← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 37

Sashe 25

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba za a gutsiri naman jikina ba. Amma kawai na ɗauki ƙafa na je na duba babansu bayan wulaƙantanin da ya yi ɗazu? Ko ba ma wannan ba, duk tarin wulaƙancin da yake min a cikin makarantar nan ni kuma kamar wadda ba ta da zuciya a ƙirjinta se kawai na je duba wani na shi. Me ye haɗina da shi? Wallahi Allah ya kiyaye. Ni fa Didi in fito miki a mutum wallahi saboda Abba da Ammi nake zaune a makarantar nan, ba dan haka ba da ina da dama da tuni na chanjawa kaina makaranta kuma duk a dalilin wannan mutumin" Ta ƙare maganar tana yamutsa fuskarta da itama take a haɗe alamar zancen da take faɗa tun daga ƙasan zuciyarta suke fitowa kuma tana jin zafinsu. Kallanta kawai Didi take yi tunda ta soma maganar har ta kai ƙarshe cike da mamakin Lulun..

https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_16

___"Ohk good.." Didi ta faÉ—a tana jinjina kai lokaci É—aya tana juyawa ta bar Lulun a tsaye. Binta Lulu ta yi da kallo har ta koma inda en ajin nasu suke. Babu daÉ—ewa suka fice daga makarantar da jagorancin malamansu mata da maza. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kama hannun Little suka fara tafiya.

"Masoyiya don Allah ki taho mu je." Fatima Kabeer ta faÉ—a tana kallan Lulun. Kallanta itama Lulun ta yi kana tace bayan ta É—auke kai

"Aou ai na É—auka ke ma kin bisu ne." Girgiza kai Fatima ta yi sannan tace

"A'ah fa, ke na zo kira." Da sauri tace

"Kin ga idan za ki tafi kawai ki tafi, wallahi ba zan je ba."

"Shi kenan.. mu tafi kawai." Se suka cigaba da tafiya. Ba su yi nisa ba Lulu ta kalli Fatiman tace

"Ke wai kin fasa zuwa ne?"

"Ban sani ba!" Ta faÉ—a tana galla mata harara. Dariya Lulu ta yi kamin tace

"Sorry Masoyiya."

"Kya ji da shi." Fatima ta faÉ—a tana sake É—auke kai.

"Wai ina Didi?" Little ya faÉ—a tana É—aga kansa ya kalli Lulu. Cikin er basarwa tace

"Sun je gaisuwa." Shi Little É—in ma be fahimci abin da take nufi ba, se Fatima da ta buÉ—e baki tace tana kallanta

"Kee Masoyiya ba fa mutuwa ya yi ba."

"Aou toh.." ta faÉ—a tana buÉ—e idanu itama kamar da gasken ba ta san ba mutuwa ya yi ba. Se ta É—ora da

"Ai da na ga an tarkata kawunanku ne na yi tunanin mutuwa ya yi. Lallae!" Ta ƙare tana ɗan taɓe baki.

"Er rainin hankali, da ban san halinki ba da kin gama dani." Se kuma suka yi dariya gaba ɗayansu. Har gida se da Fatima ta kai Lulu sunata hira. A parlour suka taradda Ammi tana karatun Qur'an. Jin sallamarsu ya sanyata kai ƙarshen ayar da take sannan ta rufe, ta ajje shi a gefe, kana ta amsa sallamarta su.

"A'ah Fatima!" Ammi ta faÉ—a tana murmushi.

"Na'am Ammi, ina yini?" Fatima ta faÉ—a sanda ta ke zama.

"Lafiya ƙalau, ya karatu?"

"Ammi kin san ina Didi ta ke?" Little ya faÉ—a yana buÉ—e idanunsa, bayan ya haye kan kujerar da Ammin ke kai. Girgiza kai Ammi ta yi tana É—an murmushi dan ta san shirmensa ne kawai

"Gaisuwa.." ya faÉ—a yana jinjina kai. Se kuma ta maida dubanta kan su Lulu da ke zaune tace

"Gaisuwa kuma? Waye ya rasu?"

"A'ah fa Ammi, babu wanda ya rasu. Babansu Gwani Affan ne ba lafiya shi ne aka je duba shi." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan tace

"Toh Allah ya ƙara afuwa."

"Ameen." Fatiman dai ta amsa. Kallan Little Lulu ta yi tace

"Little kai min jakar nan É—aki." Kafin ya kai ga cewa komai Ammi tace

"Toh me yasa ku ba ku je ba?" Da sauri Lulu ta yi caraf tace

"Ammi kaina ke ciwo sosai. Shi yasa ma Ya mu'allim yace a rakoni gida."

"Toh Subhanallahi Allah ya sawwaƙe. Sannu Fatima an gode." Murmushi kawai Fatima ta yi tana ɗan satar kallan Lulu ta maka mata harara. Ita kuwa ta ɗauke kai kamar ba ta san da ita take ba.

.. Se dab da maghrib Didi ta shigo gidan. Ammi da Lulu na parlourn a zaune. Lulu na koyawa Little home_work. Ƙarasawa ta yi ta zauna a kan kujera tana faɗin

"Ammi na gaji."

"Sannunki, ai kin yi ƙoƙari, Allah ya ba da lada. Ita waccan malalaciyar da ciwon kai ya hana zuwa yanzu ai kin ga tana nan zaune ke kin samu lada."

"Ciwon kai kuma?" Didi ta faÉ—a tana kallan Lulu. Da sauri Lulu ta soma kaÉ—a mata kai tana sake maida fuskarta kalar tausayi a kan ta tausaya mata ka da ta faÉ—awa Ammi gaskiya. Se kuwa ta É—auke kai daidai lokacin da Ammi ke faÉ—in

"Ba ki ganta tana wani mashau_mashau ba kamar wadda Asibitin ke kanta gaba É—aya."

"Kai Ammi!." Lulu ta faÉ—a tana tura baki.

"Tashi maza ki yi sallah, ki zo ki sha magani. Idan ba haka ba ranki ya ɓaci. Bana son irin ciwon Didi na ƙin shan magani." Ammi ta faɗa. Se da Didi ta saci kallan Lulu sannan ta soma faɗin

"Ammi wallahi ba wani ciwon kai." Ta faɗa dan yau ɗin kamar yanda ta yi alƙawari se ta faɗawa Ammin abin da ta sake yi tunda ba ta jin magana.

"Ban gane ba?" Ammi ta faÉ—a tana kallan Didi.

"Cewa ta yi wai ba za ta je ta duba shi ba, tunda ba su da haɗi. Wai dan ɗazun ya koreta daga aji saboda ba ta da littafi, kuma bayan tana sane taƙi tafiya da littafin." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana maida dubanta kan Lulu da ta yi saurin ɗauke kai tun bayan da didi ta fara magana.

"Anya kuwa ba wasu ƙawayen ke hure mata kunne ba?" Ammi ta faɗa tana kallan Didi.

"Ammi ba wasu ƙawaye. Fatima ce fa kaɗai ƙawarta ta."

"Toh ita Fatiman me ya hanata zuwa?"

"Ita fa Fatiman har ta taho za mu tafi, da ta ga Lulun ba za ta je ba, shi ne ta fasa zuwa saboda Lulun ta nuna ta ji haushi."

"Shirmen banza kenan.." Ammi ta faɗa ranta a ɓace. Se ta maida dubanta kan Lulu tace

"Zo nan!" Ammi ta faɗa har lokacin tana kallanta. Se a lokacin ta ɗaga kanta ta kalli Ammin, duk rashin gaskiya ya gama bayyana a kan fuskarta. A hankali ta taso ta soma takawa zuwa inda Ammin take, a sukwane ta zame ta zauna a ƙasan ƙafar Ammin kanta a ƙasa bayan ta faki idon Ammin ta jefawa Didi harara, itama ta maida mata tana ɗauke kai. Hannu Ammi ta kai ta kamo kunnen Lulu ta ja shi, har se da Lulun ta ɗan saki ƙara tana kai hannunta kan hannun Ammin.

"Wato ba kya jin magana koh? Duk irin faɗan da Abbanku ya yi miki ba ki ji ba? Dan kin ga ban saka baki ba a lokacin, wallahi da kin bari na saka baki dukanki zan yi ko kuma na kaiki wajen malamin ya zane min ke da kanshi. Wai me kike taƙama da shi ne Lulu? Me kike ƙoƙarin ɗauka ki azawa kanki? Ke babu wanda ya isa ya sarrafaki kenan bayan iyayenki ko me kike nufi? Shi ba malaminki bane? Be isa ya sakaki ko ya hanaki ba? Kin yi laifi ya hukuntaki ta fatar baki kawai amma a wajenki laifi ya yi. So kike kenan duk abin da kika yi ya zuba miki ido kawai, saboda ke ce malamin shi kuma ɗalibin? Ashe ma tsoronki yake ji. Toh ki buɗe kunnenki da kyau, wallahi daga yau aka sake ce min kin yi wa wani rashin daraja, ba ma shi kaɗai ba zamu gauraya da ke. Kin ji dai na faɗa miki." Ammi ta ƙare maganar tana sakin kunnen nata. Se ta kai hannu ta riƙo kunnen da har ya soma mata zafi, haka kuma ya yi ja kamar wanda aka yi wa wani abun. Se ta ɗaga kai a hankali tace

"Ki yi haƙuri Ammi." Ɗauke kai Ammi ta yi kamar ba ta ji ba. Ta san halin Ammi ba kamar Abba take ba, ba ta iya fushi ba, idan tace za ta yi fushi da ke har se kin wahala, dan haka gwara tun wuri ta nemi sulhu, hakan ne ya sanyata tashi gaba ɗayanta ta hau kan kujerar, sannan ta ɗora kanta a kan cinyar Ammin tace

"Don Allah Ammi ki yi haƙuri, ba zan ƙara ba." Ta ƙare maganar hawaye na zuba a kan fuskarta. Se da Ammi ta ji saukar zubar hawayen Lulun a jikinta sannan ta dafa kanta tace a hankali

"Ka da ki ƙara." Da sauri ta jinjina kai tana ɗagowa sanda farar fuskarta ta gama yin ja sosai.

.. Har suka koma É—aki ba wadda tace da er uwarta ko uffan, kowacce se wani É—auke kai take ita a lallai dole ita aka yi wa laifi. Se dai duk so suke a cikin nasu É—aya ta soma yi wa É—aya magana se a shirya. A haka dai har suka yi magribh ba su kula junansu ba, kowacce na cigaba da basarwa.

... "Amm idan ba damuwa kafin ka tafi ko za ka mun magana da Abba mana." Kaseem ya faÉ—a yana kallan drivernsu Lulu wanda wani lokacin shi ke kai Abba ya kuma É—auko shi daga duk inda ya je.

"Eyyah, ai ba ya cikin gidan ma gaskiya. Be dawo ba tukunna."

"Toh godiya nake. Bari na jira shi." Kaseem ya faÉ—a yana gyara tsayuwarsa a jikin motarsa. Se da drivern ya zo ze wuce se kuma ya sake katse shi da faÉ—in

"Yi haƙuri don Allah, ko za ka ɗan sanar wa da gidan Kaseem ne, da yake na zo mun yi magana da Abbansu so yau ɗin kuma dai zuwan na Afrah ne.." Murmushi Ado driver ya yi fahimtar abin da Kaseem ke nufi da ya yi.

"Toh babu damuwa.. bari na sanar da su." Daga haka ya juya ya koma cikin gidan. A bakin parlourn ya tsaya ya yi sallama. Ammi da ke zaune ta amsa tana faÉ—in

"A'ah ashe ba ka tafi ba."
Chapter 25 · 0% Book details