← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 37

Sashe 30

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shi kenan ai. Koma dai me ya faru ki fara tuhumar kanki.." Aunt ɗin ta faɗa tana miƙewa dan ita kam ta fusata ba ƙarya.

... Cikin wata doguwar riga me kyau ta shirya, rigar da ta matuƙar amsarta. Ta ɗauki ƙaramin mayafin rigar ta yi rolling, kasancewar rigar me ɗan faɗi ce ya sanya ta saketa sosai, ta kuma matuƙar yi mata kyau.

"Ka ga fa en matan Ammi.." Lulu ta faɗa tana dariya ƙasa_ƙasa.

"Allah kuwa ba na so.." Didi ta faɗa tana jefawa Lulun harara. Wata dariyar Lulu ta sake sheƙewa da ita sannan tace

"En mata ce mana tunda ki ka fara zance. Dan ma ban ce en matan Kaseem ba.." Juyawa Didi ta yi tana neman abin da za ta iya jifar Didin da shi. Lura da hakan da Lulu ta yi ya sanyata miƙewa da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya. Biyota Didin ta yi tana ta ciccin magani, ita kuwa Lulu tana zuwa ta faɗa jikin Ammi tana cigaba da dariya

"Tsokanar ce koh?" Ammi ta faÉ—a tana girgiza kai.

"Ammi dukanta ta yi koh?" Little da ke gefen Ammi ya faÉ—a yana kallan Lulu, se ta juya ta jefa masa harara daidai lokacin da Didi ta fito daga cikin É—akin

"Awwwn Masha Allah.. ka ga en matana" Ammi ta faɗa tana murmushi. Dariya Lulu ta fashe da ita yanzun har da ƙyaƙyatawa, tana cigaba da dariyar kuma tace

"Ammi nima fa abin da nace mata kenan take jin haushina. Toh ai gashi nan Ammin ta faɗa miki da kanta.." ta ƙare maganar tana kallan Didi. Tura baki Didi ta yi tana neman waje ta zauna.

"Ammi ki ma Lulu magana Allah.."

"Ai dama na san tsokanarta ki ke yi ja'ira. Yoh ni ko yau Allah ya kawo miki miji ai aurar da ke zan yi na huta.."

"Chaaɓɓ.." Lulu ta faɗa tana jinjina kai lokaci ɗaya tana dena dariyar. Se a lokacin sannan Didi ta yi dariya har da yi mata gwalo.

"Tashi ki je Afrah an bar ɗan mutane na jira. Ki tsaya ki nutsu Afrah.. kin san dai Abbanki na dab da yanke hukunci, dan ina me tabbatar miki da cewar idan dai har ki ka amince toh a cikin satin nan za a iya bashi damar turo magabatansa." Ɗan numfashi Didi ta ja ba tare da tace komai ba se miƙewa da ta yi ta ja hannun Little suka fice daga ɗakin jikinta a sanyaye. Sallamar da aka yi a bakin ƙofa ne ya sanya su amsawa dukansu. Da sauri Lulu ta miƙe tana faɗin

"Oyoyo Masoyiya.." ta faÉ—a tana rungumeta.

"Yawwah.." Fatima ta faɗa tana ƙarasowa cikin parlourn. Gaisawa suka yi da Ammi. Da yake akwai sabo a tsakaninsu ya sa suka ɗan taɓa hira, daga baya Ammin ta miƙe. Da sauri Fatima tace

"Ammi wajenki na zo.." komawa Ammi ta yi ta zauna tana faÉ—in

"Toh ina jin ki.."

"Dama gobe Umma ce za ta aike ni, shi ne tace in miki magana se Afaaf ta raka ni.."

"Gobe..?" Ammi ta tambaya.

"Ehh Ammi.." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin tace

"Amma gobe ai akwai makaranta, me ze hana ku bari se Alhamis ko Juma'a?"

"Ammi ai saƙo ne za a karɓo shi ya sa." Shiru Ammi ta yi na tsawon sakanni sannan tace

"Toh shi kenan Allah ya nuna mana.."

"Ameen Ammi an gode.."

"Kun sanarwa da Ya Sayyadin naku?" Kafin Fatima tace komai Lulu ta yi caraf tace

"Ehh Ammi fa mun faÉ—a masa.."

"Toh shi kenan, babu damuwa.."

"Mun gode Ammi.." daga haka Ammin ta miƙe ta bar parlourn. Neman waje Lulu ta yi ta zauna, Fatima ta jefa mata harara tace

"Ta ya ya ma za ki ce mun faɗa masa? Bayan na yi na yi da ke mu je mu faɗa masa kin ƙi? Da kin bari nace ba mu faɗa ba ai na san Ammi za ta tura Didi ta faɗa masa.." Tsaki Lulu ta ja kafin tace

"Ke rabu da shi dallah. Sanin kanki ne dai ba ya karɓar uzuri idan ba daga wajen me yin uzurin ba. Da ki ka je faɗa masa ba har da ni ki ka ce ba? Amma me yace? Wai in zo da kaina. Toh ni a faɗan da Ammi da Abba suka min cewa kawai suka yi na dena rashin ji. Ah toh. Ban faɗa ba idan na dawo ya yankani.."

"Amma ba kya tsoron ya sanarwa da Abba?" Fatima ta faÉ—a tana kallan Lulu.

"Ke ba ze faÉ—a ba dallah. Kema me ye na damun kanki ne wai?"

"Masoyiya ka da fa ya dake ki.."

"Duka kuma? Aou dama yana duka ne?" Girgiza kai Fatima ta shiga yi kamin tace

"A'ah ba ya yi amma dai kar ya sake miki abin da ya saba yi ki ce ya dizga ki.."

"Masoyiya wai me ye haɗinku da wannan mutumin ne na ga kina ta wani kare shi? A'ah kin ga faɗa min wallahi ba wanda zan faɗawa.." Lulu ta ƙarashe maganar a hankali tana kuma gyara zama. Duka Fatima ta kai mata a fusace tana faɗin

"Ban sani ba.." Dariya Lulu ta yi tana faÉ—in

"Ah toh.. ai yanzu dai kya ƙyale ni na sarara.."

"Allah ya shirya min ke Masoyiya.."

"Ameen in da gaske ki ke.." Lulu ta faÉ—a tana yamutse fuska.

"Wai kin san mene ne?" Fatima ta faÉ—a tana gyara zamanta.

"A'ah se kin faÉ—a.."

"Abida ce ta zo gidanmu É—azun.."

"Abida kuma?" Lulu ta tambaya da sauri tana kallan Fatiman. Se ta jinjina kai, kafin ta kai ga sake cewa komai Lulu ta sake faÉ—in

"Karki faɗa min da gaske ne? Me ta zo tace miki? Yi maza ki faɗa min plss." Taɓe baki Fatima ta yi kafin tace

"Ke ba fa komai. Ba abin da tace min, kawai dai gaisawa muka yi, ban da nan ba komai.."

"Ohk toh idan ta kuma zuwa ki faÉ—a min plss.."

"Tsaya.. wai me ya faru ne haka na ga duk kin tsorata? Wani abu?" Girgiza kai Lulu ta yi tana faÉ—in

"Nop babu wani abu fa.." Daga haka suka cigaba da hira. Zuwa can Fatiman ta tafi bayan ta je ta yiwa Ammi sallama. Ba ta daɗe da fita ba Didi ta shigo cikin ɗakin hannun Little ɗauke da wata babbar leda da kaya cike a ciki. Da sauri Lulu ta miƙe tana faɗin

"Zo mu gani, me aka baka?" Baya ya yi da ita da sauri yana faÉ—in

"A'ah na wa ne fa.." Tsaki Lulu ta ja kafin tace

"Kai ba ci maka zan yi ba, kawai gani zan yi.." Se a lokacin sannan ya miƙa mata ta kama hannunsa suka nemi waje suka zauna. Didi ma neman waje ta yi ta zauna kawai. Buɗe ledar Lulu ta yi ta shiga fito da abubuwan da ke cikinta. Tarin chocolates ne kala kala kamar za su yi magana masu daɗi, aji da kuma tsada.

"Awwwn Didina ta girma wallahi. Duk wannan namu ne?" Ta yi maganar tana kallan Didi. Murmushi kawai Didi ta yi tana maida dubanta kan Little da ke faÉ—in

"Hmm Uhmm Jamm! Allah kuwa na wa ne.." Kumatunsa Lulu ta kama ta ja tana faÉ—in

"Duka wannan za ka shanye wai?"

"Ehh mana. Ai Yah Kaseem É—in ne yace na wa ne duka tunda Didi ba ta so.."

"Iyee!! Yah Kaseem! Wa ya ɗora maka sunan a bakinka haka raɗau?" Lulu ta faɗa tana riƙe haɓa.

"Didi ce.." ya faɗa yana karɓar ledar daga hannun Lulu. Se ta maida dubanta kan Didi daidai lokacin da ya nufi ɗakin Ammi hannunsa ɗauke da ledar.

"Didi.."

"Kee.." Didi ta faÉ—a tana murguÉ—a baki.

"Ba shakka.. kin san me? Faɗa min gaskiya Didina.." Lulu ta ƙare maganar tana dawowa kusa da Didi, sannan ta ɗora da faɗin

"Ki na sonshi koh?" Shiru Didi ta yi tana É—an wani juya kai kafin can tace

"Na ji ina son hira da shi. Da ze tafi ma na ji ba daÉ—i.." Tsalle Lulu ta yi kafin ta koma ta zauna a kan kujerar tana faÉ—in

"In faɗawa Ammi kin amince koh? Don Allah don Allah kar ki ce a'ah.." Lulu ta faɗa cikin zaƙuwa.

"Tohm.." shi ne abin da Didi ta faɗa tana murmushi. Kawai se Lulu ta rungumeta cikin matuƙar farin ciki.

.. "Kema fa kanki kamar na Hero ne yana ja wallahi.." Ladi ta faÉ—a tana kallan Abida. Murmushi Abida ta yi kafin tace

"Wallahi kam irin aikin nan akwai wahala. Amma idan buri ze cika ai babu matsala."

"Bayan kin tura hotunan kin goge amma?" Ladi ta tambaya. Shiru ta yi na en wasu sakanni se kuma can ta shiga girgiza kai sannan tace

"Gaskiya dai ban goge ba. Amma ai babu damuwa, za ta yi tunanin kawai hoton ne ya birge ni shi ya sa na tura. Kuma ma shi ne dalilin da yasa ban tura wanda ita Afaaf É—in take ita kaÉ—ai ba. Se na tura wanda suke tare ita da masoyiyarta ta. Kin ga ko da ta gani ba na tunanin wani abun ze zo kanta.."

"Hakane kuma" Ladi ta faÉ—a tana jinjina kai.

"Bayan nan kuma na samo mana wani information É—in.." Abida ta faÉ—a tana neman waje ta zauna. Da sauri Ladi tace

"Yi maza ki sanar min me ya faru?"

"Na ji tace gobe akwai inda za su je. Se dai duk abuna ban ji inda za su je É—in ba."

"Aiki me kyau Abida. Maza miƙo min wayata.." ta yi maganar tana nuna mata wayarta da ke ajje a kusa da Abidan. Babu musu ta miƙa mata ta shiga nemo number Hero ta kira shi.

"Albishirinka!!" Ladi ta faÉ—a tana murmushi.

"Goro.." shi ma ya maida mata yana murmushi.

"Idan kana da lokaci ka ɓillo dan an samu cigaba. Idan kuma ba ka da shi faɗa min kana ina yanzun nan ka ganni a wajen.."

"Shegiyar mata.. ba se kin zo ba, ki jira ni zan ƙaraso.." Hero ya faɗa

"Toh godiya nake.."

.. Kowaccensu cikin hijab ta shirya me kyau. Sun fito a Malaman Addini sun yi kyau abinsu. Se da ta gama ɗaura niƙab ɗinta sannan ta kalli Ammi tace

"Ammi mun gama.."
Chapter 30 · 0% Book details