← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 37

Sashe 4

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ke cikin East Bay Hotel wanda ya amsa sunansa ɗaki me kyau, ado da ƙawa, ya matuƙar ƙawatu da wasu Furniture 'yan ubansu. Kiɗa ke ta shi a cikin ɗakin cikin wata ƙatuwar speaker da ke gefe guda, sosai waƙar ke tashi da ƙarfi kamar ba mutum ɗaya ke ji ba. Babu kowa cikin ɗakin bayan speaker da ke cigaba da aikinta. Taɓa ƙofar toilet da na ji anyi ne ya sanyani saurin kai idona wajen. Farar ƙafarsa da ke cikin wani takalmin wanka itace na fara hangowa lokacin da yake zame takalmin kafin ya kai ga fitowa gaba ɗayansa. Singlet ce a jikinsa se towel ɗin da ke ɗaure daga ƙugunsa yayin da ya ɗora wani akan kafaɗarsa. Yanayin rigar da ke jikinsa itace ta fallasa halittar ƙaƙƙarfan jikinsa da ke ɗauke da wasu lafiyayyun kwantattun gargasa baƙa wuluk, wadda ta zauna ɗass akan farar fatarsa da ta gaji da gyara, hutu gami da jin daɗi. Ƙarasawa yayi gaban mudubi yana ɗan kaɗa kansa dake ɗauke da tulin suma wadda aka yiwa gyara na musamman, hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawar fuskarsa da ke ɗauke da wasu shu'uman idanu, wanda kallo ɗaya idan yayi wa mutum ze iya rikicewa, ba ga mace ba hatta ga maza idanunsa kan firgita wasu mazan, idan kuwa mace ta bari ya ɗora shu'uman idanunsa akanta idan dai har bata rikice ta faɗa ƙaunarsa ba toh ba za ta bari ta sake iya haɗa idanu da shi ba saboda yadda idanun nasa suke kamar suna ɗauke da wani maganaɗisu ne, a iya idanunsa kaɗae an ƙure kyau, dan kuwa idanunsa na ɗaya daga cikin abin da ya kwashe kaso masu yawa daga cikin kyawun da Allah ya bashi, se kuma dogon siririn hanci da ke zaune akan fuskarsa kamar an zana. Duk da yanayin yadda kiɗan ke tashi da ƙarfi hakan be hana shi rage sautin ba se ma buɗe baki da yayi ya shiga bin sautin waƙar da se ka rantse shi yayi ta saboda yanda yake bin kowanne waje cike da ƙwarewa da muryarsa me daɗin sauraro. Ya ɗauki wajen rabin awa yana shiryawa sannan ya gama cikin wata haɗaɗɗiyar riga da crazy jeans da suka matuƙar yi masa kyau. Wata er ƙaramar abin hannu me kyau da tsada ya ɗauka ya saka a hannunsa da shi kansa yake ɗauke da kwantacciyar suma me matuƙar kyau. Wayarsa da ke ajje kan gado ta shiga ruri, se a lokacin ya ƙarasa ya rage sautin kiɗan da ke tashi, wanda da alama ba dan kiran da aka masa ba ba ze rage sautin ba. A nutse ya koma ya jingina da jikin mirror shu'uman idanunsa a ɗan lumshe kamar yadda suke a halitta, shi ba irin manyan idanun nan gare shi ba, basu da girma can kuma ba ƙanana ba ne se dai tasirinsu da kuma kyansu na musamman ne kamar yadda shi ɗin ya kasance na musamman.

"Bad!" Shi ne abin da Lucky da ya kira wayar ya faÉ—a bayan É—aga kiran da Areef yayi.

"Yeah Lucky, What's going on?" Yayi maganar da muryarsa da ita kanta ta daban ce, me daÉ—in sauraro gami da wani amo da ke É—auke da ita.

"Amm ka jirani harkar nan ta samu zan kawo maka har É—aki."

"Nop, Let's meet at school couz mutanen Dad na nan." Da mamaki Lucky yace

"A'ah Bad kada kace min tsoro kake ji?" Ya tambaya dan ya san halin Bad Man É—in. Wani murmushi Areef ya saki kamar ba zece komai ba se kuma yace

"Lucky! Just let's meet there" ya faɗa yana taune lips ɗinsa na ƙasa idanunsa a lumshe..

Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.

https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_03

"Ohk mu haɗe a can ɗin." Lucky ya faɗa. Zare wayar daga kunnensa Bad yayi lokaci ɗaya yana ɗaukar karin waƙar da yanzun ke tashi cikin ɗakin. Soma takawa yayi dan barin wajen, wayarsa da ya ajje ta soma ƙara. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja yana miƙa hannunsa kan tulin kwantacciyar sumar kansa, kamar ba ze dawo ba, se kuma ya dawo ya ɗora idanunsa akan wayar. Ɗan lumshe idanunsa yayi yana murza goshinsa kaɗan, ya san idan har ya ɗaga kiran Mom ba zata bar shi ya fita da wuri ba, shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ya tafi wajen kayan da Lucky ɗin ya samo musu a sirrince. Wayar na dab da tsinkewa ya ɗaga duk da sautin kiɗan da ke tashi har lokacin se dai ba kamar ɗazun ba, hakan be sa shi ya kashe gaba ɗaya ba. Cike da soyayyar ɗan nata tace

"Boy!" A hankali yace

"Yes Mom!"

"Kana lafiya? Ya zaman kaɗaici?" Wani miskilin murmushi ya saki wanda ya matuƙar ƙawata kyakkyawar fuskarsa haka waɗannan idanun nasa se suka ƙara yin wani kyau na musamman. Kafin yace komai ta ɗora da

"Ai dai ya kusa ƙarewa, ka fara shirye-shiryen ne?" Ɗan shiru ya sake yi dan shi kam da za a bi ta tashi da ya cigaba da zama a ƙasar nan yanda ze cigaba da cin karansa babu babbaka, babu me saka shi babu me hana shi, amma se ya basar kawai yace

"Yeah Mom!" Murmushi Mom tayi sannan tace

"Ni fa na fara shirye-shiryen dawowarka tun yau, hope dai ba zaka wuce jibi ba?" Kamar me nazari ya É—an yi jimm, lallae tabbas yau É—in dole ne yawa kansa charge me lasisi, dan ya san idan har ya dawo Nigeria Daddy se yafi sakawa an saka masa ido fiye da yadda yanzun ake saka masa.

"Ehh ba zan wuce ba" shi ne abin da ya faÉ—a, kafin Mom É—in tace komai ya É—ora da

"Amm Mom, zan É—an shiga school ne. Zan kiraki later" Sauke ajiyar zuciya Mom tayi sannan tace

"Ohk Boy." Ko ajje wayar be yi ba bayan katse kiran Mom kawai ya jefata cikin aljihu sannan ya fice daga ɗakin jikinsa se tashin ƙamshin turarensa me matuƙar daɗi yake, wanda in dae ka shaƙa se ka so ka sake shaƙa saboda daɗinsa. Angry face ɗinsa ya sake tattarowa waje ɗaya ya ɗorata akan fuskarsa, cike da izza da isa yake takawa bayan ya sakko daga stairs inda ɗakin da yake ciki yake. Kai tsaye ya ƙarasa inda motarsa take, duk da uban mutanen da ke zagaye da ita hakan be hana shi saka hannu da niyyar buɗewa ba. Wani baƙin mutum me sanye da baƙaƙen kaya yayi ƙarfin halin faɗin

"Yallaɓae ina zamu cewa Mai gida ka je?" Dakatawa yayi daga niyyar buɗe motar da yayi, a yadda ya dakata kawai ba zaka yi tunanin ze amsa ba se kuma ya ɗaga waɗannan idanun nasa ya kafe wanda yayi maganar dasu. Da sauri ya janye saboda yadda ya duburburce lokaci ɗaya.

"Aikin da aka sakaku kenan?" Ya tambaya cikin tsare gida kuma cikin basarwa. ÆŠaya daga cikinsu wanda da alama duk tare suke shi ne yace

"Sorry Ranka ya daɗe. Sabon ɗauka ne be san yanda abin yake ba." Be tanka ba duk da yaji abinda ya faɗa ɗin se buɗe motar da yayi ya shiga ya tashi motar ya bar Hotel ɗin zuwa makaranta. Ɗaya daga cikin mutanen Daddy ne ya bi bayansa a bisa umarnin Daddyn. Be kuma bar shi ba har se da ya tabbatar ya shiga cikin makaranta sannan ya dawo, dan su basu taɓa tunanin tantirancin Areef ɗin ya kai ya dinga shan wani abun a cikin makaranta ba, shi yasa daga zarar sun gan shi a makaranta hankalinsu ke kwanciya. A inda suka saba haɗuwa yayi parking na motarsa, saboda yanda ya taho a guje ya sa ya ɗan tunkuɗi wani keke yayi gefe sannan ya faɗi ƙasa. Duk da ya ga hakan amma be saka shi yayi yunƙurin yin wani abun ba, se ma ɗauke kansa da yayi kamar be gani ba ya sauka daga motar hannunsa ɗaya saye cikin aljihun wando. Lucky da ya hango shi ya ƙaraso yana kwashewa da dariya. Hannu ya ba shi suka tafa kana yace har lokacin yana dariya

"Mutumina gaskiya kai shege ne. Wai bayan duk waÉ—annan mutanen se da ka fito?" ÆŠan murmushi ya saki wanda na fahimci murmushinsa kodayaushe baya wuce wannan miskilin murmushin da kamar ya san kyau yake masa idan yayi. Kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Mu je kawai Lucky!"

"Bad Man!" Lucky ya sake faÉ—a yana jinjina basirar abokin nasa da yace su haÉ—u a makaranta.

.. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin soron gidan wanda Abeey ke zaune da wasu ɗalibansa yana karantar da su. Dakatawa yayi anan ɗin ya zame takalmin ƙafarsa sannan ya zauna akan tabarmar da ke shimfiɗe a wani ɓangare na soron gidan kasancewarsa me yalwar girma sosai.

"Barka da wannan lokacin Abeey"

"Barka dai Affan, ka dawo lafiya?" Dattijon mutumin da kana kallansa zaka san shekaru sun ja masa sosai ta faÉ—a, se dai duk da haka hakan be hana shi karantar da É—alibai ba wanda kusan kullum cikin hakan yake.
Chapter 4 · 0% Book details