Sashe 11
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki ta ja, Lubna da ke zaune kan kujera tana danne-danne a waya ta É—ago ta kalleta ta sake mai da kai ga waya.
Ba tare da ta É—ago ba, ta ce'
"Ke! Ki É—auko min ruwa a firij."
Waiga-waige ta shiga yi, ba ta ga kowa ba. Kenan ma da ita, ita ce Ke!
Lallai wannan rainin hankalinta ya wuce inda take tsammani.
Juyawa ta yi ta bata baya.
"Wai ba ki ji me na ce ba ne?"
Ta yi tambayar.
Shiru ba amsa.
"Zainab! Wani salon iskanci ne haka? Ina yi miki magana, kin yi banza da ni."
Jin ta ƙira sunanta yasa ta juyowa tana faɗin,
"Ji nayi kin ce ke! A iya sanina Inno da Baffa Zenabe Abu suka raɗamin wanda wasu ke ƙirana da, Abuwa, Abulle. A garin Jinjin kuma Zenabu, kinga ko ai ba lallai in san da ni ki ke yi ba."
Kallon mamaki ta bita da shi. Lallai yarinyar nan bata da kunya.
"Idan ba da ke nake yi ba, da wa nake yi? Za ki tashi ko sai na ɓaɓɓallaki."
Kallon sama da ƙasa ta yi mata, ta ƙare mata kallo tsaf!
'Wai ɓallawa? Allah na tuba ai ko dusa nake ci wuce nan. Yasin damƙa ɗaya na yi miki sai kin gane kurenki. Renon dawa ce ni.'
A fili kuma ta ce,
"Zan karɓo miki da gudu ma."
Ta miƙe ta bar falon.
****
Inna Talle da 'yan uwanta sun yi cigiyar Hamusu har sun fara gajiya ba labarinshi.
Yau kwana biyar kenan da tafiyarshi.
Tun tana kukan fili har ta dawo na zuci.
An shaida mata ya tafi garin Jinjin, lokacin da ta sa a yi mata cigiya a tasha.
Duk wanda ta ji zai je garin Jinjin, saƙonta baya wuce a sanar ma Hamusu ya dawo gida.
Duk wanda ya dawo, ce mata yake bai ganshi ba.
Sosai ta tashi hankalinta, lokaci guda duk ta zabge ta fita hayyacinta.
Ganin halin da take ciki ne, yasa Wani ƙaninta Garbati ya tafi da ita garinsu Ɗan kurma.
Ƙauye ne sosai, ga ƙauyanci har ya fi na Mai Ludaya.
Tafiyar awa goma za ka yi daga Mai Ludaya, zuwa ÆŠan kurma.
Su Inno shirye-shirye ake ta yi, ba ji ba gani. Haka ma gidan Mai Unguwa ana ta shirin tarbar sabuwar amarya.
Yayin da galibin 'ya'ya da jikokin Mai Unguwa ke ji kamar su kamashi da ranshi su jefashi cikin tukunya, su gangama mai wuta ya mutu ko su cakuɗa mishi abincinshi da shinkafar ɓera ya mutu kowa ma ya huta.
A fadar Mai Unguwa ma, tawagar ta kasu biyu.
Tawagar da ta fi rinjaye, suna tawagar ƙin auren Abulle da Mai Unguwan, tawagar amincewa kuwa! Ba su fi a ƙirga ba.
***
A hankali take tafiya a kan simintin bature, gudun kaiwa kasa irin na ɗazu, har ta isa ƙofar ɗakin.
Buga ƙofar ta shiga yi.
Daga ciki aka tambaya da waye?
"Nice Abulle."
Tasowa ya yi ya buɗe ƙofar.
"Yaya ne?"
Ya tambayeta.
"Cewa aka yi in karɓo ruwan sha a wajenka."
Kallon rashin fahimta ya yi mata,
"Ruwa a wajena kuma? Duk gidan nan ace ba ruwa sai an aiko ki wajena? Waye a aikoki?"
Taɓe baki ta yi itama, tana tunanin kinibibi irin na waccar mai kama da takardar. Ace duk ruwan gidan ya gagareta sha, a na wajen Afirij!
"Uhmmm! Nima shi nagani. Akwai ruwa a gidan amma wai in karɓo mata a wajenka."
Tsaki ya yi, ya ce
"Wai waye ne?"
"Labano mana?"
"Labano kuma? Waye haka?"
Ya yi tambayar cikin rashin fahimta.
Kallon rashin fahimta itama ta yi mishi.
"Labano ta gidan nan mana. Ko akwai wata ne."
Dariya ne ya kufce mishi, da ya gane ashe Lubna take nufi.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_Ku yi haƙuri da jina shiru, zazzaɓi ya riƙe ni. Amma sauƙi sosai, masu yi mini addu ar samun sauƙi ina godiya._
_Masu yi min magana ba amsa a private ko cikin group ba amsa ku yi hakuri don Allah, na É—an yi fama da matsalar network ne._
_Afwan! Sunan garin su Inna Talle Kurmawa ba É—an kurma ba._
_23_
Dariya yake ta ƙyaƙyatawa, ita kuwa ta gama ƙuluwa, haushi duk ya cikata. Ba abin da ta tsana kamar a tasata gaba ai ta doka dariya ba dalili.
Juyawa ta yi cikin fushi zata tafi, da sauri ya biyota yana ƙiranta.
"Zainab!"
Tsayawa ta yi kafin ta juyo, fuskarta a haÉ—e.
"Meye?"
"Yi haƙuri! Da fari ban fahimci wa kike nufi ba."
Keɓe baki ta yi, irin kai ka sani ɗin nan.
"Je ki, ki ce mata zan kawo mata kin ji."
Juyawa ta yi ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta bashi amsa ba.
Ganin ta shigo ba ruwa a hannunta yasa ta tambaya.
"Ina ruwan da nace ki É—auko min?"
"Ya ce in je zai kawo."
Kallon rashin fahimta ta yi mata.
"Shi wa?"
"A firij!"
Tsaki ta ja sannan ta ce,
"Kin taɓa ganin Fridge ya yi ƙafa ne? Ko kuma ya yi baki da har zai ce miki jeki zan kawo?"
Kallonta ta yi, ta ce
"Dama A Firij É—in kurma ne? Naga kullum yana magan..."
Kafin ta ƙarasa maganar sai gashi ya shigo, yana faɗin.
"Aunty Labano ga ruwan."
"Yauwa, gashi nan ma kin ji yana magana." Cewar Abulle
Yamutsa fuska ta yi,
"Meye kuma wani Labano?"
"Ba ki san Labano ba?"
Ya tambayeta lokacin da ya ke zama kan kujerar.
"Ban sani ba."
"Sabon sunanki ne da Zainab ta raÉ—a miki yau." Tsaki ta ja cikin jin haushi.
Harara ta galla ma Abulle, tana faÉ—in,
"Wannan bata da saiti, don iskanci sunan nawa ne zata ƙira da sunan wani ƙasa." Dariya shikam ya sake kwashewa da shi.
"Ke kin cika masifa wallahi, yarinyar da bata iya ba, don ta kuskure ai gyara za a yi mata ba wai a yi mata masifa ba."
"Koma dai meye ku kuka sani. Dallah ni bani ruwana."
Ta faÉ—a tana faucewa.
'Kya ji da shi dai masifatu, Allah yaso gobe ma zan bar muku gidan ki ci kanki. Cewar Abulle ta juya ta fita.
"Wai gurinka ta je karɓar ruwan ne?"
"Dama ba wajena kika aikota ba?"
"Duk ruwan da ke gidan nan in kasa sha sa sha sai na wajenka? A Fridge fa nace ta É—auki min."
"To, ai wajen a Firij ɗin ta je karɓo miki."
"Ban gane ba?"
"Suna na ne fa A Firij É—in wai."
Dariya ta sa, shima ya tayata, kowa yana ƙiran sabon sunan kowa.
Bakin get ta nufa wajen ÆŠayyabu mai gadi.
Yana hangota ya wangale baki yana dariya don yasan yau, zai sha labarin Mai Ludaya har ya ƙoshi.
"Abulle! Abulle! Abulle mutan Mai Ludaya. Sai kuma gaki a Jinjin."
Ya faÉ—a yana tura mata farar kujerar roba.
Bayan ta zauna ya ce,
"Yaya kika ji Jinjin É—in?"
"Ba daÉ—i."
Zaro ido ya yi,
"Ba daÉ—i kuma? Birni ne fa!"
"To, ina daÉ—i anan don Allah? An jibge mutum waje guda kamar kayan wanki, daga barci sai kafa ma kwalba ido."
Dariya ya yi,
"Wato dai kin fi gane ki yi ta jeka ka dawo ko?"
"Iy mana! Zama waje É—aya ai haÉ—ari ne."
"Gaskiya kam, musamman ma ga wanda bai saba ba."
"A, to. Ni waje ma nake son leƙawa."
"A yi haka kuwa? Ke da kike baƙuwa idan na barki kika fita ai ba kanta."
"Yasin ba nisan zan ba, yanzu zan dawo."
"To, ai rana ya yi, ki bari zuwa anjima yanzu za a yi sallar azahar ne."
"Dan Allah Baba Ɗayyabu ka bari na leƙa, yanzu zan dawo."
Jin ta girmamashi yasa ya ce,
"To, iyakarki bakin layin nan, yanzu ki dawo."
"Yauware, Na gode."
Ƙaramin ƙofar da ke jikin jet ɗin ya buɗe mata, har waje ya fito ya nuna mata hanyar ƙarshen layin, tana zuwa kuma ta juyo ta dawo.
Godiya ta yi, ta É—au hanya.
Sunkuyawa ta yi, ta tsinci duwatsu, tana tafe tana ciccilasu sama.
Ta zo wucewa wajen wani masallaci dake jikin wani gida taga wani mai saida gauta, a tsugunne. Har ta wuce sai kuma ta dawo.
"Malam nawa kahin gautar?"
"Hansin da ta dari."
Ta nuna É—aya tiren da ba mai ita,
"Su kuma wa innan É—in fa?"
"Duk kuÉ—insu É—aya, mai ita ya zaga makewayi ne, yanzu zai fito amma."
"Ni na naira Ahirin nake so."
Ta kwanto a bakin zaninta.
"To, kawo mana sai in É—iba miki, da gani ai kema tamu ce daga gida kike."
Dariya ta yi, ta ce
"Kai ma É—an Mai Ludaya É—in ne?"
"A'a, a Bugawa nake."
"Taɓ! Ban taɓa ji ba."
"Nima ban taɓa jin naku ba."
Ya faɗa lokacin da yake miƙa mata.
Sai da ta ƙirga, ta ce
"Ƙwara fa huɗu ne?"
"Iy!"
"Taɓ! Can kam sai dai mu je mu tsinko, nan kuma ɗan wannan wai Ahirin hu um!"
Ta faÉ—a tana tafiya.
Tana barin wajen sai ga Hamusu ya fito daga magewayi.
"Ai kawai mu yi alwala kawai mu yi sallah sai mu wuce."
Cewar Hamusu.
"Kawai ba."
Abokin tafiyar tashi ya bashi amsa.
A yi haƙuri da kura-kuran ciki, ban bibiyaba.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
   _Ummyn Yusrah_
_24_
Tana tafe tana cin gautarta har ta isa bakin hanya, sai da ta tsaya ta kalli motoci da babura masu wucewa sannan ta juyo. Ci gaba da wurga duwatsunta sama ta yi tana cafkewa.
Wani gini ta hango da aka fara ba a gama ba aka mai dashi wajen zuba shara. Hango kwalayen sabulai da robobin mai da kwalaben turaruka da ta yi kan bolan yasa ta nufi wajen. Leda ta nema babba ta karkaÉ—e, Allah ya taimaketa bai yage sosai ba, ta hau tsintar kwalayen sabulu mai hoton mata da robobin mai da kwalaben turaren da basu fashe ba. A ranta tana hango yanda zata jeresu a cikin kwabet É—inta.
Ta tsinci na tsinta ta bar na bari, ta É—auko ta nufo hanyar gida.
"Lahhhh! Mai gauta har yanzu kana nan?"
Ta faɗa lokacin da ta zo giftawa wajenshi a ƙofar wani gida.
"Iy, wallahi. Mai gidan nan ne ya ce mu zo mu zubar mai da hyara, É—an uwana ya shiga ciki zai É—auko."