← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 63

Sashe 46

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ƙara fashewa da kuka ina kallon madubin dake jikin ɗakin nawa na shafa ƙasan marata na ce"Hajiya kaka dole ne fa inyi kuka,ahalin yanzu cikine dani fa?".da sauri Hajiya kaka ta dafe ƙirji ta ce"Alhmdh ai ni na yiwa Allah godiya daya sa kina da cikin ma,wannan cikin shine zai ƙara tsone idon maƙiya musamman ma Ruƙayya surukarki,don ɗazu da kiga dawo Ammaru yazo ya bani labari tana cen tana zaginki wai karuwa me bin maza,kinga kuwa yanzu zata tabbatar da hakan sannan hankalinta zai daɗa tashi".ta faɗi hakan tana ɗaga hannunta sama Alamar tana godewa Allah.

Haushin Hajiya kaka ya kamani na ce"ayya hajiya kaka bazaki gane abinda na keji acikin zuciyata ba,sosai na kejin tsanar Bilal araina,na rabu dashi har abadan,ashe harda ƙullin cikinsa ajiki na?wallahi kaka zubarwa zanyi".na faɗi haka ina share hawaye harda majina.

Hajiya kaka ta yi salati ta sanar da ubangiji sannan ta ce"ikon Allah ikon gaske,idan baka mutu ba zaka yi kallo khairat kina cikin hayyacinki kuwa?ko kuwa dai kin samu taɓin hankaline?kin zama me taurin kai Khairat,ba khairat ɗin dana sani adacen baya bace khairat ɗin dana sani acen baya yarinya ce me jin maganar nagaba da ita,amman ba wannan wadda ta tsaya agaba na tana yimin musu ba."

"Kaka nifa wallahi zubar da cikin nan zanyi,tunda ubansu ma bai san da cikin ba,kuma gashi yana zargina kinga ai zai iya ce wa shi ba cikinsa bane,to kinga idan har na bari na haifesa zai iya ce wa shi ba cikinsa bane,kinga me zan ce wa yaron?ce masa zanyi ubansa ya ce shiba shine ubansa ba?kinga kaka bani da amsar da zan bashi dole in zubar da cikin yanzu kinga kowa sai ya huta".

"To dan ubanki Malik baza'a zubar ba,zanga yadda za'ayi ki zubar da cikin idan har ban baki damar hakan ba,daga yau babu ke babu fita daga gidan nan sai inga ta yadda zaki xubar,tunda ke Æ´ar taurin kai ce".tana faÉ—ar hakan ta fita fuu cikin fushi,Hajiya kaka bata fiya saurin fushi ba idan kuwa kaga ta yi fushi to abin ya yi yawa ne.

Ranar nasha kuka kamar me,da yamma Rashida tazo waje na lokacin ina cikin ɗakin naƙi ci naƙi sha Hajiya kaka ta kawo min abinci amman ko kallon abincin banyi ba,saboda fushi itama bata ƙara bi ta kaina ba ta yi zamanta afalo ta kunna radionta,ta ware ta sosai sai ƙara take,haushi duk ya isheni idan na gaji sai in toshe kunnuwa na duka.ina jinta tana ce wa"oho dai babu inda mutum zaije,ko inyamura ce tazo nan baki isa ki fita ba,zan saka akiramin likita har gida ya duba ki eh tunda abin rashin mutunci ne,ai tattaɓa kunnen basu isheni ba eh so na ke sai sun kai ɗari sannan Allah ya ɗauki raina".

Tana cikin wannan maganar Rashida ta shigo,ta ce"a'ah Æ´ar tsohuwa ina khairat É—in?naji banji É—uriyarta ba?."chono baki Hajiya kaka ta yi ta nuna hanyar É—aki na sannan ta ce"tana ciki Æ´ar nema kin san fa tana da ciki to wai shine take son ta zubar eh saboda rashin mutunci,to nidai ba a gidana xa'ayi wannan kisan kan ba,ciki gashi nan har ya turo kai amman wai a haka akeson a zubar,saboda shashanci to wallahi baki isa ba".

Da sauri Rashida ta faɗo ɗakin dana ke ta rungumeni ta ce"Allah na gode maka daka nunamin wannan ranar da zanga ƴaƴan yaya Bilal,don Allah khairat kada ki zubar da cikin nan kome za'ayi kada ki zubar da cikin nan,wannan cikin shine zai kawo ƙarshen komai".ta faɗi hakan tana kallon ciki na wanda ya turo kai sosai.

Na ce"ni fa Rashida sai na zubar da cikin nan,saboda me xan barshi ubansa bai so,ko so ki ke in haihu É—in yazo yana ce ba shine ya yi cikin ba?a'ah wallahi sai na zubar wannan sharrin ma da ya yimin abarni dashi,don haka ki bar wannan ma maganar sai na zubar."na faÉ—i hakan ina tashi daga É—akin don dukkansu haushinsu na keji.

Farlo na fito na zauna Hajiya kaka na ƙwance ta yi matashi da filon kujera ta saka radionta akunne tana ji,ta kalleni ta watsar sannan ta ce"ai kin banza ai ko uwarki ce ta harareni sai na faɗi magana balle ke tabi'i tabi'ina."banza na yi mata ina jin yadda ɗan cikina ke juyawa kamar juyin waina,ya tattaro ya dawo ƙasan mara,ga wata muguwar yunwa dana keji.

Ina zaune Rashida tazo ta wuce ba tare da ta cemin komai ba,ta wuce cikin fushi na kalleta na watsar amman azuciyata banji daÉ—in abinda na yi mata ba,amman nima ai sai ayimin uzuri su fuskanci abinda na ke hangowa gaba.

Hajiya kaka ta ce"hmm Allah khairat kina bani mamaki,yanzu ke kina ganin Rashida duk yadda ki ke da ita baza taji haushinki ba,akan wulaƙancin da ki keyi har kike ce wa zaki zubar da cikin yayanta,kuma kice zakuyi shiri?ai kema kin san kin cuci kanki".

bance mata ƙala ba naji ina muguwar jin yunwa na ce"babu abinda ki ka dafa ne inci".?banzan kallo ta wur gamin sannan ta ce"oh yanzu abincin ki ke nema ko?wa yagaya miki barni gabas take?ai dole ki nemi abinci baka da komai ma ajikinka ka ke neman abinci?balle kuma ga ciki cikin ma ba yaron ciki ba,to wai ni yaushe rabonki ma da al'ada".?da sauri na kalleta na tuno last dana yi da sauri na ce"6 month fa na shiga uku".da sauri kaka ta ce"ke ni ban wani san turancinki ba na dai gane 6 ɗin,wato shida ko?,amman wannan yarinyar ko shasha wallahi yanzu ciki ajikinki har na tsawon wata shida amman baki sani ba?kina zaune kamar wata bagidajiya?".ah to yau ɗinnan zamuje asibiti."

Banza na yi mata na wuce kitche ɗinta na buɗe indomie na dafa da ruwa ruwa na ɗakko nama a fridge na ɗan tafasa shi da albasa da kayan ƙamshi na ɗan soyashi sannan na haɗa da indomie ɗin.na fito na samu waje na baje na cika ciki na sai a sannan na ƙara kula da cikina yadda ya fito sosai.

Hajiya kaka ta harare ni sannan ta ce"ai kin banza da mana kada kici,badon tattaɓa kunne na dake cikinki ba da baki isa ki wulaƙantamin abinci kice kuma zaki barmin shi ba,ai ko kina so ko bakya so sai kin cinyesa".ni dai bance mata ƙala ba na cigaba da cin abinci na,ina cikin cin abincin su Babana suka shigo sai da gabana ya faɗi ko kallon inda na ke baiyi ba,balle ya amsa gaisuwar dana yi masa.

Abin ya tsayamin sosai sai kuwa naji yana ce wa"Umma wannsn yarinyar me ya kawo ta gidan nan?".saboda tunda naxo ƴan gidan basu san da xuwa na ba.Babu abinda kaka ta ɓoye masa na abinda ya faru dani,sai kuwa ya ce"umma shine ke kika ɗauketa ta kika ajjeta a ɓangarenki?ni tun tuni na cire wannan yarinyar daga cikin ƴaƴa na don ba zan zauna da bara gurbi ba". . . tun kafin ya ƙarasa maganarsa Hajiya kaka ta ce"kai Malik faɗi abinda ya kawo ka amman ba wannan ba,tunda dai kai ka kasa gane ce wa sharri akewa ƴarka".ta faɗi hakan tana harararshi.

Yasan sarai halin mahaifiyarsu ba ƙara sauraransa za tayi ba koda ma ya yi magana,sai ya ce"Hajiya daman magana ce akan Yaya Abdullahi,to muna taso mu gaya miki ammsn don Allah kada ki tada hankalinki akan wannan,yanxu haka ma ya fara samun sauƙi".

Da sauri kaka ta fashe da kuka ta ce"Allah sarki ɗana bawan Allah mutum me haƙuri,me yasa kuka ƙi faɗamin abinda ya faru,kuke ta ɓoyemin kuka cemin wai ya yi tafiya ne ta gaggawa?ashe ɗana yana cen babu lafiya"?.sosai suka dinga tausar zuciyarta.

Ina kitchen ina shan sanyayyan ruwan dana fito dashi acikin fridge bayan duk na gama jin abinda mahaifina ya ke faɗa,naji zuciyata tana min suya sosai na ɗaga gorar ruwan swan sai da na shanyesa tsaf sannan na ajje,sai ga Hajiya kaka tana kuka take faɗamin abinda ya faru,sosai jiki na ya yi sanyi donshi Baba Abdullahi babu ruwansu sam da rayuwa da rikicin da ke cikinta,na shafa cikina take naji son cikin ya shige ni,ko don babu komai sai saboda Baba Abdullahi sam bazaiji daɗin hakan daga gare niba,don yana iya bakin ƙoƙarinsa.

A bayan mota muka zauna nida Hajiya kaka sai kuka take ina rarrashinta,a asibitin naga su Rashida har da jidda da Hajiya Ruƙayya,naje na gaisheta ko amsawa bata yiba,Jidda ta zubomin idanuwanta ƙuri tana kallona ganin cikina wanda ya fito sosai,itama hajiya Ruƙayyan sosai ta yi mamakin ganin hakan.

********

Captain Ahmad ya ce"a gaskiya Bilal bazan ɓoye maka ba,ka yi asarar mata irin khairat yarinya mai haƙuri da nutsuwa amman har ka yadda da wannan sharrin da aka yi mata?".wani banzan kallo Bilal ya yiwa captain sannan ya ce"ok kada ma in yadda kenan ko?in kamata da ƙwarto kace min wai ba haka bane?to meye ɗin?".

Captain ya yi murmushin takaici sannan ya ce"a'ah ni gaskiya ban yarda ba,kai meye shaidarka na yadda da hakan"?.ya faÉ—i hakan yana kallon Bilal.murmushin takaici Bilal ya yi sannan ya ce"eh to ai har masu gadi na tambaya suka shaidamin tunda na yi tafiya take yawo,kaga kuwa dole in yarda".ya faÉ—i hakan cikin gadara.

"Hmm lallai Admiral da sauranka,kai wato har yanzu baka san mutane ba?suyi maka micijin sari ka noƙe ba".?

Micijin sari ka noƙe sunan novel ɗina sa zan fara bayan na huta.

Ɗakko wayarsa ya yi cikin aljihunsa ya shiga wani vedio ya nunawa Bilal ya ce"wacece wannan?".da sauri Bilal ya ce"jidda ce".captain ya yi ɗan murmushin gefen baki sannan ya ce"wannsn vedio ɗin yafi guda biyar acikin wayata,vedion nan tun sanda ka yi tafiya na ke ɗaukarsa,abin ya juya ne kan khairat amman maganar gaskiya tunda ka yi tafiya na gano jidda na fita kullum daga gidanka,baza kuma ta dawo ba sai dare ya lula,kuma dana matsa da binciken inda take zuwa sai gashi na gano gidan maƙiyinmu Damass take zuwa".

Da sauri Bilal ya kalli captain yana jin kamar zai sume saboda tsoron abinda yaji daga wajen captain.. . . . .

MAGANCE KAUSHIN KAFARKI
Chapter 46 · 0% Book details