Sashe 8
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin shirun ya yi yawa ne yasa Hajiya Sabuwa ta tura Lubna ta dubota.
Tun daga ƙofar ɗakin ta ji iska ya canza, tana kutsa kai ta ji hanjin cikinta ya fara hautsinewa, take zuciyarta ta tashi da gudu ta fice tana yunƙirin amai.
Fallon ta dawo tana faÉ—in,
"Mami! Kin ji ɗakin baƙin can kuwa? Wallahi wari kamar mushen jaki."
Kallonta ta yi tana faÉ—in,
"Me ya mutu a ciki to? Ina ita Zainab É—in take."
"Nikam ban ganta a ciki ba, ina sa kai na fito don wallahi mutum ya É—auki tsawon lokaci a ciki zai iya tsintar kanshi a gadon asibiti."
"Ungo nan."
Ta ware yatsun hannunta alamar zagi.
"Kuma shine ba za ki shiga ki duba ko lafiya ba, kin ji yanayin wajen amma ki ka barta anan?"
Tsaki ta ja, ta miƙe.
"Baki da hankali."
Ɗakin ta nufa, tana kunna kai itama ta ci karo da baƙon al'amari.
Ba shiri ta ware É—ankwalin da ke kanta ta toshe hancinta hannu bibbiyu.
Ba Abulle babi dalilinta.
'Ina ta shiga? Warin meye haka a É—akin nan?'
Ta tambayi kanta.
Har ta juya za ta fita sai kuma ta nufi banÉ—aki ko za ta ji motsinta.
Jin shiru ba alamar motsin mutum yasa Hajiya kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar. Shiru ta ji ba magana, ta sake ƙwanƙwasa shiru, kawai sai ta tura.
Abulle ta hango zaune kan randar ta, duk jiki ba ƙwari.
Yafutota ta yi da hannu, da yake idanunta na jikin ƙofar, duk bugawar nan da take tana jin ta, kawai kuzari ne bata da shi, duk gwuiwoyinta sun mutu.
Da ƙyar ta samu ta iya miƙewa, da taimakon bango ta samu isowa kusa da Hajiyar.
Riƙeta ta yi suka fito daga ɗakin gaba ɗaya, don tanason ta yi mata magana tana tsoron buɗe bakinta ta shaƙo wari, yanzun ma ba don ƙamshin turaren da ke jikin ɗankwalin ba da abun ba dama ne.
Tana jin warin, amma ba can ba.
Suna barin wajen ta buɗe hancin, ta ja wani dogon numfashi ta shaƙi iska mai ni'ima.
"Sannu Zainab! Me ya sameki haka, lokaci É—aya duk kin fita hayyacinki?"
Suna tafiya tana tambayarta.
Ba bakin magana Abulle, gayu yau ansha wuya, an yi ma gosulo É—iban karen mahaukaciya shi kuma ya yi mata lalata.
Kan kujerar falon ta yi mata masauƙi, tana yi mata sannu.
"Hajiya wannan yarinyar anya ba asibiti za a kai ta ba kuwa? Dubi yadda idanunta ya dawo kamar na kifin nan Kafi zuru lokaci É—aya."
Cewar Afreen.
"Ai banma san me ke damunta ba, daga zuwa yau kuma sai ciwo? Me ke damunki Zainab? Ki yi magana idan na zuwa asibiti ne sai a tafi."
Hajiya ta tambayeta.
"Mami! Anya ba Salad ɗin da ta ci bane da yawa wa ɓata mata ciki?"
Kallo Abulle ta bi Lubna da shi mai haɗe da harara, da ƙyar take faɗin,
"Ni...kuma? Yaushe na ci wani salati? Wancan wancan kwaÉ—on da kuka cikashi da wasu shirgin ya waren ciki. "
Dariya suka sa dukansu.
Iya wuya ta kai don haushi, wato ma ba tsusaya mata za su yi ba, dariya za su yi mata don rashin tausayi.
Juya kai ta yi ta a basu baya.
" Wai salati?"
Ta sa dariya.
"Salad fa aka ce miki, ba salati ba."
'Koma dai mene ne ku kusa sani.'
"Ke Lubna ya isheki! Yanzu me ke damunki Zainab?"
"Ba komai."
Ta faÉ—a ba tare da ta juyo ba.
"Riƙeta Lubna ku je ɗakinki, ta yi wanka, Afreen ya kaiku Jinjin sifeshiyal hosfitan ko ruwa ne sai su ɗaura mata su bata magani ko zata ɗan ji ƙarfin jikinta."
"Mami! ÆŠakina kuma? Kada ta je ta..."
"Zan ɗaura miki mari. Riƙeta ku je. Kai ƙaramin Asabe ta je ta tsaftace can ɗakin."
Haka ta kamata tana yatsina fuska suka tafi.
***
Inna Talle ta cigaba da magana.
"Ya shiga tashin hankali mara iyaka, haka na yi ta bashi baki ina bashi haƙuri kan cewar idan Allah ya nufa Abulle matarshi ce sai ƙaddara ta bashi ita, idan kuma ba matarshi bace ya yi haƙuri tun can haka Allah ya nufa, ya yi addu'ar zaɓi na gari. Ganin yadda nima na shiga damuwa a 'yan tsakanin nan ne yasa ya daina tunƙarata da zancen, ganin haka yasa nima na kwantar da hankali na."
Shiru ya sake ratsa tsakani.
Inno kan na tsugunne kan ƙafafunta da suka gama yi mata tsami, ta kasa magana sai sauraro kawai.
"Lokacin da Abulle ta fara zaga gidajen sallamar tafiya gidan aure lokacin ne muka tabbatar da ta fita rabonmu. Ranar ya zo ya ce mun sun haɗu da Abulle ta faɗa mishi maganganu marasa daɗi, ya kuma samu labarin tafiyarta Rangwangwan a ranar tunda ya fita ban ƙara jin motsin shi ba har yau, duk wanda na tambaya sai ya ce ya ganshi da kaya a leda ya ce za shi garin Dagal aike wajen kawunshi. Ashe tafiyar kenan..."
Kuka ya ci ƙarfinta.
"Shi É—aya ke gareni, shike tallafamin saboda lalurata ta rashin ido, yau anwayi gari na rasashi, kukuma taku É—iyar tana tare da ku..."
Ta sake rushewa da kuka.
Hamusu ya yi hijira a soyayya.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
   _Ummyn Yusrah_
_Gwiwoyina a ƙasa, hannayena bisa kunnuwana ina neman afwa._
_17_
"Inna Talle ki yi haƙuri! Bansan komai game da wannan lamari ba, kwanaki dai Muntari ya faɗamin Abulle sun tafi faɗa a dandali ita da Indo, tun a lokacin na sa aka ƙirata na haneta da hakan. Ta kuma yi min bayanin dalilin faɗan cewar shi Hamusun yana zuwa gurinta, tun daga lokacin ban kuma bi ta kan zancen ba. Ko auren nan da za a yi mata da amincewar ta ba wai dole za a yi mata ba."
Sharce majina Inna Talle ta yi daga hancinta, bakin zaninta ta sa ta goggoge hancin kafin ta ce,
"Allah ya sauwaƙe wahala, tsohuwa taga kwananta ya yi kusa. Ba nema tsakanin Indo da Hamusu, shi ɗin dai wakili ne kawai. Wanda aka cuta, ai shi ake ba haƙuri.
Haƙuri kam ai ya zama dole."
"Wakili? Na wa kenan Inna?"
"Ɗan gidan kawunshi Saluhu dake Dagal ne ya ganta yake kamu, to shine fa shi Hamusun ke isar mata da saƙo idan ya je garin. Ya yi ƙoƙarin ya sanar ma ita Abullen amma ta ƙi sauraronshi."
Haɓa Inno ta kama cike da mamaki da saurin yanke hukunci irin na Abullen.
"Amma ko Abulle ta yi wauta! Ban san dalilinta na ƙin tsayawa ta saurari jawabin Hamusun ba."
"Mai hankali ai shi kan ba kaza ruwa da damina."
"Karuwa ai bata kiwon kaza. Ki yi haƙuri za mu magantu da mahaifin nata idan ya dawo, da yardar Allah kuma za mu tayaki cigiyarshi. Ko ba Abulle ai Hamusu ɗa ne a wajenmu."
Sandarta ta fara lalube, tana ɗauka ta muƙe tana faɗin,
"Uhmmm! Allah ya jishshemu alheri."
"Amun.
Inno ta amsa.
Har ƙofar gida ta yi ma Inna Talle jagora, anan ta ƙira ɗan rakiyar nata ya zo suka tafi, itama ta koma ta cigaba da aikinta.
Ba dare bayan dawowar Malam Ilu, ya yi mata banganjiya da tambayar yadda ta baro mutanen Jinjin da Yayanshi, ta sanar da shi duk suna lafiya, amma basu gamu da Yayan ba ya tafi aiki. Ta faɗa mishi irin sha tara ta arziƙin da Hajiya ta yi mata.
Godiya ya yi gami da yaba ma matar Yayan nashi na halin ƙwarai da son kyautata ma jama'a.
"Ohh! Niko Malam ka ji wani batu kuma?"
Ta faɗa tana kama haɓa.
Kallonta ya yi, ya ce,
"Batu akan me fa?"
"Batun ɓatan Hamusu ɗan gidan Inna Talle jikan Yawale mai Gurguzu."
"I, wallahi, duk gari ya É—auka. Ko ina ka gifta zancen ake."
"Allah sarki! Na tausaya ma halin da Inna ke ciki. ÆŠazu bayan dawowata har ta É—an É—au lokaci ma anan muna magana kan Abulle da shi Hamusun."
"Allah sarki! Abun ai akwai al ajabi, yaro dare ɗaya ya ɓace ɓat! Kamar wanda aka yi ma kurciya? Wannan abu da mamaki."
"Wallahi kuwa, ta sanar mun da komai, ashe shi Hamusun ba neman 'yar gidan Mai Unguwa yake ba, ɗan gidan kawunshi yake zuwa ma aike wurinta, da Abulle tagansu tare shine fa ta hau dokin zuciya, ya yi ƙoƙarin sanar da ita gaskiyar magana ta ƙi bashi haɗin kai. Da ya bita ta ƙi sauraronshi shine ya gudu wai ba zai iya ganin auren Abulle da wani ba."
"Ka ji shirmen banza! Duk tarin matan garin nan na Mai Ludaya ba zai zaɓi wata ba sai Abuwa? Wannan ai shashanci ne, dama can ya yi niyyar shiga bariki ne kawai. Ba wai rashin auren nata ba. Bana ma son sake jin zancen daga bakinki, tun wuri ki haƙa rami anan ki birne shi, kafin gari ya ɗauka."
"To, amma Malam maihaifiyar shi yaron fa? Tana cikin wani..."
"Dakata don Allah!"
Ya faÉ—a yana daga mata hannu.
"Na faɗa miki ki yi gum da bakinki, ki tayata da addu'a Allah ya bayyanashi kawai. Domin matuƙar zancen nan ya baza gari to, ina mai tabbatar miki fita ma sai ya gagaremu, ki barmu dai mu ji da wanda ake yi mana yanzun muka toshe kunnuwanmu."
Cikin marairaice fuska ta ce,
"Shi ke nan. Allah ya bayyana shi, ya yi mishi zaɓi da mafi alkairi."
"Faƙat! Amin."
Ya kaÉ—e 'yar shararshi ya fice daga gidan.
****
_Fadar Mai Unguwa_
"Sarkin fada! Yanzu ya kake ganin za a tsara lamarin bikin nan? So nake a yi biki na kece raini."
Kallon Mai Unguwa ya yi, da yake ta mamula gole a bakinshi.
"Ranka shi daɗe! Ai kasa a je cikin garin Jinjin a lafto shinkafa a zo a dafa a bi gida-gida ana rabashi, matuƙar akayi hakan to fa ina mai tabbatar maka da cewar wannan biki zai kafa tarihi matuƙa a cikin garin nan da kewayenshi."
Wangale baki ya yi, irin a dole yana dariya ɗin nan, ga haƙoran gaba, sama da ƙasa guda huɗu duk babu.
"Sarkin fada shi yasa nake son zama da kai. Ga ka ƙarami sai iya tsari wallahi."
"Ai Ranka shi daÉ—e, na fi kowa san kasance a zaman fadar nan."
Murmushi Mai Unguwa ya yi, ya ce,