← Book details Abnur Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Abnur Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai ce komai ba ya juya ya fice, ita dai Noor da ido take binsa, ta gagara gane shi wani irin mutum ne, sai ta yi ƙoƙarin gane halinsa sai ya sake canzawa completely.

Landline É—in kitchen ta Kira akan suzo suyi clearing É—in table É—in kafin tabi bayan Maami da ta wuce sama.

É—akinta ta wuce dan yin sallah, sannan ta bar Maami ta huta, a hankali ta zauna a gefen gado bayan ta idar da sallah, tana tunanin abubuwan da yayi ta yi É—azu, sai kawai tayi murmushi,

miƙewa tayi taje gaban madubi ta na kallon kanta, wasu hawaye taji sun cicciko idanunta, cikin kukan ta shiga furta

"Abba ina ka tafi ka barmu Ni da Nenne, gashi Nenne ta rasu ta barni Ni kaÉ—ai, Nenne ta rasu ba tare da ka nemi gafarar ta ba, me ya hanaka dawowa garemu Abbana."

Sai kuma ta share hawayenta ta na sake faÉ—in,

"bana buƙatarka har abada, dan dama bansan soyayyarka ba ban taso naji ɗumin kaba, sannan bansan koda kamannin ka ba,"
Kuka ne ya sarƙe ta ta zube a wajen tana cigaba da kukan gwanin tausayi.

Yasira jin shiru shiru, bata sake jin wani hayaniya ba ya sata fitowa falo, a lokacin taga Sir Zannur yana fita a gidan, da sauri ta ƙara sa ƙofar dining hall ɗin tana leƙawa, ganin Noor da Maami suna cin abinci tare, ba tare da wani alama na tashin hankali ba, ya sata ja da baya, a hankali take ja da baya kafin ta ruga da gudu ta koma ɗakinsu, durƙushewa tayi a wajen tana sakin kuka mai sauti, sai kuma ta shiga sumbatu cikin kukan tana faɗin,
" wallahi tallahi ina sonka, kuma bazan taɓa yarda na rasa ka ba, kai ne rayuwata, Allah ne ya ɗaura min sonka, kuma bazan taɓa haƙura da kai ba, kamar yadda bazan zauna da kai tare da ko wace mace ba, zan iya aikata koma miye ne dan na mallake ka, koda kuwa ta kama da wani ya bar duniyan nan ne"

sai kuma ta share hawayenta tana murmushi ta cigaba da sumbatu kamar zautacciya
"ai nayi zaton zai zo min da sauƙi ne shiyasa na kira Maami na faɗa mata, amma yanzu naga alama babban shiri kake buƙata Sir Zannur wallahi, wallahi, wallahi, duk wanda ya shiga tsakanina da farin cikina kwanan shine ya ƙare ta faɗa tana miƙewa a zabure kamar mahaukaciya.

Su dai su Asabe basu san me ake ciki ba, suna can baya suna wanki, suna hirar su, gabaÉ—aya basu ma san da zuwan Maami ba bare haukar Yasira.

*******
*_*_
AL RAJWA VILLA'S, AJMAN, DUBAI_*_*

Zaune yake a katafaren falon, ya jingina da kujera, da alama yayi matuƙar zurfi a tunani.

dafa shi da yaji anyi yasa ya É—ago idanunsa da har sun kaÉ—a sunyi jaa, farin Balarabe ne kyakkyawan gaske mai cikar kamala sosai.

Ammi, cikin harshen larabci, ta soma faÉ—in,

"me yasa bazaka daina uzura ma kanka ba mijina." kallon farar balarabiyar yayi ba tare da ya ce komai ba ya miƙe tsam ya bar mata falon, wani ɗaki ya shiga inda kana gani kasan na zane zane ne,

ƙara sawa yayi gaban board ɗin zanen, ya ɗau brush ɗaya ya saka a paint, a hankali ya lumshe idanunsa sai kuma ya buɗe ya shiga zane, wasu siraran hawaye na sauƙa a kan fuskarsa,

Ammi ce ta sake shigowa ta tsaya ranta a ɓace ta ke faɗin

"yanzu a tunaninka wannan shine abinda ya dace ka dinga yi koh?, ka zana hoto ɗaya a iya lissafina yafi ɗari, kullum sai ka zana, meyasa bazaka sauwaƙema kanka, nima ka dube Ni ba?"

ÆŠagowa yayi, ya kalleta sai kuma yace

"Please nadiya, I need a break"

Daga haka ya fice ya koma É—akinsa yana rufewa da makulli

Ƙwafa tayi,tana jin zuciyarta na suya, a fusace ta ƙarasa gaban allon ta yi wurgi dashi, tana faɗin,
"na tsaneki, ya zan yi da ke?, kin zame min annoba, kin kasa barina in ji daÉ—in rayuwata."

sai kuma ta juya a fusace ta bar É—akin tana huci.

Falonta ta wuce, inda Æ´an mata biyu da namiji É—aya ke zaune suna video game, babbar cikinsu bazata fi 15 ba sai mai bi mata wacce ita ma bazata fi 10 ba namijin kuwa bazai fi 7 ba,

A fusace tace, "farhaana, ku wuce falonku, ku barmin falona bana son hayaniya yanzu"

Da sauri farhaana tace, "Ammi Are You ok, ke da papi ko?"

Bata kulata ba, sai zama da tayi ta riƙe kanta da duka hannuwanta, da sauri farhaana ta kora ƙannen nata suka wuce part ɗin su, tana tunanin sai yaushe papi zai koma kamar kowa?, sai yaushe zai zauna tare da su kamar yadda ko wani uba yake zama da ƴaƴansu?

************

Tunda Maami ta zo, Zannur ya canza mata,

gabaÉ—aya Noor ta rasa gane ina ya dosa, a gaban Maami kulawa yake bata da har take jin dama har zuciyansa yake mata hakan, amma inaa, bayan idon Maami banda harara babu abinda ke haÉ—ashi da ita, a rashin sanin ta kuwa duk wani shiga da fitanta akan idanunsa takeyi, dan kuwa yana iya yini yana kallon ta a laptop É—in sa, TaufeeÆ™ ya tafi Bangaladash saboda wakiltar Zannur akan wasu ayyukansa,hakan yasa bata ganinsa, Asabe da Amina kuwa, kullum cikin É—ebe mata kewa da sakata dariya suke, Yasira ta sake kamar babu komai a zuciyarta, but ita kaÉ—ai ta san gagarumin abinda take shiryawa wanda zai ruguza farin cikin duka Æ´an gidan.

Satin Maami biyu ta koma Dubai, da kewan Habibi da kuma Noor, dan kuwa shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninsu, ta sake wayar mata da kai akan abubuwa da dama, sannan kafin ta tafi ta sa an nemo mata malamai har biyu na islamiyya da boko tana cigaba da karatunta, a halin yanzu Noor Bata da wata damuwa da ya shige ta Zannur, amma shiɗinma sam bata saka shi a rai ba bare ya hanata walwala.

12 ga watan August dai dai da cikar Noor shekara ɗaya da wata huɗu a gidan, shine ranar da abubuwa suka fara canzawa, ƙaddarar da bazata taɓa mantawa ba, da duk wani wanda yake gidan ya faru wanda yayi sanadiyar ruguza duk wani hasashen farincikin Noor.................

Kuyi haƙuri page ɗin yau yayi kaɗan, bana ɗan jin daɗi ne shiyasa, Amin uzuri

Maimoon#

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon*

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

*Page* *15*

I DEDICATE THIS PAGE ENTIRELY TO MY NIMCYLUV, I LOVE YOU SO VERY MUCH, THANKS ALOT FOR THE SUPPORT, AND I WONT FORGET TO THANK DUK MAI KARANTA ABNUR, I REALLY APPRECIATE THE LOVE, MORE ESPECIALLY ABNUR GROUP, I CAN'T LOVE YOU GUYS LESS, AND YOUR PRAYERS ALWAYS GOT ME, BAN MA SAN ME ZANCE BA, YOU GUYS ARE THE BEST,

******

12 ga watan August,ya kama ranar Laraba, tun safe ta ke jin matsanancin bugun zuciyan, da batasan dalilinsa ba,
tunda ta yi breakfast tare da Zannur, ba ta sake sakashi a idonta ba, har wannan lokacin, wanda agogon dakin ya nuna mata karfe 3:30 kenan.

Littafin umdatul ahkam ɗinta da ta ke biyawa ta ajiye kasancewar muallimar bata jima da tafiya ba, a hankali ta dafe ƙirjinta da ke bugu.

Akan laɓɓanta ta furta "hasbunallahu wa ni'imal wakil,auzubillahi minashaiɗani rajeem, Allah kasa inga Alkhairi."

Sai kuma ta miƙe, ta nufi kitchen gurin su Asabe, nan ma bata iya zama ba, duk da yadda suke janta da hira amma ta kasa sake jikinta, daga ƙarshe takoma ɗakinta, kwanciya tayi taja bargo tayi shiru ko zata samu bugun zuciyar nata ya ragu.

A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin nata ya shigo,

zurfin da tayi a tunani, yasa bata ma ji shigowar sa ba, harɗe hannuwansa yayi a ƙirji ya na kallonta a inda take kwance.

zuwa yanzu ya gama gasgata ma kansa, ya na matuƙar so da ƙaunar Noor, sake ware idanunsa ya yi a hankali a kanta, ya na jin yanda zuciyarsa ke bugawa, a cikin shekara ɗaya da wata huɗun da suka zauna waje ɗaya da ita, baya shiga harkarta, shi kaɗai yasan irin azabtuwar da zuciyar sa keyi bazai iya jurewa ba, ya gaji da kallonta daga nesa ko kuma ta cctv,dole ya sanar mata tsantsan soyayyarta dake zuciyarsa.

A hankali ya ƙarasa, kasancewar barci har ya fara ɗibanta, sam bata ji alamarsa ba, har ya hayo gadon, bargon ya shiga sannan ya jawota ya rungume ta sosai a ƙirjinsa, sai lokacin ta lura, ai kuwa ta buɗe baki zata kurma ihu yayi sauri toshe mata baki da hannuwansa, zare ido ta shiga yi, dan bata ma gama tantance waye bane, duk da ƙamshinsa na SHUMUKH da ya karaɗe ko ina, amma sam ta kasa nutsuwa, dan ta tabbatar Zannur, dai bazai taɓa hawa gadonta ba, balle har ya rungumeta haka,

ganin ta gagara ihun ya sa ta fara shure shure, ta ƙi nutsuwa.

Dariya ma ta bashi, ita a dole ga mai ƙarfi, a cikin kunnenta ta raɗa mata

"Baby, mijinki ne fah"

Wani banbaraƙwai taji zancen, amma sai ta rage shure shuren ta na ɗago idanunta ta kallesa, ganin ta nutsu yasa ya sake mata bakinta, ya lumshe idanunsa, sannan ya buɗe.

Tashi yayi da ita a jikinsa, ya zaunar da ita akan ƙafafunsa,sannan ya juyo da ita tana fuskantar sa, cikin murya mai nuna kulawa da tayi daban da na Zannur ɗin da ta sani yace

"Noor!"

Kasa amsawa tayi, saima sunkuyar da kanta da tayi, tana wasa da yatsunta, dan gaba ɗaya a takure take, kasancewar basu taɓa kasancewa very close irin na yau ba.

Jin bata amsaba, sai shima bai damu ba, ya cigaba da maganan sa,

"Noor, nasan Zaki yi mamaki, abinda ya kawo Ni ɗakinki har kan gadonki, but ba abin mamaki bane, idan kika yi la'akari da matsayina a wajenki, sannan yau yayi daban da duk ranakun da muka kasance tare da ke, a yau ina so in faɗa miki wani abu mai matuƙar muhimmanci da yafi komai muhimmanci a rayuwata yanzu,

sai da ya ɗan yi shiru kasancewar yayi maganan da yawa sai kuma ya nisa kafin ya furta kalma mai matuƙar nauyi a wajensa wato 'Please' dan dai banda Abbu da Maami, baya tunanin ya taɓa cewa wani please.
Chapter 15 · 0% Book details