← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 28

Sashe 10

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da wuri suka ɗauki hanyan Abuja, duk da baiyi niyyan tafiya a mota ba amma ganin bata taɓa shiga jirgi ba ya sa yace su tafi a mota kawai,

Tunda suka iso garin Abuja take kalle kalle, yau gata a birnin da take buri kullum, amma ba tare da Nennen ta ba, a take taji wasu hawaye na shirin zubo mata,kallonta yayi ta gefe, a zuciyarsa yana faÉ—in
"wai Ni wannan yarinyar hawayenta anya bazai ƙareba kuwa".

girgiza kai kawai yayi ya juyar da kansa yana kallon window É—in shima.

Tun kafin Taufeeƙ ya gama parking motar,bodyguards ɗin suka ƙara so da sauri, su ka tsaya, da sauri suka buɗe masa ƙofa, suna gaishe shi, a taƙaice ya amsa musu yayi shigewar sa ciki,

Ganin basu lura da ita ba yasa Taufeeƙ ƙarasawa ya buɗe mata ƙofan yana murmushi dan yadda yaganta duk a tsorace.

Ƙafafuwan ta zuro a hankali,waɗanda suke cikin flat shoes Wanda ya kawo mata tare da kayan jikinta,a hankali ta ƙarasa fitowa tana kallon ƙatoton mansion ɗin da aka kawota, a hankali take bin bayan Taufeeƙ ɗin har cikin main parlour na gidan,inda bodyguards suka riga suka shigo musu da kayayyakin su.

Da gudu Asabe da Amina suka fito a kitchen ɗin suna rige rigen ƙarasowa wajen Taufeeƙ,kallonsu yayi yana murmushi yace

" kukuma Fah "

da sauri Amina tace

" Sir TaufeeÆ™ yanaga kun dawo da wuri, Ni wallahi ban ma san ran dawowan ku nan da wata uku Bama wallahi"

ta faÉ—a tana kallon Noor ta ke tsaye kawai tana kallonsu"

"Sai kuma kika ganmu koh"
TaufeeÆ™ ya faÉ—a yana hawa da kayan Sir Zannur steps É—in.

sai da ya kai ya dawo ya É—au sauran sannan ya kalli Asabe da Amina yace

"ga baƙuwa,ku gyara mata ɗaki a sama, anan zata zauna and ku kula da ita sosai fah, idan ba haka ba ku da Sir Ni dai babu ruwana"

ya faÉ—a da sigar tsokana yana haurawa saman,

Har rige rigen ƙarasowa wajenta sukeyi, Asabe tace "sannunki da zuwa baƙuwar Sir" ta faɗa tana murmushi.

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *10*

Ita dai kallon su kawai takeyi,ba tare da tace uffan ba,
kallon juna suka yi sannan suka maida kallonsu gareta, Amina tace "Ni sunana Amina,wannan kuma......"

"Asabe". Asabe ta faÉ—a tana tarar numfashin Amina.

Murmushi kawai tayi musu ba tace komai ba.

Taufeeƙ da ke sauƙowa ya kallesu yace

"wai kun san waye ce ita kuwa kuka ajiyeta a tsaye, nace ku kaita É—akin sama, baku Kaita ba kun tsaya kuna cika ta da surutu koh"

ya faɗa yana ƙarasa sauƙowa

"Sir Taufeeƙ dan Allah a ina kuka samu wannan kyakkyawar yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa,wallahi har ta shiga raina"

cewar Amina tana murmushi.

"Matar Sir Zannur ce"

ya faɗa a taƙaice yana nufan ƙofan falon dan dai baya son tambayoyi,
dan ya riga ya san halin su Asabe.

a ranshi yana ayyana irin zaman da za'a yi a cikin gidan tsakanin Sir da kuma Madam É—in sa.

"Matar Sir ce", maganar daya doki ƙwaƙwalwar Yasira kenan wacce ke fitowa daga kitchen,dan yiwa su Amina magana suje su cigaba da aikinsu,

kasa ƙarasowa falon tayi daga bakin kitchen ɗin ta ƙura ma Noor idanu, wacce ke tsaye duk tsayuwar ma ta isheta.

Bata gama tantance
abinda kunnuwanta suka jiyo mata ba taji Muryar su Asabe dake ta murna kamar waÉ—anda aka ma bushara da aikin hajji

Asabe na faÉ—in "Sannu da zuwa Madam, wai da gaske ke matar Sir ce,ya ilahi,ina zansa kaina"

ta faÉ—a tana sake
kwashewa da dariya kamar taɓaɓɓiya,

Duk yadda take jin zuciyarta sai da ta É—an murmusa ba tare da ta shirya Ba.

Amina tace"mun shiga uku, matar gida muka bari a tsaye, Asabe bazaki nuna mata É—akin ba" ta faÉ—a cikin rashin sanin abinyi itama murnar ta kasa barinta.

A hankali tace"Sunana Noor, kuma ina so in yi sallah, a ina zanyi"

ta faÉ—a tana murmushi

Da sauri Dukansu suka fara rige rigen yi mata jagora zuwa É—akinta,

tsaf ɗakin yake, hakan yasa suka barta tayi sallah,suka sauƙo suna cigaba da hirar abin,

Asabe tace"anya Sir TaufeeÆ™ ba wasa yake mana ba kuwa, ya za'a yi Sir yayi aure babu sanarwa babu komai"

Amina tace wallahi kamar kin shiga zuciyata,ko Maami ma bazata yarda da wannan auren ba".

"Nima haka nake gani" cewar Asabe suna ƙara sa sauƙo wa daga matakalan.

Hango Yasira da sukayi yasa suka canza hirar

Asabe ta É—aga murya tana faÉ—in"wallahi Fah matar Sir kyakkyawa, daga gani zatayi hankali"

Amina ta karɓe "kuma wallahi ba ƙaramin dacewa sukayi ba, Allah dai ya barsu tare ya tsole idon maƙiya"

ta faÉ—a tana kallon gefe.

Har suka wuce ta bata ce musu komai ba, zuciyarta banda tafasa babu abinda takeyi.

"ya za'a kayi min haka?, ya za'a yi ka auri wata ba Ni ba?, kai kaÉ—ai na tanadawa kaina, kai nawa ne Ni kaÉ—ai,
dan Ni kaɗai aka halicceka Sir Zannur, bazan taɓa yarda ka zauna da kowace mace idan ba Ni ba,sai dai bayan raina" ta ƙara sa faɗa kamar mai shirin zarewa.

Juyawa tayi a fusace ta wuce su Amina a kitchen ta bi ta ƙofar baya ta tafi ɓangaren su, tana tunanin yadda zata ɓullo ma lamarin idan har ya kasance gaskiya ne.

Asabe da Amina suka bita da kallo sannan suka ƙyalƙyale da dariya ƙasa ƙasa suna faɗin "a sauƙa lafiya".

Tunda suka fita suka barta, ta tsaya tana ƙarema ɗakin kallo,
nan É—in É—akin ta ne kenan?, ita ce yau zatayi rayuwa a nan ba tare da Nennen ta ba, tabbas mutuwa bata barin wani dan wani yaji daÉ—i,idan ba haka ba da Nenne bazata mutu ta barta ba,

hawayen idonta ta share sannan ta juya ta nufi ƙofan da ta gani wanda tafi tunanin shine banɗaki, shiga tayi ta tsaya tana kallon toilet ɗin.
yafi na hotel ɗin da suka sauƙa a Kaduna kyau da girma da tsaruwa nesa ba kusa ba,
bata wani sha wahalan yin amfani da toilet É—inba kasancewar ta gane tun na hotel É—in hotel É—in, sai da ta yi wanka ta wanke tsefeffen gashin kanta da shampoos É—in da ta gani a toilet É—in,sannan ta É—auro alwala, sai kuma ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka,

bathtub ta gani kala kala a banÉ—akin,haka kawai taji a jikinta shi ake sakawa idan anyi wanka, murmushi tayi ta jawo guda É—aya mai kalar sky blue tana kallo,

sai da ta saka sannan ta sake jiƙaƙƙen gashin kanta a bayanta, ya sauƙa har kusan ƙugunta duk da a jiƙe yake.

A hankali ta buɗe ƙofan banɗakin ta fito tana rarraba idanu,
da sauri ta ƙara sa wajen ƙofa ta murza key tana sauƙe ajiyar zuciya,a fili ta furta

"hmm kawai sai wani ya shigo ya ganni a haka ai da kunya ta kasheni"

sake kallon jikinta tayi sai ta rufe fuskarta da hannunta tana É—an dariya,

Duk abinda takeyi yana zaune yana kallonta, a cikin laptop É—in sa, da yayi connecting da duka cctv cameras na gidan,murmushi kawai yayi ganin yadda ta rufe fuskarta a fili ya furta

"silly girl"

Amma a cikin ransa yana mamakin kyaun yarinyar ga ta da gashi abinda yake matuƙar so a wajen mace,
sai dai shi baya ganin har gaban abada zai taɓa iya zaman aure da ita.

rufe laptop ɗin yayi ya miƙe yana kai komo a ɗakin, babban damuwar sa a yanzu bai wuce yadda zai sanar da Maami da Abbu zancennan ba,

waya ya É—auka yayi dialling Numbern TaufeeÆ™ Yana É—agawa yace

" ina so zuwa gobe ka kai yarinyar can ka yi mata siyayyan kayan anfaninta and banaso ta nemi komai ta rasa i hope you understand"

daga ɗayan ɓangaren Taufeeƙ ya amsa da

"Yes Sir"

katse wayan yayi sannan yayi cilli dashi a kan gado yana kai hannunsa ya ya mutsa lallausan yalwataccen sumarsa, a hankali ya furta

"everything will be alright soon".

juyawa yayi ya fice a É—akin gaba É—aya ba tare da ya É—au wayan ba.

Knocking ɗin da taji a ƙofar ɗakin ya sata saurin mayar da kayan da ta cire, ta ƙara sa bakin ƙofan tana faɗin

"waye ne?"

jin shiru ya sa ta ƙara sawa, ta murda ƙofan ta buɗe tana kallon wanda ke bakin ƙofar,

kallon kallo suka shigayi kafin tayi murmushi tana faÉ—in

"bismilla"

daga haka ta koma ciki

Sai da Yasira ta haɗiye wani mugun yawu kafin ta yi ƙarfin halin ƙarasawa ciki tana ƙoƙarin yin abin da ya kawota ba tare da ta kwafsa ba.

Da murmushi ta dube ta tana faÉ—in

"sannunki da zuwa, Sunana Yasira ni ce in charge na kitchen É—in gidan nan gaba É—aya"

ta ƙarasa tana ƙura ma Noor ɗin ido

A hankali tace

"nagode".

É—an shiru Yasira tayi sai kuma tace ko zan iya sanin ke kuma wacece ta faÉ—a tana sake kallonta.

"Bakida hurumin sannin wace ce ita!"

da sauri dukkansu suka juya suna kallon mai magana,
da mamakin Noor ke kallonsa yayinda Yasira cikin sauri ta shiga faÉ—in

"Sorry Sir i just came to welcome her,am sorry Sir"

ta faÉ—a tana raba idanu
Bai ce mata komai ba yaƙarasa cikin ɗakin,

zuwa lokacin ƙamshin turarensa na SHUMUKH ya gama cika ɗakin,

fuskarsa babu yabo babu fallasa yace

"ina so ki haÉ—a min duka staff É—in da ke cikin gidannan by 6 o'clock",

"Okay Sir" ta faÉ—a da sauri.

"You may leave" ya faÉ—a ba tare ta ya sake kallon inda take ba.

Da sauri ta fice a É—akin tana waiwayensa.

Sunkuyar da kanta Noor tayi tana wasa da yatsunta, zuciyar ta na wani irin bugu,
dan gaba É—aya ya canza mata daga wanda ta sani a da.

Taku biyu ya ƙara yana kallonta yace

" ƙarfe 6 yayi miki a falon ƙasa, i hope you understand!?.

Girgiza kai kawai tayi batare da tace komai ba.
Chapter 10 · 0% Book details