Sashe 34
A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Didi idan Little ya tashi ya ci abinci plss. Zan kai Lulu asibiti ba ta jin daɗi.." Kallan Lulu Didi ta yi, ta galla mata harara tana ɗauke kai. Ita kuwa Lulu se ta langaɓar da kanta kamar da gaske.
"Toh Ammi. Allah ya tsare.." Didi ta faɗa tana jinjina kai, hadda ƙwafa, dan so take ƙaryar Lulun ta ƙare a yau ɗin. Bata daɗe zaune a wajen ba bayan fitar su Ammin Abba ya shigo.
"Sannu da zuwa Abba.." ta faÉ—a tana kallan Abban.
"Yawwah.. Afrah. Ina Ammin taku?"
"Ta fita kai Lulu asibiti."
"Toh Subhanallahi.. Me ke damunta?"
"Wai zazzaɓi.."
"Aou wai ne ma Didi?" Abba ya faÉ—a yana kallanta. Se ta tura baki tace
"Toh Abba haka na ji tace.."
"Kenan ba haka ba ne?" Shiru ta yi tana tunanin anya kuwa ta faÉ—awa Abban? Se dai tana so ne Lulun ta koma kamar kowacce É—iya dake son janyowa iyayenta yabo, ba kamar yadda take a yanzun ba, da take janyowa iyayensu zagi.
"Abba suspension aka bata fa."
"Suspension kuma?" Abba ya faÉ—a cike da mamaki. Jinjina kai ta yi kafin tace
"Ehh fa Abba. Laifi ta yi wa Gwani Affan shi ne ya bata. Amma Abba ka yi haƙuri, na faɗa ne ba dan komai ba, se dan ko za a yi haƙuri kawai a cire Lulu daga makarantar nan Abba. Wallahi bata so ne kawai, kuma Abba ka da ta janyo a zageku.." Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jujjuya kai.
"Wannan yarinya, wannan yarinya.. Kai!!" Abba ya faɗa. Se kuma ya miƙe yace yana kallan Didi
"Bari na je na dawo kafin su dawo.."
"A dawo lafiya Abba.." ta faÉ—a tana bin Abban da kallo. A ranta tana fatan Allah ya sa ya yadda ya cire Lulun daga wannan makarantar. Kai tsaye Abba wayarsa ya É—auka ya kira Gwani, se da ya tabbatar masa yana gida sannan ya katse wayar, bayan ya ji kwatancen gidan.
"Ya ya me jikin?" Abba ya faÉ—a yana kallan Gwani.
"Alhamdulillah.." Gwani ya faÉ—a da murmushi kan fuskarsa, dan ba kaÉ—an ya ji daÉ—in zuwan Abban ba.
"Fita za ka yi ne?"
"Wallahi kuwa.. Amma Abeeyn na ciki.." Gwani ya faÉ—a.
"Toh babu damuwa. Dama zuwa biyu ne ya kawo ni. Na farko na duba jikin Malam, na biyu kuma na ba da haƙuri a kan abin da ya faru.." Kallan Abba Gwani ya yi dan be fahimci abin da yake magana a kai ba. Dan haka da mamaki yace
"Haƙuri kuma?"
"Ƙwarai kuwa. Wato Malam ka san yaran yanzu ka haifesu ne amma ba ka haifi halinsu ba. Na ji duk abin da yarinyar nan ta yi, shi ya sa na ɗauko jiki na zo na ba ka haƙuri don Allah ka yi haƙuri ka yi haƙuri kamar dai kodayaushe.." Girgiza kai Gwani ya yi yace bayan ya ɗan yi murmushi
"Ban so ma ka shiga cikin maganar nan ba. Babu komai In Sha Allah. Allah ya shirya.."
"Ameen ya rabbi. Na gode.."
"Haba babu komai."
"A ƙara haƙuri dai don Allah.." Murmushi kawai Gwani ya ƙara yi, mutuncin Abban na ƙaruwa a cikin idanunsa. Ba Abba ne ya bar gidan ba se da ya shiga ya gaishe da Abeey sannan ya baro gidan. Sosai Abeeyn ma ya ji daɗin zuwan nasa, da ze tafi kuwa ya masa godiya dan lokacin ma ya ji sauƙi Alhamdulillah.
.. A kwance yake kan gadon idanunsa a lumshe, kansa a kan hannayensa, yana ɗan bubbuga ƙafarsa dake sauke a ƙasan gado. Ya kasa sukuni tun jiyan, gaba ɗaya hankalinsa na kan Hero ne, yana jira ya zo masa da labari a kan yarinyar nan. Kamar daga sama ya ji wayarsa na ringing. Da ɗan sauri ya buɗe idanunsa da suka ɗan kaɗa saboda ɓacin rai. Ya miƙe zaune sannan ya ɗaga wayar.
"Ya?" Ya faÉ—a tun kafin Hero É—in yace wani abu.
"Komai ya kammalu.."
"Kana ina?" Bad ya faɗa bayan ya miƙe tsaye.
"Tun yau za ka je ne?" Iska ya ɗan fesar yana lumshe idanunsa da ɗan ɓacin rai yace
"Just tell me kana ina?"
"Ohk..." Be ajje wayar ba se da Hero ɗin ya sanar da shi inda yake, sannan ya jefata cikin aljihunsa kana ya ɗauki shegiyar hularsa me kyau ya ɗorata a kan kwantacciyar sumar kansa ya fice daga ɗakin. Cikin sa'a Daddy baya nan, hakan ne ya sa be samu tsaiko ba ya fice daga gidan bayan ya kartawa masu tsaron rashin kirki. Dan kuwa idan dai Daddyn na nan shi ne kawai suke aikinsu, dan ma dai shi ɗin idan Daddy na nan be cika fita sosai ba. Idan kuwa Daddyn baya nan, daga ya yi musu magana a kan ze fita za su ƙyale shi ya fice jiki na rawa, ba tare da lura da amanar da Daddyn ya basu ba.
"Tafiyar za ta É—auke mu minute nawa?" Ya faÉ—a sanda yake kallan Hero.
"30 minute.."
"Ohk let's go.." ya faɗa yana shirin miƙewa.
"But Bad. I think ya kamata ka ɗan sha wani abun, ina me tabbatar maka da rashin kirkin da za ka yi se yafi wanda ka shirya masa.." Wani wulaƙantaccen kallo ya bi cup ɗin da Hero ya miƙo masa da shi sannan yace bayan ya ɗan ja ƙaramin tsaki
"Ba na buƙatar komai dan zan yi rashin kirki.. Idan za ka je ka miƙe mu tafi.. Idan kuma ba za ka je ba just give me the address.."
"Toh juice fa?" Ya faÉ—a yana kallansa. Jin be ce komai ba ya sanya shi sake faÉ—in
"Sorry my man. Mu je.." ya faɗa yana miƙewa. Se kuma ya cigaba da faɗin
"Ina fatan za ka koyawa yarinyar hankali, yanda ko da wani ne ya sake sakata aiki a kan kowanne game gari ne ba za ta karɓa ba ballantana a kanka.. Mari fa..?"
"Heeyy!!!" Bad ya faÉ—a cikin É—aga murya yana kamo Hero kamar ze dake shi.
"Na bar maganar.." Hero ya faÉ—a. Komawa Bad ya yi ya zauna jin kansa ya É—an sara masa. Se ya saka hannu ya É—auki sassanyan Juice É—in da Hero ya zuba masa ya kai bakinsa ya shanye tass sannan ya ajje yana É—an sauke numfashi idanunsa a lumshe. Wajen sakanni talatin sannan ya buÉ—e idanun nasa, ya kalli Hero yace
"Let's go.." ya faɗa yana miƙewa. Babu musu a wannan karon Hero ya yi gaba yana faɗin
"Ohk Sir.." Ko da suka isa wajen motar Bad Man, Hero har da saka hannu ya buɗe masa ƙofa, ya shiga ya zauna har lokacin fuskarsa babu fara'a saboda ɓacin ran da ya kwana da shi. Zagayawa Hero ya yi ya tayar da motar kai tsaye suka wuce gidan na Muhammad Aji.
... Se da ya ɗaga kai ya kalli motar lokacin da ta shiga cikin layin. Be kawo komai ba suka cigaba da ciniki da me saida ɗatar. Har ƙofar gidan Hero ya yi parking na motarsa, ya kalli Bad Man yace
"Ga gidan nan.." Hero ya faÉ—a yana nuna gidansu Lulu. Bin gidan ya yi da kallo kamar me nazari, se kuma ya É—an yi murmushi yace
"Well done. Za ka iya tafiya.." Babu musu yace
"Allah ya bada sa'a.." ya faɗa yana murmushi. Daga haka ya sauka daga motar, shi ma Bad ɗin ya sauka. Shi Hero se ya fice daga layin yayin da Bad Man ya yi cikin gidan. Hannunsa ya saka ya tura ƙofar gidan. Da wani banzan kallo yake bin gidan da shi. Be dakata ba har se da ya durfafi inda ɗakunan gidan suke. Ƙofar ɗakin a buɗe take, hakan ne ya sanya shi shigewa ciki kawai. A nutse ya soma jefa idanunsa cikin ɗakin ko ze hango fuskarta. Ko ma ba tata ba ya hango ta wata, se dai be hango kowa ba. Hakanne ya sanya shi ɗan soma takawa zuwa cikin ɗakin. Motsin da ya ɗan ji a ɗakin da yake shirin gettawa ne ya dakatar da shi. Se ya dawo da baya ya saka hannunsa ya tura ƙofar ɗakin. Daidai lokacin da ta fito daga toilet. Se ta ɗauki hijab ta saka, dan ta riga da ta saba, ko da tana gida ne ta zauna da hijab. Kamar a mafarki ta ji an turo ƙofar ɗakin. Se ta ɗaga kai da sauri, ta ma ɗauka za ta ga ki Little ne, se dai me? Cikin lokaci ƙanƙani idanunta suka sauka a kan Bad Man dake tsaye bakin ƙofar hannayensa saye cikin aljihu, fuskarsa a ɗinke kamar wanda be taɓa dariya ba. Ba ta san lokacin da ta saki ƙara ba jikinta na ɗaukar rawa. Se ta yi hanyar banɗaki cikin matuƙar tsoro, firgici da rikicewa. Se dai me? Se ta ji toilet ɗin a rufe, ta manta ita da kanta ta cire key ɗin ta ajje shi kan drawer. Kallan wajen ta yi kamar za ta ɗauko, se dai Bad ɗin ya soma matsowa. Se kawai ta fashe da kuka tana kallansa.
"Tsoro kuma kike ji yanzu? Wace ce ke? Waye ya aikoki?" Ya yi tambayar duka a lokaci É—aya kyakykyawar fuskarsa kuma har lokacin a haÉ—e.
"Wace ce ni kuma?" Ta tambayi kanta cikin mamaki. Se dai ba ta san tambayar ta fito fili ba.