← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 37

Sashe 29

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uhmm, wacce er aiki kuma? Dukka ayyukan gidan ma nawa suke? Ni da yaron nan ze taimaka ya yi aure ai ka ga na samu er tayin hira nima.." Ummeey ta ƙare maganar tana juyo da kujerar da take kai ta koma tana kallansu Abeey. Kallan Gwani da ke zaune gefensa yana karatun wani littafin addini Abeey ya yi yace

"Toh kai ka ji.." Se a lokacin ya ɗaga kansa ya kalli Abeeyn, ya ɗan yi yaƙe sannan yace

"Abeey wai ni?"

"Ja'iri.. da wa nake nufi idan ba kai ba?" Ummeey ta faÉ—a tana kallansa.

"Ummeey idan aiki ya miki yawa ni me taimaka miki ne fa.." ya faÉ—a yana kallan Ummeeyn.

"Ni babu wani aiki da ya min yawa. Kawai dai ina buƙatar er tayin hira ne.."

"Tohm.." ya faÉ—a kawai. Murmushi Ummeeyn ta yi tana maida dubanta kan Abeey tace

"Ya jikin?"

"Jiki ya warware Alhamdulillah.. Anjima ma ina so na leƙa wajen ɗaliban can, saboda na kwana biyu ban yi musu karatu ba. Affan kuma kin ga akwai inda yake zuwa, ba ze yiwu ace kodayaushe kuma ba shi da lokacin hutu ba.."

"Abeey lokacin hutu kuma? Babu damuwa fa Abeey, ka cigaba da zamanka har zuwa lokacin da za ka warware gaba É—aya se ka koma karatun." Ya É—an dakata sannan ya É—ora da

"Zan je na musu karatun.."

"Allah ya yi maka albarka Affan. Allah ya albarkaci gaba ɗaya rayuwarka. Ya nuna min wata rana da ni da Ummeeynka muka daɗe muna jiranta kafin na bar duniyar nan. Idan hakan ta faru shi kenan ni kuma burina ya cika." Ya riga ya san maganar da Abeeyn ke yi a kan aure ce, dan ba yau ne karo na farko da ya saba yin makamanciyar wannan maganar ba. Se dai da yake shi ɗin ba ma'abocin magana bane ya sa be taɓa tambayar Abeeyn ba, se shi da kansa da ya fahimci aure Abeeyn ke nufi.

"Ameen Ameen.." Ummeey ta amsa itama tana murmushi.

... "Mami lafiya kuwa na ga kina ta murmushi?" Jadwa da fitowarta kenan daga cikin É—aki ta faÉ—a tana kallan Mamin.

"Ke zo ki zauna ki ji min abin da ya faru." Mami ta faɗa tana riƙo hannun Jadwa suka zauna a kan kujera. Dariya Jadwa ta yi kafin tace

"Ke dai Mami duk sanda ki ka je gidan Abba se kin dawo da labari.."

"Ke dallah can ƙaruwarki ce yanzun ba tawa ba.."

"Ƙaruwata kuma Mami? Me ya faru?" Jadwa ta faɗa tana gyara zama.

"Ashe Kaseem ba Lulu yake so ba."

"Kamar yaya Mami? Toh wa yake so?"

"Afrah.."

"What? Didi kuma? Ta ya ya?" Ajiyar zuciya Mami ta yi kamin tace

"Ke ba wannan ba. Na haƙura ne dama saboda Lulu yake so, amma tunda na san Didi yake so ba zan haƙura ba, zan yi yanda zan yi na sama miki shi. Ke ki ka fi buƙatar shi ba wannan yarinyar me baƙin hali irin na uwarta ba.."

"Mami.." Jadwa ta faÉ—a tana buÉ—e idanunta.

"Ke ban son iya shege. Ba kya son Kaseem É—in ne?"

"A'ah idan zan samu ina so mana.." Jadwan ta faÉ—a tana tura baki.

"Ja'ira.. Ahh toh.." Mami ta faÉ—a tana murmushi.

... Driving yake yi, babu abin da ke tashi cikin motar se sautin kiɗa me ɗan karen daɗi. Yana driving ɗin yana bin sautin waƙar cike da ƙwarewa. Hero da ke ɓangaren me zaman banza ma yana taya shi bin waƙar, se dai shi lokaci zuwa lokaci ya kan tsaya ya kalli wayarsa. Zuwa can wayarta sa ta shiga ruri daidai lokacin da Bad Man yace

"Wannan jahilin ringtone É—in fa?" Ya faÉ—a yana yamutse fuska lokaci É—aya kuma yana jijjiga kansa saboda bin sautin da ke tashi da yake yi.

"Kawai dai be yi maka. Right?"

"Ƙwarai.." Bad Man ya bashi amsa yana cigaba da driving ɗin.

"Hero!!" Shi ne abin da Ladi ta faÉ—a bayan Hero É—in ya É—aga wayar.

"Jakadiyar Mata.." Hero ya faÉ—a yana dariya.

"Shegen kaya, da alama yanzu haka kana wani hamshaƙin club ɗin ne koh?" Ta faɗa saboda yanda ta jiyo kiɗa na tashi sosai kamar a club. Se da ya yi dariya sannan yace

"Ko kaÉ—an fa.."

"Ah toh ai na san hali ne.." Dariyar ya sake yi sannan yace

"Yanzu dai ya ake ciki? Dan na san tunda na ga kiran nan na ki akwai wani abu.." Ajiyar zuciya Ladi ta sauke kafin tace

"Don Allah idan ba za ka damu ba ina son ganinka.."

"Toh fa. Ganina kuma?" Ya tambaya. Se da ta jinjina kai kamar yana gabanta sannan tace

"Ƙwarai kuwa don Allah. Taimakamin za ka yi ne a kan wata matsala da na san za ka iya magance min ita cikin ƙanƙanin lokaci.."

"Kina ina?"

"Ina gida." Ladi ta faÉ—a cikin farin ciki. Be ce komai ba ya katse wayar ya juya ya kalli Bad Man yace

"Pls Bad ajiye ni anan mana.." Kamar be ji shi ba ya cigaba da bin waƙarsa hankali kwance. Se kuma da aka ɗan wula sannan ya yi parking motarta sa. Hero ya sauka yana faɗin

"Zamu yi waya plss."

"Ohk.." ya amsa yana jan motar.

... "Na ji daɗin zuwanka Hero. Wannan na ɗaya daga cikin alfarma masu muhimmanci da aka taɓa yi min a rayuwata.." Ladi da ke sanye cikin ƙananan kaya babu ɗan kwali a kanta se tulin gashin doki da ke a kan nata ta faɗa tana kallan Hero. Murmushi ya yi yana gyara zamansa sannan yace

"Just tell me me ya faru? Kiran me ki ke min? Kin san dai ban fiye son harkar da babu ƙaruwa a cikinta ba.." ya faɗa yana gyara zaman hular kansa. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke kafin tace

"Ka da ka damu mutumina. Wannan harka ce ta ƙaruwa irin sosai ɗin nan. Aiki nake so ka min a kan wata yarinya, na san wannan ɗin ba baƙon abu ba ne a wajenka musamman idan za a biyaka."

"Uhmm Ladi kenan. Ka da kice min aiki kawai zan yi miki babu wata ƙaruwa a ciki? Manta da batun biyana kuɗi, idan dai har zan ƙaru a tafiyar toh ba na buƙatar ko sisinki. Ke dai kawai ki saka a ranki komai ki ke buƙata kin gama samu.."

"Shi ya sa na yi yanda zan yi na nemoka Hero.."

"Akwai wata yarinya, ina sonta. Se dai ina so ne na ɗan saita mata zama dan ta nuna min ita ɗin mutuniyar kirki ce. Toh wannan batun na mutuniyar kirki nake so ya fita a kanta. A idanun kowa ta tashi daga me wannan sunan. Ni kuma daga nan ka gama aikinka zan ƙarasa sauran.." wata dariya Hero ya fashe da ita kafin ya soma faɗin

"Idan dai har na fahimci abin da ki ke nufi.. so ki ke a lalata rayuwarta, ta kuma zo ta rasa mijin aure, ta rasa kallan mutuncin da mutane ke mata, ta yadda za ta rasa mafita se kawo kanta gare ki?"

"Dalilin da ya sa nake ƙaunar aiki da kai kenan mutumina. Akwai ka da kwanya." Ta faɗa tana nuna saitin kanta fuskarta ɗauke da murmushi. Ajiyar zuciya Hero ya sauke sannan yace

"Ka da ki damu, har ma abin da ba ki ce ba za a yi miki, tunda dai nima ƙaruwata ce.."

"Hero kai ɗin na musamman ne. Allah ya ƙara maka kwanya.."

"An daÉ—e ana faÉ—a min hakan. Ke dai kawai faÉ—a min sunanta. Er gidan waye? Ya ya kamanninta su ke? Idan ze samu ma a samar min hotonta. Kwatancen gidansu kuwa ba wahala ze min ba idan dai har na san sunan ubanta.."

A yi manage da wannan pls, ba na jin daÉ—i ne. Da bama zan yi ba, kawai dae dan kar na barku a gantale ne shi ya sa na yi wannan É—in.

https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_19

___"Yanzu abin da za a yi zan haÉ—aka da yarinyar da ta santa sosai. Ta san gidansu, ta san sunan uban yarinyar, za ta kuma iya samo mana hotonta.." Jinjina kai Hero ya yi kamin yace

"Hakan ma ya yi.."

... Sake buÉ—e idanunta dai ta yi sosai dan sake tabbatar da da gasken Areef É—in ne ya sauke Mommah a motarsa. Juyawa ta yi da sauri tana faÉ—in

"Mom... Mom kina ina ne wai?" Ta yi maganar ranta a ɓace.

"Gani nan. Wannan uban kira haka irin na tashin hankali.."

"Toh ai wannan ya fi tashin hankali, kin san abin da na gani yanzu kuwa?" Ta faÉ—a tana neman waje ta zauna har lokacin fuskarta a haÉ—e.

"A'ah se kin faÉ—a. Me ki ka gani?" Mom ta yi saurin faÉ—a tana neman waje ta zauna.

"Areef na gani fa ya sauke waccan matar a motarsa.." Cikin rashin fahimta Mom tace

"Wace matar kenan?"

"Wacce mata ce a cikin gidan nan bayan Sa'a..?" Aunt Makiyy ta faÉ—a tana kallan Mom É—in.

"Bari mana Makiyy, ki bari mana don Allah.."

"Ke wallahi ba wasa nake ba. Ni abin ne ya ɗaure min kai wallahi, kina ina har haka ke faruwa cikin gidan nan? Wace irin sakewa ki ka yi har hakan ke faruwa? Drivernta ya zama ko kuwa me ne?" Jinjina kai Mom ta shiga yi cike da ɓacin rai. Shi Areef ɗin ne ba ɗan goyo ba, ba abun tace za ta masa faɗa ba yanzun nan ya tubure mata ya yi fushi da ita, abin da ba ta so kenan. Se dai koma dai mene ne dole ne ta masa magana tun kafin Mommah ɗin ta sake zaƙewa, duk da dai shi ke biye mata.

"Zan san abin yi.." Mom ta faɗa tana soma tafiya. Da sauri Aunt Makiyy ta miƙe tana faɗin

"Wane za ki san abin yi? Ai yanzu nake so mu je mu ɗauki mataki, babu wani za a san abin yi.." Komawa Mom ta yi ta zauna ta yi murmushin yaƙe kafin tace

"Ke daÉ—ina da ke gaggawa. Halin Areef ne ba ki sani ba? Yanzu muna cewa za mu masa faÉ—a ko kuma mu ci mata mutunci fushin kanmu ze koma. Saboda haka ki bari kamar yanda na faÉ—a É—in zan san abin yi.."
Chapter 29 · 0% Book details