← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 28

Sashe 16

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yace "pleaaaaase Noor, Ina so kiyi min kyakkyawar fahimta, sannan kar ki hukunta Ni akan laifuka na a gareki."

Jin yayi shiru ya sata ɗagowa suka haɗa idanu, da sauri ta sunkuyar da kanta, dan ta kasa gane inda maganganun sa suka nufa, sannan ita bai mata laifin komai ba, hasali ma bata da wani wanda take matuƙar darajawa da kuma so da ƙauna kamar sa, dan shi ya tsamota sannan ya tallafa mata bayan Nennen ta,

Amma ita tasan ya fi ƙarfinta har abada, bazata taɓa samun shi ba, cigaba tayi ta wasa da yatsunta, dan ta rasa me zata ce masa.

zagayo da hannuwansa duka biyu yayi akan cikinta, batasan sanda ta sauƙe ajiyar zuciya ba tana sake sunkuyar da kanta dan wani irin kunyarsa ce ta kamata lokaci ɗaya, muryarshi taji dai-dai kunnenta da har sai da tsigar jikinta ya amsa, cikin raɗa ya ce,

" kin bani dama in faÉ—a miki abinda yake raina da zuciyata, and you promise you won't judge me?"

Ya faÉ—a da sigar tambaya dan so ya ke ta buÉ—e baki tayi masa magana.

girgiza masa kai alamar Ah ah,
da sauri ya É—ago fuskarta yana kallonta,

"why" ya faɗa yana ƙoƙarin cigar da ƙwayar idonsa nata,amma ta ƙi.

Cikin inda inda tace

"saboda lokacin sallah yayi, ka bari ka dawo daga masallaci"

Wani ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauƙe yana jan hancinta, sai kuma yace,

"ok wifey your wish will always be my command."

daga haka ya ɗaga ta daga jikinsa, ya sauƙa a kan gadon.

A bayan gidanta ya yi alwala, sannan ya fice a É—akin,

Ita dai da ido kawai take binsa, yau gabaɗaya ya canza mata, sai kuma tayi murmushi itama ta miƙe ta wuce toilet dan yin nata alwala

********

"Ka saurareni Sir TaufeeÆ™, wallahi idan har ban samesa ba mutuwa zanyi, dan Allah ka taimaka min, pleaaaaase"

ta faÉ—a tana kuka wiwi kamar ranta zai fita
Wani irin kallo yayi mata na tsana, kafin ya soma magana cikin matuƙar ɓacin rai

"Yasira ke wace irin mara tunani ce, taya zakiyi tunanin Sir zai taɓa sonki, bare har ya zauna tare dake, kin manta irin taimakon da ya mana, a lokacin da namu dangin suka wofintar da mu, tayaya ma zaki fara tunanin rama alkhairi da sharri."

shiru yayi yana furzar da numfashi, kafin ya cigaba

"Wallahi tallahi, ni Taufeeƙ Muntasir, idan har ina raye bazan taɓa bari ki ruguza farincikin Sir Zannur ba, idan baki sani ba ki sani, Noor itace kaɗai wacce Sir zai iya rayuwa da ita, saboda shi kanshi ya fara sonta ne batare da ya sani ba, kuma idan har ina raye zai zauna da wacce zuciya, ruhi da gangar jikinsa keso ne, ba son raina ba, ko kuma son ran ƴar uwata Yasira Muntasir ba."

Daga haka ya juya yana shirin barin gun,

da gudu ta ƙara so ta riƙe ƙafafuwan sa tana faɗin,

"yaya wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba, mutuwa zanyi, ita Noor ɗin mai ka haɗa da ita, da ka zaɓe ta akaina, wallahi zan iya kasheta akan na mallaki Sir Zannur, Ni kaina bansan wani irin so nake masa ba, pleaaaaase Yayana ka taimaka min"

Dakatawa yayi yana kallonta sai kuma ya naɗe hannuwansa a ƙirji yana faɗin

"ok to yanzu me kike so in yi miki"

hawayenta ta shiga gogewa cikin sauri tace

"yaya so nake Noor ta bar duniyan nan, ko kuma ta yi nisa da mu, yadda zan samu daman rayuwa da Sir Zannur Ni kaÉ—ai"

Wani kallo da yake binta da shi yasa ta gagara ƙarasa zancen tana kallonsa

"Yasira when did you turn to be a monster ban saniba, how could you even think of that, kin San me kike faÉ—i kuwa, wallahi billahi, kiyi hanzarin cire wannan banzan tunanin daga kanki, sannan yanzunnan ba sai anjima ba zan je na sanar da Sir Zannur duk abinda kike shiryawa, yasan yanda zai yi dake, bana son yayi la'akari da cewa ke Æ´ar uwata ce, don kuwa kin zama guba a cikin mutane, idan har zaki iya tunanin kisa"

daga haka ya juya ya fice a É—akin yana huci.

kamar zautacciya haka ta miƙe daga durƙuson, tana faɗin

"Zaka faÉ—a ma Sir, wallahi babu wanda ya isa ya rabani da Sir koda kuwa uban da ya kawoni duniya ne bare kai da muke Æ´an uba, badai idan har kana raye ba to wallahi yanzu zaka bar duniyan nan."

daga haka ta fice da sauri, har tana haɗa wa da gudu ta nufi kitchen, su Asabe da ke aikin girki, basu ma lura da ita ba, da sauri ta zari wuƙa ta cusa cikin zaninta, ta fice a kitchen ɗin da sauri.

A tsakar gida ta riske shi, shi kaɗai yana Safa da marwa, tunanin abinda ƙanwar tasa take shirin aikatawa ya hanasa sukuni, ƙarasowa tayi ta na faɗin

"yaya"

Idanunsa da suka kaÉ—a suka yi ja,ya É—ago ya zuba mata, yana mata wani irin kallo

"yaya dan Allah kayi haƙuri, wallahi nayi dana sanin abinda na furta tun farko dan Allah yayana"

Juyowa yayi sai kuma ya kasa cewa komai.

"yaya dan Allah muje garden muyi magana,na maka alƙawarin, zanyi duk yadda yace."

Wani ajiyar zuciya ya sauƙe yana faɗin

"ok muje"

Har cikin garden ɗin suka shiga sai da ta tabbatar su kaɗai ne kafin ta soma kukan ƙarya tana faɗin

"yaya dan Allah, yanzu bazaka tausaya min ba ka duba halin da nake ciki"

Cikin ƙunar rai yace

"kina kan bakan ki kenan, ai nayi zaton kin haƙura ne shiyasa ma na biyoki nan, kuma banga amfanin zama na a nan ba, tunda bazaki ji magana ta ba, kiyi duk abinda zuciyarki ta raya miki, nima kuma ina mai tabbatar miki, zanyi duk abinda zuciyata ta raya min dan ganin ba abinda ya samu Sir Zannur ko kuma Madam Noor."

Daga haka ya juya zai bar gurin.

Cikin ƙaraji ta nufe sa da wuƙar, juyowa yayi da sauri, amma ko kafin ya farga, ta luma masa wuƙar a cikinsa, tana kuka, tana faɗin

"meyasa baka barni da zaɓi ba yaya, dan Allah ka yafe min amma bazan iya zuba maka ido ka ruguza min farin ciki na ba"
sake luma wuƙar tayi tana jujjuyasa a cikinsa, wani irin murmushin takaici yayi, amma ya gagara ko da motsi saboda azaban dake ratsa shi, sannan bakinsa ya gagara furta komai,

Dafa shi tayi ta zare wuƙar ta sake caka masa ita, dan bata so ko kaɗan ya tsira, tanayi tana kuka wiwi, daga ƙarshe ta hankaɗa shi ya faɗi a wajen.

Da sauri ta bar wajen tana bar masa wuƙan a cikinsa, ɗakinsu ta wuce, ta shiga banɗaki tana ƙoƙarin dai dai ta nutsuwarta, wanke hannunta tayi da fuskarta, sannan ta fito a bayin, sai data gyara fuskarta, sannan ta fito ta nufi ɗakin Noor, wacce ta idar da sallah kenan, tana jiran Zannur, dan ta ƙagu ta ji abinda yake son sanar da ita.

Knocking tayi, cikin sauri tace "come in."

A zatonta Zannur ne, ganin Yasira yasata É—an haÉ—e fuska ba tare da tace komai ba, cikin in ina, ta soma faÉ—in

"Ma, daman Sir ne yace ki samesa a Garden yanzu"
ta faÉ—a tana sunne kanta,
Kamar bazata kula ba sai kuma tace

"kice ina zuwa"

"Ok Ma" ta faÉ—a tana barin É—akin da sauri,

miƙewa tayi ba tare da ta cire hijab ɗin da tayi sallah ba, ta naɗe sallayan ta ajiye sannan ta zura takalman ta ta fice a ɗakin, dan gudun kar ta ɓata masa lokaci.

Yasira da ke tsaye, tana kallonta ta wuce, ta sauƙe ajiyar zuciya, duk ac ɗin dake gurin, amma gumi take haɗawa, tana tsaye sai ga Zannur zai wuce ɗakin Noor, da sauri ta fito daga inda ta maƙale tana mai shan gabansa,

dakatawa yayi ganin ta a gabansa, "lafiya" shine abinda ya furta yana kallonta yadda duk take a birkice

"Uhm babu komai Sir, dama ce maka zanyi, Madam bata É—akinta, tun fitarka naga ta tafi Garden, da alama akwai abinda suke tattaunawa da Sir TaufeeÆ™."

Shiru yayi yana karantar ta sai kuma yace
"TaufeeÆ™?"

Da sauri tace "eh"

Bai sake cewa komai ba ya juya ya nufi Garden É—in yana tunanin to me suke tattaunawa kuma da TaufeeÆ™.

Cak ya ja ya tsaya, numfashin sa na ƙoƙarin fin ƙarfinsa, ganin Taufeeƙ cikin jini mala mala, ita kuma tana tsugunne a gabansa tana kuka wiwi, da wuƙa a hannunta, sannan duk hijab ɗin ta ya ɓaci da jini.

Kasa gane tunanin da zaiyi yayi, dan dai ya gagara gane me ke faruwa a wajen

Taufeeƙ dai, personal assistance ɗinsa,Wanda yake gani kamar ɗan uwansa, wanda ya riƙe da amana, yake jinsa a cikin jininsa, shine a kwance a cikin jini.

yayinda matarsa, wacce yake jin bazai iya rayuwa ba tare da ita ba, wacce ya gama gasgatawa kansa ta cancanci ta zama mahaɗin rayuwarsa, itace a durƙushe akan Taufeeƙ da wuƙa, no it's not possible.

Da sauri ya ƙarasa wajen yana ɗagota

FaÉ—awa jikinsa tayi tana sake fashewa da wani irin matsanancin kuka,

"Wallahi a haka na zo na gansa, bansan wa ya masa haka ba, mu kaisa asibiti kar ya mutu."

Kasa cewa komai yayi, saima ɗaga ta da yayi daga jikinsa, cikin tsananin tashin hankali, ya sunkuya ya rungume Taufeeƙ tsam a jikinsa sai kuma ya ɗauke sa cak, ya nufi barin Garden ɗin dashi, yana iya ƙoƙarin sa ganin ya hana kansa hawaye, gudu gudu ya fito dashi, daga cikin Garden ɗin jikinsa na wani irin rawa,

Da sauri bodyguards ɗin sa suka ƙara so, amma sai ya ƙi basu shi, ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya kwantar da shi a baya, ya gagara furta komai a bakinsa, zagayawa yayi ya shiga mazaunin driver.

Noor da ta biyosa ganin zai tafi ya barta, ya sa tayi saurin buÉ—e motar ta shiga, bai ce mata komai ba, ya tada motar, ya fice a gidan, bayan ya hana bodyguards É—in binsa.

Gudu kawai yake shararawa, akan titi, amma gani yake baya sauri sam, ita kam banda kuka babu abinda take, satan kallon sa tayi, taga yadda fuskar sa tayi jajazir, amma babu ko É—igon hawaye, kana ganinsa zata fahimci tsantsan tashin hankalin da yake ciki.
Chapter 16 · 0% Book details