← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 37

Sashe 32

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Just ka binciko min gidan ubanta.. Wallahi ko waye ubanta ba ze hana ni shiga har cikin gidan, kai har cikin ɗaki zan shiga na bata wulaƙantaccen mari da kuma tarin gargaɗi. Haters??" Ya ƙare a mamakance. Shi har yanzu abin mamaki yake bashi. Ajiyar zuciya Hero ya sauke yana jinjinawa rashin ji irin na Bad Man. Ya riga ya san tunda ya faɗa hakan ze cika ne, ko me kuwa za a yi se ya cika abin da ya faɗa. Lallai yarinyar ta janyowa kanta ruwan dafa kanta. Daga tarkon Ladi ta janyowa kanta na Bad Man.

"Shi kenan.. ka bani kwana ɗaya zan bincika maka.." ya faɗa a ransa yana saƙa yanda ze jewa da Ladi maganar nan. Shi har ya ma gama tsara yanda komai ze tafi, tabbas shigowar Bad Man cikin wannan tafiyar shi yafi komai daɗi, shigowarsa ciki za ta ƙarawa abubuwan armashi. Koma yace shigowarsa ce ma za ta gyara komai.

... "Wallahi Allah ya isana.." Lulu ta faɗa tana share ƙwallar da ta ƙi tsayawa a kan fuskarta.

"Masoyiya ni fa kina bani tsoro wallahi. Yanzu duk girman mutumin nan, kwarjini da sauran abubuwa ki ka kasa jin kunyar marinsa cikin jama'a? Ba kuma ya rama fa?" Da sauri Lulu ta juya ta kalli Fatima.

"Shi be ji kunyar taɓa jikina ba, se ni zan ji kunyar marinsa? Ɗan iskan banza kawai, mugu, azzalumi.." ta sake faɗa tana kuma ɗauke ƙwallar idanunta.

"Haka ne kuma.." Fatima ta faɗa. Har suka isa gida Lulu bata dena mita ba, tun Fatima na bata haƙuri har ta gaji ta yi shiru. Se da suka kusa shiga gida sannan Fatiman ta kalleta tace

"Amma dai ya kamata ki tsaya ki saita kanki in case kar Ammi ko Didi su fahimci wani abun.." Shiru ta yi kamar ba zata amsa ba. Se kuma can tace

"Na ji.."

"Yawwah ko kefa.." da ƙyar dai ta tsaya ta nutsu ɗin sannan suka shige cikin gidan. A parlour suka tarar da Little da Didi da dawowarsu kenan daga islamiyya.

"Sannunku da dawowa." Didi ta faÉ—a tana murmushi.

"Yawwah Didi.." Fatima ta faÉ—a, yayin da Lulu ta nemi waje ta zauna a kan kujera. Didi ta kalleta tace

"Ke kuma lafiya?"

"Ƙishirwa nake ji.." ta faɗa tana turo baki. Jinjina kai Didi ta shiga yi tace

"Lallai Lulu kullum taɓararki ƙara gaba take yi, wai ƙishirwa kike ji.." Fatima ba ta daɗe ba ta yi wa Ammi sallama sannan ta wuce gidansu bayan ta yi wa Lulu sallama.

... Cikin takun ƙasaita ta shigo ɗakin, tana tafiya tana yauƙi kamar wata budurwa, hannunta ɗauke da tire da ke ɗauke da wani glass jug da cups ɗinsa a gefe. A hankali ta ƙaraso ta aje a gaban Daddyn sannan ta koma ta zauna tace bayan ta ɗan yi fari

"Barka da hutawa Yallaɓai.." Murmushi ya yi yace

"Barka dai.. Kina lafiya?"

"Lafiya ƙalau nake.."

"Toh madallah.."

"Bari na zuba maka.." ta yi maganar tana miƙewa ta tsiyaya juice ɗin cikin glass cup ɗin sannan ta miƙa masa. Babu musu ya karɓa daidai lokacin da Mommah ke faɗin

"Barka da wannan lokaci.." kamar ba za ta amsa ba, se kuma can tace

"Barka.. Yawwah Yallaɓai dama magana ce na zo mu yi a kan ɗana.." Se da Daddy ya ɗan kurɓi juice ɗin sannan yace

"Toh ina jin ki.." Kallan Mommah Mom tayi sannan ta maida shi kan Daddy tace

"Ai na ga akwai baƙuwar fuska ne.."

"Baƙuwar fuska kuma? A ina?" Daddy ya faɗa yana kallan cikin ɗakin. Yamutse fuska Mom ta yi kafin tace

"Dole nace baƙuwar fuska mana Yallaɓai, tunda dai magana ce da ta shafi tsakanin iyaye biyu a kan ɗansu.." Se a lokacin ya fuskanci abin da take nufi, se ya girgiza kai cike da takaicin halinta yace

"Amma dai kin san É—a na kowa ne koh?" Se ta girgiza kai da sauri tana faÉ—in

"In ji hausawa ba? Amma É—a ai na me shi ne.."

"Ranka ya daɗe, a huta lafiya.." Mommah ta faɗa tana murmushin yaƙe. Amsa mata Daddy ya yi yana binta da kallo cike da tausayawa har ta fice. Se a lokacin ya dawo da dubansa kan Mom yace

"Ki dena wannan abin da kike, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba na sha yi miki faɗa a kan irin wannan halin, amma kin ƙi dainawa. Se yaushe ne za ki dena?" Ya yi maganar yana kallanta.

"Tom.." ta faɗa dan so take kawai a bar maganar, kafin ran Daddyn ya sake ɓaci, yanzun nan ya chanja mata fuska bayan magana take so su yi.

"Dama magana ce a kan Areef.." ta faÉ—a a tausashe.

"Ina jinki.." Daddyn ya bata amsa a taƙaice. Se da ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Dama so nake na roƙi alfalmar ko za a samar masa aiki a wata ƙasar na ga yafi sabawa da can ɗin.." Kallanta Daddy ya yi kamar me nazarin wani abu daga fuskarta. Ba tace komai ba ta yi shiru tana jiran ta ji amsar da za ta fito daga bakinsa. Murmushi Daddy ya yi yana girgiza kai yace

"Aiki a wata ƙasar, ke ba ma a wata ƙasar ba matsala ce a wajen Areef. Dama ya lafiyar kura bare ta yi zawo? Idan dai har aiki na samar masa, toh ya zame masa dole ya dinga zuwa kodayaushe. Idan kuwa kasuwanci ne babu ruwansa, ze iya ɗora wani a kan wani abun idan ya yi niyya. Ko kuwa kin fi so ya dogara ne da gwamnatin nan tamu? Idan hakan ki ke so shi kenan. Amma dai ki tabbatar kin fara tuntuɓar ɗan naki, dan idan dai har na yanke hukunci ba zan chanja ba.." Numfashi Mom ta ajje kana tace

"Ai Yallaɓai ba ina nufin aiki gama gari ba.."

"Duk wani aiki sunansa aiki ne.." Daddy ya katseta da faÉ—in hakan.

"Shi kenan.. Zan tuntuɓe shi na ji daga bakinsa.."

"Hakan ma ya yi.." Daddy ya faɗa yana kai juice ɗin hannunsa baki ya kurɓa.

... Tare suka fito daga asibitin shi da Abbati kamar ko yaushe, da yake shi ɗin amintaccen Abeey ne ya sa se ya zama kamar shi ne mataimakin Gwani a duk wasu al'amuran da suka shafi rashin lafiyar Abeey ɗin. Abbatin ke ɗauke da ledar maganungunan Abeey haka suka fito titi. Gwani yana cikin favourite shigar nan tasa da ke matuƙar yi masa kyau, wadda kodayaushe ba a iya ganin sumar kansa da ke a rufe, se zahirin kyakkyawar fuskarsa da ke a buɗe, shigar da a lokuta da dama idan mutane suka kalle shi kafin ya yi magana kai tsaye suke kiransa da balarabe, saboda babu wani abu da ya banbanta shi da su. Fari, kyau, shiga da komai da komai irin nasu ne. Kai Gwani fa na daban ne a komai.

"A'ah Malam Affan, yau ma dai mun sake haɗuwa.." Abba ya faɗa yana murmushi. Shi ma murmushin ya maida masa yana miƙa masa hannu suka gaisa. Suka gaisa ma da Abbati, sannan Abba yace

"Ya me jikin?"

"Alhamdulillah.." Gwani ya faÉ—a cikin nutsuwa.

"Madallah.. Allah ya ƙara afuwa.." Abba ya faɗa

"Ameen" Gwani da Abbati suka haÉ—a baki wajen faÉ—ar hakan.

"Dama ina so na sake ganin jikin nasa. Se dai yanzu ina sauri ne, akwai inda zan je.. Ka saka min numberka, idan na shirya zan zo na duba jikin Malam.." Abba ya faɗa yana miƙawa Gwani wayarsa. Karɓa ya yi a nutse ya shigar da numbersa sannan ya miƙawa Abban. Daga nan Abba ya yi musu sallama ya shige inda ya zo.

"Malam wannan mutumin na da kirki wallahi.." Jinjina kai Gwani ya yi kamin yace

"Tabbas.."

"Allah ya saka masa da alkhairi, ya ƙara zumunci... ko shi ma dai ɗalibin Malam ne?" Girgiza kai Gwani ya yi daidai sanda suka tare adaidaita yace

"A'ah.."

... Allah Allah take kawai ya gama abin da ze yi ya fita ba tare da ya tashi waÉ—anda suka yi fashi ba. Babu daÉ—ewa ya gama littafin, sannan ya rufe shi. Se kowa ya shiga mayar da littafan cikin jaka ana jiran ya yi addu'a a tashi. Se dai me? Abin da dai ba ta son ji shi ne abin da ya faÉ—a wato

"Wanda duk ya yi fashi ba tare da ya sanar min ba, ya fito.." Kamar kar ta tashi, se kuma ta tuna irin wannan abin da take yi ma fa yana janyo raini. Cikin ikon Allah yau se ya kasance su biyu ne suka yi fashin. Kallanta Didi ta yi sanda ta miƙe a mamakance. Ƙasa_ƙasa tace da Fatima

"Dama ba ku faÉ—a ba?" Girgiza kai Fatima ta yi kunya na kamata se kawai ta yi shiru tana kallan Lulu da ta fita zuwa wajensa. Da É—ayar er ajin tasu ya fara, fuskarsa a tamke, dan shi ba ya son raini, idan yace ba ya son abu kawai ba ya so. Babu daÉ—ewa suka gama da ita, ashe mamansu da kanta ta zo ta sanarwa da Malam Ahmad a kan rashin zuwan nata, saboda Gwani da bata samu ba. Dan haka se ya sallameta, sannan ya maida dubansa kan Lulu yace

"Me ya hanaki zuwa?" Shiru ta yi a ranta tana tunanin abin da ya kamata ta faÉ—a. Se kawai ta yi shiru tana É—an motsa jikinta. A karo na biyu ya sake maimaita tambayar tasa. Se a wannan karon sannan ta É—an soma motsa baki fuskarta a haÉ—e kamar me faÉ—ar wani abun.

"Babu dalili kenan?" Ya faɗa ransa a ɗan ɓace.

"Toh Ya Sayyadi ƙarya zan yi?" Ta fada tana ɗan yamutse fuska a kuma gajiye.

"Hafsa! Karɓo min bulala.." ya faɗa yana kallan Hafsa Abba da ta kasance Monitor. Da mamaki gaba ɗaya en ajin ke kallan Gwanin jin abin da ya faɗa, dan a iya saninsu, tun zuwansa makarantar ba ya taɓa shiga aji da bulala, a gaba ɗaya makaranta ma babu wanda ya taɓa ganin sanda ya yi duka.
Chapter 32 · 0% Book details