← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 15

Sashe 7

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Abulle ta yi ido biyu da shinkafar da ke cikin kulan da ake ta zuzzubashi kan faranti take haɗiyar yawu, inda tare yawun nan ake a ƙiyasi zai iya kaiwa durom biyu.

Iya zaƙuwa ta yi shi, sai dai sam Lubna bata lura da hakan ba, sai wani yanga take wajen zuba abincin, wani abun mamakin ma sai ɗigashi take tamkar za a ba yaron goye. Domin duka-duka baya wuce rabin farantin.

Ganin abun nata ba na ƙare ba ne, yasa Abulle hangame baki alamar hamma.

"To mai cikin zani! Idan kika haƙura yanzu za ki ci."

Kallon Innon ta yi, ta kuma maida hankalinta kan ƙwaryar shinkafar, tana kuma jin kamar ta wafce kular ta afka miya ta hau loda ma cikin ta.

"Ka ji Inno! Ai ta ma yi ƙoƙari, tun karin safe gashi har wajen daya da rabi ace bata buƙaci abinci ba? A kinsan da kamar wuya, idan ke kin iya daurewa ai ita da yaranta ba za ta iya ba."

Kallon Lubna ta yi ta ce,
"Ke ki yi ki ba mutane abinci da Allah. Kina abu kamar mai karyayyen hannu."

Ta gama zubawa ta zuba miya da ya sha namar kaji, ga kuma ruwan lemo a kofuna da kuma ruwan gora duk a wajen.

"Ina kos lo É—in kuma? Ko gaya za mu ci abincin?
Hajiya ta watso mata tambaya.
Da sauri ta miƙe ta nufi hanyar kicin.

'Gosulo? Gaya? To duk wannan miya da ya rufe hinkahwar ta mene ne da za a ƙirashi da gaya? Mene ne kuma gosulon Ohho!'

Abulle ta gama tunanin zuci, lokacin da ta kai hannunta cikin farantin abincin tana shirin gauraya.

"A a, Zainab! Ba ga cokali a cikin abincin ba?"
Hajiya ta tambayeta.

"Hajiya da hannun yafi É—ebuwa ne, tattara É—aya za ka yi ya cike hannu, cokali kuwa sai ka yi ta fafutukar tattarowa. Idan ma akai rashin sa a wajen juyewa a baki, duk sai ya zube, kinga ai gara in sa hannuna da Allah ya min ba hannun bature ba."

Ta faÉ—a tana afa shinkafar a bakinta.

"To, ki jira a kawo kos lo É—in mana, ai ya fi daÉ—in ci da shi."

'Uhmm! Ke kika ma san wani gosulo. Ni burina in gama a ƙaramin.'
Ta faÉ—a a zuciyarta.

A fili kuma ta yi yaƙe, ta tsame hannu a farantin tana zaman jiran zuwan gosulo.

Takaici ne ya rufe Abulle lokacin da gosuln ya iso.

'Shegen sanabe! A ƙira abu da kwaɗon kabeji an wani lauyance masa suna wai gosulo. Koda yake ma naga an yi haɗe-haɗe, barin ji shi kuma ya yake, don in shiga gidan Mai Unguwa da sabon salo da sabon tsari. Na shigo Jinjin na waye.'

Wani murmushi ta yi, da ta tuno da gidan Sahibi Mai Unguwa.

"Nikam in ce ko dai Abulle ta ƙoshi ne? Kin bar abinci kin tafi karanto wasiƙar jaki."

Kallon Inno ta yi ba tare da ta amsa ta ba, ta hau laftar shinkafa da gosulo.

Sosai ta ci, don abun ya kai mata karo. Ya mata daÉ—i sosai, sai da kowa ya tashi ya bar Abulle a wajen tana ta lodar abinci kamar jaka.

Salamar da Inno suke yi da Hajiya Sabuwa ce ta ankarar da ita, ashe har tafiyar Innon ya tashi.

Ba shiri ta baro wajen cin abincin ta taho gun su Innon.

"Hajiya don Allah kada ku bar Abulle ta wuce sati biyu don akwai gidajen da za ta je sallama idan ta dawo."

"In Sha Allahu ba za ta wuce kwanakin ba. Lado direba zai kawota har gida."

"Allah ya kai mu lokacin."

"To, Allah ya tsare hanya ya kaiku lafiya, sai mun zo kenan."

Inno ta amsa da amin.

Sai da suka iso bakin get, ÆŠayyabu ya É—auki kayan da Hajiyar ta sallameta da shi suka nufi bakin hanya neman abun hawar da zai kai ta tashe.

Tana ta addu ar samun abun hawa don biyu ma ta wuce har da minti ishirin.

Allah kiyaye ya yi mata, tare da alƙawarin zuwa ɗaurin Abulle idan lokacin ya zo. A lokacin da ta shige cikin adaidaita bayan ta mishi bayanin inda zai kai ta.

****

Sai daf! Magriba Inno suka isa Mai Ludaya.

Mai mashin na sauƙeta a ƙofar gida, yara na ganinta rugo da gudu, suna ihu da murnar dawowar Inno kamar wacce ta shekara da tafiya.

2019

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
                     (*HWA*)

         _Ummyn Yusrah_

_Ina miƙo saƙon godiya a gareku masoyana na tayani murna lashe gasar gajerun labarai da muka yi, wanda labarina mai suna Rashin Kula ya zo na ɗaya. Na gode sosai Allah ya bar zumunci._

_Haɗin Allah da Hazaƙa banda kalmar da zan iya faɗi a gareku, sai dai fatan alkairi da ƙaruwar so da ƙaunar juna da kuma ƙarin haɗin kai da zaman lafiya. Na gode sosai._

_15_

Tura ƙofar gidan ta yi, yaran suka ɗebi kayan da ta zo da shi suka shigar ciki.

"Inno! Inno!! Inno!!!"

Da sauri ta ɗago daga sunkuyon da ta yi da niyyar cire ɗan kwaɗon da aka maƙala a jikin ƙofar.

"Wannan wani irin ƙirane Muntari? Na hanaka irin hakan amma ba ka ji ko?"

Ƙarasowa ya yi yana haki ya ce,

"Inno kin san meye?"

Bai jira amssrta ba ya ci gaba da faÉ—in,

"Wai Hamusu ne ya ɓata, yau kwana uku kenan ba a ganshi ba."

"Ya ɓata!"

Ta faÉ—a cikin mamaki.

"Ya ɓata fa ka ce?"

"Eh, an nemeshi ba a sameshi ba."

"Yo allura ne shi da za ai ɓata a rasashi? Wataƙila dai ya yi tafiya ne ba a sani ba dai ko?"

"Wallahi ɓata ya yi Inno, Baba Marka ma fa yau sau biyu tana zuwa gidan nan bata samun kowa, ta ce idan kika dawo za ta zo."

Cikin yanayi na jimami da zancen Muntari ta buɗe ƙofar ta shiga ɗakin, zuciyarta na ta tufka da warwara.

Kaya kawai ta ajiye, ta fito ta nufi É—akin girki don haÉ—a musu abincin dare, duk da kasancewar dare ya yi.

Tana tsaka da haɗa wuta a murhu ta ji ƙarar buɗe ƙofar gidan tare da sallama.

Fitowa ta yi, tare da amsawa.

"Inna Talle ke ce tafe?"
Inno ta tambaye tana mai isa gurin da tabarma ke jingine ta shimfida musu.

Wacce aka ƙira da Inna Tallen ta amsa da,
"Gani tafe, na taki sa a. Zuwana sau uku yau bakyanan wai kin je Jinjin."

Ta faɗa tana ƙara dogara sandar da ke riƙe a hannunta na dama, na hagun kuma riƙe da kafaɗar yaron da ya rakota.

"Bismillah Inna! ku zauna. Na je raka yarinyar nan ne gidan Baffanta, kinsan abun ya matso."

Hawayen da ya gangaro a idanunta da ke rufe ta sanya hannunta na hagu ta goge.

"Iro je ka yi wasa wajen yara, idan na gama zan yi ƙiranka mu koma."

Ta faÉ—a ma É—an jagoran tana, lokacin da ta zauna akan tabarmar.

A guje ya É—iba kamar dama jira yake yi.

Zama Inno ta yi daga can gefe ta gaida Inna Tallen.

Shiru ne ya ratsa wajen na É—an lokaci kafin ta ce,

"Sai kuma kika ji ɓatan Hamusu?"

"I, É—azu ina dawowa Muntari yake faÉ—amin. Na É—auka ma shirmene kawai irin na yara."

Sake share hawayen tayi,

"Na rasa Hamusu! Na rasa shi, shine mun É—a daya tilo da ke É—awainiya da ni. Tunda aka ba Mai Unguwa yarinyar nan hankalinshi ya tashi, ya kasa sukuni."

Ta tsagaita tana mai jan zuciya, da alamar jin ciwon lamarin.

"Hamusu ya kasa samun nutsuwa, kullum cikin kuka yake. Babbar ma abum da ya dameshi ya ce sam Abulle ta ƙi ta tsaya ta saurareshi ya yi mata cikakken bayanin dalilil zuwanshi gurin 'yar gidan Mai Unguwa."

Sake dakatawa ta yi, tana sheshsheƙar kuka.

"Tun lokacin da ya zo min da zancen samun saɓaninsu da ita, da kuma ƙin saurareshi na ce ya bari in zo in yi muku bayani, amma ya hanani. Ya ce, yasan halin Abulle, fushi kawai ta ke yi, nan ba da jimawa ba za ta sauƙo."

Shiru ta yi, da alama hutawa take yi, gami da jimamin lamarin.

"Ikon Allah! Amma kuma Inna duk an bincika yanda ya kamata kuwa?"

Bata bata amsar tambayar ta ba, sai ma ci gaba da ta yi da zancen ta.

"Haka muka haƙura zuwa hucewar tata. Duk da haka yana ci-gaba da bibiyarta da bata haƙuri a duk inda suka haɗu. Ba mu kwatsam sai muka ji labarin cewar anba Mai Unguwa Abulle."

Tunowa da ta yi na halin da É—an nata ya shiga ne ya sanya ta kuma tsagaitawa.

***

Tunda aka yi mata bayanin cewar ba wani mutumin da zai fito ta cikin akwatin talabijin ɗin ta saduda, don har hannunta aka iza bisa ƙwalbar don ta tabbatar.

Idanunta da duk wani imani nata ta tattara ta bar ma kwalbar, masu jajayen kunnuwane ke ta kaiwa da komowa daga mazan har matan.

Ita dai mamaki take yi, ganin kowa tsaf-tsaf! Tambayar kanta ma take anya ko suna yin dotti kuwa? Daga jikinsu har cikin garin nasu ba wani dauÉ—a kamar na garinsu.

Zabura ta yi kamar an tsikareta, yayin da cikinta ya sake murÉ—awa a karo na ba adadi.

Zuwa yanzu kam, ta kai magaryar tiƙewa domin kuwa ba abinda take buƙata baya ga kai ma banɗaki ziyara.

A guje ta miƙe ta nufi ɗakin da aka saƙesu da Inno ɗazu, ta shige banɗaki.

Yadda Allah ya taimaketa ma, ɗazu kafin tafiyar Inno ta gwada mata randar kashi, ba don haka ba, da sai dai ta sauƙeshi a ƙasa.

Tana shiga ko kamar an buÉ—e bakin famfo, ga azabar murÉ—ewar ciki.

A iya tunaninta dai tasan ba ta ci komai ba.

A wahale ta fito, hannunta na dama riƙe da ciki, na hagun kuma riƙe da ƙwanƙwasonta.

Zuwa yanzu duk ta gama laushi, don ta zaga ba adadi. Tun tana tafiya da ƙafafunta har ta dawo yi a durƙushe, ta sake dawowa da rarrafe. Ƙarshe ma mazauni kawai ta nema a cikin banɗakin domin abun ya ci tura.

2019

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

*NA*
*Ummyn Yusrah*

_Alhamdulillah! Ido da sauƙi, ras nake kallonku_

_16_
Chapter 7 · 0% Book details