← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 37

Sashe 31

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh.. gashi nan. Idan ki ka kai se ki taho ki zo ki wuce makaranta tunda dai ke ba ki sanar da ba za ki je ba. Dan haka se ki barsu su su je aiken Umman Fatiman. Allah ya tsare.." Ammi ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙawa Didin ledar hannunta.

"Ameen ya rabbi Ammi.." suka amsa a tare, sannan suka fito zuwa compound. Drivernsu Lulu ne ya ɗauke su kai tsaye zuwa gidan da Ammi ta aikesu. Babu laifi sun ɗauki mintuna masu ɗan dama a gidan, saboda da farko ma da suka je matar bata nan, se da suka jirata ta dawo suka bata saƙon, sannan suka yi mata sallama suka fito.

"Didi toh ki zo kawai mu tafi tare mana. Gobe se mu je makarantar duka.." girgiza kai Didi ta yi tace

"A'ah ni kam. Na san Gwani ze shigo yau ɗin nan, kuma ban faɗa masa ba.." Taɓe baki Lulu ta yi sannan tace

"Ai shi kenan.."

"Toh se kun dawo. Amma fa kar ku saki jiki magribh ta yi muku a waje.."

"In Sha Allah Didi.." suka amsa a tare. Har ta fara tafiya se kuma ta juyo tace

"Toh Baban na jiranku, ko me za ku jira anan?"

"Ahh haba Didi ki hau ya maidaki gida mana. Ta baya zamu ɓilla ne, akwai hanya me sauƙi, anan za mu samu mota ta kaimu unguwar.."

"A'ah ni dai na samu abin hawa kawai.." Didi ta faÉ—a.

"Ba komai fa Didi.."

"Shi kenan toh. Allah ya tsare.. Se kun dawo"

"Ameen.." nan ma suka amsa a tare. Motar Didi ta shige yayin da su kuma suka yi baya kamar yanda suka faɗawa Didin. Tafiya kaɗan ce kuwa ta kaisu titin. Babu daɗewa kuwa suka sami abin hawa suka hau. Da yake gidan na en uwansu Fatima ne ya sanya babu laifi sun ɗan jimawa matar. Se dai kafin gabatowar magribh suka suka soma shirin tafiya. Babu yanda ba ta yi da su a kan su zauna ba su ka ce an ce ka da su kai magribh. Babu yadda ta iya haka suka mata sallama suka tafi. Suna tafiya suna hira abinsu har zuwa sanda suka ƙaraso titi.

"Laaa pls Masoyiya zo mu je yau dai na siyi wannan popcorn ɗin. An daɗe ana tallarsa amma ban taɓa ɗanɗana irinsa ba duk sona da popcorn." Lulu ta faɗa tana kallan wani haɗaɗɗen wajen saida gugguru wanda ke kusa da wani hamshaƙin restaurant.

"Ai kin ji kuma kwaÉ—ayi. Ni wallahi ma yunwa nake ji. Ki bari kawai mu tafi gida.."

"Amma er uwakkun nan tace ki zauna ki ci ki ka ƙi ci?" Taɓe baki Fatima ta yi kafin tace

"Abincin na su ne be min ba." Dariya Lulu ta sheƙe da ita tace

"Wallahi na bar abin ne kawai a raina saboda er uwakku ce. Ashe ke ma da kanki haka za ki ce. Kai jama'a!" Ta ƙare tana saka hannu a baki ta kare tana cigaba da dariyarta.

"Kya ji dai da shi.." Fatima ta faÉ—a tana yin gaba.

"Aou wai nufinki ba za a siya ba?" Lulu ta faɗa tana riƙo hannunta.

"Masoyiya wallahi na gaji. Don Allah ki taho mu tafi.."

"Kin ga ki ce dai yunwa kawai ki ke ji. Ga restaurant nan ki zo mu shiga na san za a samu wainar shinkafa, ki yi kodimonki da ita kin ga kowa an yi abin da yake so kenan.." Se da ta ambaci wainar shinkafar kuma sannan ta yi murmushi, dan kasancewarta me son wainar shinkafa sosai. Se suka taka zuwa wajen saida popcorn ɗin. Se da ta siya sannan suka shiga restaurant ɗin da ya gaji da haɗuwa. Abin da ya kawo su kawai shi suka yi. Aikuwa cikin sa'a suka samu wainar shinkafar. Ita dai Lulu da yake ba yunwa take ji ba, kuma wainar shinkafa ba ta wani daɗata da ƙasa ba ya sanya ba ta ci komai ba, se kawai ta jira Fatiman ta ci abincin.

"Masoyiya wallahi ko ba yunwa nake ji ba na ga abincin nan se na ci.. Chaaɓɓ kin ji daɗi kuwa?" Ta faɗa tana cigaba da cin abincinta.

"Ke mu dai ki yi sauri wallahi. Nima na gaji.."

"Ehh tunda kin samu abin da ki ke so ba?" Ta faÉ—a tana watsa mata harara.

"Oho dai.. Ai kema kin samu.." Se da ta ci yanda take so sannan ta kora da lemo, kana suka miƙe a tare dan barin wajen. A daidai sanda suka gama fitowa daga inda ya kasance nan ne mutane ke zaune suna cin abinci da sauransu, a daidai lokacin da Lulu ke kallan Fatima suna magana, se kawai ji ta yi kamar ta bugi wani abu, kafin ta gama tantance mene ne se ji ta yi an zagayeta da hannaye guda biyu. A daidai kuma wannan lokacin ne sautin ɗaukar hoto ya daki dodon kunnena "Ƙyaras.." daga haka Hero ya saki Lulu ba tare da ya bari ta kalli fuskarsa ko shi ya kalleta ba ya yi ciki da saurin da cikin sakannin da ba su wuce a ƙirgasu ba ya ɓacewa ganina. Cikin tsananin ɓacin rai, haushi, takaici gami da baƙin ciki ta ɗaga hannunta da niyyar tunkuɗe wanda ta ke tunanin rashin hankali ne ya saka ya zo wucewa ze mata irin wannan bangazar, se dai cikin sakanni ta ji an riƙeta alamar ba da gangan aka yi hakan ba. Kafin kuma ta ɗauki wani mataki se ji ta yi an saketa. Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar gangar da ake kaɗawa. Fararan manyan idanunta sun cika fall da ƙwallar baƙin ciki, se dai har wani huci take fitarwa saboda ɓacin rai. A fusace ta juya dan ɗaukar matakin da ya dace tun kafin ma hankalin wasu ya dawo kansu, ballantana a san abin da wani dabban ya yi mata ba. Daidai lokacin da Bad Man da ke sanye cikin wasu tsadaddadun kaya en ubansu ya kalli Hero sanda ya wuce da gudu kamar wanda aka kaɗo, ganin be fahimci dalilinsa na yin hakan ba, ya sanya shi juyawa fuskarsa kamar ko yaushe babu walwala dan dubawa ko wani abin ne ya faru? Se dai yana juyawar ita kuma fusatattun idanunta da ke cike da fushi suka sauka a kansa, kasancewar shi kaɗai ne ta gani a wajen wanda ya ke kusa da su, se waɗanda ke nesa da su. Ta kuma riga ta san wanda ya mata wannan haukan be ci a ce sun samu tazara da yawa ba, dan haka ganin Bad Man kusa da su ya sanyata sake tabbatar da cewa lallai shi ne ɗan iskan da ke ƙoƙarin yi mata akuyanci. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba ta ɗaga hannunta ta sauke masa lafiyayyuyan yatsun hannunta guda biyar reras a kan farar hamshaƙiyar fuskarsa..

https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_20

___"Ɗan iska kawai.." ta faɗa fuskarta ɗauke da zallar ɓacin rai, har kuma lokacin ƙwallar da ta taru a idanunta na nan. Kyawawan ianunsa da basu da yalwar girma ya sake ƙanƙancewa yana kallanta cikin yanayin da na kasa fahimtar wane iri ne. Cikin lokaci ƙanƙani ya ɗaga hannunsa a nutse ya shafa kyakkyawar fuskarsa. Kafin ya kai ga yin wani yunƙuri saboda yanda man kansa ya tsotse da wannan al'amarin, so yake ma ya gama tabbatar da da gasken abin da ya faru ya faru. Wace ce ita? Fatima ta yi saurin riƙo Lulu tana faɗin

"Zo mu tafi ke.." kafin Lulun tace komai Fatima ta saka hannu ta jata da ƙarfi suka wuce. Daidai lokacin da Hero ya ƙaraso dab da Bad Man yace a hankali

"Ka da ka yi wani yunƙuri. Za ka jan yo hankalin mutane.." Hannunsa ya saka ya tunkuɗe Hero, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, har wani huci yake fitarwa, angry face ɗinsa ta sake haɗewa waje ɗaya. Saboda yadda ya tura Hero ɗin da ƙarfin gaske ya sanya shi yin gefe kamar ze kifa, dan Bad Man ɗin ba daga nan ba wajen ƙaƙƙarfan jiki. Da wani irin sauri ya sake yin gaba yana faɗin

"Plss Bad. Ka da ka yi haka. Babu wanda ya gani, idan ka yi wani yunƙuri kowa ze san abin da ya faru.."

"Heyy leave me. I said leave me.. Me ye ka ke faÉ—a ne? Waye kai da kake tunanin za ka faÉ—a min magana na ji? Na ce who are you?"

"Ni ba kowa bane Bad. But abin da kake ƙoƙarin yi ne nake ganin kamar be kyautu ba, ace kamar Areef Matawalle da kansa ya tsaya yana sa'insa da er gidan talakawa.."

"Er gidan talakawa.. Er gidan ko uban waye ba damuwata bane.."

"Don Allah ka zo mu je mu zauna mu yi magana. Ba dan halina ba don Allah.." Hero ya faɗa kamar mutumin arziƙi. Da ƙyar ya samu Bad Man ɗin ya yadda suka koma suka zauna bayan ya tabbatar masa da cewa ko ɓurɓushin en matan be gani ba.

"Ka santa ne?" Bad ya tambaya har lokacin a kufule.

"Noo ban santa ba. But abin da ta maka ze sanya ni nemota in É—auki fansa.."

"Fansa? Har na yi wannan lalacewar?" Bad ya katse shi da faÉ—in hakan. Kafin ya É—ora da

"Ka nemo min wace ce ita. Ina ne gidan ubanta.. ban san dalilinta na marina ba but zan nuna mata true colour É—ina.."

"Amma Bad har yanzu na kasa gane dalilinta na marinka fa? Anya kuwa lafiyarta ƙalau?" Ɗan runtse idanunsa Bad ya yi yana jin kamar lokacin ne en yatsunta suka sauka a kan fuskarsa. Da sauri ya buɗe idanunsa ya saukesu a kan Hero ɗin daidai lokacin da yake shafa fuskarsa yana kuma hasaso irin wulaƙantaccen marin da ze yi wa yarinyar da tafi kama da mara hankali. Jin be ce komai ba ya sanya Hero sake faɗin

"Anya kuwa lafiyarta ƙalau? Ko kuma tana ɗaya daga cikin maƙiyanka, shi ya sa ta zaɓi tozartaka a cikin jama'a. Da ka biye mata kuma ka ga kai ta janyowa zubewar mutunci ba kowa ba.."

"Hero!!" Ya faÉ—a a zafafe yana watsa matsa rikitattun idanunsa. Babu shiri ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya

"Sorry Bad.. Yanzu dai me kake so a yi?"
Chapter 31 · 0% Book details