← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 15

Sashe 1

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

_Rubutawa_
_Ummyn Yusrah_

_Gajeren labari domin nishaÉ—i_

*Garin Jinjin*

_Ƙaramar hukumar Mai Ludaya_

_Yammaci lis!_

_Fadar mai unguwa_

1

Mai unguwa ne zaune kan kujerarsa, yayin da sauran jama ar fada ke kewaye da shi kan wata ƙatuwar tabarmar ana ta hira da mai da zance.

Tunda suka doso fadar idon mai unguwa ke kanta.

Kanta É—auke da tiren talla, kunkumin nan an É—aureshi tamau da gyale, ga fuskarka ta sha kwalliya da fauda buda jaka.

Masifa kawai ta ke ta zubawa har bakinta na kumfa.

"Karime Wallah gobe sai na ci uwar Indo, hegiya kucaka ta rasa wa za ta yi zance da shi sai Hamusu rabun raina! Ke alƙur an ji nake kamar na kifar da kayan tallar nan na je na ragargaji tsinanniya."

"Yo ke Abuwa tun yaushe na ke gaya miki ki rabu da tsinanniya? Shegen kwashe-kwashe irin naki yasa ki ka kwaso mai ƙwatar miki masoyi. Yo ni ban isheki ƙawance ba ne?"

Kallon sama da ƙasa ta yi mata ta keɓe baki

"Taɓ! Kin manta ita ɗin ƴar waye? Ƴar gidan mai unguwa ce fa! Duk sati ranar juma'a sai mun je cin hinkafa gidansu. Ke ko sau ɗaya aka taɓa dafata gidanku. Shima albarkacin yayanku ya bi doguwar mota ya yi kabo-kabo zuwa burni ya auno muku ita."

Cikin yanayin jin haushi ta ce
"Shegiya kwaɗayayya, ai ke wallahi kin ji jiki. Dama tunda naga kin liƙe mata nasan da biyu ne, shiyasa duk ranar juma a kike korata idan na biyo miki yawon juma a. Har kike wani cewa sau ɗaya kika taɓa ci a gidan mu. Ke sau nawa na ci a gidanku?"

"Ko sau É—aya. Amma ai kina zuwa kwaÉ—ayin tuwan biski da miyar ja."

"Aikin banza! Abunda sai a share mako uku ko hudu ma ba ai ba, duk ranar ko da a ka yi Æ´ar hali ki ke yi mun, kin yi ta haÉ—e fuska kenan kuna kumbura kamar Fanken Dudu na bakin kasuwa."

"Kam bala i! Nice Fanken Dudun Yasin sai na hau kan gandar bakinki na yi luguden leɓe, yar jakar ub..." Ta sauƙe tiren tallan dafaffiyar gyaɗar ta ta nufota gadan-gadan za ta cafko ta, da sauri ta matsa can gefe tana faɗin

"Idan na tsaya kenan za ki yi luguden ko? Ai wallahi ke da Indo ne sai na faÉ—a mata kwaÉ—ayi ki ke zuwa yi gidansu."

_Ya a ci gaba?_😃
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

_Rubutawa_
_Ummyn Yusrah_

_Godiya mai yawa da Addu'o'inku_

3

"Kai! Kun raba mana hankali, maganar wa za mu ɗauka cikinku?" Ɗaya daga cikin jama ar ya daka musu tsawa. "Cewa ta yi Inno Mai Ƙosai." "Ƙarya ta ke yi, ita ta fara cewa Talatuwa mai Tafasa." Sarkin fada ya ce "Yau naga shashanci gurin yara. To ai abun alfahari ne a san mutum asan sana a tasa, naga duk faɗin unguwar nan da Inno Mai Ƙosai ake ƙiranta, ita kuma Talatuwa mai Tafasa. Duk ai sana ar tasu ta gado ne, shine har kuke husuma a kai don an ƙira sunansa?" Liman da ke zaune gefen hannun damar mai gari ya zuba ma yaran ido, ya kaɗe idonshi guɗa ɗaya na dama, yana nunasu da yatsa ƴar manuniya da ke hannun dama ya ce "Wai wannan kam ba Abuwa bace ƴar gidan Ilu mai Amalanke?" Sarkin fada ya amsa yana mai jijjiga kai kamar riƙaƙen gadangare "Ita ce fa! Ai fitinaniyar yarinya ce. Waccar kuma Karime ce ƴar gidan Mudi mai jaki." "Ikon Allah! To, mai Ilun yake jira da bai sallamata ba? Duba fa, duk ta ƙere sa anninta a girma." "Man liman ai yariyar saurin girma ne da ita kamar wani kaji da na gani a can Binni, cikin garin Jinjin, wai kajin turawa, can garin yahudu da nasara a ke kawo su, haka nan suke gaɓa-gaɓa. Girma ba hankali." "To, ai kam gara ya miƙata, tun kafin a fara sata cikin waƙa. Wannan ai abun kunya ne ma a gareshi. Ƴa ta kai har wannan lokacin." "Ai kam! Sa ar fa Huwaila ce ta wajena. Yanzu suke shiga shekara na sha uku, amma kaga ita Huwaila ai bata kai ta ba, nan da mako biyu ne ma za a kai ta ɗaki." "Ikon Allah!" Duk ka-ce-na-ce ɗin da ake Mai Unguwa nashi ido, don ya ma rasa ta cewa. Hasalima tunanin shi daban ne. "Ke me ya haɗa ku da Indo ƴar gidan Mai Unguwar?" Ɗago kai ta yi sai hawaye sharrrr! "Ba komai." "Da gani ba ki da gaskiya, domin duk wani mai saurin kuka rashin gaskiya ne da shi." "A a, dama... Dam...!" "Dama me? Ke Karime, me ya haɗa su da Indon?" Gyara zama ta yi, kamar dama jira take. Nan ta ɗauko zance tun daga tushe har zuwa ƙarshe.

Salallami gurin ya ɗauka da. Sarkin fada ya ce "Ikon Allah! Ke kuma haka Allah ya yo ki da kwaɗayin hinkahwa? Yo in ba gidan Mai Unguwar ba, ina ake dafa ta? Shima dai albarkacin dangantakar da ke tsakaninsu da kansilan yankin Mai Auduga ne yake kawo mishi shi, wataran a turo ƴar Kwafarati wataran ƴar Hausa. Shine har za ki ɗarsa rayinki a kai? Ikon Allah." "Kwankwatsi ƙarya ta ke yi mini. Ba haka nan bane." "Rufe mana baki ja irar yarinya kawa..." Mai Unguwa ne ya katseshi yana faɗin "Ku barsu haka nan, ku kuma kada na kuma jin kun yi hayaniya a tsakaninku. Maza tashi ku tai." Jiki na rawa duk suka miƙe, kowa ta sunkuci kayan tallarta. Canza hanya su ka yi, sai da su ka daina hango fadar Mai Unguwa Abuwa ta ce "Yasin da an dokeni kanki zan rama." "Yo ko da ba a dokeki ɗin ba ai kin ɓare baki kamar ɓaure kina ta sharɓar kuka, Tuɓu luɓus kawai, mai kama da kazar masu jajayen kunnuwa." Tana kaiwa nan ta sa gudu. "Hegiya da ƙafa kamar Mazarin tsire. Za mu haɗu da dare a dandali."

_Ummyn Yusrah_
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

_Rubutawa_
_Ummyn Yusrah_

_To, ga ci gaban._

2

"Idan kin fasa faÉ—a mata kin raina Talatuwa mai Tafasa!"

"Ko kuma Inno mai Ƙosai ba!"

"Kam bala in can! Innar tawa?" "Ita dai, ai uwa ba ta fi uwa ba."

Har zuƙowa ta yi, itama Karime ta dire kwanon tallarta . "Zo mana! Kada ki ganki haka gaɓa-gaɓa ki ɗauka tsoron ki na ke, Aradu idan ban kwasheki na laftaki a ƙar ba."

"Kai! Kai!! Kai!! Kai!!! Kunga Æ´an nema, me ya haÉ—aku kuma?"

Abuwa da takaici ya gama cikata, na rashin luguɗen leɓen da ba ta samu ta yi a kan gadar Bakin Karime ba ta ce.

"Ƙiran sunan Inna ta ta yi." Tana faɗa tana hararar Karimen, kamar wacce idanunta zai zazzago ƙasa don harara. Ga wani ƙarin takaicin ma da ta ƙirata da sunan da ta fi tsana (Gaɓa-gaɓa.)

"Ƙarya ta ke yi Baban Lanti. Ita ta fara ƙiran sunan uwata."

"Ya isa, ku wuce mu je, tun É—azu Mai unguwa ke hango hayaniyar da ku ke, da ya ke ku ba ku san zuru ba sai an tanka shine ku ka ci gaba ko? Za ku yi bayani ne."
Jin Mai unguwa ne ya turo ƙiransu duk hanjin cikinsu ya kaɗa, tsoronsu ɗaya kada ya ƙira musu tsabga, don wannan baƙin mugun idan ya riƙe mutum da dorinar nan tashi ba ƙaramin jibgar mutum ya ke ba.

Nan suka bar kayan tallar suka ranƙaya gaban mai unguwa.

Ɗan aiken ya gurfana gaban Mai Unguwa yana mai dunƙule yatsun hannunshi na dama, yayin da ya ɗaga babbar yatsarshi yana mai jinjina wa Mai Unguwar yana faɗin "Ranka shi daɗe! ga yaran nan na taho da su."
Ya ƙarashe maganar yana mai nuna su Abuwa da Karime da ke durƙushe can a ƙasa, duk sun yi tsuru-tsuru, kamar wanda su ka kar uwar Mai Unguwa.

Sai da ya É—an É—au lokaci kafi ya fara magana cikin isa da mulki "Menene ya faru ku ke ta sa insa a tsakaninku tun É—azu?" Shiru su ka yi ba amsa

Tsawa mahukuncin fadar ya daka musu yana mai nuna su da miƙaƙƙiyar doninarshi ya ce,
"Ba Magana a ke yi maku ba ne? Ko nan ma rashin kunyar za ku yi mana? Ahir ku kula, fada ku ke."

"A...A...Ab!"
"Ta ce me? Kin bi kin ishemu da in ina." "Cewa ta yi wai Indon gidan Mai Unguwa ta..." "Ƙarya ta ke kwarankwatsa. Sunan Innata ta ƙira." "Ƙarya ta ke, ita fa fara ƙiran sunan tawa uwar."

Duk suka karaÉ—e wajen da hayaniya, da wannan ta É—auko zance sai wannan ta katse, musamman ma Abuwa da ta ke tsoron tonon tonon asirinta.

_Mu haÉ—e a gaba_
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

_Rubutawa_
   _Ummyn Yusrah_

_Tsangayar Marubuta da ke fuskar littafi ina miƙo jinjina da fatar alkairi gareku._

4

Da É—ai-É—ai mutanen da ke fadar Mai Unguwa suke tafiya, har ya rage saura Mai Unguwa da sarkin fada. Sunkuyowa yayi da kanshi saitin fuskarka Sarkin fadan.
Chapter 1 · 0% Book details