← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 37

Sashe 12

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Woww, amma gaskiya na ji daÉ—i, na yi farin ciki Kaseem." Ta faÉ—a tana jin wani irin daÉ—i na ratsata, dan kuwa tun da yayi maganar ita Jadwa kawai ta hango ta kuma san ita yake nufi, idan kuwa har Jadwan ta amince to fa shi kenan ta samu mijin aure na nunawa sa'a, dan kuwa Kaseem É—in akwai abin hannu. Be ce komai ba ban da murmushi da ya sake yi. Sakkowa daga kan kujerar Mami tayi tana faÉ—in

"Bari na kira maka ita." ÆŠan zamowa yayi daga kan kujerar da yake kai yace

"A'ah da kanki kuma." Ya ƙare yana murmushi. Itama murmushin tayi kana tace

"Toh mene ne Kaseem? Kada ka damu." Tayi maganar tana ficewa daga ɗakin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin lallai tabbas komai ze zo masa da sauƙi In Sha Allah.

Cikin matuƙar farin ciki da jin daɗi Mami ta faɗo dakin fuskarta murmushi yaƙi barinta tun ɗazu.

"Maza maza tashi ki je kin yi baƙo." Mamin ta faɗa tana dukan ƙafar Jadwan.

"Baƙo kuma?" Jadwa ta faɗa cike da mamaki, dan dai ita ta san ba suyi da kowa ze zo wajenta ba. Jinjina kai Mami tayi tana faɗin

"Ƙwarai kuwa, tashi.. Lulu maza tashi ki tayata shiryawa kin ji?" Ta ƙare maganar tana kallan Lulu. Babu musu kuwa Lulu ta miƙe daga kan kujerar tace tana kallan Jadwa

"Mu je!"

"Kin ji ki kema, in je ina?" Tsaki Mami ta ja kafin tace

"Shashasha sakarya, da alama yau kin yi babban kamu, kamun da idan dai har ba wasa kika yi ba kin yi dace da smaun miji me kuÉ—i kuma na gari.. Ina Kaseem da kika sani a baki?" Da sauri Jadwa tace

"Ehh.. ehh.."

"Toh shi ne yazo wajenki." Mami ta faÉ—a. Da sauri Jadwa ta diro daga kan kujerar tana faÉ—in

"Kai Mami.." Hannunta Mami ta kama tace

"Maza mu je ki shirya pls, ka da a ɓata masa lokaci" Yanzu kam babu musu Jadwan ta bi Mami zuwa ɗaki. A wannan karon ita dai Lulu taɓe baki tayi kawai ba tace komai ba se bin bayansu da tayi. Wasu haɗaɗɗun kaya Mami ta fitowa da Jadwa su, babu musu ta ɗauka ta saka, sosai kayan suka mata kyau, suka zauna ɗass a jikinta, ta ɗauki ƙaramin mayafi ta saka sannan ta shafe fuskarta da powder.

"Ki ɗan yi kwalliya mana ko yaya ne!" Mami ta faɗa tana kallan Jadwan, dan ita dai tafi so ta ƙure wanka a yau ɗin.

"Mami haka ma fa ya isa." Ta faɗa tana ajje turaren da ta gama fesawa. Da sauri Mami ta karɓa tana faɗin

"Shashasha, har kin gama sakawa? Ni gyara min na sake feshe miki jiki da shi, so nake na ji ko ina na jikinki na tashin ƙamshi." Ta faɗa tana sake feshe turaren a jikin Jadwa..

Ku yi manage da wannan pls, mu haÉ—e gobe idan Allah ya kai mu.

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_08

___Ita dai Lulu binsu kawai take da kallo, se kace waɗanda aka ce an musu albishir da wani abun na musamman, ko kuma za su je su ga wani abun na musamman ne. Sosai Mamin da ita kanta Jadwan suka bata mamaki, duk yanda suke amma a kan namiji sun bi sun ruɗe kamar ba su ba. Ɗan taɓe baki kawai tayi tana bin Jadwa da kallo sanda ta zo gaban mudubi tana juyi tana kallan jikinta. Zagayeta Mami tayi tana murmushi tace bayan ta ɗaga yatsanta ɗaya alamar jinjina

"U look so take away.." Murmushi Jadwa tayi sanda take faÉ—in

"Awwwn, Mami ki bar zugani haka nan." Komawa Mami tayi ta zauna kusa da Lulu sannan tace

"Heyy! faɗa mata tunda ni sa'arta ce" yaƙe kawai Lulu tayi kamar ba za tace komai ba, se kuma tace

"Sosai ki ka yi kyau fa.."

"Mami, bari na je, kada yayi ta jira." Jadwa ta faÉ—a bayan ta sakarwa Lulu murmushi.

"Toh se kin dawo." Mami ta faɗa, ita kuma Jadwa ta fice daga ɗakin. A hankali take takawa tana wani rangaji kamar agwagwa, ƙafarta dake ɗauke da hill shoe tana bada sautin 'ƙwas_ƙwas'. Ɗan lumshe idanunta tayi sanda tazo dab da shiga ɗakin tana sauke numfashi, dan bata taɓa ganinsa a fili ba. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, cikin matuƙar farin ciki yadda yake tunanin ze yi arba da kyakkyawar fuskar da ta hana shi bacci tun ranar da ya soma ganinta ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan Jadwa da ke cigaba da takowa cikin ɗakin. Shi da ya buɗe baki da niyyar amsa sallama cike da karsashi duk se yaji jikinsa yayi matuƙar sanyi, hakan ne ya sanyashi ƙarasa sallamar a hankali. Ba tare da ta kalli inda yake zaune ba, ita a lallai dole me kunya, ta nemi waje ta zauna sannan tace

"Barka da zuwa. Ina wuni?" Ta ƙare maganar tana ɗago wa ta kalle shi. Ƙaƙalo murmushi yayi yace

"Yawwah, barka dai." Se dai duk hankalinsa yafi tunanin meyasa ya ga daban da wadda ya gani a jiya? Toh ko dai rakiya tayo ne? Abar ƙaunarta sa na ciki? Hakan da ya tuna ne ya sanya shi ɗan gyara zama sannan yace

"Sannu koh? Ya makaranta?" Wani irin daÉ—i ne ya ziryarceta tace bayan itama ta gyara zama tace

"Alhamdulillah."

"Madallah." Ya faÉ—a. Daga haka se shiru ya mamaye É—akin, ita tana jira yace wani abun, yayin da shi kuma yana jira ne ya ji tace 'yar uwarta ta na nan zuwa. Jin shiru ya sanya shi faÉ—in

"Amm sisterta ki fa?" Ya tambaya yana murmushi. Da mamaki ta É—ago ta kalle shi, se kuma ta É—an basar tace

"Sisterta kuma?" Ta tambaya a mamakance. Yanzu kam shi kansa abin ya bashi mamaki, shi dai ya san tabbas ba wannan ya gani ba, amma ya tabbatar wadda ya gani gidan nan ta shigo kuma yanzu an turo masa wata a matsayin ita ya gani. Shi kam sam ba ze yadda yayi saki na dafe ba, hakan ne ya sanya shi faÉ—in

"Amm, na haɗu da wata ne tana shirin shiga Islamiyya, so na bi bayanta na ga kuma gidan nan ta shigo." Cikin mintuna ƙalilan Jadwa ta ji jikinta yayi wani bahagon sanyi, duk wannan kunyar da ta aro ta yafa ta ji tana warewa zuwa na ta wajen. Se kawai ta basar tace

"Ohh lem me call her." Ta faɗa tana miƙewa.

"Ohk.. Thanks sistor.." ya faÉ—a yana murmushi gami da binta da kallo sanda take ficewa daga É—akin. Haushi ita kuwa ya sake cikata, wato har da wani kiranta da sister duk wannan uban kashe kalar da tayi. Cikin sauri da kuma takaicin da ya cikata take tafiya har zuwa parlourn. Jefar da mayafinta tayi a kan kujera, tana tuna yanda mutuncinta ya gama zubewa a wajen Kaseem É—in.

"Kee! Me ya faru?" Mami ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. Saboda yanda take jin zuciyarta na wani irin zafi yasa ta kasa furta ko kalma ɗaya se ajiyar zuciya da take ta saukewa.

"Oh ni Sadiya, ba dai wannan banzan halin naki kika nuna masa ba?" Mami ta faÉ—a bayan ta zauna. Shirun dai Jadwa tayi har lokacin tana tuna wannan cin mutuncin.

"Wai ba za ki min magana ba ne?" Mamin ta faÉ—a a É—an zafafe, dan zuwa yanzun ta fusata.

"Mami dama kin san ba wajena ya zo ba amma kika ce na je? Ba kya tsoron mutuncina ya zube?" Hannu Mami ta saka ta dafe ƙirji kafin tace

"Ke ban san shashanci mana, kamar yaya? Toh idan ba wajenki ya zo ba, wajen wa ya zo? Ko ina da wata É—iyar ne bayan ke?"

"Lulu!" Jadwa ta faÉ—a kai tsaye. Shiru Mami tayi tunda Jadwan ta ambaci sunan Lulu. Daga lokacin da Kaseem yayi zancen ya ga wata a gidanta ita sam ta manta da Lulu, kawai Jadwa ta hango, ashe ta manta akwai wata a gidan bayan Jadwa. Ajiyar zuciya ta sauke tace tana jinjina kai

"Tirƙashi!"

"Mami ba tunani zaki tsaya yi ba fa, nace masa zan kira masa ita ne, and am sure yanzu haka jiranta yake." Jadwa ta faÉ—a. Kallanta Mami tayi tace

"Ina zuwa!" Ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da ta fito yayi daidai da lokacin da motar Abba ta shigo gidan. Se kawai ta ƙarasa wajen, daidai sanda ya fito daga cikin motar.

"Sannu da zuwa Yaya." Ta faÉ—a bayan ta É—an rusuna.

"Yawwah." Ya faÉ—a ba yabo ba fallasa. Hakan da Mami ta lura da shi ne ya sanya ta ji duk jikinta yayi sanyi, se ta kalli Abban da ke faÉ—in

"Ina yaran suke?"

"Suna ciki.." ta É—an dakata anan sannan ta É—ora da

"Ka shiga Yaya, ina da baƙo ne. Zan je na sallame shi yanzun nan se na zo."

"Toh ki yi da jiki." Da "toh" ta amsa tana yin gaba, yayin da ita kuma ta shige cikin parlourn. Duk jikin nata a sanyayen dai ta ƙarasa ɗakin da Kaseem ke ciki, yanzun ma ya ɗauka ze ga Abar begen tasa ne se ya ga Mami ta shigo. Se da suka sake gaisawa sama_sama sannan Mami tace

"Wato Kaseem ka taki rashin sa'a dan kuwa yarinyar da kake nema bata nan, kuma yanzu haka Yayana yazo. Amma In Sha Allah zamu yi magana da kai ko da ta waya ne se na haÉ—aka da yarinyar.." Ba dan ya so ba ya amsa da

"Toh, na gode sosai Madam, Allah ya kai mu. A gaishe min da Yayan."

"Toh ze ji. Ka gaida gida." Ta faɗa sanda yake dab da ƙarasawa bakin ƙofa. Se da ya fice da motarsa daga gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dawowa cikin gidan. A parlour ta samu Abba zaune ta ƙarasa suka sake gaisawa sannan ta miƙe tana faɗin

"Bari na kirasu, da alama basu san da zuwanka ba." Be ce mata komai ba ta shige É—akin.

"Lulu fito ga Abba ya zo." Ta faÉ—a bayan ta shiga É—akin. Da sauri ta É—auki hula ta É—ora a kanta tana faÉ—in

"Don Allah Mami?." Ta faɗa tana jin wani irin daɗi, dan ba ƙarya tayi missing Abban nata sosai. Murmushi Mami tayi kana tace
Chapter 12 · 0% Book details