← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 37

Sashe 14

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Pls ki bani hanya." Yayi maganar gaba ɗaya fuskarsa a cunkushe babu fara'a ko misƙala zarratun. Cikin kwantar da murya tace tana ɗan murza hannunsa

"It's ohk..it's ohk Uhmm?" Ta faÉ—a cike da rarrashi.

"Pls Mom." Ya sake ambata ba tare da ya kalleta ba. Da dai ya fahimci ba matsawar za ta yi ba, kawai se ya zagayeta ya fice daga É—akin ya barta tsaye a wajen.

"Oh my goodness.." ta faɗa tana yarfe hannunta. Ta riga dama ta san halin Bad Man ɗin amma bata san wannan ɗan abun da tayi ze fusata shi haka har ya ƙi cin abinci ba.

"Munafukar mata!" Ta faɗa tana jin yadda ɓacin rai ke taso mata musamman idan ta tuna da Hajiya Sa'adah.

Yana fitowa Compound ɗin yayi daidai da lokacin da Daddy ya sauko daga cikin motarsa. Se ya ƙarasa a nutse fuskarsa na sassautawa daga ɗauretan da yayi kamar ba shi ba. A nutse ya ƙarasa ya rungume Daddyn yana faɗin

"Welcome Daddy.."

"Welcome my Son.." Daddy ya faÉ—a yana É—an dukan bayan Bad Man É—in.

"Ina zaka je?" Daddy ya faÉ—a bayan sun saki junansu. ÆŠan shafa sumar kansa Bad Man yayi kafin yace

"Amm, zan É—an fita ne.. in zaga gari.." Jinjina kai Daddy yayi yace

"Hakan ma yayi. Buh zuwa anjima ina so muyi hira sosai.. Amma yanzu let's go to mosque, kaa ji ana kiraye_kiraye.." Babu musu yace

"Ohk.." daga haka be sake cewa komai ba. Kai tsaye masallacin suka wuce, wanda ke cikin tafkeken gidan nasu. Tare suka yi Sallahr cikin ƙaton masallacin. Cigaba da zama suka yi na tsawon mintuna, har lokacin Daddy addu'a yake, yayin da Bad Man tun kusan minti nawa baya ya idar da tasa addu'ar. Kallan Daddy yayi, sannan ya fito da wayarsa ya duba tym. Ya san idan dai har ya ƙara mintuna a gida ba ze samu abin da yake so ba. Dan haka cikin muryar nan tasa yace bayan ya ɗan ranƙwafo kusa da Daddyn.

"Daddy! Tym na tafiya.. Zan tafi.." se da Daddy ya kai ƙarshen abin da yake kafin ya kalle shi yace bayan yayi murmushi, a ransa yana farin ciki da yadda ya ga Areef ɗin nasa ya girma sosai yayi kyau, kuma da alama babu wani shashanci da yake yi, dan kwata_kwata yanayinsa be nuna ba. In banda askin da ke kansa da cikin ruwan sanyi ze san yanda ze yi ya sauya shi. Yanzun ma ya bar shi ne dan ya san hakan ba komai bane a can ƙasar da ya baro.

"Ohk.. Akwai yara za a haÉ—aka da su.." Cikin rashin fahimta yace

"Yara?"

"Yeap, yara mana.. waɗanda zasu kula da kai.." Se da ya soma ƙanƙantar da idanunsa sannan yace

"Kula da ni fa kace Daddy? Ba na buƙatar kowa. I can take care of myself couz am matured enough.." ya faɗa cike da jin haushin yanda burget ɗinsa ke neman rugujewa.

"Ga ka ga su ai Areef.. Je ka fita.." Daddy ya faɗa yana gyara zamansa ya cigaba da addu'oinsa. Har wani huci yake sanda ya miƙe ze fita daga masallacin. Tafiyarsa ta sake mugun ƙawatuwa saboda yanayin da yake ciki na fushi, se ya koma tafiya cikin wani irin taku kamar wanda baya son yin tafiyar. Se dai da yake tafiyar cike da kuzari yake yinta kasancewarsa ƙaƙƙarfan namiji ya sanya tafiyar tayi armashi. Kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya buɗe ya shiga, ya ɗan lumshe idanunsa na tsawon sakanni sannan ya buɗesu lokacin da suka chanja colour. Abin da baya so kenan shi yasa be so dawowa Nigeria ba. Wannan wane kalan takurawa ne, a ce duk inda mutum ze je se da wasu a bayansa kamar wani ɗan fashi? Be taɓa tunanin idan ya dawo nan ɗin ze soma da wannan ƙalubalen ba. Amma a yau ɗin ze gama da wannan chapter, ya shiga next chapter. Idan kuma hakan taƙi toh dole se dai ya sake bar musu ƙasar.

.. Tunda Abba yayi parking sum_sum ta fice daga cikin motar, jin har lokacin bece da ita komai ba. Hakan ba ƙaramin sake sakawa jikinta yayi sanyi bane. Ammi da Didi na parlour suna kallan Sunnah TV. Ta shigo a sanyaye. Kowa ya ganta ya san akwai wani abun, dan da babu komai, tana shigowa zaka san ta shigo da maganarta. Se dai yau ɗin babu wanda ya jiyo muryarta, babu wanda ta nufa dan runguma, se ƙarasawa da tayi kan kujerar da Ammi ke kai ta ɗora kanta a kafaɗarta sannan tace

"Amminmu!" Murmushi Ammi tayi tana jin daÉ—in dawowar Lulun fiye da zato tace

"Na'am 'yan matan Ammi.."

"Kai Ammi" Lulu ta faɗa tana murmushin itama. Ɗan satar kallan Didi Lulu tayi, yanda take wani cika tana batsewa tana ɗaɗɗama rai ne ya sanya ta sake tuna abin da ya dawo da ita gida. Se kawai ta sake yin shiru tana kuma jiran shigowar Abban, dan ta san a yadda ta gan shi yau ɗin nan kam se ta sha faɗa. Se dai ga mamakinta har bayan wajen mituna 20 da shigowarta Abba be shigo ba, tun tana jin tsoro har tazo ta dena. Se kawai ta miƙe da sauri ta shige ɗakinsu. Didi na tsaye bakin wardrobe tana gyara kayanta. Lulun ta ƙarasa ta rungumeta tana faɗin

"Na yi missing na ki fa Didina.."

"Ni sakeni Malama." Didi ta faɗa tana mazewa. Maƙe kafaɗa Lulu tayi lokaci ɗaya tana faɗin

"A'ah, naƙi ɗin.."

"Toh jikinki ne?"

"Ehh mana, ai dai na Didina ne." Lulu ta faÉ—a tana murmushi. Jin Didin ba tace komai ba ya sanyata faÉ—in

"Abba ne fa ya É—akkoni. Kuma ya min faÉ—a na dena abin da nake yi In Sha Allah.."

"Ke ɗin?" Didi ta faɗa tana juyowa ta kalleta. Se ta jinjina kai tana sake marairaice fuska kamar wata marainiya. Yadda tayi ɗin ne ya tilastawa Didi yin dariya. Se kawai ta rungume Twinnynta ta cikin matuƙar kewar junansu. Tun daga lokacin ma duk se suka sake suka manta ma da abin da Lulun tayi. Shi kansa Abba tun dawowarsu gidan basu sake ganinsa ba, kamar ma baya cikin gidan kwata_kwata. Hakan ne ya ƙara sawa Lulu karsashi wajen sakin jikinta ta cigaba da harkokinta. Har zuwa washegari kuma Abban be yi mata magana ba, hakan ne ya sanya ta soma tunanin ko ya manta, ko kuma ya bar maganar. Ita idan haka ɗin ne ma tafi kowa farin ciki, dan haka ta sake sakin jikinta, ta dinga kakkaucewa duk wata hanya da zata haɗata da Abban, duk da yadda daga jiyan zuwa yau be samu zama a gida sosai ba.

... Ammi ce kaɗai cikin parlourn tana kallan tashar Arewa 24 inda suke nuna shirin Akushi da rufi. Da yake Ammin tana son shirin ya sanyata zama tana kalla, duk da ita ɗin ba ma'abociyar kallo bace. Babu daɗewa se ta miƙe zuwa wajen fridge ɗinsu da ke cikin ɗakin dan ɗaukar ruwa. Sallamar da taji cikin parlourn ita ce ta sanyata juyawa. Se tayi murmushi ganin me shigowar tace

"A'ah... Sadiya! Sannu da zuwa." Ammi ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin cike da mamakin ganin Mamin, tunda dai ta ga jiya Lulu ta dawo, ba dai tana nufin ta zo ta sake tafiya da ita ba ne? Idan kuwa haka ne gaskiya a wannan karon dole ne ta magantu. Zama Ammi tayi tana ajje ruwa da lemon da ta ɗauko cikin fridge. Yayin da Mami ma ta ƙaraso ta zauna kan kujerar kusa da Ammin tana murmushi tace

"Se kuma kika ganni?" Itama Ammin murmushi tayi kafin tace

"Uhmm. Kina lafiya? Ina Jadwa?"

"Alhamdulillah. Ina 'ya'yana?" Mami ta faÉ—a tana É—an duba bayanta.

"Suna ciki.. Ina ga ko bacci suke"

"Toh madallah. Yayan na nan ne?" Mami ta faɗa tana miƙewa.

"A'ah ya fita dai."

"Toh bari na je kafin ya dawo" Inji Mami.

"Toh." Ammi ta faÉ—a tana binta da kallo sanda take dab da shiga É—akinsu Lulun. Kamar kuma wadda aka tambaya se ta juyo tace

"Kin san na zo ne na sake bawa Yaya haƙuri, sannan na yiwa ɗiyartawa faɗa." Jinjina kai Ammi tayi tana ɗan murmushi tace

"Uhmmm." Daga haka ba ta sake cewa komai ba har Mamin ta shige ɗakin. Suna zaune kan gado, Didi da Little ke kwance a jikinta na karanta musu wani English novel da aka basu a school Mamin ta shigo. Da gudu Lulu dake sanye cikin doguwar riga kanta babu ɗan kwali ta miƙe ta rungume Mamin tana faɗin

"Oyoyo." Hugging nata back Mami tayi tana murmushi lokaci É—aya tana faÉ—in

"Wannan kannaki daughter.." ta faɗa tana riƙe baƙin gashin Lulun. Er ƙara ta saki tana saka hannu ta riƙo hannun Mamin. Se a lokacin ta saki sannan suka ƙarasa cikin ɗakin. Ajiye littafin hannunta Didi tayi, tana kwantar da Little da yayi bacci a kan gadonsu. Sannan ta juyo tace a nutse

"Sannu da zuwa Mami."

"Yawwah Afrah. Ya karatun?"

"Alhamdulillah.."

"Toh madallah."

"Daughter ina fata dai Abba be sake miki faÉ—a ba?" Mami ta faÉ—a tana kallan Lulu da ke zaune kusa da ita. Se da ta É—an turo baki sannan tace

"Ehh fa. Ai be ma yi ba fa, inaga se yau.." ta ƙarashe maganar a narke. Shafa kanta Mami tayi kana tace

"Shi kenan, shinkenan. Didi.." ta kai ƙarshen maganar tana kallan Didi.

"Uhmm" Didi ta faÉ—a cikin sanyin nan nata.

"Ɗan bamu waje zan sake yi mata faɗa.." kusan a tare Lulu da Didi suka kalli junansu, sannan Didi ta maida duban nata kan Mami, kamar za tace wani abu se kuma ta fasa, kawai ta miƙe ba tare da tace komai ba. Riƙo hannunta Lulu tayi da sauri tana faɗin

"Didi ki zauna.." Lulu ta faÉ—a har lokacin fuskarta a narke. Hannu Mami ta kai ta zare hannun Lulu daga cikin na Didi tace
Chapter 14 · 0% Book details