Sashe 12
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lahhhh! Aiko zan jirashi ko zan sam wasu kwalayen."
"Yanzu zai fito kuwa."
Suna tsaye sai ga ÆŠayyabu da saurinshi.
"Abulle! Zo yanzu Alhaji ya dawo sallah yake tambayar ina kike na ce kin fita sai faÉ—a yake, me ya sa na barki ki ka fita."
"Allah sarki Baba Ɗayyabu! Yanzu fa zan dawo. So nake a fito da sharar gidan nan sai in ƙara wasu. Kagama wanda na samu a wancan jujin."
Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe ledar shirgin.
"Taho mu tafi, ki zubar da wannan sharar don ba yarda za a yi ki shiga da shi gida ba."
"Abunfa jeren É—aki ne."
Ta faÉ—a tana zaro ido.
"Mu je, nan ai su basu amfani da shi. Ana gamawa da shi sai bola."
Ya faɗa lokacin da ya tasa ƙeyarta.
"Hu umm! Nikam ina so, zan ajiye a wajenka, gobe idan zan tafi sai in É—au abuna. Har Sarai ma zan É—ibar ma wasu itama ta jera a É—akinta tunda ta kusa aure itama."
"Oh! Mutanenmu akwai son jere. Har yanzu dai ba a barta ba?"
"Tana nan, ku ai nan sai dai ku aje ƙaton kwalba da kujeru muko cika ɗaki ake da jere mai kyau."
"Ci gaba ai aka samu."
Ta taɓe baki
"Amma dai anjima zaka barni na dawo na sake É—iban wasu ko?"
Zaro ido ya yi,
"Rufamin asiri, so kike Alhaji ya sallame ni a aiki."
"A'a."
"To, ki haƙura da wanda kika samu."
Suna shiga ta ɓoye a cikin wani ɗan lungu da ke gefen ɗakin Ɗayyabu, ta nufi cikin gida.
Duk a falo ta samesu zaune kan kujera.
"A'a! ÆŠiyata har kin fara gane gari ne kika fita yawo?"
Alhaji ya faɗa yana miƙo mata hannu.
Zama ta yi a ƙasa can nesa ta ce,
"Gajiya na yi da zaman shine na fita."
"Nan ai ɓata za ki yi, zuwa yamma yayanki zai fita da ke sai kiga gari ko?"
Da murna ta ce,
"To, Baffa!"
"ÆŠan gidan wanene angon ne? Na manta ban tambayi Ilu ba."
Sunkuyar da kainta ƙasa ta yi, ta kamo bakin mayafinta rufe rabin fuskarta sannan ta ɗago fuskar ta buɗe ido ɗaya ta ce,
"Mai Unguwar yankinmu ne."
Ta ƙarashe faɗa cikin jin kunya, ta duƙar da kai.
Dariya suka sanya, Hajiya Sabuwa ta ce,
"Da alama ana ji da maigidan nan! Wannan irin jin kunya haka?"
Ta kaÉ—a kai ba tare da ta sake dagowa ba.
Alhaji ya sake tambayarta.
"Wani yaro ne É—aya daga cikin gidan? Ko cikin jikokin gidan ne?"
Ɗagowa ta yi, fuskarta na nuna alamar rashin jin daɗin tambayar, har da 'yar ƙaramar harararta.
"Mai Unguwa fa nace Baffa!"
Gyara zama ya yi sosai don bai fahimci wani Mai Unguwar take nufi ba.
"Mai Unguwar Yankin mai Ludaya ƙarama kike nufi kokuma yaronshi da ake cema Mai Unguwa?"
KaÉ—a kai ta yi ba tare da ta bashi amsa ba.
"Ban fahimta ba, ki buÉ—e baki ki yi min bayani."
"Baba Mai Unguwa Rabi..."
Bata kai ga karasawa ba, ta miƙe a guje ta yi ɗaki.
Hannu ya shiga tafawa yana salati yana sanar da Ubangiji.
Su kuma yaran sai dariyar Abullen suke yi.
"Alhaji lafiya kake ta jero salati?"
Hajiya Sabuwa ta tambayeshi
"Ina fa lafiya?"
"Me ya faru?"
"Ban taɓa sanin cewar Ilu baya da hankali ba sai yanzu. Kin san wa zai aura ma yarinyar nan kuwa?"
Girgizar kai ta yi, kafin ta amsa
"A'a."
Tsaki ya ja cikin ɓacin rai kafin ya ce,
"Tsoho ne fa da ya kusa ba shekaru É—ari baya."
Kirji ta buga ta ce,
"Mun shiga uku! Shi ko Ilu me ya yi mishi daÉ—i haka da zai É—au 'yar jaririyar 'ya ya ba wannan tsoho?"
"Rashin tunani da rashin hankali mana."
"Gaskiya Alhaji gara tun wuri asan abun yi. Ni kam da haƙura aka yi da auren nan ta yi zamanta anan, a sama mata makaranta."
"Hakan ma za a yi, ba sai sun ga ƙafarta a goben bama."
"A, to. Ai wannan abu da cutarwa. Duka-duka Zainab É—in nawa take da har za a yi mata aure?"
"Kin san mutanenmu ai, yanzu idan kin je can ma za ki samu ana ƙorafin girmanta."
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
   _Ummyn Yusrah_
_25_
"Lallai akwai su da yi ma yaro auren wuri."
  "Ai ba auren wurin ne ma damuwa ba, da ya zaɓa mata tsaranta ai ba damuwa. Amma a ce  ya ɗauki yarinya ya danƙata hannu tsoho ai abun bai yi ba."
  "Kuma fa kaga ita yarinyar kamar tana son shi, ji wani sunne kai da take ta yi ita a dole kunyar nan."
  "Koma menene ita dai ta sani na riga na gama magana."
Ya kalli Afreen ya ce,
"Anjima ka kaita taga gari, kasan su basu saba zama waje É—aya ba, tanan za a É—auke hankalinta."
"To, Daddy! Amma ka faÉ—a ma Labano ta daina kyararta."
Hajiya ta ce,
"Waye kuma Labano?"
Dariya yake yana nuna Lubna da hannu
"Wai Lubnan ce ta dawo Labano? Wannan suna daga ina kuma?"
"Daga wajen Zainab, wannan ai kafin ta saitu sai ansha fama. Daddy wai kai ma haka ka yi ne farkon zuwanka Jinjin?"
Filon dake kan kujera ya É—auka ya jifeshi da shi yana faÉ—in,
"Ka ci gidanku! Kana raina mana 'yan gari ko? Can zan kai ku ku yi wata É—aya ku saba da 'yan uwa."
Afreen har da murnarshi
"Eh, wallahi Daddy ina son zuwa ƙauye."
Labano kuwa yamutsa fuska ta yi, ta turo baki tana faÉ—in
"Daddy har wata É—aya? Ni dai ba za ni ba. Sai dai ko Afirij."
Duk suka sa dariya, Hajiya ta kalli Alhaji
"Ni ko Lubna za a ba Mai Unguwar tunda ta girmi Zainab É—in?"
Kwaɓe fuska ta yi, kamar zata yi kuka, ta ce
"Mommy!"
Sai kuma ta miƙe ta nufi hanyar ɗaki.
Afreen da ke ta kwasar dariya harda kwanciya kan kujera ya ce,
"Labano ta Mai Unguwa! Kuma fa za su dace sosai Mommy."
Juyowa ta yi, ta jefomishi remote É—in tibin da ke hannunta.
"Wayyo Allah matar Mai Unguwa zata yi min illah."
Ya sake ƙular da ita, Daddy ya ce
"Ya isheka, zo abunki 'yar Daddy ba mai yi miki wannan aikin ina raye."
Da gudu ta shige É—aki abunta.
"Sai ki je ki rarrasheta, kin santa ai idan ta kumbura sai an nemi allurar da za a soka mata ta sace."
"Ai Lubna ban san wace irin yarinya ba ce, bata son mutane ko kaɗan ga ta da ƙin 'yan ƙauye, ko don ba ta zuwa ne yasa hakan?"
"Zata daina ne, yanzu duk lokacin da aka yi hutu zan riƙa kai su akai-akai."
"Gaskiya ya kamata kam."
Ta kalli Afreen da tun É—azu ke kwasar dariya ta ce,
"Kai kuma abun na ya samu ko? Ba a taɓa ganin dauriyarka sai ta ɓaci. Tashi ka je ka shirya idan zaku fita ku sauƙeni gidan Suwaiba in dubata da jaririyarta."
Ciki ya shige ya bar su suna ci gaba da tattaunawa.
Sai ƙarfe uku aka gama abincin rana, lokacin duk yunya ya addabi Abulle, tun tana shan ruwa yana riƙe mata ciki har ya dawo da ta sha jimawa sai banɗaki.
****
"Daga É—auko shara ka je ka zauna, wata yarinya ta yi ta jiran zuwanka zai ta tsinci kwalin sabulu ta yi jere baka fito ba."
"Bari kawai Ɗalliti, na yi zaton sharan kaɗan ne ashe da yawa, na yi tunanin in ce ka shigo sai naga gara ka zauna ko za mu sami masu saye kada mu ɓata lokaci a waje ɗaya mu zo kuma bamu sami komai ba."
"Gaskiya! Kuma ka yi farar dabara don ina nan mutane biyu ma sun zo sun saya."
"Kaga ai da yanzu ciniki ya wuceemu, don ma naga layin nan ba ba irin layin masu sayen gauta bane."
"Yo, Hamisu gautar abinci ne da mutane zasu yi ta jidarshi? Ina jibi idan na tafi gida in zan dawo zan nimo wasu 'yan kuÉ—aÉ—en in sake jarraba wani sana ar."
"Allah ya kai mu. Barin kai wannan É—in idan na dawo sai ka shiga kaima ka É—ebo."
"To, ba damuwa."
Ya tura baron zuwa wajen da ake tara shara.
"Na yi tunanin fa kai zaka zaga da gautarnan, ni sai in ƙarasa kwashe sharar kawai."
Hamisu ya faÉ—a ma abokinshi lokacin da ya dawo daga kai shara.
"Allah ko? To inaga kuma za a yi fa! Kada mu taru mu zauna waje É—aya."
Ya faɗa lokacin da ya ɗaura tirenshi a kai, ya miƙo hannunshi Hamisu ya ɗoramishi nashi tiren.
Har ya yi gaba ya juyo ya ce,
"Idan ka gama kawai mu haÉ—u wajen Goshi mai abinci."
"To, ba damuwa."
*Ummyn Yusrah*
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_Ina taya Haziƙan Marubuta murnar kammala littafinsu, mai suna TA FI BAGARUWA IYA JIMA. Zeety, Ummyn Yusra, Beauty Queen. Allah ya kara hazaƙa ya ƙaro kaifin ƙwaƙwalwa._
_Ruƙaiya Haroun (Maman Nour) ina tayaki murnar kammala littafinki mai suna RUƊANIN RAYUWA (Ƙalubalenmu a yau) Allah ya kara hazaƙa da fikra._
_26_
Bayan sun ci abinci, sun yi sallar la asar ne, Abulle ta je ta tsalo wanka. Kwalliya sosai ta yi cikin atamfarta riga da zani da É—ankwali mai kalar koriya da ruwan É—orawa.
Ta shafe fuskarta da fauda, ta ɗauko ƙwalli ta yi ɗigo uku a saman goshinta, biyu a ƙasa ɗaya a sama. Haka ta yi a gefen kumatunta na hagu da dama da kuma ƙasan haɓarta.
Ta sanya jan jambaki a leɓenta ta sa kwalli a cikin idanunta. Sabon silifas ɗinta mai soso ta sa ta sanya hijabinta, sai gata ta fito cas! Kamar ranar sallah.
Ta fi minti goma tana kallon madubi, tana ƙare ma kanta kallo, domin ita kanta ta san yau ta yi kyau! Idan ta juya furkarta gefe ta yi fari da idonta, sai ta sake juyawa ɗaya gefen ta sake fari da idanun. Tana yi kuma tana murmusawa.