← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 28

Sashe 6

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun shigowar ta wajen ya lura da ita, ya tsaya da É—aukan hoton da yakeyi yana kallonta,shi kansa bai san dalilin da yasa yake kallonta ba,samun kansa yayi da É—aukan ta hoto ba tare da ta sani ba,
yayi mata yakai kala uku, kafin ta juyo, karaf idanunta ya shiga nashi,kallonsa tayi taga yana É—aukan ta hoto ai kuwa ta wani murguÉ—a baki ya É—auka a haka,

sai da ya kalli cikin
camera É—in sai ya samu kansa da yin murmushi kawai,bai sake kallonta ba ya cigaba da É—aukan abinda ake yi,

A ƙarshe aka kira ƴanmata,aikuwa ita da ƙawayenta suka shiga,waƙa aka saka musu na mutan ƙauye,suka hau yin rawar a nutse, a hankali, baya ya koma yana kallonsu, yadda suke rawar a tare suna juyawa, ba ƙaramin burgesa abin yayi ba, hoto ya shiga ɗaukan su,wanda duk nata ya fi yawa a ciki,

Ba a tashi taron ba har kusan magrib, duk aka fara watsewa, Taufeeƙ ya ƙara so inda yake a tsaye ya jingina da wata bishiya, yana kallon hotunan, a kan nata ya tsaya yana kallo, yanda ta murguɗa baki da taga yana ɗaukan ta murmushi yasake yi, a zuciyarsa yana faɗin"she is just Soo naive".

Taufeeƙ yace "Sir Are we leaving now,Yakamata ka huta fah,". Ɗagowa yayi yakallesa yana jin nishaɗi wanda ya daɗe baiji irinsa ba,ko dan bai taɓa ganin al'adu namu na ƙasar Hausa bane,shi kansa bai sani ba,

Batare da ya kalle shi ba yace "kaje zan dawo anjima, ina son na yi wani abu first".

TaufeeÆ™ ya buÉ—e baki zai yi magana ya É—aga masa hannu kawai, bai sake cewa komai ba ya juya ya bar wajen.

Tsayawa yayi yana tunanin to me ya hanashi komawa gida,what is he waiting for,shi kansa bai sani ba,
kamar ance ya ɗaga kansa ya hangeta tana nufo inda yake,ita kaɗaice sai ɗan ƙaramin sanda,da ta riƙe a hannunta tana wasa da shi,

tsayawa tayi tana magana da su lantana, sai dariya takeyi, Camera ya É—auka ya cigaba da É—aukan ta hoto, yadda take dariyan ya sa ya kasa É—auke idanunsa a kanta,

kamar ance ta juyo kuwa taga, yana É—aukan ta, a fusace ta taho inda yake, tana kallonsa ta fara faÉ—in,

"malam wai lafiya", sai da ya kalleta kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsayuwa yace, "me kika gani,na Sanki ne da zaki tambayeni lafiya".

Da mamaki take kallonsa sai kuma tace "baka Sanni ba, Ni ma ai ba saninka nayi ba, to meyasa kake É—aukana hoto?,

Wani kallo yayi mata sannan yace"sai kuma wa ya ce miki ke nake É—auka?, saboda ke kaÉ—ai ce, sai ke zan É—auka?,ga kyawawan Æ´anmata nan in rasa wa zan É—auka sai ke".

Sake baki tayi tana kallonsa sai kuma ta juya a fusace zata bar wajen ba tare da ta ce masa komai ba,
riƙe hannunta taji anyi, da sauri ta juyo tana kallonsa da mamaki, da sauri ya sake hannun nata yana kallonta da idanunsa da suke sakata jin ta kasa nutsuwa,

A hankali cikin lallaɓi yace, "ƙanwata me yake haɗa mu ne kam naga tunda nazo garinnan muke samun matsala da ke", jin a yadda yayi maganan ya sata faɗin"to waya sanine,"

murmushi yayi sai kuma yace to shikenan tunda baki sani ba, can we be friends? Da sauri ta kallesa sannan ta ce ƙasa ƙasa"Ni bana abota da maza"

Kallonta ya ƙarayi,shi dariya ma take basa wallahi, sai kuma yace "kinga Ni baƙo ne a garinnan, ko a garinku bakwa son baƙi ne?

Girgiza kai kawai tayi, yace yauwa ƙawata, to yanzu miye sunan ƙawar tawa a hankali ta ce "Noor"

"Ni kuma Zannur" ya faÉ—a yana kallonta,murmushi kawai tayi,sai kuma yace to,yanzu kinga tunda mun zama friends shikenan nima sai ki nuna min garinku koh!?, Gobe insha Allahu zan jira ki sai ki zaga dani in ga garinku, ko bazaki nuna min ba? Ya tambaya yana kallonta,

"Zan nuna maka " tafaɗa tana kallonsa, kawai mamaki takeyi daman ashe yana da sauƙin kai?,ai ita gani takeyi, yadda yake da kyau ɗinnan bazai ma kulata ba,

A hankali tace "sai da safe dare nayi zan tafi gida,

"To ƙawata sai goben zan jira ki anan"

Bata sake cewa komai ba ta juya ta wuce abinta,tsayawa yayi yana kallonta, shi mamakin kansa ma yakeji, sai kuma yayi murmushi, yana shafa kansa ya juya ya bar wajen,

a zuciyarsa yana tunanin maybe it's because the girl is too naive and tana da innocent face,bai taɓa tafiya da yayi masa daɗi irin wannan ba,yaje ƙasashe da yawa Amma the happiness daya samu a nan is something else,

ɗakin Taufeeƙ ya buɗe yaga har yayi bacci, kawai ya ja masa ƙofan ya koma nasa ɗakin

sai da wanka, yayi Sallah, sannan ya shirya acikin kayan bacci masu matuƙar taushi, ya kwanta bai daɗe ba bacci yayi awon gaba dashi.

Itama hakan ce ta ɓangaren ta tunani tayi tayi dama haka ƴan birni suke da sauƙin kai, ko dai wannan ɗinne ya fita daban,sake shigewa jikin Nenne dake bacci tayi, itama bacci yayi awon gaba da ita.

What will happen next is the unthinkable,ƙaddara a ko da yaushe dama akace ta riga fata🤗🤓

*💖 ABNUR 💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*
*Page* *7*

Washe gari,haka kawai take jinta cikin farin ciki,wanda har Nenne sai da ta fahimci hakan,amma da ta tambayeta,sai tace babu komai,bata sake ce mata komai ba,ita dai fatanta irin wannan farincikin ya dauwama akan fuskarta.

Har taje makaranta ta dawo,murmushi bai gushe a fuskarta ba.

Wanka tayi, ta ɗauko riga da zanin ta sanya,tayi ɗigon da ta saba,guda uku a ƙasan haɓarta,sannan ta ɗauko ɗan kwali ta ɗaure tulin gashinta,da bai samu wani isasshen gyara ba.

fitowa tayi daga ɗakinta,ta shiga na Nenne,ta sameta, tana ninke kaya,wanda ƙarfin hali kawai takeyi, saboda bata so ta ɗaga ma Noor hankali, idan taci gaba da kwanciya.

"Nenne zanje gidansu lantana",sai da ta kalleta da kyau,sannan tace"kar ki kai dare, ki gaishe min da baabarta,

"Toh insha Allahu"ta faɗa tana barin gidan,a inda ya ce ta sameshi nan ta nufa, bataga kowa a wajen ba, ta lelleƙa bata ga ko wa ba,kawai taja tsaki tana diddire ƙafafunta.

Juyawa tayi,tana ƙoƙarin barin wajen,a ranta tana faɗin, "dama can,ba zuwa zai yi ba, kawai dai ya raina mata wayo ne,itama ina ita ina abota da wannan balaraben,

har tana jin É—aÉ—i zai faÉ—a mata yadda birni yake kafin ta tafi karatun da gwamnati ta É—auke ta"

Kamar daga sama taga mutum a gabanta,har ta ɗan tsorata, ta ɗanyi baya,tana dafe ƙirjinta,tana kallonsa.

"Kai ƙawata haka kike da tsoro daman?" ya faɗa yana kallonta yana murmushi.

Kallonsa tai tayi daga sama,har ƙasa, shigar da yayi ba ƙaramar kyau yayi masa ba.

Hure mata ido yayi, yana kallonta yace"kee wannan kallon fah,ko munina kike son ganine!?,ya faÉ—a yana É—an dariya.

Ai sai ya sake shagaltar da ita, ashe ma kyau É—in sai yayi dariya ma,
can kuma tayi ƙwafa tana kallonsa, tace
"Ku a garinku malami ne yake zuwa ya jira ɗalibi dama? Ta faɗa tana wani ɓata rai,

Kallonta yayi sannan yace toh"ashe Fah ke Malama tunda ke zaki nuna min gari, to afwan Malama,wannan É—alibin bazai sake latti ba,ya faÉ—a yana kama kunnensa.

Dariya tayi,sannan tace "shikenan an yafe maka na yau".

Godiya yayi sannan yace "shall we"

Suka jera suna tafiya suna hira.

TaufeeÆ™ dake tsaye,yana kallonsu, mamaki ya kusa kasheshi a tsaye,
Sir Zannur Ne ya sake haka da mace,macen ma ƴar ƙauye,tabbass akwai wani al'amari,amma yana fatan ko miye ne yazo da alkhairi,sannan yabi bayansu yana murmushi,

Sun yawata sosai, tana nuna masa abubuwa na birgewa a garin, ko ina suka bi kallonsu ake ana mamakin, a ina Noor tasan wannan Balarabe mai É—aukan hoton,

Wani dutse ya samu ya zauna,yana faɗin"kee bakya gajiya da tafiya ne,gaskiya bazan iya cigaba ba" ya faɗa a shagwaɓe.

Dariya ta dinga yi, tana nuna shi
"to miye hakan kaman ba wani namiji ba, Ni da nake ƙarama ma kuma mace ban gaji ba sai kai".
shagala yayi da kallonta kawai, ganin yana kallonta ya sa ta tsagaita tana faÉ—in,

"to shikenan, in ya so gobe sai in ƙara sa nuna maka koh!? Ta tambaya tana kallonsa,

kai ya gyaÉ—a mata, ita ma gefe ta samu ta zauna, tana kallonsa, sai kuma tace "nima ai na kusa komawa birni"

"Haba" ya faÉ—a yana kallonta,"Allah da gaske gwamnati ta É—auki Nauyin karatuna a cikin gari"

Murmushi yayi yace "congratulations ƙawata".

Taufeeƙ ya ƙaraso wajen da suke, da Camera a wuyanshi shima, yana kallon Zannur,gaishesa yayi, ya amsa yana miƙewa tsaye,

"To ƙawata we shall talk tomorrow Koh?"
Ya faÉ—a yana kallon ta,

Ita ma miƙewa tayi tana faɗin,
"Allah ya kaimu",

sai lokacin ta gaishe da TaufeeÆ™,ya amsa yana murmushi,sannan ya juya ga Zannur yace"Sir shall we?"

Bai ce komai ba ya juya ya soma tafiya, shikuma ya bishi a baya.

Itama gida ta wuce,kai tsaye,tana shiga gidan, ta samu Nenne a durƙushe a tsakar gidan, da sauri ta ƙarasa,tana faɗin

"Nenne me ya sameki,

Nenne bata iya cewa komai ba,sai girgiza kanta kawai takeyi,kuka ta soma yi, tana kiran sunan Nenne, sai kuma ta miƙe da sauri ta ɗebo ruwa tazo tana bata,
da sauri Nenne ta karɓa tana sha da alama tana buƙatar ruwan, wanke mata fuska tayi, sannan ta taimaka mata suka shiga ɗaki,

kuka ta ringayi tana kallon Nenne, Nenne dama baki da lafiya har haka shine kike ɓoyemin,
tafaÉ—a cikin kuka sosai,girgiza mata kai kawai Nenne tayi.

miƙewa tayi, da sauri Nenne ta riƙe hannuwan ta tana kallonta,"ki zauna da Ni Noor", "Nenne Ina nan tare dake,zan je in Nemo mai magani ne kar ki damu Nenne na".

Duk yadda ta so taje, sam Nenne hanata tayi, haka ta haƙura,amma sam bacci ya ƙaurace mata, a zaune ta kwana riƙe da hannun Nenne da ta samu bacci da ƙyar,

sallah kaÉ—ai ta tashi tayi,ta dawo ta zauna.

har aka kira sallah,ta miƙe ta ɗauro alwala, sai da tayi nafila tayi raka'a tanul fajr sannan ta gabatar da sallar asuba kamar yadda Nenne ta koyar da ita, tun tana ƙarama.

Addu'a tai tayi , kan Allah ya bawa Nennen ta lafiya,sannan ta shafa ta miƙe.
Chapter 6 · 0% Book details