Sashe 3
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me ya haÉ—aki da Indo 'yar gidan mai unguwa?"
"Ba komai."
"K'arya ki ke yi, za ki gayamin ko sai na sassab'a miki."
Sake turo baki gaba ta yi tana mai matsawa baya, don tasan abu mai sauk'ine Inno ta sauk'e mata wannan busheshshen hannun nata.
"Da gaske ba komai fa Inno."
"Amma ai an ce kun je fad'a ne."
"Lahhhh! In ji wani munafukin?"
"In ji ni."
"A a!" Tana mai gyad'a kai.
"Ahir d'inki wallahi na kuma jin, ko a ce mun kin je gidan mai unguwa wallahi sai na tara miki gajiya. Æacemun da gani shashasha kawai."
Wuf! Ta mik'e kamar tana jira, ta nufi d'aki zuciyarta fal tunanin me Inno take nufi da har zata hanata zuwa gidan mai unguwa? Kenan sun yi ban kwana da 'yar sati kenan ko kuwa? Taɓ! Da sake wai an ma mai zani ɗaya sata.
Washegari Mai Unguwa da sarkin fada.
Bayan 'yan zaman fadan sun watse ne mai unguwa ya ke tambayar Sarkin fadan.
"Kai! Wai yaya ne zancenmu?"
"Ai yallaɓai wannan fa inaga so yake ya hanamu. Bai wani bani k'wararren amsa ba, cewa ya yi in je zai zo har fadan idan sun zanta da shak'ik'anshi."
Shafe fuskarshi ya yi, tare da tsefe gashin gemunshi da ya gama zamewa fari.
"Ba komai, mu bishi a hankali, kasan 'yar shi ce. Mu da muke nema muke da hak'uri da k'ask'antar da kai. Yanzu dai abun da za a yi ita 'yarinyar zaka yi k'ok'arin shawo mana kanta."
"Yallaɓoi shi da ke k'ark'ashinmu ai shi zai bimu ba mu za mu bishi ba."
"Kai! Wa ya fad'a maka? Ai inda aka san darajar goro, nan ake nema masa ganye. Mu jira dai muji me Baba Ilun zai ce."
Cike da mamaki sarkin fada ya d'ago kanshi, ya kafe 'yan k'ananan idanuwanshi ya sauk'esu kan mai unguwar ya ce, "Am fad'o daga dabino, an fad'a rijiya. Yallaɓoi Ilune fa!"
"Eh, shi dai."Â "Ikon Allah! Wai na kwance ya fad'i."
Cike da mamaki Mai Unguwa ya bishi da kallo yana fad'in, "Wanda ya cika, ai ya mallakeka kai da iyalanka. Tunda naga d'iyar shi ina so ai dole in girmamashi."
Yana karkad'a kai ya ce "Um! Haka ne."
Nan suka ci gaba da zantawa.
Tafe take hannunta rik'e da ganyen rama, ta sayo a kasuwa za ta gida, sai ga Sarkin fada.
Wangale baki ya yi yana fad'in, "A a! Kaga manyan mata, kalan manyan mutane. Ina aka fito kuma?"
Cikin jin kunya ta durk'usa k'asa tana sunkuyar da kai, ta ce "Baba sarki ina wuni?" "Lafiya lau Abulle. Abulle ta mai unguwa."
Kunya ce ta sake kamata jin ya k'irata da Abulle ta Mai Unguwa, tasan tsokanar ta yake kan yadda aka ritsasu a fadar Mai Unguwa.
Mik'ewa ta yi za ta tafi, ya ce "Za a je gida ne?" "Eh." "To, a gaida Malam Ilu kuma ki fad'a mishi ina tuni da sak'onnan." "To." Kawai ta ce ta yi gaba.
_Ummyn Yusrah_
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕ðŸ»: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HWA*
_Ummyn Yusrah_
_Ina mai baku hak'urin rashin jina da ku ka yi na 'yan kwanaki, jiki da jini._
_6_
"Kai Muntari, wai Ina Abulle ta yi ne tun É—azu bata É—au tallan GyaÉ—ar nan ta tafi dandali ba."
"Inno, wata Abuwar? Sai dai ki tura mata da shi can. Don tun da aka ida sallar magariba suka fice ita da Saratun gidan Shawai wai za su dandali faÉ—a."
"La ilaha illallahu! FaÉ—a dai? Ita da wa."
"Da Indon gidan Mai Unguwa."
"Na shiga magana! Yi maza ka je ka yo k'iranta tun kafin ta jawo mana magana a gari."
A guje ya fice, ya d'au hanyar dandali.
Abulle ne da Saratu ke tsaye a kan hanyar zuwa dandali, jiran isowar Indo kawai suke yi, sai dai shiru har yanzun ba alamar zuwansu da tawagarta.
"Sarai! Anya ko Indo zata zo yau kuwa?"
"Yo, nima shi nake tunani, har yanzu banga ɓullowarsu ba."
"To, ya za a yi?"
"Binta zamu yi har gida, mu yi kamar mun biyo mata zuwa dandali, idan ta fito mu tari mu tara mata gajiya, mu fitar mata da jini da majina, daga baka har hanci."
"Ke! Kina hauka ko? To Yasin ba dani zaki je ba. Kin san wannan me sharb'eb'iyar dorinar idan ya rik'emu sai d'an burinmu."
"Haka fa! To kawai mu yi jiranta."
"Ke nifa ba Indon ce damuwata a yanzu ba."
"Hamusu ko?"
"Hamusu? Hamuso. Ni baya gabana ma yanzu, don naga idonshi rawa ya ke yi, baya tsayuwa waje guda. Yaje can su k'arata da Indon."
"Kuma don iskanci shine kika tsaidamu kan hanya kamar wasu ram-santi na cikin garin Jinjin."
Dariya Abuwa ta tuntsire da shi, har da durk'usawa k'asa tana fad'in.
"Sarai meye kuma wani rafsanti?"
Tsaki ta ja tana hararar Abuwar, "Matsalata da ke k'auyanci. Ram-santi ake cewa dallah. Lokacin zuwanmu cikin garin Jinjin bikin 'yar gidan Baffana Tallene muka wuce wasu da kayan sarki tsaye a kan kwalta suna bincike, dana tambayi su kuma su waye? nagansu da kaya daban ba irin na holis d'in da suke zuwa kama mai laifi bane a garin Mai ludaya ba. Shine aka ce mun wai Ram-santi sunansu."
Cike da mamaki Abuwa ta ce,
"Yo shi cikin Jinjin ai komai gani ake, Allah dai ya kai ni nima inga yarda take."
"Amin dai, inda kuna da dangi a can."
Kallon sama da k'asa gami da yatsina fusa ta bita da shi, "Mu a suwa da zamu yi dangi a birni? Ku da ke da dangi ai shiyasa naga kullum k'afarku na can, dad'in abun dai k'auye dai tushen birni ne, idan aka bi diddigi su Baffa a cikin k'auyen mai ludaya za a bankad'osu." Ta k'arashe maganar tana mai d'auke kanta daga kan Saratun.
"Ikon Allah! Daga magana kuma sai cibi ya zama k'ari? To, Allah ya baki hak'uri. Kinga tafiyata." Ta k'arashe maganar tana kunce mayafinta da ta d'aure a k'ugunta shirin fad'a.
"Sauk'a lafiya, agaida na gaba."
Sak'e-sak'e tashiga ya azuciyarta, na takoma gida ne? Ko tawuce dandali? Idan kuma ta je dandalin ba wani burgewa abun za ta gani ba.
Har ta juya zata yi gida, sai kuma ta sake juyowa ta nufi hanyar dandalin.
Tana gab da isa ne ta ji an k'wala mata k'ira, ko bata juyo ba ta shaida muryar mai k'iran nata.
Juyowa ta yi don ganin dalilin k'iran nata.
Hasken farin watan da ya haskaka duniya ne, ya hasko mata fuskar Muntari da yake ta zuba haki dalilin gudun da ya ci.
Tsaki ta ja kafin ta ce, "Lafiya ka ke k'wala min uwar k'ira a daren nan?"
"Inno ce ta ce in zo in k'iraki, na manta na tsaya yin Langa dasu Sabitu. Sai da naga wucewar Saratu na tuna Aradu."
"Jeka da Allah ina zuwa."
Ta juya zata tafi.
"Alk'ur an ta ce ki zo yanzu-yanzu."
Juyowa ta yi ta zabga mishi harara sannan ta d'au hanyar gida.
Indo da Karime da k'awayensu guda biyu da suka iso Dandalin tun da magribar fari suna jiran zuwan Abulle shiru ba labarinta, yasa suka fara taraddadin zuwan nata.
"Karime anya ko Abulle zata zo?"
"Tsaf zata zo in dai Abulle ce, kinsanta bata fashin zuwa dandali sai da dalili mai k'arfi, balle kuma yau a cike take, mu jira muga zuwanta."
"Ke nifa tunda kika zo gida ki ka gayan zancen nan nake tsuma, Allah-Allah nake ta iso. Aradu in sunkuya na kwashi k'afarta ku bita da duka."
"Ke, ni kayan tallana nake tunani a gidanku."
"Yanzu kika tuno da tallan naki?" Inji d'aya k'awar tasu.
"Lantana ai ina nan hankalina na can ne, tun fa rana dana fita ban koma gida ba."
"Ni fa kunga tafiyata ma zan yi."
"Ke Sahura ai dama ruwan ciki ne da ke."
"Hu umm! Ku ji Indon nan? Kuma dare ya yi sai in yi ta zaman jiran gawon shanu ko? To, ba da ni ba. Sai kun zo." Ta juya ta yi tafiyar ta.
Karime ta ce
"Kai, mu tafinku muna, gobe za ta fito ne, sai mun kwashi 'yan kallo."
Duk suka amsa da, "Mu je."
_Ummyn Yusrah_
[9/11, 9:31 AM] Ummyn Yusrah🧕ðŸ»: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*© UMMYN YUSRAH*
*8*
Da dare, Abulle suna zaune a kan tabarmar da suka shimfiɗa a ƙarƙashin barandar ɗakin Inno, suna cikin tuwon dare.
Wani kafcecen loma Abullen ta yanko, ta iza shi cikin bakinta, ji ka ke ya ba da sautin "Muƙutt!" Sanadiyar haɗiyar da ta yi masa ba tare da ta tsaya taunawa ba.
Haka ta yi ta wurga lomomin nan, tana haɗiɗɗiyar su, ba tare da ta tsaya ɓata lokaci wajen taune su ba.
Ga zufar da ta gama wanke mata fuska, wanda har ɗiga ya ke a ƙasa.
Inno da ke can gefe kan kujerar tsuguno, ta ɗago fitilar ƙwan da ke gefen ta ta haska fuskar Abullen, a daidai lokacin da ta yanko wani tiƙeken loma ta zazzaro idanuwanta waje masu kama da ƙwan zabbi, tana shirin wurgashi baka, ganin hasken fitilar yasa ta tsagaitawa tana mai kallon Innon da ta saki baki tana binta da idanuwanta kafin ta ce.
"Ikon Allah! Wai ke a rayuwarki ba ki iya cin abinci cikin nutsuwa ba ne? Ki duba dai ki gani, ke ɗaya ke ci amma Allah-Allah ki ke ya ƙare, kamar wata mai warwaso kina tsoron kada a ƙwashe a barki hannu rabbana."
Turo baki ta yi gaba ta yi tana faÉ—in,
"Inno! Nifa a hankali na ke cikin abincina."
"HoÉ—ijam! A hakan?" Ta tambayeta.
"Eh." Ta bata amsa a taƙaice gami da wurga lomar da ta ke ta juya shi a hannunta.
"Ummmhh! Lallai da aiki. Da alama gidan Sarkin noma za a wurgaki, domin wannan irin ci naki ba dai gidan rago ba."
Ta faɗa a lokacin da ta ke ajiye fitilar da ke hannunta a ƙasa.
"Shiyasa kullum ki ke ta hawa kamar farashi ai, daidai da sakan guda ba ki fatan bakin ki ya zauna shiru, ko da yaushe yana cikin motsi hayayam-hayayam. Ki sama ma kan ki lafiya tun wuri ina gaya miki, ba ko wani namiji ne zai iya da wannan cin naki ba ina gaya miki."
Ta ƙarashe maganar tana mai ci gaba da saƙar hular da ta ke yi da ƙwarashi.