← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 28

Sashe 17

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiyar minti talatin ne zuwa asibiti, amma a minti sha biyar ya isa, da sauri ya fito, ya ma rasa mai zai yi, cikin asibitin ya nufa har da gudunsa, ita dai tana, zaune a motan, taga sun fito daga cikin asibitin tare da nurses da gado.

Buɗe motan tayi ta fito, nurses ɗin suka ƙaraso, suka ciro Taufeeƙ aka kwantar da shi a gadon suka nufi cikin asibitin dashi.

Daƙyar Zannur ya samu suka yi attending ɗinsa, kasancewar sun sansa, dan cewa sukayi sai an saka police a cikin lamarin.

Tunda aka shiga da TaufeeÆ™ É—akin, yake Safa da marwa ya gagara, zama, ita kanta ta gagara daina kuka.

A hankali ta ƙara so inda yake tana faɗin

"Kayi haƙuri insha Allahu zai samu lafiya"

Wani irin kallo da ya watsa mata ya sata saurin yin baya, dan bata taɓa ganin yayi ma wani irinshi ba, bare kuma ita.

Cije lips É—insa, yayi, amma ya kasa cewa komai,

Likitan da ya fito ne ya sashi, saurin ƙarasawa yana faɗin

"Doctor ya É—an uwa na yake"
Dafa shi Doctor É—in yayi sai kuma ya girgiza kai kawai"

Da sauri ya sha gaban doctor ɗin dake ƙoƙarin wucewa yace

"tell me is he alive"
Shiru doctor É—in yayi sai kuma yace

"He is alive, but bayan nan babu abinda zan iya ce maka saboda cause he is in a very critical condition, dan he may slip into a coma"

Daga haka ya juya ya bar wajen.

Baya yayi jikinsa na wani irin rawa, sai lokacin yaji hawaye na sauƙa akan fuskarsa.......

Maimoon#

*💖*ABNUR💖**

*By Maimoon*

*Elegant online writers*📚📖

*Free book*

*Page 16*

Itama durƙushe wa tayi a wajen tana kuka,
ta ma rasa tunanin me zatayi, wani irin tsana ne da har zai sa mutum yayi ƙoƙarin kashe mutum ɗan uwansa, wannan wani irin ƙaddara ce da ta faɗa musu.

A hankali ta ɗago idanunta, tana kallonsa, yadda ya samu guri can gefe ya zauna, yayi shiru, kai tsaye bazaka taɓa gane me ya ke tunani ba, sam sai taji batason ganinsa a haka, zuciyarta bazata iya ɗauka ba.

A hankali ta nufe sa, har tazo dab dashi bai ɗago ba, kansa a sunkuye yake, gashin kansa ya sauƙo ya rufe fuskarsa, saboda sunkuyar da kan da yayi.

Tsugunnawa tayi dai-dai ƙafafunsa, ta lalubo hannuwansa ta riƙe gam.

Sai lokacin ya ɗago kansa, yana sauƙe idanuwansa a kanta, yadda idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir, har sai da gabanta ya faɗi, amma sai ta dake.

Cikin ido take kallonsa, kafin a hankali ta soma magana, cikin muryarta mai matuƙar sanyi.

"Dan Allah kayi haƙuri, ka zama musulmin na ƙwarai, mai yarda da ƙaddara, yau koda ace Taufeeƙ ya mutu ne, babu yadda muka iya, saboda Allah ya riga ya rubuta kwanansa ya ƙare, bare yana raye, kuma insha Allahu zai farfaɗo, kamar yau zai tashi akan ƙafafuwan sa, nasan yana da muhimmanci a wajenka, but dan Allah ka masa addu'a, kar ka kasance cikin waɗanda basa komawa ga Allah idan masifa ta samesu, kuma na yarda da kai, ɗari bisa ɗari, zaka nemo duk wanda ya aikata masa hakan kuma ka hukunta shi, hukuncin da ya dace dashi."

A hankali hawayen da ta ke ta ƙoƙarin dannewa, ya sauƙo a kan fuskarta, dan ita kanta ba juriyar ce da ita ba, but ganin haalin da yake ciki yasa dole ta danne nata raunin.

Kallonta kawai yakeyi, ya kasa cewa komai, a hankali ya sa hannunsa yana share mata hawayen da ya zubo a samman kyakkyawar fuskarta, sai kuma ya ɗagota gabaki ɗaya daga tsugunnen da tayi a gabansa, kusa da shi ya zaunar da ita, yana sauƙe numfashi, ɗago idanunta tayi, suka haɗa ido dashi har lokacin hannuwansu na cikin na juna, a hankali kuma ya kwantar da kansa a kan kafaɗar ta, yana ajiyar zuciya,

Zare hannunta tayi daga nasa, ta maida a kansa tana shafa gashin, gyara masa sumar tayi, tana cigaba da shafa kansa, tana jin zuciyarta na ƙara tsananta bugu.

Har kusan magrib, suna zaune a haka, sai lokacin ya ɗago kansa, gani yayi ta jingina bayanta da kujeran, ta lumshe ido, alamar bacci ya ɗauke ta, tashi yayi ƙoƙarin yi, amma sai yaji ta sake damƙe dayan hanunsa da ke cikin nata, bai san sanda yayi murmushi ba, yana sake kallonta, irin kallon da bai taɓa nutsuwa yayi mata ba, kallo yake mata ma ƙurilla.

Juyar da kanta tayi tana ɓata fuska dan sam baccin kawai ya ɗauke ta ne, amma ba dan tana jin ɗaɗinsa ba, lips ɗin ta ta motsa a hankali, kamar zatayi magana, sai kuma ta maida su tana tsotsan na ƙasan, ƙuri yayi ma lips ɗin nata da ido, yana kallonsu, sai kuma yayi saurin juyar da kansa, yana shafa sumarsa, wacce ta ke ɗabi'arsa.

A hankali ta buɗe idanunta, sai kuma ta ɓata fuska tana gyara zamanta akan kujeran, motsinta da yaji, yasa ya juyo yana kallonta, sai kuma ya mata murmushi yana faɗin,

"Zaki tafi gida yanzu!"

Cikin innocent and calm voice É—inta tace " tare zamu tafi?"

Ta faÉ—a da sigar tambaya, kwaikwayon yanda tayi maganan yayi yana faÉ—in

"ke kaÉ—ai zaki tafi"

Sai da ya ɗan nisa kafin ya sake damƙe hannunta yana faɗin

"bazan iya tafiya na barshi ba, Taufeeƙ yana cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, zan iya cewa he is my only friend, saboda bani da aboki, but ya fiye min kowani irin aboki, for the past 16 years, da nake tare dashi, bai taɓa bani ƙofar da zanyi complain ba, he was with me tun Ƙanwarsa Yasira tana da shekara biyar, shine ƙadai gatan ta, duk da kasancewar ba ciki ɗaya suka fito ba, but sukaɗai suka taso, cikin maraici, da rashin gata,
a lokacin babansu was a drunkard, mashayin giya ne, wanda bai damu da iyalinsa ba, hakan yasa iyayensu mata suka bar gidan.
TaufeeÆ™ Yana son Yasira sosai hakan yasa da ya yanke shawarar barin gida, ya taho da ita, dan yana ganin she can't handle all that alone.

tunda na haɗu dashi nake matuƙar jinsa a jikina, saboda mutum ne shi mai amana, Maami kanta tasha faɗa min Taufeeƙ mutum ne in riƙesa, haka zalika Abbu, sai kuma yayi shiru, kallonta ya kuma yi sai kuma kawai ya jawota ya rungumeta sosai a jikinsa, kamar wani zai raba sa da ita, ita ma bata hanashi ba sai ma kwanciya da tayi shiru a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.

Cikin É—acin rai ya cigaba da magana

" bazan taɓa yafewa duk wanda yayi masa haka ba, koda kuwa waye ne shi a wajena, sannan zan gano ko waye ne, kuma zan hukuntasa da mafi raɗaɗin hukunci,"

sai kuma ya sake yin shiru yana sauƙe ajiyar zuciya.

Itama shiru tayi ba tare da tace masa komai ba, tana fatan Allah ya sassauta masa zuciyarsa, ya bashi daman yanke hukunci, cikin nazari, dan idan rai ya ɓaci, hankali gushewa yakeyi.

ÆŠagowa tayi daga jikinsa, tana sake kallonsa tace

" ba zaka tambaye Ni me nakeyi a kusa da TaufeeÆ™ ba "

Da sauri ya juyo yana kallonta, sai kuma ya shiga girgiza mata kansa, ba tare da yace komai ba.

Kuka ta shiga yi a hankali, kafin ta buɗe bakinta tana ƙoƙarin faɗa masa abinda ya kaita Garden ɗin, har ta riski Taufeeƙ a haka

Da sauri ya saka yatsansa a bakinta yana kallon tsakiyar idonta

"Shhhhhh not another word, ko ki faɗa min, ko karki faɗa min, nasan a haka kika samesa, bazaki taɓa koda tunanin kisa ba, bare har ki aikata, i trusted you after so many trials, so baki da buƙatar yi min bayanin komai"

Kallonsa kawai takeyi, itama ta kasa cewa komai.

"Yanzu ki tashi, za'a kaiki gida, nima zan dawo idan na tattauna da Doctor É—in kinji?"

Hawayenta ta share, kafin ta miƙe a hankali tana kallonsa, shima miƙewa yayi, har ta kai ƙofa, sai kuma ta dawo da sauri ta rungume sa, tana sakin sabon kuka

Shafa kanta yayi, yana raÉ—a mata a daidai kunnenta

"everything will be alright, ba ke kika ce in bar damuwa ba"

ÆŠago idanunta da suka kaÉ—a sukayi jaa tayi tana dubansa, sai kuma tayi murmushi tana faÉ—in

" dan Allah ka dawo, zan jiraka, kazo ka faÉ—a min abinda kace zaka faÉ—a min dazu"

Murmushi yayi shima, wanda kana gani kasan a iya fuska ya tsaya,

"kina son in fada miki ne!?"

Gyada kai tayi alamar eh

"To ki jirani komin dare zan faÉ—a miki"

"Do you promise?"

"I do" ya faÉ—a yana sakin hannunta da ke cikin nasa.

A hankali ta juya ta nufi barin wajen duk jikinta a sanyaye.

Da ido kawai ya bita, yana kallon irin baiwar kyau da Allah yayi mata, wanda shi bai taɓa lura ya gani ba sai yau, yanda take tafiya a hankali, cikin sanyi yake kallo har ta fice kafin ya sauƙe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya.

Tana fitowa, da sauri bodyguard É—in dake jiranta, ya fito yana zagawa ya buÉ—e mata motan yana gaisheta, shiga tayi ta zauna, tana kallon compound din asibitin, har suka fice, fuskarta ta juyar daga kallon window É—in, ta mayar tsakanin cinyoyinta, tana sake tunanin wa yake son kashe TaufeeÆ™ a cikin gidan,kuma me ya musu.

Har suka iso ta kasa gano komai, yana yin parking, bata jira ya buÉ—e mata ba, ta buÉ—e motan ta fita, tana tafiya a hankali, a falo ta samu su Asabe, duk idanunsu sunyi jajir saboda kuka, Amina har lokacin kuka takeyi wiwi, suna ganinta suka nufo ta sauri,

"Madam ya jikin Sir TaufeeÆ™"
kasa ce musu komai tayi.

Yasira da ke gefe tana jira a ce mata ya mutu, sai zare ido takeyi, ta kasa nutsuwa, da sauri ta bi Noor da ke ƙoƙarin haurawa sama

"Ma dan Allah ki faÉ—a min halin da yayana yake ciki, shikadai nake dashi, ya mutu ne?"
ta tambaya tana matsar kwalla

Dafa ta Noor tayi sannan tace

"kar ki damu bai mutu ba, kuma insha Allahu bazai mutu ba, yana nan da ransa kuma za'a gano duk wanda ya aikata masa hakan."

Dakatawa tayi da kukan da takeyi, hawayen ya ƙafe jin Taufeeƙ bai mutu ba, batasan sanda ta furta

"Bai mutu ba?" da ƙarfi tana zare ido
Chapter 17 · 0% Book details