← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 28

Sashe 7

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin har lokacin Nenne bata farka ba,sai bata tashe ta ba, ta fita tsakar gida, ta gyara ko ina ta share tsakar gidan tsaf,sannan ta share É—akinta, ta hura wuta ta É—aura musu É—umame, sannan ta koma É—akin.

a zaune ta samu Nenne akan sallaya, fuskarka looking so pale,a kusa da ita ta zauna, ta gaishe ta,Nenne ta amsa da ƙarfin Hali tana murmushi,tace yau bazaki je makarantar bane,sai da ta kalli Nenne, idanunta na cikowa da hawaye tukun tace

"Nenne ta yaya zan iya zuwa makaranta, bayan halin da naga kina ciki jiya, Nenne jiya naji tsoro...",sai kuma ta kasa ƙarasawa, ta fashe da kuka.

shafa kanta kawai Nenne tayi tace Noor Kar kiji tsoron mutuwa, mutuwa dolece, kawai ina fatan ki zama mai juriya akan duk abinda ya sameki.

Noor ta katseta tana faÉ—in"Nenne mubar taÉ—in mutuwar nan,Nenne tace shikenan mun daina Noor"

Ranar dai wuni tayi a gida, tana maƙale da Nenne, a zuciyarta tana tunani ko balaraben can yaje yayi ta jiranta,amma dai a yanzu batada abin da ya wuce kula da Nenne a wajenta.

Kamar kuwa yanda tayi hasashe,tun ƙarfe 2 yake tsaye,tun yana tunanin zata zo, har ya fara cire rai, Taufeeƙ dai kallonsa kawai yakeyi.

can da ya gaji da tsayuwar ya juya ya kalli TaufeeÆ™,kamar zaiyi magana, sai kuma ya fasa,
can kuma sai ya sake É—agowa, yace

"TaufeeÆ™" da sauri TaufeeÆ™ yace
"Sir"
"Is this girl really going to come?

TaufeeÆ™ yayi murmushi yace "ko zan bincika maka gidansu ne Sir"

ÆŠan shiru yayi sai kuma yace "uhmm... ok I think it will be better, we should check on her"

TaufeeÆ™ ya É—an gyara tsayuwar sa yace "Sir amma zan iya tambayanka please if u won't bother"
É—aga kai yayi ya kalleshi sai yace
"go ahead"

TaufeeÆ™ ya sosa kansa yace "Sir dama tambayan is too personal zan iya yi?

Ya sake tambaya, Zannur daya zuba masa ido yana kallonsa yace "go ahead"

"Sir do you have any feelings for the girl.....?"

Wani kallo da ya masa yasa sauran magana ya maƙale ya kasa ƙarasawa, da sauri yace
"Sorry sir"

Sai da yayi ƙwafa alamar ransa ya ɓaci sosai kafin yace
"how can You even think of that, dan kawai yarinya tana nuna min garinsu sai kace ko ina da feelings akanta.
I think ko da wani ya ce maka zanso mace irin wannan, kai ne mutum na farko da zaka ƙaryata"
da sauri TaufeeÆ™ ya sake faÉ—in
"sorry Sir"
bai sake ce masa komai ba but ga dukkan alamu ransa ya ɓaci sosai.

TaufeeÆ™ yace "Sir bari na binciko gidannasu"

Da sauri ya É—agamasa hannu "No need, barta kawai, idan har kai zaka yi wannan tunanin,bansan kuma sauran mutane me suke tunani ba" daga haka ya juya ya bar wajen".

TaufeeÆ™ ya bisa a baya,jikinsa duk yayi sanyi.

sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gida, but duk hankalinsa na kan me ya hanata zuwa

Juyawa yayi ya kalli TaufeeÆ™ sai kuma yace "ummm...mr, can You look for the girl's house yanzu,Yakamata mu duba ko bata da lafiya ne?"

da sauri yace "sure" sannan ya miƙe ya fice, shikuma Camera ɗin sa ya ɗauka yana kallon hotunan da yayi mata sanda tazo nemansa bata gansa ba.

Taufeeƙ bai wani sha wahala ba ya gano gidan ya dawo ya sanar dashi miƙewa kawai yayi yace "muje"

Taufeeƙ ya bisa a baya amma ya kasa daina kokon to a ransa, but yanzu ya yarda ba sonta yake ba maybe kawai, tausayinta yakeji,ganin bayi da amsa kuma bayi da hurumin tambaya ya sashi kawar da tunanin daga ƙwaƙwalwarsa.

A ƙofar gidan ya tsaya,yana tunanin ta yadda zasu yi magana da ita, gashi har kusan 9 o'clock duk da garin har yanzu akwai sauran mutane,but babu yara da zai iya tura wa ciki

Juyawa yayi ya kalli Taufeeƙ sai yace "jirani ina zuwa",daga haka ya kutsa kansa tsakar gidan,tsayawa yayi yana ƙare ma tsakar gidan kallo dake ɗauke da ɗakuna biyu kacal.

Fitowa tayi daga ɗakin Nenne da kwanon da suka ci abinci,duk da da ƙyar Nenne taci kaɗan, idanunta duk sun kumbura saboda kukan da tai tayi,
"wayyo Allah na!" ta faɗa tana ƙoƙarin komawa ɗakin da sauri ya riƙe hannunta yana faɗin "ke nine,babu wanda zan aiko ne shiya sa na shigo, abokinki ne".

Tsayawa tayi da zille zillen da takeyi tana kallonsa, sai kuma tace

"mai ya kawoka gidanmu"

Tsura mata ido yayi yana kallonta,yadda idonta ya kumbura,duk da babu wadataccen haske,amma hasken farin wata na bashi daman ganinta ,
"me ya sameki,baki zo ba,nayi ta jiranki"

Kuka ta fashe da shi tana faÉ—in "Nenne ne batada lafiya"

"Ok stop crying, zata samu lafiya, me ya sameta"

Nima ban saniba,tunjiya take wani irin numfashi,É—azu har aman jini tayi"

"Subhanallahi"muje na ganta

Da sauri tace "ah ah.... " Bai saurari me zatace ba ya nufi É—akin da ya ga ta fito,da sauri tabi bayansa.

Akwance suka samu Nenne sai numfashi take yi da ƙyar,da sauri ya ƙara sa wajenta ya durƙusa kusa da ita yana faɗin

"sannu mama"

Kallonshi tayi a wahale,sai kuma ta juya ta kalli Noor,da sauri ta ƙaraso wajen kafin ma Nenne tace komai ta fara faɗin,

"Nenne baƙo ne daga birni ya zo,shine yace in nuna masa gari, to shine yanzu da yaji baki da lafiya,yazo ya gaishe ki".

Kallonsa Nenne tayi,sai kuma ta ƙura masa ido,kallon shi takeyi kamar wanda takeso ta gano wani abu,sai kuma tace

"nagode"

"Allah ya ƙara lafiya," ameen tace a hankali
Yana ƙoƙarin miƙewa yaji ta riƙe hannunsa sai kuma tace "Noor ɗan bamu guri"
Cike da mamaki, Noor tace "Nenne.."

Kallonta yayi yace "kije mana" kamar bazata fita ba sai kuma ta juya a sanyaye ta bar É—akin, kwanon da ta yar a tsakar gida ta É—auka ta kai kitchen, ta fito ta zauna tayi shiru,tana tunanin wani magana Nenne zatayi da shi.

Yakai minti fiye da 20 sannan ya fito a É—akin,idanunshi sun kaÉ—a sunyi jajir.

Da sauri ta tashi ta ƙara so inda yake bai tsayaba,sannan bai kalli inda take ba, yayi hanyar fita a gidan,tsayawa kawai tayi tana kallonsa, to me Nenne ta ce masa.

Har ya kai ƙofa,sai kuma ya dakata yace "gobe ku shirya zamuje asibiti a cikin gari", daga haka ya fice.

Tsayawa tayi tana bin hanyar da ya bi da kallo, ganin tsayuwar bazata fishsheta ba ya sa ta koma É—akin,a kwance ta samu Nenne, idanunta a lumshe ta zauna a gefenta tana kallonta.

Tunda ya koma gida,hankalinsa ya kasa kwanciya, miƙewa yayi ya nufi ɗakin Taufeeƙ,ya samu har yayi bacci, tashinsa yayi,da sauri ya miƙe yana mutsuka idanu ahankali yace

"Sir is everything ok"

A hankali yace
"we will be leaving tomorrow, so ka shirya"

da mamaki yake kallonsa amma bai basa daman magana ba ya fice a É—akin.

Cikin dare jikin Nenne ya tsananta, gashi ta ƙi bari Noor tayi Nesa da ita,ƙarfe 3 daidai na asuba Nenne ta cika, da kalmar shahada a bakinta, tana riƙe da hannun Noor.

Tashin hankali da ba'a sa masa rana.

Mafarin ƙaddara🤗
Maimoon#

💖*ABNUR*💖

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *8*

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,tashin hankali wanda ba'a saka mata rana.

Sam Noor Bata fahimci cewa Nenne rai yayi halinsa ba, ganin jikinta ya saki,sannan ta daina motsi,sai ta matso kusa da ita, tana faÉ—in

"Nenne kinji sauƙi ne!?,Nenne kiyi haƙuri da sassafe zamu tafi asibiti,wannan da ya zo ya gaishe ki,yace zamu je asibiti,insha Allahu zaki samu lafiya.

Jin Nenne bata amsa ba,sannan bata motsa ba,yasa hankalinta sake tashi,kukan ta ya ƙaru,

da sauri ta kama hannuwan Nenne duka biyu ta riƙe ƙam,tana kuka kamar ranta zai bar gangar jikinta,girgizata ta shiga yi tana cigaba da kiran "Nenne na ki tashi,Nenne ki taimaka min,ki tashi,idan baki tashi ba nima mutuwa zanyi.

Wani tunani da yazo ranta, ya sa tayi sauran miƙewa ta fice a ɗakin da sauri.

Ruwa ta É—ebo ta dawo da sauri tana shafawa Nenne,a tunaninta ko dogon suma tayi,but har lokacin Nenne bata motsa ba.

Wani kukan ta sake fashe wa dashi da sauri ta miƙe,fice a gidan,har lokacin kuka take.

Gidan Malam Habu,wanda yake maƙwabtansu ta shiga bugawa, duk da dare yayi amma ko tsoro bata ji, dan kusan asuba ne ma a lokacin.

Ta ɗan jima tana bugawa, babu ƙaƙƙautawa, kafin Malam Habu,ya buɗe ƴar langa langa kofar yana faɗin "waye ne da talatainin daren nan"

Cikin kuka sosai tace "Baba Noor ce".

"Ha'a Noor lafiya da darennan me ya faru kike kuka"

"Nenne, ce bata da lafiya, kuma ta ma suma,bata ko motsi, dan Allah ka taimaka min.

Da sauri Malam Habu yace "subhanallahi muje muga abinda zamu iya yi".

komawa ciki yayi da sauri ya taso matarsa Jummai, suka fito tare.

A tsakar gida ta tsaya ta kasa ƙarasawa ɗakin,tana jin malam habu da matarsa suna ta salati,
kasa gasgata abinda zuciyar ta ke sanar da ita tayi, a hankali tayi baya ta jingina da bango, tana maimata ma kanta

"Nenne bata mutuba, batada lafiya kuma zata ji sauƙi".

Jummai ta fito a É—akin idon ta cike da hawaye,
gurin Noor ta ƙara sa ta dafa ta tana faɗin"Allah ya baki haƙurin rashi Noor, Nenne rai yayi halinsa,Allah da ya fiki sonta ya karɓi abinsa"

Ai bata ƙarasa jin abinda take sanar da ita ba ta yanke jiki ta faɗi a wajen sumammiya.

Ƙarfe 7:00 na safe ya fito cikin shirinsa, Taufeeƙ na biye da shi a baya,
bayan ya fitar musu da duk wani abu nasu trolley yake ja,yayinda shi kuma TaufeeÆ™ yake É—auke da jaka na matafiya da kuma jakan kayan cameras É—in su,

A hankali yake tafiyar amma duk zuciyarsa a cunkushe,

"do you really think this is a good idea!?, is this the right step daya kamata ka É—auka!?"

abinda zuciyarsa ke tambayan sa kenan.

Da sauri ya furta

"wannan shine right step É—in da ya kamata na É—auka, idan ba haka I will regret it for the rest of my life"

Da mamaki TaufeeÆ™ ya kalleshi yace

"Sir Are You ok"

Sai lokacin ya gane ashe a bayyane yayi maganar
"i am alright" ya faɗa a taƙaice yana cigaba da tafiya.
Chapter 7 · 0% Book details