← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 28

Sashe 18

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki Noor take kallonta, kafin tace,

"kina so ya mutu ne?, nace miki bai mutu ba, kuma insha Allahu kwanannan zai dawo akan ƙafafunsa"

Da sauri ta sake fashewa da wani irin gigitaccen kuka, tana faÉ—in shikenan na shiga uku, yayana shi kaÉ—ai nake dashi,

Abinda bakinta ke furtawa kenan amma zuciyarta tana raya mata, idan har bai mutuba ai kuwa ta kaÉ—e, ta shiga uku,

Ganin kukan da takeyi yasa Noor faÉ—in

"Yasira ki yarda da ƙaddara yayanki ya shiga coma, but insha Allah zai tashi da yardar Allah kiyi masa addu'a"

Kasa cewa komai Yasira tayi da sauri ta juya ta bar wajen, duk suka bita da kallon tausayi.

Sai da Noor tayi wanka sosai, duk da haka daga zaran ta tuna yadda jini ke malala daga jikin TaufeeÆ™ sai ta runtse idanunta,
wasu hawaye na sake taruwa a idanunta.

har ƙarfe goma babu Zannur babu alamar sa, tun tana jiransa, har bacci ya fara ɗaukan ta, a kishigiɗe haka tayi bacci, dan bataso ta kwanta bacci ya ɗauke ta batare da ya dawo ba.

A bangaren Zannur, tun bayan fitowarsa daga asibiti, kasancewar asibitin basa barin kowa a wajen majinyaci su suke kula da shi da kansu, tun da ya fito yake tunanin abinyi, tunanin cctv daya zo masa yasa shi nufar gida kai tsaye,

ÆŠakin sa ya wuce ba tare da ya bari kowa yasan da shigowar tasa ba.

ƙuri yayi ma na'urar yana kallo, ganin babu footage ɗin Garden kwata kwata, da mamaki yake sake kallon computer, ya maimaita dubawa ya kai sau biyar, Amma still babu wannan footage ɗin, a hankali ya shiga duba sauran gurare na gidan, yana so ya gano taka maimai abinda ya faru.

Cak ya tsaya akan inda Yasira ta fito tana kuka, ta samu Taufeeƙ a compound, baya iya jin me suke faɗa, amma da alama faɗa sukeyi, sai kuma yaga sun nufi Garden dukansu, baiga fitar Yasira ba sai kuma yaga Noor ta shiga, pulsing yayi, ya miƙe da sauri ya fita a ɗakin.

Ƙasa ya sauƙo, sannan ya ɗau landline ya Kira ɗakin su Yasira, Amina ce ta ɗau wayan, a taƙaice yace

"Yasira ta sameni a falo immediately" daga haka ya kashe wayar.

"Ni kuma?, meyasa yake nema na?" Yasira ta faɗa tana kallon Amina da ta isar mata da saƙon Zannur,

"Idan kinje sai ki tambayesa Ni kawai cemin yayi kije"

Miƙewa tayi zuciyarta na wani bugu ta fice a ɗakin,

A zaune ta samesa, ita ma ta samu waje can ƙasa ta zauna, tana shirin gaishesa ya ɗaga mata hannu, fuskarsa babu alamun wasa ya soma faɗin

"Me ya haÉ—a ki da yayanki É—azu?"

ÆŠago ido tayi ta kallesa, kafin tace

"Ni.. babu komai" ta faÉ—a tana kame kame

"Babu komai?"ya sake tambayan yana kafe ta ido

Daburcewa tayi, sai ta soma inda inda,

"eh dama, au babu Fah, Amma dai kawai cemin yayi zai kaini gurin baba, shine nace masa bazan je ba, shine yake min faɗa, sai kuma yace muje can muyi magana, muna cikin magana sai Madam ta zo, ranta a ɓace, shine sai ya ce min in tafi, shikenan kawai sai muka ji wai an kashesa."

tana kaiwa nan ta fashe da matsanancin kuka, harda shesheƙa.

Kallonta kawai yakeyi, kamar mai ƙoƙarin gano wani abu, kafin a hankali ya furta

"Yasira kina jina?"

GyaÉ—a masa kai kawai tayi, tana cigaba da kukan

"Yayanki zai samu lafiya, ki kwantar da hankalinki, kina jina?, na miki alƙawarin duk wanda yayi masa wannan abun, da kaina zan bincikosa, sannan in hukuntasa, ki cigaba da yi masa addu'a kinji?"

"To" ta faÉ—a tana fyace majina

"Tashi kije" ya faɗa a taƙaice, yana jingina kansa da kujera.

Miƙewa tayi, ta wuce, tana sake waiwayowa ta dubesa, a hankali kuma tayi murmushi, a zuciyarta tana faɗin

"Kaɗan ya rage na mallakeka Zannur, kuma nayi alƙawarin, duk wanda ya kawo min cikas wallahi sai na kawar dashi"

sai kuma tasa yatsa ta share guntun hawayen idanunta, sannan ta wuce É—akinsu.

Miƙewa yayi daga kan kujeran, yana jin gabaɗaya kansa ya kulle, ta yaya ma Yasira zata cutar da ɗan uwanta, bazai yiwuba,

har ya koma É—akin sa ya faÉ—a kan gadonsa yana cigaba da tunani,

to me ya kai Noor wajen Taufeeƙ?, kuma ranta a ɓace, me ya mata?, dole ne ta amsa masa waɗannan tambayoyin nasa, shin ko dai yayi kuskuren amincewa da ita ne?, wata zuciyar ta raya masa, da sauri kuma ya girgiza kansa, yana maimaita
"Allahummu ajirni fi musibati."

GabaÉ—aya ya manta da wani tana jiransa, har bacci ya dauke sa.

Mun kusa dawowa kan labari🤓so get ready, gumurzun yana gaba

Maimoon#

*💖ABNUR💖*

*By maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

*Free book*

*Page 17*

Da safe ma kiran doctor ne ya tashe sa, akan yana nemansa da gaggawa, a gaggauce ya shirya ya bar gidan, ba tare da ya ma Noor sallama ba.

Noor kam, tunda tayi sallah, ta gagara koma wa bacci, tunani takeyi meyasa bai zo ba?, bayan ya mata alƙawarin zai zo komin dare.

"to ko bai dawo bane jiya" abinda zuciyarta ta raya mata kenan, Definitely bai dawo ba, tasan da zai shigo, to ko jikin TaufeeÆ™ É—in ne, ya hanashi dawowa,

wani zuciyar ta sake raya mata, haka tayi ta tunane tunane, kafin daga bisani ta miƙe ta wuce toilet.

Wanka tayi, ta fito ɗaure da pink towel mai kyau, fararen ƙafafuwanta, sanye cikin room slippers pink,

jiki a sanyaye ta ƙarasa ta buɗe sif tana kallo, riga da skirt ta zaro na atampa, ɗinkin riga da skirt, ta ajiye akan gadon, kafin ta ƙara sa gaban mirror ɗinta, dake shaƙe da abubuwan anfaninta.

Mai ta É—auka tana shafawa akan lallausa fatar ta mai santsi, amma duk tunaninta na wani wajen daban,

a haka har ta ƙara sa, kayan da ta ajiye ta ɗauka ta sanya, yadda suka zauna ajikinta tubarakallah masha Allah, kallon kanta ta tsaya yi a madubi, sai kuma ta ɗan yi murmushi, dan ko ba'a faɗa mata ba tasan ita ɗin mai kyau ce, akan laɓɓanta wanda suke pink shar, sannan kamar ta shafa musu lip gloss, saboda yadda suke koda yaushe da santsi da yalƙi ta furta

"Alhamdulillah"

Gefen gado ta koma ta zauna, tana kallon agogon hannunta, ƙarfe takwas saura, da sauri ta miƙe tsaye a ranta tana faɗin "bari kawai na dubo shi, anya ma ya kwana a gidannan."

Daga haka ta fice a ɗakin, tana tafiya a hankali, turus tayi a bakin ƙofan tana kallon Yasira, da ta fito daga ɗakin, daga ita sai kayan bacci wanda ko Cinyarta basu gama rufewa ba, idanunta da alamun, tana ganinta itama tayi saurin yin baya, tana kallon ta, sai kuma ta zo zata gilma ta,

Hannu Noor tasa ta dawo da ita, tana kallonta cikin ido tace

"Yasira me kike yi a É—akin Zannur"

Ta faɗa tana zare mata ido, kamar zasu faɗo ƙasa

Cikin nuna tsoro da kuma kuka Yasira ta soma magana

"Madam dan Allah kiyi haƙuri, ba komai bane, kawai Sir yaga halin da nake ciki jiya saboda rashin lafiyan Yayana, shine yace nazo, to shine bacci ya ɗauke Ni a nan, ba komai bane"

Noor kallonta ta tsaya yi kafin cikin tsawa tace

"ƙarya kikeyi, aka gaya miki shi jahili ne da zai gayyaceki ki kwana a ɗakinsa, alhalin ke ba muharramarsa bace"

Cikin kuka wiwi, Yasira ta soma faÉ—in,

"wlhy da gaske nakeyi Ma"

"Ok to da ya kiraki ke kuma sai kikazo, saboda ke munafuka ce harda sako kaya irin waÉ—annan"

Ta faɗa tana nuna jikin Yasira, rai a ɓace idanunta sun gama canza kala

"Ma kiyi haƙuri Sir ne ya bani yace in saka, nima bansan dalilinsa ba, kuma Ni bazan iya yi masa musu ba shiyasa nasaka"

Girgiza kai kawai Noor takeyi, kafin ta sake Yasira ta juya a fusace ta nufi É—akin ta, wato abinda ya hanashi zuwa gareta jiya kenan!

me yasa zuciya ta yaudareta da har take ganin kodai Zannur ya fara sonta ne, gadonta ta faÉ—a tana cigaba da rusa kuka wiwi.

Da sauri Yasira ta zaro dogon hijab ɗinta, a inda ta ɓoye ta zura, sannan ta koma ɗakin Zannur cikin sassarfa, inda tasan yana ajiye laptop ɗinsa ta nufa, kasancewar babu security yasa ta buɗe da sauri, sai da ta tabbatar ta goge wannan footage ɗin kamar yadda ta goge na Garden, kafin ta shiga tafa hannunta tana murmushin mugunta,

"Yaya Taufeeƙ, kayi kuskure, da har kake ƙoƙarin rabani da rayuwata, dan kuwa Zannur rayuwa ta ne, zan iya komai dan na mallakesa, amma bazan ƙi gode maka ba, saboda makarantar computer da ka sakani, har na zama computer guru, idan ba haka ba, da tuni asirina ya tonu, sannan ina mai tabbatar maka bazan taɓa bari ka farfaɗo ba,bare har ka tona min asiri, har sai Zannur ya Zama nawa."

Daga haka ta fice a É—akin tana murmushi, da jinjina ma kanta.

******

"Congratulations, gaskiya dan uwanka, yana da matuƙar Sa'a, ba kowa bane ya ke shiga coma ya dawo da wuri, but da izinin Allah jiya ya motsa, kuma daga nan zuwa ko wani lokaci, zai iya farkawa."

Da sauri Zannur ya É—ago yana kallon likitan, jinjina masa kai doctor yayi alamar tabbatarwa,

"But saboda lafiyarsa, yasa bazamu bari ya gana da kowa ba, har sai bayan kwana uku"

Likitan ya ƙara sa faɗa yana gyara glass ɗin idanunsa, da murmushi a kan fuskarsa.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, alhamdulillah"

shine kaÉ—ai abinda Zannur ke iya faÉ—a, ko babu komai, TaufeeÆ™ zai faÉ—i wanda ya aikata masa hakan da kansa.

Miƙewa yayi yana miƙa ma doctor ɗin hannu, suka yi musabaha, kafin ya fice a office ɗin yana jin matuƙar farin ciki, bai zarce ko ina ba sai gida.

ÆŠakin Noor ya nufa, dan yana so ta amsa masa tambayoyin da ya kwana dasu,

Tunda ya shigo ɗakin taji shigowar sa, amma sai tayi kamar tana bacci, ƙarasowa yayi ya zauna a gefen gado yana kallonta, kafin a hankali ya sa hannuwansa duka biyu ya ɗago ta gabaɗaya,

yatsine fuska tayi kafin tace "miye hakan?"

Bai kulata ba ya zaunar da ita a tsakiyar gadon yana kallonta da fuskar da babu wasa yace " " " Noor! "
Chapter 18 · 0% Book details