← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 37

Sashe 17

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___"Allah ya kiyaye gaba." Shi ne abin da Gwani ya faÉ—a yana maida dubansa kan Abba da ya soma faÉ—in

"Toh Malam Affan, na gode." Ɗan murmushi ne ya wanzu a kan fuskar Gwanin ba tare da yace komai ba, se miƙa masa hannu da ya yi suka sake gaisawa. Daga haka Gwani ya yi hanyar ajinsa cikin nutsuwa. Kallan Lulu Abba ya yi da har yanzun take tsugune a wajen, ta kasa ko da motsa wa ne ballantana ta miƙe. Har kuma lokacin idanunta a rufe suke, ta kasa buɗe wa dan ji take yi kamae tana buɗe wa ɗin za ta ga idanun kowanne ɗalibi a kanta wanda hakan ze tabbatar mata da cewa kowa ya ga wannan dizgin da ya faru da ita.

"Afaaf.." Abba ya faɗa yana kallanta, ganin har lokacin ba ta tashi ba. Se a lokacin ta buɗe idanun nata, se dai har lokacin ba ta tashin ba, saboda yanda take jin ƙafafunta har lokacin na rawa.

"Kee!!" Abba ya sake faɗa. Se a lokacin ta yi saurin tattaro duk wani kuzari da ya rage mata, ta soma miƙewa a hankali, har ta miƙe a kan ƙafafunta.

"Na'am Abba.." ta yi ƙarfin halin faɗar hakan. Duk da ya lura da yadda idanunta suka yi ja, hakan be sanya shi tambayarta dalili ba, dan ya san dalilin. Dan haka se cewa ya yi

"Maza ki wuce aji. A yi karatu lafiya, Allah ya ba da sa'a."

"Ameen." Nan ma ta yi ƙarfin halin faɗa. Se da ya ga ta soma takawa zuwa hanyar da za ta kaita ajinsu sannan Abban ya fice daga makarantar. A hankali ta cigaba da taka wa, tana ɗan lumshe idanunta ko za ta samu ƙwallar da ta rage cikin idanunta ta koma. A haka har ta ƙarasa ajin nasu. Ba tare da ta kalli inda yake zaune ba ta shige cikin ajin lokaci ɗaya ɓacin ranta na ƙaruwa, tana jin wata irin tsanarsa na ratsata. Kai tsaye waje ta samu ta zauna, ba tare da ta lura ma da inda ta zauna ɗin ba. Tunda ta shigo Didi ke kallanta, ta ɗauka yanzun da ta shigo za ta ga canji daga gareta, se dai ba ta gani ba. Ta ɗan lumshe idanunta tana fatan a ce za ta ga ranar da Lulun za ta shiryu.

Wani murmushi Abida ta saki lokacin da Lulu ta zauna a kusa da ita. Se ta saka hannu ta riƙota tana faɗin

"Subhanallahi, masoyiyarta me ya faru?" Ta yi maganar tana kallanta. Hannu Lulu ta saka ta janye hannun Abidar sannan ta ɗauke kai tana jin kamar ana ƙara mata ɓacin rai ne. Ba ta haƙura ba ta sake kai hannunta za ta riƙo na Lulun. Da sauri Lulu ta juya ta watsa mata wani kallan gargaɗi ranta a matuƙar ɓace tace a hankali

"Malama ki bari mana.." ta faÉ—a muryarta a cunkushe. Jinjina kai Abida ta yi, ashe kenan duk yanda take tunanin Lulun ta wuce haka? Lallae kam akwai aiki babba a wajenta. Ita tunda ta zauna a cikin ajin ba ta san me yake magana a kai ba, saboda takaicin yanda muryarsa ke ratsa cikin ajin cike da nutsuwa, kamar me tantance kowacce kalma. Hakan ne ya sanya gaba É—aya en ajin suka nutsu, kowanne na saurarar bayaninsa. Kasancewar yau É—in ba ranar hadda bace ya sanya littafai suka dinga yi babu sanya.

... "Wai me ya faru ne?" Didi ta faÉ—a tana zama a kusa da Lulu. Girgiza kai Lulu ta yi sannan tace

"Babu komai fa Didi, kawai dai kaina ke ciwo.." Da sauri Didi ta miƙe tun kafin ta ƙarasa maganar

"Kuma na sha magani." Shi ne abin da Lulu ta ƙarasa faɗa kafin Didi ta fita daga ɗakin. Dawowa Didi ta yi tana ɓata fuska, se da ta zauna sannan tace

"Kin tabbatar kin sha?" Da sauri Lulu ta jinjina kai lokaci É—aya tana faÉ—in

"Ehh fa.."

"Me ƙarya.?"

"Ɗan aljanna.." in ji Lulu. Se suka yi dariya dukansu, kafin Didi ta miƙe tace

"Se na faɗawa Ammi kuwa.." da sauri Lulu ta riƙo hannun Didi tana narkar da fuska tace

"Ni fa da wasa nake. Kawai dai.." ta faÉ—a tana cigaba da yamutsa fuska.

"Kawai dai me..?" Didi ta tambaya

"Abin da ya faru a makaranta ne.."

"Oh my goodness.. Lulu me yasa kike son ɗorawa kanki damuwa ne babu gaira babu dalili? Me Gwani ya miki? Me ya tsare miki? Shi fa mutum ne me kirki da sanin ya kamata, me ze sa ya miki wani abun da ba za ki ji daɗi ba? Ya fa san me yake yi, wallahi idan dai har kika bi abin da yake so shi kenan zaku koma zaman lafiya. Mutumin kirki ne.." ta ƙarasa faɗa a gajiye, dan bata san kuma me za ta cewa Lulun bayan haka ba. Dan kuwa ba yau ce ranar farko da ta zauna tana fahimtar da ita kirkin Gwani ba, ba kuma ta san sanda za ta gane hakan ba.

"Tohm Didi na ji.." ta faɗa cike da ƙosawa. "Gwani mutumin kirki ne" ita har ta gaji da jin wannan maganar. Kowa haka yake faɗa a lokuta da dama, se dai ita har yanzun ba ta gani ba. Ita a wajen ta ma ba ta taɓa ganin mutum mara kirki, me girman kai irinsa ba. Kuma abin da ke sake ƙona mata rai da shi, yanda yake taƙama da wata izza bayan shi ba ɗan kowa ba ne. Harara Didi ta jefawa Lulu ba tare da tace komai ba, ta sauka daga kan gadon ta wuce zuwa inda wardrobe ɗinsu take. Kai tsaye wardrobe ɗinta ta buɗe ta soma dubawa da alama wani abun take nema. Zuwa can anjima ta rufe tata. Se ta koma kan ta Lulu ta soma dubawa, duk abin da take Lulu na kallanta, har ta zo za ta ɗauke kai se kuma ta maida kanta wajen Didin da sauri. Babu ɓata lokaci ta diro daga kan gadon ta ƙaraso wajen Didin tana faɗin

"Wai me kike nema ne? Je ki zauna zan duba miki.." ta faɗa tana tuna wayar da Mami ta ajje mata a ƙasan kayanta. Da mamaki Didi ta kalleta, ta riga ta san halin Lulun da kan son jiki, amma yau ita ce ke cewa ta je ta zauna ta bincika mata abu? Lallae. Se ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya tace

"Anya kuwa Lulu? Yau waye ne ya miki faÉ—a haka?"

"Abba mana." Ta faɗa cikin basarwa tana ƙaƙalo wani murmushi ta yi. Dan ta san idan har ta yi murmushin yaƙe toh Didin kan iya ganota cikin lokaci ƙanƙani.

"Tohm.." Didi ta faɗa tana harɗe hannunta a ƙirji ta koma ta zauna tana kallan Lulun.

.. Da sauri Mommah ta miƙe tana kallan Bad Man ɗin da ya shigo cikin ɗakin. Murmushi ya suɓuce a kan fuskarta. Se ta ƙarasa tana faɗin

"Areef..!"

"Mommah.." ya faɗa da wannan kakkaurar muryar tasa me daɗin sauraro. Babu ɓata lokaci ya cigaba da takawa zuwa cikin ƙaton parlourn har zuwa sanda ya ƙarasa inda jerin kujerun suke, ya nemi waje ya zauna ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya. Neman waje itama Mommah ta yi ta zauna, duk da yanda ta ji daɗin ganinsa amma ba ta son abin da ze janyo tashin hankali tsakaninta da Mom. Dan ta san daga wannan ɗan zuwan da ya yi idan har ta sani za ta iya tayar mata da hankali.

"Areef.. Mom ta san za ka zo nan É—in?" Da mamaki ya kalli Mommahn jin tambayar da ta fito daga bakinta. Se ya É—auke kai kawai ba tare da ya amsa mata tambayar ba yace cikin er basarwa

"Gud evening.." Ta riga ta san halinsa. Ta san sarai ya ji ta, amsar ce dai ba ze bayar ba. Hakan ne ya sanyata yin murmushi sannan tace

"Ka na lafiya? Ya hutu?" Ɗan murmushin gefen baki ya yi kafin ya ɗan taɓe bakinsa yace

"Uhmm.. Cool.." Murmushi Mommah ta sake yi lokaci ɗaya tana miƙewa ta wuce ƙatuwar freezer da ke can wani ɓangare a cikin ɗakin ta buɗe. Kafin ta kai ga ɗauko komai ta jiyo muryarsa yana faɗin

"I don't need anything Mommah.." ya faɗa yana miƙewa lokaci ɗaya yana gyara zaman hular kansa.

"Haba Areef, ka tsaya ko ruwa mana ka sha.." Mommah ta faÉ—a sanda take kallansa. Se ya girgiza kai yace

"Not dis tym gaskiya."

"Ohk se yaushe?" Mommah ta faÉ—a. Kamar me tunani ya É—an tsaya se kuma yace

"Ahmm bye.." ya yi maganar yana soma takawa ya fice daga É—akin. Se ta bi shi da kallo, duk da be ci komai ba, amma ta ji daÉ—in zuwansa sosai.

Kai tsaye bayan fitarsa daga É—akin part É—in Daddy ya wuce, dan ba tun yanzu ya ke kiransa a kan yana nemansa ba. Zaune kan kujera yana kallo a Al_jazeera, kan kujerar da ke gabansa kayan marmari ne reras waÉ—anda suka sha haÉ—aÉ—É—en yanka me É—aukar idanu. Se kuma juice shi ma da ke ajje, wanda har ya tsiyaya shi a cikin tambulan yana É—an sipping lokaci zuwa lokaci. Kai tsaye shigewa yayi kawai ya nemi waje ya zauna yana kallan T.Vn shi ma, daidai kuma lokacin da suka gama labaran. ÆŠaukar remote Daddy ya yi ya kashe T.Vn sannan ya juya ya kalli Bad Man yace

"Haka ya kamata É—an musulmi ya shigo É—aki?" Daddy ta faÉ—a yana kallansa. ÆŠan yamutse fuska ya yi sannan ya zamo daga kan kujerar da yake kai yace

"Sorry Dad.. Assalamu alaik.." sosai muryarsa ta yi daÉ—i sanda ya furta sallamar kamar wani balarabe. Daddy ya yi murmushi yana faÉ—in

"Ko kai fa..Wa alaika assalam." Gaisawa suka yi sannan Daddy yace

"Yaushe za ka fara aiki? Ko se ka huta?"

"Yes Dad.." ya faÉ—a kamar me jiran tambayar Daddyn da ma.

"Ba lokaci me tsayi dai za ka É—auka ba.." Daddy ya faÉ—a.

"But.. zan ɗan soma ziyatar en uwa da abokan arziƙi, idan na gama se na fara aikin.." Kallansa Abba ya yi jin abin da ya faɗa ɗin. Se da ya girgiza kai yana murmushi kafin yace

"Kamar gaske.. kai É—in..?" Shi ma murmushin ya yi kamar ba shi ba amma be ce komai ba har zuwa sanda Daddy ya sake faÉ—in
Chapter 17 · 0% Book details