← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 63

Sashe 19

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna dawowa daga islamiyya kai tsaye na wuce sashen hajiya kaka,ina shiga na tarar da mutane sosai,muna cikin gaisawa sai kuwa hajiya kaka ta ce"inno kin gane wannan kuwa?".

"A'ah gaskiya ban gane taba?kinsan rabona da birni na daɗe tun su khairat suna ƙanana".sai kuwa kaka ta ce"ahaf ai wannan i'ta ce khairat ɗin?".gwalalo idanuwa inno ta yi sannan ta ce"ikon Allah girman ɗan mutum babu wahala yau shekara 17 kenan rabona da garin nan tun sunansu,amman kinga yara sunyi wayo".

ɗan murmushi na yi kawai sai kuwa kaka ta ce"khairat sunzo saukarku ne fa?ga mairo cen don Allah ta zauna a sashenku,tunda ita dai ta dawo nan da zama yanzu,kunga idan tana cikunku za ta ƙara gogewa".kallon wadda aka kira da mero na yi sai kuwa ta ce"hannunki dafatan kina lafiya".nima murmushin na maida mata muka cigaba da hirarmu,na fuskanci mairo aƙwai ƙauyanci sosai akanta.ga ƙiriniya sosai ni kuwa dariya kawai na ke azuciyata don tun yanzu har sun fara faɗa da Hajiya kaka.

****
Su Rashida suna zaune a farlonsu harda mahaifiyarsu sai ga yaya Bilal nan ya shigo,da sauri Su Rashida suka tashi don sunsan karon nasu bai musu ƙyau dashi.

Suna fita hajiya Ruƙayya ta kallesa ta ce lafiya kuwa Bilal".?

Babu abinda ya ɓoye na dangantakarsa da Jidda,har unguwarsu babu abinda ya ɓoye mata.sosai ta yi murna da jin hakan sannan ta ce"to insha Allah kuwa xan gayawa Babanku idan ya dawo,sai ayi bincike sosai don daga jin labarinta mutuniyar kirki ce sai dai yana da ƙyau binciken.
*****

"wallahi khairat atsorace na ke sosai,don gaskiya ni tsoron rikici ne dani ko yaya ya ke?,ni fa har yanzu ban amsawa yaya Aliyu ina sonsa ba?".

kallonta na yi sosai sannan na ce"ke dai kawai ki fito kice min bakya son yaya Aliyu?amman ina ruwanki da anty khadija wanine ya ce kada ta riƙe mijinta da ƙyau".?

Murmushi maryam ta yi sannan ta ce"hmm khairat ko dai ma yaya ne?ai macece Æ´ar uwata nima kuma bazan so hakan ya faru dani ba".ta faÉ—i hakan kamar za ta yi kuka.

"Maryam ni dai don Allah ki taimakeni kiso yaya Aliyu,don wallahi ina jin tausayinsa wannan auren da zaiyu shine zai kawo solution ga dukkanin matsalolin da suke faruwa tsakanin yaya Aliyu da anty khadija".

"Khairat bari in fito miki a mutum sosai kinga nan na daɗe inason yaya Aliyu amman ban taɓa nunawa kowa ba,sai dai in shiga ɗaki inyi kuka idan abin ya dameni,amman duk da haka ina jin tsoron abinda zai faru khairat?kin san ku ƴan uwane ni kuma bare ce acikinku to kinga aure na da yaya Aliyu zai iya kawo matsala tsakanina dashi."

"Babu wata matsala da zai kawo?".da sauri muka ɗaga idanuwanmu Rashida ce tsaye akanmu tana murmushi ta samu waje ta zauna ta ce"Maryam haƙiƙa na jima ina jiran wannan ranar tazo da wani ɗan gidanmu zai aure ki maryam,kina da tarbiyya sosai da kuma nasaba mai ƙyau babu namijin da zaiso ya auri macen da take da hali irin na anty khadija.tunda har ya buɗe bakinsa ya ce yana sonki don Allah kada ki bawa maraɗa kunya ki yadda musha biki".ta faɗi hakan tana dariya.

Maryam dai ta kasa ce wa komai,a wani ɓangaren na zuciyarta son yaya Aliyu ne tsan-tsa acikinsa,tsoronta ɗaya anty khadija don ita sam a atsarinta ba zata so ta auri namiji mai mata ba.

Nan dai mukaci gaba da hirarmu akan saukarmu da kuma bikinsu Rashida,anan ne Rashida ke yi mana albishir da Babansu ya nemo mana admission a makaranta,ni ɓangaren law sai kuma Rashida, nadiya,Iman, khalisat,Bara'atu sai kuma maryam aminiyarmu duk harkar lafiya ne amman kowa da nasa ɓangaren.

Ni daman tunda na taso ina masifar son karatun lawyer don ina tausayawa talakawa musamman idan suka shigar da ƙara aka yi biris da abin ko kuma a cuce su,ko kuma fyaɗe da akewa ƙananan yara wanda ayanzu ya zama ruwan dare sai dai Allah ya kawo mana mafita.

Soyayyar A.D da jidda sai daɗa haɓaka take,wani mugun son Bilal ne ya ke damun jidda ko bacci zata yi idan ta rufe idanuwanta shi take gani,ta rasa wani irin love take masa.uwa uba ga irin taimakon da ya ke mata ba kaɗan bane,yanzu haka ya bada kuɗi a ruguje gidansu a sake musu wani,daga haɗuwarta dashi zuwa yanzu ya kashe mata kuɗi yafi a ƙirga,ko a mafarki ita jidda bata taɓa tunanin za ta auri miji irin Bilal ba,haƙiƙa tafi kowacce mace sa'a.ga wani irin mugun kishinsa da ke cin zuciyarsa sai take ji kamar duk ranar da ta ganshi da wata mace za ta iya yin komai akanshi.

****

Ina shiga sashen Hajiya kaka na tarar Mero ta tsaya tana wani muzurai,Hajiya kaka na tsaye da É—an madoki hannunta,tana bin mero ita kuwa mero sai gwaliya take wa hajiya kaka tana dariya tana mata gwalo tana rufe ido.

Sosai abin ya bani dariya,sai kuwa hajiya kaka ta ƙara biyo mero ji ka ke timm,kaka ta faɗi a tsugunne ta kasance a ƙasa hajiya kaka ta saki kuka ta ce"shegiyar yarinya aljana wallahi na ɗauki masifa tun ba'aje ko ina ba".

ta faɗi hakan tana fashewa da kuka,sosai na tausayawa hajiya kaka na matso na ɗagata sai kuwa mero ta ce"ai wallahi don baki san yadda na taɓa kada megari bane shiyasa,har rawar banjo na sakasu da na saka musu karara ajikinsu,ni fa wallahi ba'a taɓani in ƙyale".ta faɗi hakan tana yi wa hajiya kaka dariya.

Abin takaici abin baƙin ciki yarinya ƙarama na caskare hajiya kaka amman ta kasa magana,ina ƴar dariya ta na ce"to wai kaka me ma ya haɗaki da wannan basa mudiyar yarinyar?ai sai taji miki ciwo wallahi".

Da sauri kaka ta ce"ai wannan shaiɗaniyar yarinya ce ta ƙarshe,wai fa daga na ce ta ɓatamin tap ɗina shikkenan take wannan rashin mutuncin".muna cikin maganar yaya Salim ya shigo fuskarnan a murtuke yasha ɗanyar shaddarsa skye blue ya yi ƙyau sosai don shi daman da Babanmu ya ke kama sosai kamar an tsaga kara.

Sai kuwa ya ce"a'a Hajiya kaka waye kuma ya taɓa mana ke?".kukan ta cigaba da yi ta faɗa masa duk abinda mero ta yi mata.cikin ɓacin rai ya ce"ke ma kaka ai kinga matsalarki ko wace shara sai ki kama ki ɗakko mana i'ta,ai gashinan yanzu kin ɗebo ruwan dafa kanki".

Sai kuwa yaji mero ta ce"caɓɓi ai wallahi ko yanzu idan ta yi min wallahi sai na rama,tsohuwa masifaffiya kawai. . .tun kafin ta ƙarasa maganar yaya salim ya ƙwarfeta ta faɗi ƙasa ta hau kuka wai ya bugeta a cikinta,ƙara haurinta ya yi sai kuwa ta tashi zumbur za ta arta ana kare ya cafkota sai kuwa ta rungumesa taba ce wa"don Allah kaji ƙaina ka ƙyaleni wallahi ƙafafunka da guduma aka yi su".

wani irin shork yaji tunda ga kansa har ƴan yatsunsa da sauri ya saketa yana nuna ta da yatsansa ya ce"to oya! ɗauki bocket kije ki ɗabo ruwa a tap ɗinmu ki cika mata komai ko kuma inyi miki tsinannan duka wawiya ƴar ƙauye kawai.

Sosai ta zabura ta É—auki bocket É—in ta fita tana mita,inno da ke cikin É—aki tana yi wa Æ´ar ta addu'ar Allah ya shirya mata mero.tunda mero ta taso bata huta da magana ba ita ce ta shiga gonar wane,ta tsokani wane.

Ni na nuna mata yadda ake É—iban ruwan a tap sannan na wuce sashen maman arman.

Tare da maman arman muka fito sashen Hajiya kaka,sai dai fa muna zuwa naga mero tana kallon kaka tana murguÉ—a baki,kaka kuwa tana tsaye idanuwanta sun cika,na ce"a'ah hajiya kaka bata gama É—iban ruwan bane?".

Kaka ta ce"hmm taya ni baƙin ciki khairat yarinyar nan hawan jini take so ta sakani,yanzu fa tunda ki ka fita babh abinda na gani na alamar an zuba ruwa."

sai kuwa mero ta ce"anty khairat don Allah zo muje in nuna miki inda na zuba ruwan"binta na yi kamar raƙumi da akala sai me a masai ta zama take ta zuba ruwan".

sai kuwa mero ta fashe da kuka ta ce"wallahi anty tun ɗazu na ke ta zubawa ya ƙi cika"?sai kuwa ta fashe da kuka.

Dariya ce ta kamani har da riƙe ciki,lallai na yadda da abinda kaka ta faɗa ƙauyanci da gidadanci sun cika ƙwaƙwalwar mero.

*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

*miss green ce👉🏿*

[23/09, 16:19] Miss Green🍀: *_🥚ABIN CIKIN ƘWAI..!🥚_*

NA💋
*_Ummu maher(miss green🍀)_*

GAWURTATTU BIYAR✨✨

27🟨28
Chapter 19 · 0% Book details