Sashe 2
A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah se na faɗa wa Abba.." ya faɗa yana shirin yin gaba.Da sauri ta riƙo shi ta ɗan sassauta fuskarta kaɗan kafin tace
"Ka je kace bani da lafiya.." maƙe kafaɗa yayi yana faɗin
"A'ah.." Tsaki ta ja dan ta san in dae ta biyewa wannan yaron se dai faɗan da Abban ze nata ya ƙaru, hakan ne ya sanyata sakinsa kawai ta shiga shiryawa tana sake cika tana batsewa. Ta san halin Abba sarai, gudun kada ya gane ciwon ba na gaske bane ya sanya ta yin kalar tausayi da fuskarta hadda aro ƙwallar ƙarya cikin idanunta sannan ta fito, a hankali tace
"Abba sannu da zuwa" ta faÉ—a da muryarta da ta sake yin rawa fiye da yadda take. Cikin tausayawa yace
"Yawwah. Bari na É—akko miki magani ki sha se ku wuce" Tun da dai ta san makaranta ce dole se taje tun da Abba ya saka baki ya sanyata faÉ—in
"A'ah Abba ai na sha, ciwon kai ne dama kuma ya warke"
"Toh madallah. Se kun dawo Allah ya tsare." Didi da Little kaɗai suka iya amsawa ita kuwa Lulu ta kasa faɗin komai dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan yadda zasu ƙarke ne da Gwani bayan ba tayi hadda ba, duk da yadda hankalinta ke a kwance da rashin yin haddarta ta amma yanzu se da ta ji wani tsoro tsoro na neman kamata tayi saurin basarwa tana sake cika tana batsewa. Ita kuwa Didi dariya kawai take yi a ɓoye dan kada Lulun ta gani yanzu se ta sake fusata.
"Yau ba zaki biyawa Masoyiyarta ki ba?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu sanda suke dab da wuce gidansu ƙawar Lulun. Hararar gidan tayi kamar shi ne ya mata laifi sannan tace
"Ehh É—in.." ta faÉ—a tana wuce gidan ma da sauri. Ba tace komai ba Didi se bin bayanta da tayi suka cigaba da tafiya. Sakin hannun Didi Little yayi ya koma kusa da Lulu yace
"Ki riƙeni kin ji!"
"Ba za a riƙe ba" ta faɗa tana maka masa wata uwar harara, dan yau ɗin gaba ɗaya haushin kowa take ji, musamman ma Little ɗin da kamar shi ne ya janyo mata, da yace bacci take da yanzu tana can a matsayin mara lafiya tana bacci hankalinta kwance. A yanzu kam dariya Didi tayi sosai ta cikin niƙab ɗinta, ta janyo hannun Little suka cigaba da tafiya. A haka har suka ƙarasa makarantar..
*** ***
Gida ne da ya amsa sunansa gida, ƙato wanda idan baka sani ba daga kallan farko zaka iya kiransa da ƙatuwar plaza. Haɗaɗɗen gida ne wanda tsayawa faɗar irin haɗuwar da yayi ɓata baki ne, dan kuwa anyi ɓarin kuɗi kamar me, an gina shi cikin tsari da ƙwarewa kamar ba a Nigeria ba. Ko daga Compound ɗin gidan kaɗai se an tashi kanka saboda yadda ta matuƙar ƙawatu da abubuwa kala kala se dai marasa hayaniya. Idan kuwa tun farko dama a cikin Compound ɗin ka tsinci kanka to fa ba zaka taɓa cewa a Nigeria kake ba. Ƙaton parlour ne da ya lamushe kujeru saiti uku a gefe guda na cikinsa, wanda anan ne aka zuba kayan ado da ƙawa aka ƙawata haɗaɗɗen parlourn da ko na shugaban ƙasa albarka, parlour ne da ya amsa sunansa parlour, parlour ne da a karan farko zaka iya kiransa da aljannar duniya saboda matuƙar haɗuwar da yayi. Akan ƙaramar kujera wani kyakkyawan babban mutum ne dake sanye cikin wata dakakkiyar shadda da kallan farko zaka mata ka san ta lamushe kuɗi na musamman, fuskarsa kuwa a kallan farko baka isa ka ƙayyade adadin shekarunsa ba, saboda yadda jin daɗi da kuma hutu suka lamushe kaso masu yawa daga cikin shekarunsa. Kyakkyawan babban mutum wanda aƙalla ya bawa 50 baya, idanunsa saye suke cikin glass me matuƙar kyau da tsada, wanda yake amfani da shi idan ze yi wani aikin da ya shafi Computer ko waya. A yanzu ma idanunsa na kan hamshaƙiyar waya ne yana dannawa cikin ƙwarewa. A nutse take takowa cikin parlourn, duk da yanayin shekarunta da suka tura hakan be hanata cin kwalliya kamar yarinya er shekara 20 ba, ƙafarta saye cikin wani hill shoe, sanye kuma cikin rantststiyar atamfa me shegen kyau da tsada, ta sha ɗauri irin wanda ake kira da ture kaga tsiya. A haka take takowa zuwa cikin ƙaton parlourn da kafin ƙarasowarta inda mutumin nan ke zaune ta ɗauki sakanni masu yawa. A nutse ta nemi waje ta zauna cikin kissa da kisisina tace
"Barka da wannan lokaci Yallaɓai." Se da ya ƙarasa abin da yake yi cikin waya kamin ya ɗago ya kalleta bayan ya ɗan zame glass ɗin fuskarsa yace
"Barka kadai.."
"Aiki ake yi ne?" Ta tambaya tana gyara zama akan haÉ—aÉ—É—iyar kujerar da ke kusa da tasa.
"Ƙwarae kuwa. Kin je kin duba abokiyar zaman naki? Bata ji daɗi ba." Se da ta taɓe baki sannan tace bayan ta yamutsa fuska
"Zan dai shiga, amma yanzu magana ce ta kawoni akan Boy." Ƙarasa cire glass ɗin yayi ya ajje a gefe kamin ya juya ya kalleta sannan yace
"Yaya muka yi da ke?" Girgiza kai Hajiya Salma tayi kana tace
"A'ah fa Yallaɓae, ka sake kwantar da hankalinka ba wani abun yayi ba. Akwai manufofi da dama da suka saka na takura se ya tafi ƙasar waje karatu, misali raba shi da Abokansa na nan ɗin waɗanda yake biye musu, acan kuwa idan babu su na san dole ze rage wasu abubuwan. Kawai dai zuwa nayi in ji ko zaka tura a ɗakko shi ne?" Sauke ajiyar zuciya yayi, bayan yayi murmushi sannan yace
"Kamar na faɗa miki zan cire hannuna daga wannan maganar koh? Babu yanda ban yi dake akan fitar AREEF ƙasar waje ba kika dage, yanzu ma se kiyi komai da kanki."
"Haba kai kuwa me yasa za kace haka? Ta yaya zan yadda Boy yayi karatu anan bayan ga 'ya'yan manyan mutane na ta fita waje suna karatu wasu ma sun koma da zama acan. Se nawa ɗan ƙwalli ɗaya takk, ace yayi karatu a cikin ƙasar nan. Yanzu yallaɓae mu ba abin kunya ba ne a garemu ace ɗan gidan ALHAJI MATAWALLE guda yana karatu a cikin ƙasar nan bayan babu sa'anninsa? Wannan ma ai salon raini ya shiga tsakaninsa da 'ya'yan talakawa ne.!" Ta ƙare tana yatsina fuska kamar wadda ta ga kashi..
https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_02
__Kallanta Alhaji Matawalle ke yi har ta ƙare zancenta. Ya girgiza kai yana ɗaukar juice me sanyi cikin tambulan ya kai bakinsa ya ɗan kurɓa kana ya sauke. Baya son zancen nasu yayi nisa dan be ƙarasa aikin da yake yi ba, ya kuma san idan har be amsa mata ba ba zata tafi ta bar maganar ba, shi kuma ya riga da ya tsara mutanen da zasu je taho da Areef ɗin. Se dai a kodayaushe baya nuna mata yana bin bayan yadda take shagwaɓa Areef ɗin, take so ta dinga nuna yafi kowa a cikin garin saboda kasancewarsa ɗan wanda yafi kowa kuɗi a garin a wannan lokacin.
"Ki je zamu yi maganar.!" Ya faɗa bayan ya kalleta fuskarsa a ɗan cunkushe, baya ma so yayi mata magana akan irin maganganunta marasa daɗi da kullum basa ƙarewa alan talaka, yayi maganar, yayi faɗan har ya gaji.
"Amma Yallaɓae da gaske ka damƙa komai a hannuna?" Girgiza kai yayi kafin yace
"Na ɗauki wannan aikin, ke dai kawai ki shiryawa dawowarsa." Murmushi me ƙayatarwa ta saki har cikin ranta tana jin daɗi, musamman idan ta tuna yadda tilon ɗan nata ze dawo bayan tsawon shekarun da ya ɗauka a harvey Mudd College da ke California U.S. Ba ta kai ga cewa komai ba Alhaji Matawallen ya sake faɗin
"Ki saka a gyara masa part É—insa." Da sauri ta soma faÉ—in
"Yallaɓae halin Boy ɗin ka manta? Ni da kaina zan gyara masa, idan ba haka ba yanzu zaka ji yace ɗakin yana warin 'yan aiki." A wannan karon ma se ta ƙare maganar tana yamutsa fuska.
"Allah ya taimaka" yayi gaggawar katseta.
"Ameen. A huta lafiya." Tayi maganar tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Bin ta da kallo yayi kafin ya dawo da dubansa cikin ɗakin yana girgiza kai, a kodayaushe al'amuran Hajiya Salman ƙara ƙaimi suke yi, shi har mamaki take ba shi da ta yadda ya cire hannunsa akan tafiyar Areef ƙasar waje. Bayan ta manta waye shi wajen kula da tarbiyyar Areef ɗin, shi ne take tunanin ze bar shi sakaka haka a can wata ƙasar ba tare da yana sakawa ana duba shi ba? Ya sake girgiza kai kawai yana maida glass ɗinsa ya cigaba da abin da yake yi cikin wayar.
.. Wayarta da tayi ƙara ta kalla, ganin kiran wadda ya shigo wayar ya sanyata ɗagawa tana cigaba da taku ɗai_ɗai.
"Hello Auntyn Areef" shi ne abin da Hajiya Salma ta faÉ—a. Murmushi wadda aka kira da Auntyn Areef tayi kana tace
"Na'am, toh ya ake ciki?"
"Cikin satin nan Boy ze dawo!"
"Woww!! Amma gaskiya na ji daÉ—i ki ce na kira a daidai."
"Aikam dai. Bari zan kiraki akwai abin da zan yi yanzun." Babu ɓata lokaci suka yi sallama da ƙanwarta ta daidai lokacin da ta ƙaraso bakin ƙaton part ɗin abokiyar zamanta. Se da ta ɗan tsaya kamar me son ganin wani abu, se kuma ta ɗan saki ƙaramin tsaki kana ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ya ƙawatu da Furniture masu kyau da tsada, komai kuma na cikin ɗakin milk da coffee ne irin masu ɗaukar idon nan. Ƙaton parlour ne se dai duk girmansa be kai na Alhaji Matawalle ba. Daidai lokacin da ta shiga ɗakin ta tsinci muryar Atine (Er aikin kishiyarta) na faɗin