← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 63

Sashe 60

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:31] Miss Green🍀: 1001. . . .1002

tashin hankali sai ya zama guda biyu don nima wannan haihuwar har tafi tasu Ƴan huƊu,don har an fara fitar da rai dani,shi kuwa shahid nema ya ke ya fita daga cikin hayyacinsa,ba don ma ammi ba da ba'asan abinda zai faru ba,har an fara haƊa kayan aiki na sunkutu Ƴa ta mace kyakkyawa me tsananin kama da mahaifinta,kyakkyawa ce sosai har tafi mahaifinta ma kyau.

hajiya kaka ma tazo ta yimin barka sai dai fuskarta atamke tsaf,haka ma duk wanda zai zo duba ni sai inga fuskarsa a haÆŠe sosai na rasa gane kan kowa,kai hatta yaya Aliyu dasu mamana kowa sai inga fuskarsa tamau,abin ya dameni sosai,na rasa wanda zan tambaya gashi nima ban gama warwarewa ba don nasha wuya sosai.

Shahid ne ya shigo shima duk jikinsa ya yi sanyi,yana shigowa ya kalleni sannan ya ce"khairat ya jikin"?.sosai maganarsa ta girgizani don bai taƁa kirana da khairat ba sai dai hayatee,na kallesa sosai Na ce"hubby yau kuma sunana ka ke faƊa"?.na faƊi hakan ina me kallonsa kamar ya yimin laifi.

sunkuyar da kansa ya yi ya Ƙaraso inda jaririyar take ya saka hannu ya Ɗauketa ya rungume ta a Ƙirjinsa hawaye masu zafi suka zubo masa a kuncinsa,a zuciyarsa ya ce Allah sarko Ƴata ashe bazan rayu da mahaifiyarki ba?ashe bazanyi rayuwa da ita me tsayi ba?yanzu me na aikata haka?shin nima ina tunanin zan iya wani auren idan na rabu da khairat?shin ya rayuwar Ƴarsa yaya za ta kasance alhali babu me kula da ita sai mahaifiyarsa zai Ɗorawa wahala.

jin kukan da khairat ta fashe dashi ne ya saka ya juyo da sauri ya ce"khairat lafiya ki ke kuka me aka yi miki?".ya faƊi hakan yana matsowa har ya riƘe hannuna wanda na Ɗora aka ina gunxuma ihu kamar wani ya dake ni.

da sauri na yar da hannunsa gefe na ce"haba na gaji wallahi,yaya kuke so inyi ne?kO cikakkiyar awa ÆŠaya banyi da haihuwa ba,amman kowa ya shigo sai inga duk hankalinsa atashe kuma ya ÆŠauremin fuska?Haba wannan wani irin rashin tausayi ne?ku faÆŠamin mana idan wani abune ya faru?"

da sauri ya koma gefe ya ce"khairat babu komai fa haka dai ke ki ka gani,amman babu komai bari inje wajen Ammi sai mu taho tare taje duba wanine ba shida lafiya".yana faƊar hakan ya fita da mugun saurinsa,tuni naji zuciyata ta tsinke na shiga wani irin kuka wanda na kasa gane kansa,na kalli Ƴata wacce kebta shan hannu alamar tana neman abincinta,da ta gaji da shan hannun sai ta fara kuka sosai,nima uwarta ta kuka nake sosai kamar wacce aka aiko mata iyayenta sun mutu duka.

ana cikin wannan halin ne anty hakisa tazo,da sauri ta Ƙaraso cikin Ɗakin tana ce wa"subhanalillahi khairat me ya faru haka?ga yarinya na ta kuka alamar tana neman mama kuka kinƘi bata?".ta saka hannunta cikin gadon babyn ta Ɗakko ta tana Ɗan girgiza ta,ta zauna ta ajjemin ita akan cinya ta tace"khairat yi haƙuri ku bata tasha kinji?koma menene ya faru bai kamata ki yiwa Ƴarki ta cikinki haka ba,ki bata tasha sannan sai muyi magana".

Sai shashsheƘar kuka ba ke harda majina ta kalleni kawai,tana jin tausayina har cikin ranta,a hankali na ke shayar da ita jaririyar ta riƘe babban Ɗan yatsana tana kuma kallon cikin idona sosai,ina kallon yarinyar sai naji zuciyata ta fara sanyi tabbas ƳaƳa rahama ne arayuwa,Allah ubangiji ya bawa duk wanda basu haihu ba,ya basu masu albarka wanda za'ayi alfahari dasu aduniya da lahira.

sai da tasha ta Ƙoshi sosai sannan anty halisa ta amsheta ta sakata a kafaƊarta har ta yi gyatsa,sannan ta kalleni sosai ta fara yimin nasiha sannan ta ce"khairat yanzu fa daga dubo baban Ƴan huƊu na ke".da sauri na kalleta sannan na ce"me ya same shi kuma?daman ba shida lafiya ne?".

Na faƊi hakan zuciyata na bugawa sosai,ganin na shiga wani hali ne yasa ta gane ce wa ban san ba shida lafiya ba ta ce"khairat come down,kinga yanzu kin haihu fa kina buƘatar ki samu kulawa sosai don haka kada ki Ɗaga hankalinki don Allah ciwon fa yanzu da sauƘi".

da sauri na miƘe na ce"haba anty halisa ni fa ba yarinya bace kamar da,kowa fa ya shigo fuskarsa babu daƊi,ni nasan aƘwai abinda ake Ɓoyemin."Na faƊi hakan cikin kuka na tashi tsaye ina jin wani irin jiri yana Ɗiba ta,ga uwar yunwa da na keji wacce ta gama cika min ciki na ce"anty halisa don Allah zo muje ki nunamin Ɗakin da aka Ƙwantar dashi"?.

da sauri ta ce"a'ah fa khairat bazan iya rakaki ba gaskiya,kinga ba kida lafiya kuma bayan haka mijinki ma fa yana cen yanzu na baro sa acen,kinga ai babu daƊi ki dai bari ki samu lafiya sai kije".da sauri na Ƙarasa kusa da ita ina kuka na ce"don Allah anty halisa ki rakani in duba sa,zuciyata ji na ke tamkar zata fito don Allah".

sosai take kallona cikin mamaki,wato khairat micijin sari ka noƘe ce,wato duk tsanar da take ce wa ta yiwa yaya Bilal ashe duk Ƙarya ne?to idan ba Ƙarya ba me yasa ta damu don ba shida lafiya?.

ganin khairat Ɗin ta dage ne yasa ta ce"to khairat muje".ta Ɗakko min jaririyar muka fito,ina dafe bango ina tafiya jirin yana Ɗiba na amman a haka har muka isa Ɗakin,duk naji jikina ya Ƙara yin sanyi sosai.

da mutane sosai a Ɗakin duk suka zubomin ido mamaki Ƙwance kan fuskarsu har da shahid a Ɗakin,da ammi mahaifiyarsa da kuma mama har dasu yaya Aliyu,ga hajiya kaka a gefe su Rashida,sai maryam wacce bata fi wata biyu da haihuwa ba,ta haifi Ɗanta na miji,me sunan yaya Bilal.

saurin dafe jikin bango na yi ina waro ido waje,ganin yaya Bilal Ƙwance kamar matacce an saka mishi abin shan numfashi ya yi wani irin fari fauu ga kuma ramar da ya yi,an saka masa kaya ruwan skye blue irin na marasa lafiya.

wani irin kuka na fashe dashi tuni na tsugunna Ƙasa da rarrafe na Ƙarasa bakin gadon,saboda Ƙafufuwa baza su iya kaini wajensa ba,na ce"Yaya Bilal anya kuwa kai ne?me ya faru da kai?wani irin ciwo ne wannan?".duk ni kaƊai ke sambatu na kamar mahaukaciya sabon kamu,babu wanda ya cemin Ƙala,sai ma harara da wasu ke bina dashi.

ban ma san na riƘe hannunsa ba sai yanzu na Ƙara ƘamƘame hannunsa na ce"don Allah yaya Bilal ka tashi,idan ka mutu nima tabbas zan iya mutuwa,da kai na saba yaya Bilal tun ina Ƙarama ta ka nuna min so,ka nunamin Ƙauna,haƘiƘa banyi maka adalci ba".

Da sauri shahid ya tashi ya fita waje,duk zuciyarsa babu daƊi wani irin kishi yaji ya turniƘe masa Ƙirjinsa,ya zauna kan wani benci ya saki kuka kamar Ƙaramin yaro,mutane sai wuce wa suke suna kallonsa yana son khairat da duka zuciyarsa yana jin ciwon rabuwa da ita,amman ya zama dole ya yi hakan don ayanzu ya gano ce wa ba Ƙaramin so khairat ke yi wa tsohon mijinta ba.

Yana zama ammi ta biyo bayansa don ganin halin da Ɗanta ke ciki,itama duk zuciyarta babu daƊi ko kaƊan,ta ce"shahid ka yi haƘuri ka ka baiwa Allah lamarinsa,sam banji daƊin hukuncin daka Ɗauka akan aurenka da khairat ba,ka sani shi Allah yana tsara lamarinsa yadda yaso,khairat suruka ce ta gari a azamana da ita dana yi,bata taƁa yimin wani abu da raina zai Ɓaci ba,kullum ƘoƘarinta shine ya za'ayi ta kyautatamin,don haka ni sam banji daƊin wannan abinda ka aikata ba."

Murmushi shahid ya yi wanda masu iya magana suka ce yafi kuka ciwo ya ce"Ammi ki daina magana ki yi shiru,saboda ni kaƊai nasan halin da nake ciki xuciyata tana yimin zafi sosai akan wannan sakin da na yi wa khairat,wanda ita kanta bata san na yi mata ba,ammi jiya fa dana shiga wannan bawan Allahn kiran sunan khairat kawai ya ke,sannan ciwon zuciya ya kamasa saboda Ƙaunar khairat da ya ke yi,Ammi ina da imani ina kuma da tausayi bazanso nima ayimin hakan ba,ni nasan nima zan iya shiga wannan halin akan Ƙaunar khairat,amman babu komai zan karƁi Ƙaddarata insha'Allah".

ya rungume mahaifiyarsa yana kuka me tsuma zuciyar me sauraro,shahid kiran sunan Allah kawai ya ke yi,halisa ta fito daga cikin Ɗakin da jaririyar a hannunta ta tsaya a tsaye tana kallon shahid wanda ke Ƙwance kan cinyar mahaifiyarsa yana kuka kamar Ƙaramin yaro.

sosai ya bata tausayi ta matso a hankali inda suke ta fara magana cikin harshen turanci ta ce"shahid ka yi haƘuri ka fauwalawa Allah komai,amman banji daƊin sakin da ka yiwa matarka khairat ba,don ba'a wasa da aure".

a hankali shahid ya tashi daga kan cinyar ammi ya ƙarasa wajen halisa ya amshi ƴarsa.wacce ke ta baccinta hankali ƙwance.me kama dashi sosai ya zauna yana kallon ƴarsa cike da so da ƙaunarta.sai yanzu ma ya tuno bai yi mata huɗu ba ba.wasu hawaye suka zubo masa ya share su tuno da halin da yarinyar zata kasance na rashin mahaifiya akusa da ita.shi da yarasa mahaifinsa ma ya damu sosai balle kuma mahaifiya.gashi nigeria ba wajen zaman bane dole zai koma masar.ko england tunda dai shi ɗan asalin ƙasar england ɗin ne.

yana gama raÉ—a mata sunan Ammi ta amshe ta.tana manna mata kiss a goshinta na jin daÉ—in ganin jikarta Æ´ar shahid gudan jininta.lallai wannan yarinya zata sha gata.ya ce"Ammi na raÉ—a mata suna da Rahma(khairat)taci sunan mahaifiyarta.

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿

1003. . . . . . .1004
Chapter 60 · 0% Book details