Sashe 26
A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi kuwa Hajiya. Na zo tafiya ne se kuma na haɗu da baƙon da kuka yi. Yace min dai sunansa Kaseem kuma ya zo wajen Abban En biyu ne. Toh da na faɗa masa baya nan shi ne yace min ko zan kira masa Afrah.."
"Afrah kuma? Ikon Allah." Ammi ta faɗa, dan ita gaba ɗaya tama manta da maganar, ko tuntuɓar su ma ba ta yi ba bayan dawowarsu, dan ta yi tunanin ma za su mata maganar da kansu, se dai tunda su basu mata ba, gwara ita ta yi musu.
"Toh shigar da shi ɗakin baƙi.."
"Toh Hajiya." Ado driver ya faɗa yana wucewa. Miƙewa Ammi ta yi ta wuce ɗakin Twins. A kan gado ta samesu dukansu suna karatun wani english novel ba wadda ke kallan wani. A nutse ta ƙarasa cikin ɗakin ta nemi waje ta zauna a kan gadon tana kallan en biyun nata. Se ta yi murmushi kawai dan ta gane zaman nasu ba lafiya ba, kowacce haushin er uwarta take ji.
"Wajen wa Kaseem ya zo ne?" Duk tare suka É—aga ido suka kalli Ammin kafin suka kalli junansu. Jin sun yi shiru ne ya sanyata sake faÉ—in
"Tambayarku fa nake."
"Ammi wajen Didi fa ya zo." Lulu ta faÉ—a tana tura baki, ita a lallai dole ba ta so faÉ—ar sunan Didin ba.
"Allah ya shirya min ku. Duk ku zo nan." Ammi ta yi maganar duka a tare. Se suka sakko gaba ɗayansu zuwa ƙasa. Kusan a tare suka ɗora kansu a kan cinyar Ammin. Se ta ɗauki duka hannayenta ta ɗora a kan kowacce sannan ta soma faɗin
"Shi ne ba ku faÉ—a min ba? Ba dan na tambaya ba wato shiru za ku min koh?" Se suka girgiza kai a tare. Lulu tace
"Ammi ya É—auka ni ya gani a ranar, shi ne na faÉ—a masa Didi ce, dan lokacin da ya ganta ma ni ina gidan Mami."
"Toh Masha Allah. Tashi ki ɗauko Little ya miki rakiya zuwa ɗakin baƙi ku gaisa."
"Ni dai Ammi Allah.."
"Allah me..? Je ki idan kin dawo se ki faɗa min idan ya yi miki toh shi kenan. Idan kuma be miki ba se mu bashi haƙuri." Ammi ta faɗa tana murmushi. Dariya Lulu ta yi tana ɗaga kai ta kalli Didi daidai lokacin da ta kulle fuskarta tana faɗin
"Ammiiiii.." ta ja ƙarshen sunan tana murmushi itama.
"Tashi maza." Ammi ma ta faɗa tana murmushin. Se ta miƙe a hankali ta ƙarasa wardrobe ɗinta ta ɗauko gogaggen hijab ɗinta jalbab ta saka sannan ta kalli Lulu bayan ta marairaice fuska tace
"Ki zo ki rakani kin ji?"
"Naƙi ɗin." Lulu ta faɗa tana murguɗa baki gani da ɗauke kai.
"Pls mana.."
"Kin ga, ɗauki Little ya rakaki, idan kin dawo har faɗan naku ma zan shirya.." Ammi ta faɗa tana kallan Didin da ko er shafa powder ma a kan fuskarta be dameta ba. Hakan kuma ba shi da wani muhimmanci dan kuwa ko a yanzun da bata shafa komai a kan fuskarta ba ta fito ta yi kyau abinta. Parlour ta fito ta kalli Little da ke kallan Mbc 3 hankalinsa kwance. Tace sanda ta ƙarasa kusa da shi
"Little zo ka rakani." Da sauri ya sakko daga kan kujerar da yake kai yana murmushi yake faÉ—in
"Toh mu tafi.." ya faɗa yana miƙa mata hannunsa. Se kuwa ta riƙe shi ɗin suka fita daga ɗakin zuwa ɗakin baƙin.
Cikin sanyayyiyar muryarta ta yi sallama cikin É—akin. Kaseem ya É—aga kansa da sauri yana kallanta, be san sanda ya sauke ajiyar zuciya ba a daidai lokacin da ya yi arba da kyakkyawar fuskarta.
"Kai!! Dama ba unguwa zamu ba." Little ya faɗa a shagwaɓe. Murmushi Kaseem ya yi yana kallan Little ɗin da ko ba a faɗa ba kamarsa ta gama fallasa cewa ƙaninsu ne. Se ya miƙe ya ƙaraso inda suke ɗin ya riƙo hannun Little yana faɗin
"Unguwa zamu je mana." Sakar masa hannu Didi ta yi, se suka koma cikin É—akin yayin da ita kuma ta rufa musu baya.
"Barka da fitowa gimbiya.."
"Ina yini?" Ta faÉ—a dai a nutsen kuma cikin sanyi.
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah. Kin fito lafiya?" Ya sake tambaya yana kafeta da idanu.
"Alhamdulillah.." ta faÉ—a tana É—an satar kallan Little da be ce komai ba har lokacin. Se kuma can ta jiyo muryarsa yana faÉ—in
"Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau Little.. me ye sunanka?" Ya tambaya yana kallansa
"Ai ka faÉ—a." Little ya faÉ—a yana buÉ—e ido.
"Me fa?" Kaseem ya tambaya dan be gane abin da Little É—in ke faÉ—a ba.
"Little sunana."
"Ohhh! Haka ake kiranka da shi? Nyc name. Me ye sunanka na gaskiya?"
"Areef."
"Woww.. suna me daÉ—i..Sunan brother É—ina" Kaseem ya faÉ—a yana murmushi.
"Kai fa?" Little ya tambaya shi ma yana murmushi
"Kaseem!" Yamutse fuska Little ya yi kafin yace
"Nawa ya fi daÉ—i.." dariya Kaseem ya yi yana ji yaron na sake burge shi. Se ya saka hannu ya É—ora shi a gefensa sannan yace
"Zauna nan mu yi magana da gimbiyata." Ya ƙare yana kallan Didi da ta zauna lokaci ɗaya yana miƙawa Little wayarsa. Se kuwa ya karɓa cikin ƙanƙanin lokaci ya kamo game ya fara yi.
"Na san za ki yi mamakin sake ganina yau. Se dai ni a wajena idan kullum za ki amince na dinga zuwa gidan nan se na fi kowa farin ciki. Toh amma na san ko masauki ba a min ba ko da kuwa raɓani ne a yi a wani ɓangaren." Ya ƙare maganar kamar me neman taimako. Se ta ɗaga kai ta kalle shi. Ganin ita yake kalla ya sanyata saurin ɗauke kai. Jin ba tace komai ba ya sanya shi ɗorawa da
"Wata babbar mantuwa na yi a gidan nan. Na tafi ba tare da na karɓi abin da ze dinga sakawa kodayaushe na dinga jinki ba. Na tafi ba tare da na karɓi abin da ze sanyani na haƙura da zuwa gidan nan kullum, na samu ko da a sati ne na dinga zuwa sau 3 a lalace kenan." Yanda ya yi maganar ne ya tilasta mata yin ƙaramar dariya. Hakan da ta yi se ya ga tamkar ƙara mata kyau aka yi. Se ya gyara zama yana cigaba da kallanta.
"Allah kuwa a lalace mana."
"Sau ukun?" Ta faÉ—a tana buÉ—e ido.
"Tohm shi kenan zan rage. Amma dai yanzu ki bani number ka da Abba ya zo ya sameni yace na fiya naci har na dawo."
"Ba ni da waya."
"Da gaske?" Ya tambaya still dai yana kallanta. Se ta jinjina kai kawai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace
"Shi kenan, zan samu mu yi magana da Abba idan ya amince na kawo miki waya se na dinga jin muryarki ta nan, har kuma na samu na ƙarasa isar da saƙon zuciyata." Ya ƙare maganar yana murmushi. Da sauri ta girgiza kai kafin a hankali tace
"A'ah Abba ba ze bari ba.." Sosai hakan da tace ya sake birge shi, dan kuwa yanda yake gani emmatan yanzun masu irin shekarunta nawa ne ke riƙe da waya ba tare da hakan ya damesu ba ko ya dami iyayensu ba.
"Na san me yasa Abba ze hana.. toh amma kuma yanzu idan kin tuna ai da ni kaÉ—ai za ki dinga waya. Ni kaina ba zan bari ki dinga waya da kowa ba, kuma ba za ki dinga amfani da wayar ba saboda karantunki.. saka miki ido zan yi.." se ta yi murmushi kawai ba tace komai ba.
"Didi bacci.." Little ya faÉ—a yana hamma. Se ta kalle shi sannan ta kalli Kaseem É—in tace
"Bari mu tafi.."
"Kai haba tun yanzu?"
"Didi bacci.." Little ya sake faɗa yana riƙo hannun Didin, bayan ya sakko daga kan kujerar da Kaseem ke kai. Se ta miƙe kawai tana riƙo hannun shi. Ba dan ya so ba, se dai shi ma baya so ya zaƙe, hakan ne ya sanya shi miƙewa yace
"Tohm shi kenan.. Allah ya tashemu lafiya. A gaida min da Twinnynmu.."
"Tohm." Didi ta faÉ—a, se kuma a hankali tace
"Ka gaida gida." Lumshe idanunsa ya yi yana jin daÉ—in abin da ta faÉ—a É—in.
"Gida ze ji kyakkyawata." Daga haka ta fice daga ɗakin, shi kuma ya bita da kallo har ta fice. Se ya koma ya zauna a kan kujerar yana lumshe idanunsa. Anya kuwa ze iya bari har se Didin ta gama secondary kafin a aura masa ita? Ba dan ba dan ba da yace Abban ya aura masa ita har secondary ɗin ta ƙarasa a cikin gidansa, se dai dan kawai ka da a ce ya zaƙe ne. Tana komawa gidan kai tsaye hayewa kan gado ta yi ta kwanta dan ba ta so kowa ya mata maganar dan wallahi kunya take ji. Ko Lulu sanda ta shigo cikin ɗakin tana toilet, dan haka da ta fito ma se ta ga Didin kwance kan gado kamar me bacci. Ita kuwa Ammi ta fahimci dalilin Didin na yin hakan, dan haka kawai se ta yi murmushi tana ƙyaleta zuwa gobe sa yi maganar har Abba.
... Tun ɗazu ta ke attempting na yi wa Lulu magana, se dai kuma yanda ta ga ta wani haɗe rai, haka zalika ta nuna ma kamar ba ta san da zamanta a wajen ba, ya sa ta maaze. Har dai zuwa sanda aka fita sallah. A daidai sanda Lulun ta ke ƙoƙarin shiga aji saboda mantuwa da ta yi Abida ta tareta da faɗin
"Afaaf!" Se ta É—aga kai ta kalleta da mamakin yanda rashin kunyar ta ya iya barinta ta mata magana. ÆŠauke kai ta yi da niyyar barin wajen, se ta sake matsowa da sauri tace
"Haba ke kuwa don Allah ki tsaya ki ji abinda zan faɗa miki." Jin abin da ta faɗa ne ya sanya Lulun dakatawa, dan ta ɗauka ko za ta bata haƙuri ne ko kuma ta sanar da ita ta yi nadama.
"Lafiya? Ki yi maza ki faÉ—i abin da za ki faÉ—a ina da abin yi.." Lulu ta faÉ—a bayan ta tsaya a wajen.
"Amm don Allah ki taimakamin Afaaf, ki taimakawa rayuwata, ki taimakawa shugabarmu da ke matuƙar buƙatarki ki zo na kaiki wajenta ko da zuwa ɗaya ne don girman Allah.."