← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 28

Sashe 12

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya buÉ—e idanunsa da har sun fara canza kala daga farare tass zuwa ja,

hannunsa ya sa ya shafa sumarsa,sannan ya gyara kwanciyarsa a kan gadon yana sauƙe numfashi.

Ƙarar wayar sa yasa ya janyota a hankali yana ɗagawa

"Habibi me ya ke damunka ne,what's keeping you this busy?"

Abinda Maami ta fara faÉ—i kenan.

Cikin kwantacciyar murya mai nuna akwai abinda ke damunsa yace
"Maami na!"

take Maami ta rikice ta soma jero masa tambayoyi

"son are you alright?,am sure you are not, me ya faru? faÉ—a ma Maami kaji, ko nazo Nigeria?,"

Cikin son ya kwantar mata da hankali yace

"Maami, babu komai fa, but akwai wani magana da nake so nayi dake, a very serious one"

Ya faÉ—a yana lumshe idanunsa

"Ina jinka Habibi tell me"

"Ba ta waya ba,zanzo Dubai"

When?

"Next week"

"Allah ya kaimu,but you are sure babu abinda ya sameka koh"

"Maaamiiiii"

Ya faÉ—a yana jan sunan,

Dariya tayi kafin a hankali tace

"Habibi bazaka gane ba,I won't be able to do without you, you are my life Habibi".

"I know Maami, and you are mine too,Abbu ya dawo daga ukraine?"

Ya tambaya da kulawa,

"Bai dawo ba but Gobe insha Allah Zai dawo"

"Ok Allah ya kaimu"

"Ameen"

"I guess I will hang up now Habibi, we will talk later okay"

"Uhm" ya faɗa ƙasa ƙasa

"Okay bye Maami loves you" Bata jira amsar sa ba ta katse wayar ta.

Ajiye wayar yayi yana miƙewa dan tafiya masallaci.

Yadda suka yi tagumi suka ƙura masa idanu yasa Taufeeƙ ɗan murmushi yana kallon su Amina yace

"kai haba duk kallon na me ne ne haka"

Cire tagumin Asabe tayi tana faÉ—in "to Sir TaufeeÆ™ ba dole ba, tun É—azu ka kasa faÉ—a mana maganan da ka kiramu a kai, kuma kasan waccar jarababbiyar yanzu zata fara nemanmu a kitchen".

Murmushi yayi sannan ya ce

"okay tom kuna jina"
suka amsa da

"eh" kafin ya cigaba da magana

Sai da ya faÉ—a musu duk abinda ya sani ga me da auren Sir Zannur kafin ya É—aura da faÉ—in

"Kunsan me yasa na faÉ—a muku"

Girgiza masa kai sukayi mamaki ya ƙi sake su,

"Ok,so nake ku ja ta a jiki, ku nuna mata komai,kunga Ni namiji ne, sannan bana tunanin Sir zai nuna mata komai,dan Allah kar ku bari tayi kaÉ—aici,

and kamar yadda kuka sani, mu biyar kaɗai muka sani banda ƴan ƙauyensu, please Kar ku faɗa ma kowa matar Sir ce kunji?"

Asabe ce ta sauƙe ajiyar zuciya tana faɗin "ai kuwa akwai shidan mu wallahi".

TaufeeÆ™ yace "waye?"

Waye kuwa banda Yasira itama tasan Matar Sir ce, dan sanda ka faÉ—a mana,ina kyautata zaton taji.

Shiru yayi sai kuma yace babu damuwa, na san yadda zanyi da lamarinta ku dai kuyi abinda nace .

"Baka da damuwa Sir"suka faÉ—a a tare.

Miƙewa yayi yace "I know I can count on you both nagode sosai"

Haba haba Sir TaufeeÆ™, ya kana haka, ai duk taimakon kai ne ko ba haka ba Asabe?

"Haka take"Asabe ta faÉ—a tana dariya.

Shi dai bai sake cewa komai ba ya juya ya bar garden É—in,

suma miƙewa sukayi suka bar garden ɗin suna jinjina maganan.

Yasira dake laɓe ta fito tana murmushi, a fili ta furta,

"Sir Zannur zan tabbatar da na mallakeka, kuma wannan shine mataki na farko da zan mallakeka, tabbass na san yanda zanyi anfani da labarin nan in samu abinda nake so".

daga haka ita ma tabi bayansu Amina dan dama tun fitowarsu ta biyo su dan tace musu su koma bakin aiki amma ganin inda suka nufa yasa ta bisu taga me zasuyi a wajen.

Washegari kamar yadda Zannur yayi umurni haka Taufeeƙ ya ɗauke ta, ya kaita sukayi shopping ɗin duk abinda zata ɓuƙata,

kama daga kayan sakawa,zuwan kayan shafa,da ma duk wasu kayan anfani na mata.

ganin bata san wasu abubuwan ba yasa ya haÉ—ata da ma'aikatan wajen kasancewar babban supermarket ne na manya, yasa matar ta zage ta kwasa mata komai kamar mahaukaciya,

and daÉ—in daÉ—awa ce mata da TaufeeÆ™ yayi she is important to Sir Zannur, kuma shi ya turo su,

ai kuwa sun sha shopping kamar na hauka har yamma tukun suka dawo gida.

Su Amina su suka shirya mata komai,

sannan suka nuna mata yadda ake anfani da komai, duk da yawanci kafin ma su faÉ—a take karantawa ta gane miye ne sai dai a nuna mata yadda ake anfani da shi.

Haka suka saka ta, ta shirya suka zagaya da ita gaba É—aya gidan,

a ranar ta sha mamaki ganin irin girman gidan,wani irin mutum ne shi kuwa? tambayar da ta yi ta yi ma kanta kenan.

Zuwa yanzu ta gama sabawa da gidan dan kuwa kwananta shida kenan,amma har ranan bata sake sakasa a ido ba,

TaufeeÆ™ ma sai jifa jifa take ganinsa,

su Amina sune abokan hirarta, har kitchen take zuwa ta zauna, suna hirarsu,

Yasira kam tsakaninta da ita gaisuwa,idan ta gaisheta ta amsa shikenan babu abinda ke sake haÉ—ata da ita.

What?
Maami ta faɗa ta ƙarfi tana miƙewa, me kike nufi?, You must be out of your senses, do you want to tell me Habibi yayi aure ba tare da nasani ba!?,wannan ma ai maganar banzace,

Shiru tayi tana sauraron mai maganan daga haka ta katse wayanta tana kallon farin balaraben dake gefenta da laptop akan cinyarsa yana operating,
idanunsa sanye da fararen medicated glasses.

Abbu, kanajin wata maganar banza, wallahi i won't take it,I am leaving for Nigeria tomorrow morning.

Ta faÉ—a zama kusa dashi,É—agowa yayi ya dubeta sannan cikin kulawa yace

"What happened Hilwa!"

Wai Habibi yayi aure,ake faɗamin, zancen banza, zancen hofi,Ni nasan hakan bazata taɓa faruwa ba da amincewata ba, saboda haka zan tafi Nigeria,dama ina so inga Habibi, jikina Yana bani Yana cikin wata damuwa.

Janyota yayi yana manna mata kiss a forehead kafin yace

"ok but ki kwantar da hankalinki,Zannur yana lafiya,and bazai yi aure bada yardar ki ba, so now smile"

Murmushi ne ya suɓuce mata,ya shafa kanta yana murmushin shima,shigewa jikinsa tayi tana faɗin

"Abbu what if da gaske yayi auren?,kasan Habibi Yana da Zurfin ciki.

"Ki kwantar da hankalinki everything that happens is for the best okay,zan sa ayi miki booking flight É—in don't worry".

Ta gyaɗa masa kai tana sake kwantar da kanta a ƙirjinsa, tana tunanin Allah yasa ba da gaske bane dan kuwa bazata taɓa yadda da hakan ba.

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *12*

_Washegari_

Tun safe Zannur yake jinsa wani iri,ya kasa fita,ko nan da can.

ganin ya kasa nutsuwa
ya sa ya jawo laptop É—insa,yana kallon ta,
yadda ta shige cikin bargo ta rufe har kanta.

sai kuma ya ja tsaki yana faÉ—in,

"mutum yayi ta bacci tun safe".

Yana ƙoƙarin rufe laptop ɗin yaga tayi miƙa tana yaye bargon daga jikinta,
sai ya fasa rufewa, ya cigaba da kallon ta,

miƙewa tayi zaune a kan gadon tana mutsuka idanunta,sai kuma ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa, slippers ɗinta ta sanya kafin ta miƙe,

har ta shige banɗaki,kafin ya sauƙe ajiyar zuciya yana shafa sumar kansa a fili ya furta

"Ke amana tace, saboda haka dole ne in sa ido akanki"

sai kuma yayi murmushi yana rufe laptop É—in, dan har yaji mood É—insa ya canja, yana jin sa cikin nishaÉ—i,
duk da wani sashi na zuciyar sa na fargaba wanda bai san fargabar miye ba.

Agogo ya kalla, ganin ƙarfe goma saura minti goma, ya sashi miƙewa shima ya wuce toilet.

sai da yayi daɗe a banɗakin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa,
cikin abinda bai fi 30 minutes ya shirya tsaf cikin riga da wando na *_Louis Vuitton_* Agogo ya sanya da pcap a kansa duka na *_Louis Vuitton_* sannan ya feshe jikinsa da mayen turarensa na *_shumukh_* slippers ya sa a ƙafan sa shima na *_Louis Vuitton_* sannan ya koma gefen gadon ya zauna,ya jawo laptop ɗinsa Yana dubawa, dan baya tunanin zai fita ko ina.

Iska da fara sauƙan yayyafi ya shashi miƙewa yana leƙa waje,
ai kuwa sai ruwa ya tsuge kamar da bakin ƙwarya, saurin matsawa yayi daga jikin window,aransa yana tunani yadda za'a yi wasu da basu san ciwon kansu ba har su bari ruwa ya jiƙasu idan ba tsautsayi ba.

Komawa yayi ya zauna ya sake jawo laptop ɗin,kai tsaye ɗakinta ya duba ganin bata ciki yasa yayi ƙwafa yana kashe laptop din gabaki ɗaya, ya miƙe ya fice a daƙin,

Ɗakin hoto ya shiga yana ƙarasawa ya ɗauki Camera,saboda yana son yin capturing ruwan yanda yake sauƙa,

a hankali ya yaye labulen balcony É—in yana saka Camera É—in a idanunsa,iskan ruwan na kaÉ—awa yana sa rigar jikinsa haÉ—ewa da jikinsa .

Abinda ya gani ta cikin Cameran ya sashi saurin janyewa daga idanunsa yana ƙura mata idanu,

tabbass ba gizo idanunsa ke masa ba, ita É—ince a cikin ruwan sama, baki a sake yake kallonta, yanda take juyi tana nishadi a cikin ruwan,

shagala yayi da kallonta, tundaga sama har ƙasa yake yake kallonta,

riga da wando ne a jikinta masu laushi na *_Dior_* kanta ta saka band Wanda ya Bama gashinta daman sauƙa ta bayanta, *_Stuart weitzman Cinderella slippers_* ne a fararen ƙafafuwan ta,

yanda take dariya ya sa shi mayarda Cameran idanunsa ba tare da ya sani ba.

hotuna yayi ta mata ba tare da tasan ma yana gun ba,Dan kuwa babu wanda yake zuwa ta bayan balcony ɗin,shiyasa ma ta je can dan bazata iya ƙin shiga ruwa ba.

Ajiye Camera É—in yayi a hankali ya fice a É—akin.

Hannuwanta ta tara a ruwan ya cika ta watsa a fuskarta,ta sake tara hannun tana shirin watsawa taji an riƙe hannuwan nata,

a tsorace ta ɗago, idanunta suka shige cikin nasa,fuskarsa babu alamar wasa,gaba ɗaya ya gama jiƙe jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ta sake bayyana saboda yadda ruwan yasa kayan ya manne da ƙirjinsa,

Kallonta kawai yakeyi ba tare da ya ce komai ba, da sauri ta ƙwace hannunta tana shirin barin wajen dan batasan sam zaizo wajenba,

ita bata mayi zaton yana gidan ba,dan rabon ta da shi tun ranan da ya kawota,
Chapter 12 · 0% Book details