← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 63

Sashe 32

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*addu'ar samun lfy ga ko wani irin ciwo*

an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ɗauka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ƙasa sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka;

"bismillahir turbati ardina biriqati ba'dina yashfa Taqimuna bi'izni rabbina".

47. . . .48

. . . .Nasha kuka na sosai kamar ma bazan daina ba,na tashi na shiga banÉ—aki Na É—aura alwala sannan na shimfiÆŠa sallaya na tayar da sallah,na yi isha'i da kuma shafa'i da wuturi Na ÆŠaga hannaye na sama ina kuka ina addu'ar Allah yasa yaya Bilal wataran yaso ni kamar yadda na kesonshi,Allah kuma yasa albarka acikin auranmu.

na shafa addu'ar na tashi na Ƙwanta na Ɗaga idanuwa na sama ina tuno da wasu abubuwa,waƊanda suka wanzu arayuwata,gashi haryanxu ban samu sauƘinsu ba.

Babu zancen zuwan ango,don tun ina yaudarar kaina wai ina tunanin zaizo har naji shiru babu shi babu labarinsa,na rintse idanuwa na hawaye yana fitowa.

***
"Jidda ki faƊamin abinda ya faru da rayuwarki?Jidda ni fa ba yaro bane balle kice ko yau ne aka haifeni?nasan komai ayadda ya ke duk dani ba mazinaci bane amman ki sani shekaruna sun kai in san hakan,kada ki Ɓoye min komai,na yi miki alƘawarin indai ki ka faƊamin gaskiya,bazan taƁa zarginki ba".

ya faÆŠi hakan yana kallon jidda wacce ta yo tsuru kamar munafuka,tana kallon yadda Bilal duk yana yinsa ya canja jijiyoyin kansa sunsha ta ruÆŠu-ruÆŠu.

tana kakkarwar jiki dana baki ta ce"Bilal ka yi haƘuri haƘiƘa banyi maka adalci ba,dana Ɓoye maka komai na rayuwata,amman yau zan gaya maka gaskiyar lamari."

Kasa cewa komai Bilal ya yi zuciyarsa na masa wani irin turiri,ta cigaba"Bilal wata rana baba na ya aikeni shago,naje na yo siyayyata na fito,wasu mutane waƊanda bansan su waye ba,suka Ɗauremin Idanuwa na suka sakani a mota sukayi gaba dani,tun daga ranar Bilal na rasa martaba ta na Ƴa mace,na rasa mutuntaka ta baki Ɗaya,Bilal bayan wannan lokacin nasha wuya sosai don har sai dana Ƙwanta agadon asibiti,an Ɗaukama ko ina da wata cuta ne,ashe babu komai wahalar da nasha awajensu ne."ta faƊi hakan tana shessheƘar kuka.

sosai ta bawa Bilal tausayi,sai dai awani sashe na zuciyarsa sai ya kasa gasgata hakan,gani ya ke kamar ba haka bane?wani sashen na zuciyarsa kuma ya ke tunatae dashi ga barin zargi tsakaninsu don muddin zargi ya shiga to babu aure.

samun kansa ya yi da rungume ta yana Ɗan bubbuga bayanta,har ta yi shiru,sannan ya Ɗaga Ƴar Ƙaramar haɓarta ya ce"jidda ke matata ce,ki daina saka komai aranki game da hakan,insha Allah na yi miki alƘawarin zama da ke da amana,kuma babu mai jin wannan sirrin namu".ya faƊi hakan yana Ɗaga mata gira ta yi masa wani mugun murmushi wanda ita kaƊai ce tasan manufar yin hakan.

tun daga ranar komai ya koma dai-dai,sosai jidda ke jin daƊin Bilal,don yana nuna mata so da Ƙauna,tare da tarairayarta,abinda yafi yi mata daƊi bai wuce yadda Bilal ya watsar da matarsa ba,don haka sai ta Ƙara miƘe Ƙafafuwa,wai ita gata matar so.
****

Rayuwa ta yi min zafi,komai ya tsayamin cak don iya wulaƘanci yaya Bilal ya yimin shi,yau ina Ƙwana huƊu agidansa,amman ko shinge na baizo Ba,ballan tana ma ya duba lafiyata,Ƴan gidanmu cak suka Ɗauke Ƙafarsu babu wanda ya leƘomin.

waya ta dake ringing na Ɗauka Ƴar gidan mama ce Ƙanwar mahaifinmu me suna maryam,na Ɗauka naji muryarta kamar zata yi kuka ta ce"khairat yau dai gani nazo gidanku amman me gadi yaƘi ya barni in shigo,wai hajiya jidda bata bayar da oder in shigo ba,jiya ma baƘi da yawa sunxo amman wallahi ba'a basu damar shigowa ba,wai wannan wani irin abune haka ya ke faruwa".?

jin na yi shiru yasa ta ce"a to nidai babu inda zani,don yanzu na kira hajiya kaka ta ce kada in sake in dawo sai na shiga,to nima Ɗin na yarda da maganar kaka don haka ki fito ayi ta ta Ƙare".ƙit ta kashe wayar ba tare da ta Ƙara magana ba.

abin ya yimin zafi sosai,na ciji leƁena na Ƙasa azuciyata na ce eh lallai jidda tazo da sabon salo,ai kuwa bazai taƁa yiwu a hana Ƴan uwana shigowa gidan ba,tunda duk gidan mijinmu ne.

na saka takalmina soso mai tudu wanda na ajje don sakawa afalo,na fita raina aƁace Na yi hanyar gate Ɗin,a garding Ɗin gidan na hango jidda tana waya,ta kalleni ta zubar sannan ta yi saurin kashe wayar,don daman ta yi hakanne don in hassala,kuma gashi na hassala Ɗin.

ina zuwa na kalli me gadin wanda keda kayan kaki ajikinsa,na ce"meye dalilin Hana Ƴan uwana shigowa Gidan mijina"?.

Cikin girma mawa ya ce"hajiya ki yi haƘuri jiya me gidan ya yi tafiya kuma bai bani apointment akan wani zai shigo ba,ya bani umarni akan duk wanda zai shigo in kira hajiya jidda idan ta yadda sai mutum ya shigo."
kallon jidda na yi wadda ke nufo inda muke.tana sanye da wani shegen takalmi mai mugun tsayi,ga wani uban glass afuskarta no respect.taɗan janye glass ɗin kaɗan sannan ta ce"obinna duk wanda bazai bi dokar mai gidan ba.ka ƙyalesa kada ka kuma wata magana,ka koma bakin aikinka".

Ta faÉ—i hakan tana mana wani kallon banza,Maryam ta ce"hmm idan kunsan wata baku san wata ba".sai ta danna wayarta ta kira hajiya kaka tana shaida mata abinda ya faru.

Kai tsaye Hajiya kaka ta shiga ɓangarensu Bilal.ta yi sa'a kuwa Baba Abdullahi yana nan suna hira da matarsa.hajiya Ruƙayya na ganinta ta gimtse fuskarta don tasan ba alheri ya kawo hajiya kaka ba.

Hajiya kaka ta nisa ta ce"Ruƙayya zo ki dake ni ba murtuke fuska ya kamata ki yi ba?uwar rashin ɗa'a.yanzu gashinan kin koyawa ɗanki Bilal ya wulaƙanta ƴan gidansu,saboda shima yanzu ya yi gida ko?to wallahi ko awata uwa duniya ya ke ki kirasa ki faɗa masa wallahi ya yi maza yabar maryam ta shiga gidan nan idan ba haka ba.masifar akanki zata ƙare,yo idan ma ba rainin hankali ba tayaya za'ace a hana ƴan uwan mutum shiga gidan ɗan uwansa?a ina aka taɓa yin hakan?ko ke ƴan uwanki sun taɓa zuwa nan aka hanasu shigowa?to wallahi ahir ɗinki daga ke har ɗan naki mara kunya".

sunkuyar da kai hajiya Ruƙayya ta yi,Baba Abdullahi ransa yakai ƙololuwar tashi,ya nisa ya ce"Ruƙayya yaushe Bilal ɗin ya yi tafiya?ashe shi yanzu idan zaiyi tafiya haka kawai ya ke yinta?saboda ya zama babba ko?babu saka albarkar iyaye?."

"wallahi nima bansan ya yi tafiya ba?amman ka yi haƙuri".

Number Bilal ɗin ya kira,ya ɗaga yana tsaka da aiki bayan sun gaisa ne ya rufesa da faɗa sosai,ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,Bilal ya yi shiru kawai yana jin faɗan mahaifinsa,ya basa haƙuri ya kashe wayar ya kira obinna ya bada umarnin maryam ta shiga.

Maryam na shiga ta kalli jidda ta ce"to uwar mata yanzu ma ai sai ki hanani shiga?uwar iyayi mai son raba kan Æ´an uwa".

Ta faɗi hakan tana hararar jidda ɗin.jidda ta yi ƴar dariya ta harɗe hannayenta a ƙirji tana wa maryam ɗin kallon rainin hankali ta ce"hmm kin bani dariya wallahi,ai ta banzar tunda ita dai wacce take cikin gidan ba tada wannan matsayin da zata bada doka da order aji,don haka ni baku burgeni ba".

Ta faɗi hakan tana nuna halin ko in kula,har maryam ta yi gaba sai kuma ta dawo ta ce"hmm jidda ma ki ke kowa?to idan ban mayar miki ba kice ni ba jikar hajiya kaka bace?kema da ki ke wani fiffigewa wai ke gaki star awajen miji ko?to wallahi kiji tsoron Allah don duk matar da ta saka ido ana wulaƙanta ƴa mace tana jin daɗi to wallahi wataran itama sai an wulaƙantata wataran itama,don haka ki guji ɓacin rana".

Dariya sosai Jidda ta yi ta ce"oho dai tsabar rashin zuciya ya ce baya so amman sai da aka liƙa masa."ta faɗi hakan tana tin tsirewa dariyar muguntar ta faɗamin magana.

Har na yi gaba sai kuma na dawo,na kalleta idanuwa na suka cika ɓam,da hawaye ban yarda sun zubomin ba na wuce sashe na.na barsu ita da maryam suna ɗauki ba daɗi.

Sosai maganar da jidda ta faɗamin take bin dukkan gaɓɓan jikina,na ƙwanta akan ɗaya daga kujerun farlona na saki kuka mai ƙarfi,tabbas na cancanci Jidda ta yi min gori,yau ƙwanana huɗu amman ko albarkacin haƙƙina da ke kansa ai ya kamata ya saukemin,amman madadin rashin hakan gashinan matarsa na wulaƙanta ni.
"Haba Khairat yanzu don wannan banzar ta faɗa miko magana shine ki ke kuka?ai kuwa matuƙar zaki dinga yi mata kuka to kuwa ta samu lagon ƙuntata miki agidan aurenki,ki zama jajirtacciya agidanki,nasan kina da dauriya amman ki ƙara daurewa kinji".ta faɗi hakan tana sharemin hawaye na.

Nan dai muka shiga hira take cemin gobe za'a kawomin gara ba'a gama haÉ—awa bane,na ce mata babu komai.

Ta ce"yanzu ma daga asibiti na ke naje dubo Rashida,kinsan tun bayan bikinku ba tada lafiya".ta faÉ—i hakan cikin damuwa.
Nima cikin damuwar na ce"innalillahi ashe haryanzu jikinne?shiyasa dana buga mata waya naji shiru?tun shekaran jiya na ke kira amman switch up".na faÉ—i hakan cikin damuwa.

Maryam ta ce"ke dai bari ɓari ta yi wallahi ciki wata huɗu".da sauri na saki salati tsabar tausayi kamar zanyi kuka,na ce"yanzu ya jikin na ta?".maryam ta ce"ai da sauƙi ma yanzu don wallahi ranar da tayi ɓarin da mukaje baki ga ba abin tausayi,ko magana bata iyawa sai dai idanu,don ta zubar da jini sosai ai yanzu da sauƙi".

Tuni jikina ya hau tsuma na idanuwa na suka kawo ruwa,don komai idan aka saka Rashida aciki mai mahimmaci ne,tun muna ƙanana idan ɗayanmu ba shida lafiya to zaka samemu cikin wani hali.

Maryam ce ta dinga rarrashina,amman duk da haka ban daina kukan ba,tunanin halin da Rashida take ciki shine yafi tsayamin,na ce"insha Allah zanje in duba ta fatanmu dai Allah ya bata lafiya me É—orewa,na faÉ—i hakan muryata na rawa.
***

Har washe gari jikina duk babu daɗi,na kira wayar yaya Aliyu mijin Rashida yafi sau 5 amman bai ɗaga kiran ba,ƙarshe dai na haƙura.
Chapter 32 · 0% Book details