← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 63

Sashe 10

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon kaka na yi rau rau da idanu na ce"a'ah ni dai kaka babu inda zanje wannan sashen na ki mutum yaje ki yi ta yimai masifa abu kaÉ—an ki zageni".galala Hajiya kaka ta yi tana kallon Khairat ta ce"eh lalla ai barewa ba tayi gudu É—anta ya yi rarrafe ba eh halin Malik ki ka yi tsaf na taurin kai to wallahi ko zaki yi kashin jini yasin sai kin bini sallamammiya kawai".tana faÉ—ar hakan ta fito.

A farlo suka haÉ—u da Nadiya da iman suna kallo a tv da sauri kaka ta murza idanuwanta ta ce"yo ikon Allah khairatu zo ki ganemin waÉ—annan masu halin mutanen annabi luÉ—i sunyi rashe rashe suna kallo,ko uban waye ya basu damar zama suna kallo?su da sukayi wannan mummunan laifi".

Da sauri su Nadiya suka kalli kaka sukayi wuƙi wuƙi da idanuwansu,don sun san kakarsu aƙwai tonon asiri suka haɗa baki wajen ce wa"hajiya kaka ina wuni".zaro idanu kaka ta yi sannan ta ce"oh ni ina ganin rashin hankali a gidannan ke Nadiya don ubanki sadakar yalla ce ta raɗamin wannan sunan Hajiya?ke kuma imani fulanin daji ce ta raɗamin ko kuwa?".da sauri suka haɗa idanu don mamakin zagin da kaka ta yi musu,ganin mamakin zagin da ta yi musu suke ta ce"to wannan kallon da kuke min munafukai nima ƙwaƙwuleni zakuyi?kamar yadda kuka yi wa ƴar uwarku khairat?to wallahi ahir ɗinku don ni na fi ƙarfin maitarku,kuma bari Malik ɗin ya dawo duk sai an kori masu aikin gidannan ku koma masu yi mana aiki,tunda rashin aikin yi ne yasa kuke saƙule ƴaƴan mutane".

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*miss green ce*
[23/09, 16:17] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------

*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------

masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.

*Sirrinmu*

mata mu kasance masu tsafta,ladabi,biyayya,haƙuri,juriya.domin shi namiji ba ta ƙarfi ake samunsa ta lallami da lumana.Allah yasa mu dace amin.
----------------------------------

15⬜16

. . . .Ina ƙwance duk abin duniya ya isheni tun jiya Yaya Bilal ya i'so gidan amman tsoron fita na ke don bana son abinda zai janyo mana tashin hankali dashi don matuƙar yazo to fa tabbas sai an ɗebi ƴan kallo,shi yasa ma na rufawa kaina asiri na yi zamana a ɗakin,ina jin tafiyar mama ta taho na yi saurin lulluɓa da bargon don bana son ta aikeni gun kaka don yau ita ce da girki.

"Khairat!Khairat!! Mama ta fara tashi na, na buɗe idanuwa na gaisheta sannan ta ce"kalli garin mana rana ta fito sosai amman kina cikin ɗaki kina bacci?yanxu Khairat kin lalace da bacci wallahi da tun kafin in tashi zaki shiga kitchen ki girkamin abinci?amman yanzu sai na tashi da kaina na yi sannan kuma ki ƙi tashi da wuri?ni dai gidan miji na ke jiye miki don wannan salon da ki ka ɗauka ba mai ɓullewa ba ne?yanzu ki tashi ki kaiwa kaka abinci don ya zama ready".tana faɗar hakan ta fita nasan halin mama ba ta san jira don haka na tashi da sauri na shiga ba yi na yi brush sannan na wanke fuskata,daman na yi sallah tun asuba gabana yana ta faɗuwa don bana son na haɗu da Yaya B,don nasan ko ban kulasa ba dole ne na yi laifi,don idan na gaishesa ma ba ya amsawa ko kallon inuwa ta bayayi,ni na rasa wannan wacce irin tsana ce haka?.

ina fitowa farlon na iske Amira ƙanwar su iman tana homework,da murmushinta ta juyo ta ce"la Anty daman ke na ke jira ki tashi wallahi".murmushi na yi mata sannan na ce"to little sis me kuma ya faru?".shagwaɓe fuska ta yi sannan ta ce"assignment aka bani kuma wallahi na kasa yi guda 3,ne na yi ɗaya sauran ban iya ba,kuma na bawa su Anty iman sunce wai baza su iya ba aikin na da wahala"?.

"To Meeraty bari dai yanzu in kaiwa Kaka abinci in dawo sai in yi miki kinji?"da to ta amsamin ni kuma na wuce don kai aiken kaka.inason Amira don kaf cikin Æ´an uwanta ta fita zakka ita kaÉ—ai ce take sona acikinsu sauran duk sunbi layin iyayensu mata.

Tun daga ne sa na ke jiyo ƙamshin turarensa gabana yana ta faɗuwa na tsaya cak sai da na karanta addu'ar tsoron mutune sannan na yi hanyar.

Ƙamewa na yi kawai ina kallonsa yadda ya haɗu cikin wata farar jallabiya farar fatarsa sai shining take kamar ta mata,sak balarabe haka ya fito,shima tun daga nesa ya hango ta yaga ta kafesa da idanuwa azuciyarsa ya ce kai wannan yarinyar kamar mayya take wallahi ƙwata ƙwata ba tada kamun kai irin na mata,shi fa arayuwara na fi son mace mai kamun kai,tun ba yau ba yasan Khairat na sonshi irin son nan na ƙarshe,shi kuma tun daga ranar yaji ya yi wani irin muguwar tsanarta wadda ko ganinta ya yi sai yaji gabansa yana faɗuwa ainun,ga ta wata mummuna da ita don kaf gidan kamar ita Aka ɗorawa muni.

Har ya wuce ta kusa dani ban daina kallonsa ba,ya yi tsaki ya wuce shima sashen kaka É—in ya shiga,cikin faÉ—uwar gaba nabi bayansa muka shiga atare.

Kaka tana sharar É—akinta ta ce"kai!"cikin tsawa duk sai da muka tsorata ta ce"duk ku tsaya anan shara na ke ko mijina yasan idan ina shara tsayawa ake har sai na gama don bana son ju shigarmin da datti".

"to in koma kenan ko?"ya ce wa Hajiya kaka kawai sai na ji ta ce"kai soja ni na i'sa in ce ka koma?jiya ma fa haka ka aikomin da abin arziƙi lodi lodi,yauma ka ga kayan shayin da ka lodomin shi na haɗa da safen nan nasha abina,kafin a kawomin makararren abincin da aka saba kawomin".ta kalli abincin hannuna ta yi wani gyatsine.

Shiga ɗakin ya yi ni kuma naja na tsaya har ta gama sharar ta sai kuwa ta ce"to dogariya ke ko kunya ma baki ji ba?ina ta aiki ko ki taya ni?kema kin fara ɗakko hali irin na su Nadiya ko?to kuwa wallahi wahala zakisha,agidan miji don ni har na fara tausayin jikokina da aka haɗasu dasu Nadiya don babu abinda suka iya sai rashin arziƙi".
ni dai bance mata ƙala ba na wuce zuwa ɗakin cikin nutsuwa na ajje abincin sannan na gaisheta,na wuce ɗakinta don na tuno duk ranar asabar ni ke mata gyaran kayan cikun sif ɗinta.
Ina jin kaka bayan tafiya ta ce"Allah sarki Abin cikin ƙwai yarinya kirki yanzu haka fa gyaran ɗakin za ta yimin abinda kaf jikokina basa yin hakan,Allah ya baki miji nagari yarinya ga haƙuri ga kunya".ta faɗi haka tana buɗe abincin dana kawo mata.

Azuciyarsa ya ce lallai bakisan yarinya mai kunya ba abinda idan taga maza kamar za ta cinyeshi take,ita wannan maitar ta ta ma har tafi tasu Nadiya ma.yana cikin wannsn tunanin yaji kaka ta fashe da kuka ta ce"ikon Allah yau kuma abincin inyamurai akayi agidan,ka duba fa ka gani Bilal?wai ruwan shayine da wannan soyayyiyar ayabar,ayabar da tunda na ke ban taɓa cinta ba ko da na yi zaman cikin yare,shine ni za'a kawomin ni wallahi bazan ci ba".ta faɗi hakan tana ajje abincin a gefe.

Rarrashin kaka ya dingayi har ta É—an É—auki plaintain É—in ta fara yaga kamar kashi,abinda aka kawo mata cikin flask sai ga kaka ta kusa handumeta ta ce"ikon Allah É—annan ashe dai daÉ—ine da wannan abar?shiyasa ka takuramin naci gaskiya tana da daÉ—i,ita ba doya ba ita ba dankaki ba gata nan dai.
Ana cikin haka na fito na ce"Kaka na gyara miki ɗakin ni zan tafi zanje islamiyya ne,ko aƙwai abinda ki ke so"?.murmushi ta yi sannan ta ce"wallahi ga ɗakin nan sai ƙamshi ya ke Allah dai ya yi albarka ya baki miji nagari abin son kowa".da Amin na amsa mata na ɗan daure na ce wa Yaya Bilal"sai anjima".ko kallona bai yi ba ya cigaba da danna wayarsa yana dariya,kaka ta kula da hakan sai dai bata yimai faɗa ina nan ba sai da na fita ta ce"haba Bilal wai me yasa ka kewa yarinyar nan haka ne?ina fa lura da kai ko gaishe ka ta yi baka amsawa me yasa haka ne?".

Ɗago kansa ya yi sannan ya ce"kai kaka ni fa idan damuna zaki yo sai in fita?kawai daga shigowarta sai ta haɗamu".?ganin irin mirmisisin da ya yi da idanuwa bata ƙara ce masa komai ba suka cigaba da hirarsu kaka na ɗarsa wani abu azuciyarta.

Ina fitowa na samu wani ɗan lungu na fashe da kuka mai ƙarfin gaske,na yi mai i'sa ta sannan na juya xan tafi sai muka ci karo da yaya Aliyu da Yaya Mukhtar.da mamaki suke kallona sannan suka haɗa bakinsu wajen ce wa"a'ah little sis me kuma ya sameki haka?me ya faru agidan?".saurin goge fuska ta na yi to me zance musu?ce musu zanyi inason yaya Bilal shi kuma yana wulaƙanta ni ko me?no ai abin da kunya.

Ganin bance komai ba suka sakani agaba wai sai na gaya musu abinda ya faru?bakina yana rawa na ce"kukan rabuwa ta na ke yi da Rashida".na faɗi hakan cikin shagwaɓa.dariya sukayi dukansu musamman yaya Aliyu ya ce"to ikon Allah kukan kuma tun yanzu?ai haƙuri zakuyo dukanku don ku daman rayuwar mace ƙanƙanuwa ce daga gidan iyayenta sai gidan miji,don haka ki share hawayenki kinji?"da to na bisu sannan na wuce.
Chapter 10 · 0% Book details