← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 63

Sashe 16

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

. ..dukkaninsu kallon Hajiya kaka suke ta ce"to me ye kuma akr kallona kamar na faÉ—i ba dai dai ba?shi fa Damas É—innan É—an shege ne ma bashi da uba,asalinsu arnan daji ne tun kakarsa ta wajen uwa,uban dai nasa ne ba'asan inda ya ke ba".ta faÉ—i hakan tana kallonsu.tabbas haka ne mahafiyarsu ta faÉ—i gaskiya sai dai mutuminne yana da hatsari sosai.

Wanene Alhaji Damas?

Adamu shine asalin sunansa nahaifiyarsa kuma Sadiya sunanta,asalin Damas ɗin sunansa ya haɗa dana mahaifiyarsa,ya taso da sonta sosai sai dai baiyi rayuwa da ita mai tsayi ba,aka shigo har cikin gida aka kasheta kisan wulaƙanci,sai dai ba kowane ya janyo mata wannan kisan wulaƙancin ba sai ɗanta Damas faɗa ne ya haɗashi da wasu miyagun mutane kuma ya cucesu akan harkar don haka suka ɗauki wannan mummunan matakin,don mutane ne marasa imani sosai tun daga mutuwar mahaifiyarsa shikkenan wani rashin imani yazo mai,kashe mutum awajensa ba kimai bane,kowa yasan yadda arnan daji ke da asiri,don ma a haka mahaifiyarsa ta musulunta kafin ta mutu shine ma yasa ta dawo cikin gari taje zaune gidan haya,tana ƴar sana'ar mai da ƙuli ƙuli dashi take samu take ciyar da ƴaƴanta,yaranta biyu mace dana miji,Ruƙayya da Adam Ruƙayya ita ce ƙarama sai Adam saɓanin Adam bashi da uba,ita kuma Ruƙayya taba da uba,shi Adam tun a garinsu ta haifesa ita kuma Ruƙayya sai bayan ta shigo birni ne ta yi auren ta haifeta auren ma kuma ya mutu.

Bayan mutuwar mahaifiyarsa ya taso cikin ƙuncin rayuwa shi ya ke zuwa ya samowa ƙanwarsa abinci ta kowacce irin hanya haka ya ke zuwa ya samo ya kawo mata,Ruƙayya ta kasance mai ƙyamar mahaifinta ako da yaushe,don wataranma idan ya kawo mata abincin bata ci don tasan ta hanyar daya samo.

Tun abin na Adam bai yi nisa ba har ya yi nisa,babu irin aikin da ba ya yi,shine safarar miyagun abubuwa daga ƙasar nan zuwa wata ƙasar,shine safarar mata daga waccen jaha zuwa wannan kai har ya zama har ƙasar waje,sai a ɗauki yara dag nan ace za'a fita dasu birni aiki amman kuma daga haka bazaka ƙara ganin ɗanka ba,shikkenan kunyi bye bye.

Ganin haka yasa ƙanwarsa Ruƙayya guduwa garin mahaifinta tunda tasan garin,Adam ya yi baƙin cikin barin ƙanwarsa gida don yana sonta sosai,kai tsaye shima yabar unguwar don daman saboda ƙanwarsa ya zauna agidan,don ya yi da ita ta koma gidansa daya ƙera taƙi yadda dole ya ƙyaleta ya cigaba da miyagun aikinsa,aka daina jin ɗuriyarsa a unguwar don daman suma ya fara isarsu,ko da idan ya yi wani kaifin ka kaishi wajen ɗan sanda to fa washe gari za'a sakosa don ya samu masu goya masa baya cikin manyan masu kuɗi na ƙasa baki ɗaya.Ga shi da mugun asiri don ko biyosa akayi ba'a samunsa saboda ɓacewa ya ke.

Wannan shine taƙaitaccen tarihin Alhaji damas.
****

daga zuwa na gidan Anty Khadija gidan ya koma gidan amarya sak saboda tsafta ina tashi da safe babu abinda na ke farawa da na yi sallah na yi azkhar da karatun alqur'ani to ajjewa na ke in fita in gyara gidan tsaf ɗakinta kuma sai bayan ta tashi na ke gyarawa,sannan inyi girki inyi wanka sai dai matar gidan ta fito taci ta koma tana yimin sannu,ni kuwa har mamakinta na ke,wata shegiyar rigar bacci tun ranar da nazo gidan na sameta da ita kusan sati biyu har yanzu bata wanketa ba,kuma me wanke yana zuwa wai sai ta ce mai ya tagi bata da wanki,kuma ga kuɗin me wankin anbata amman tana baƙin cikin fitar da kuɗin,ko da daman yaya Aliyu yasan halinta sai da ya siyo komai na kayan da ake buƙata komai da komai har nama sai da ya saka a fridge don shegen son kuɗine da ita.

Ko da nazo gidan har nan yaya mk ya ke biyoni yazo ya tafi ya barni da tunanin waninsa yaya Bilal don nifa babu namijin da ke cikin ƙwaƙwalwarnan tawa idan ba shi ba,ko da na yi tunanin ciresa araina bai taɓa ciruwa.sam ko kaɗan bana son yaya mk har tausayi ya ke bani yadda duk ya matu akaina,bana son nuna masa bana sonsa ne saboda halinda zai shiga ina dai lallaɓasa ne dai mu rabu lafiya.

Babu yadda baiyi dani ba da in amshi wayar daya kawomin naƙi amsa saboda Baba ya ce baza a bamu waya yanzu ba,haka ya koma da abarsa sai dai tun a fuska naga bai ji daɗi ba don fuskarsa ta canja,na lallaɓashi na bashi haƙuri.muna rabuwa na dawo cikin gidan na sameta tana cin abinci,daman aikin kensn taci abinci ta ƙoshi shine aikinta babu abinda take sai bacci,sai kuwa ta juyo ta ce"wai ni Khairat in tambayeki?"da sauri na ce"ina jin ki anty khadija".

Gyara zamanta ta yi sannan ta ce"wai da gaske yaya mk sonki ya ke"?.ta jeho mun wannan tambayar alokacin da ban shirya ba na ce"eh sona ya ke".na bata amsa nima sai kuwa ta ce"kai Æ´an gidan mu ma sai abarsu Bara'atu fa baki ga yadda take sonshi ba,kuma wallahi har soyayya suke amman shine ya komo wajenki?amman ya cika mayaudari".ta faÉ—i hakan tana kallona.
ɗan murmushi na yi sannan na ce"to ni yanzu Anty khadija meye na wa a ciki?ina shi ya ce yana sona ko?kinga ba ni na ce ina sonsa ba kinga ai ta ƙwana gidan sauƙi ko?soyayyarsu kuma da suke yi da Bara'atu su cigaba da yin soyayyarsu ko kada su cigaba wallahi ba damuna zaiyi ba".ina faɗar hakan na tashi na shige kitchen dan ɗora girki don ni ko san hirar yaya mk ɗinma bana son ayi,ni dai ba ni na ce ina sonsa ba?hasalima ni bana sonsa wallahi ni da zai auri Bara'atu wallahi daɗi xanji don sam bana son in koma gida ya cigaba da zuwa wajena a matsayin saurayi sam bana son hakan,wata dabara ce ta faɗomin na fito na samu Anty khadija har ta fara chat ita da yaya Aliyu sai shagwaɓe mai take wai ya dawo,ni dariya ma abin ya bani da kuma kunya bayan sun gama ne na ce"yauwa Anty khadija don Allah magana na ke son muyi".kallona ta yi sannan ta ce"to ina jinki ya aka yi"?.

"Anty na don Allah so na ke ki faÉ—awa hajiya kaka soyayyar yaya mk d kuma anty bara'atu".kallona ta yi sosai sannan ta ce"to wai ke ba kya son yaya mk É—in ne?".
"Eh anty".

É—an murmushi ta yi sannan ta ce"yo ke wa ki ke so"?.anxo wajen kallonta na yi babu ko kunyar ta na ce"na ce yaya Bilal."

da sauri ta tashi sannan ta ce"ah yarinya gyara zancanki wannan guy ɗin yafi ƙarfinki wallahi kina ganin mutum har mutum kamar shi ya yi kansa mutum mai izza ji-ji da kai uwa uba ƙyau da komai kin san ba fa zai yadda ya soki ba?don nasan duk nasan irin tsanar da ya yi miki sannan ki ce wai shi ki ke so?ni dai shawarar da zan baki ki yi haƙuri ku cigaba da lallaɓawa da yaya mk ɗin ina ganin hakan zai fiye miki".tun kafin ta gama naji wasu hawaye masu mugun zafi suna zubomin,yanxu idan na fuskance ta tana nufin yaya Bilal bazai iya aure na ba,saboda ni mummuna ce kuma baƙa?sosai maganganunta sukayi min ciwo sosai na tashi na tafi ɗakina na faɗa kan gado na fasa wani irin kuka mai cin rai,ciwo sosai na ke ji acikin zuciyata aduk sanda aka danganta ni da yaya Bilal bazai iya rayuwa dani ba yafi ƙarfina,tabbas nasan da hakan ya fi ƙarfina ne sa ba kusa ba,amman kuma ni a duba yadda na ke sonshi mana ayi min adalci.

ta baya na naji an dafa ni na juyo a hankali naga anty khadija ce ta ce"yi haƙuri ABIN CIKIN ƘWAI ta hajiya kaka,ki yi haƙuri kinji ban zata ranki zai ɓaci ba,insha Allah bazan sake ba kinji,ni da ki ke ganina zan tsaya miki har sai na ga kin auri yaya Bilal ɗinki".

Sosai na ji wani farin ciki ya baibaye ni na tashi zaune na rungumeta,ta buga baya na a hankali ta ce"yi shiru daina kuka kinji ta yaya Bilal".ɓoye fuskata na yi a bayanta wai ni kunya.

Tun daga ranar idan yaya mk yazo sai anty khadija ta ce mishi ai ina gidan koyon ɗinki da ta sakani,tun yana daurewa har dai rannan ya ce azuciyarsa zakusan baku da wayo idan kunsan wata baku san wata ba. rannan da ya tashi zuwa sai ya ɗakko Rashida da kuma aminiyata Maryam,wacce duk duniyw ba ni da aminiyar da ta wuce sai Rashida daman mu uku muke rayuwarmu ita maryam anan ƙasan unguwarmu take iyayanta masu matsakaicin ƙarfine ko islamiyayya da mukeyi tare babanmu ke biya mata har skull ɗinda ta yi babanmu ne ya ɗauki nauyinta,ganin dai irin zaman amanar mukeyi da ita tun muna ƙananu ita ta ce bata ra'ayin yin skull ta boarding mu kuma muka zaɓi boading ɗin to tun daga nan ne fa muka ɗan raba jaha saboda sai mun dawo hutu ne muke haɗuwa.
Ina kitchen ina girki kawai sai Naji anyi ihu an rungumeni ta baya,ina juyowa naga Maryam da gudu nima na ɗafeta muna juyi a kitchen ɗin sai kuwa ta ce mu da Rashida ne tana waje a hanya ne taji ciwo,to kinsan Rashida da kafiya yanzu haka da bin bango ta shigo ta hana ko in ɗan taimaka mata"...ai bata ƙarasa faɗar maganar ta ba da gudu na fito don ganin Rashidar to sai dai me Yaya mk na gani yana face ɗi na ya kalleni sosai ya yi dariya sannan ya ce"ah Hajiya me ɗinki ƙaraso mana"?.ya faɗi hakan yana ƴar dariya.

Wata best ce ajikina wacce ta É—ameni sosai sai zanin dana É—aura da kuma irin hular na ta zaren lilo wadda yare suka fiye amfani da ita musamman a awajen bacci.
Na rasa yadda zanyi gashi na riga dana fito ya gama kallona tsaf,sunkuyar da kaina na yi kamar wata munafuka kawai sai naji maryam ta zuramin hijabin da ta zo dashi da gudu ta koma farlon.
Chapter 16 · 0% Book details