba zan kuma sha ba alƙur an. Wannan abun sai ta iya yin ajalin mutum. Fuuuuuu! Fa na ji ta hauro min aka."

Duk suka sake sanya dariya.

"Inno amma dai za ki yi sallar azahar ki ci abinci kafin ki tafi ko?"

"Eh, kinsan motar garin namu ƙarfe biyu take tashi, kafin na yi sallan sai in wuce."

"To, Allah ya kai mu."

"Amin."

Nan suka ci gaba da hirarsu, Afrin, Lubna da Abulle kuwa duk imanimsu na ga tibi.

Ƙiran sallar azahar yasa duk suka watse daga falon, ɗakin sauƙar baƙi aka kai su Inno.

Nan suka yi sallah, Abulle ko addu ar kirki babu ta miƙe ta nufi falon, don dama bata so aka dagata kan kallon ba.

Ba kowa a falon, sai ƙaton tibin da ke ta faman aiki. Zama ta yi, ta kuma baza idanunta, kan kwalbar. Tashar turawa take kallo, wani tsamurarren bature sai zabga surutu yake, ita dai ba ji take ba nata ido.

A hankali-a hankali taga yana ta tahowa yana kuma nuni da hannunshi tamkar mai nunata.

Ganin yana shirin faso kwalbar ya fito ne yasa Abulle fasa wani uban ƙara. A kiɗime ta zabura, duk ta gigice ta rasa ina ta dosa? Ta ma rasa inda za ta gudu ta tsira kafin aljanin tibin ya gama fitowa ya risketa.

Shiko gadan-gadan yake ƙara matsowa, a waige-waigen da take na neman yanyar tsira ne ta hango hanyar da zai sadata da ɗakunan gida.

A guje ta É—iba, yayin da mutanen gidan suma suka fito a guje don ganin ihun me take yi?

Karo suka yi da Hajiya, take ta sake sake ihu ta hau roƙo da magiya gami da bada haƙuri.

"Ke wai lafiyarki ne?"
Hajiyar ta tambayeta, karkarwa ta shiga yi tana magiyar kada ya cutar da ita tasan shi namiji ne ya koma muryar mata, ta tuba ya mata rai, yau ma zata bar gidan ta fasa yin kwana biyun.

Cike da mamaki Hajiya ta ce,

"Abin Allah! Budurwa da ciki; Gwauro da yaye. Inno 'yar taki na tare da ƙwanƙwamai ne?"

Ihu ta sake kurmawa tana faÉ—in,
"Don Allah kada ku cutar da Inno! Tare za mu tattara duk mu tafi. Mun tuba ku yi mana rai, har abada ba zamu kuma Jinjin ba."

Duk suka yi tsuru-tsuru suna kallon ikon Allah.

"Ina fa wani ƙwanƙwamai! Rashin kunya ne kawai, mace ta auri mace."

"Na shiga uku! Muryar Innon ma É—aukewa ku ka yi." Ta sake zabura.

Janyota Inno ta yi tana faÉ—in,
"Wai wani iya shege ne haka ƙauri da kare? Mu ne zaki mayar aljannu? Zaki buɗe idanuwan ko sai na kwakwkwaɗa miki mari?"

Da sauri ta ware idanunta, taga jama an gidan duk tsaye suna kallon ikon Allah.

Juyawa ta yi ta kuma kallon tibin, sai taga wasu masu jajayen kunnuwane ke ta tiƙar rawa.

'Ikon Allah! Wai na kwance ya faÉ—i. Ko ina ma mutumin ya nufa ne ohho.'
Ta tamabiyi zuciyarta.

"Tambayar ki ake, me ya faru kike kurma mana ihu a cikin gida?"
In ji Inno.

"Wani mutumi na gani yana ta ƙoƙarin fitowa a cikin kwalbar can, yana ta zuwa inda nake."

Duk suka sa dariyar ƙauyancin Abulle.

"Kedai akwai shashanci, tayaya mutum zai fito daga cikin tibi har yakamaki? Sai kace wani almara? Allah ya shiryeki. Inno muje ku ci abinci kada ki rasa moto tunda kinƙi kwana, kuma kince ba za ki jira Alhajin ba."

"Gaskiya kam!"

Duk suka nufi wajen da aka tanadar musu abincin.

'Ikon Allah! Shima wajen cin abincin har da wajenshi? To ko dai nan ne aljannar duniyar?'

Tana daɗi a zuciyarta tana ƙare ma wajen kallo.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
                       *(HWA)*

        _Ummyn Yusrah_

_Ku yi haƙuri, idona ke ciwo._

_14_
Chapter 6 · 0% Book details