← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 37

Sashe 19

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameen na gode." Gwani ya faɗa da ɗan murmushi kan fuskarsa, dan sosai ya ji daɗin yadda Abban ya nuna kulawarsa a kan Abeeyn. Dama tun sanda ya zo wajensa ya fahimci mutumin arziƙi ne, se dai yanzun ma se mutuncinsa ya ƙaru sosai a cikin idanunsa. Sallama suka yi, Abba ya yi inda ze je, yayin da shi kuma Gwani ya tafi wajen Ummeey da ya tabbatar tana can tana jiransa ne. Aikuwa tun kafin ya ƙaraso ta miƙe cike da zumuɗin jin abin da ze faɗa ɗin. A nutse ya ƙaraso wajen yana kallan Ummeeyn da duk damuwa ta gama bayyana a kan fuskarta yace

"Ummeey.. ki kwantar da hankalinki. In Sha Allah babu damuwa me yawa. Zan fita yanzun, zan yi ƙoƙari na samu na haɗa kuɗin da za a yi masa wankin ƙoda ko na wannan satin ne.." ya ƙare yana ɗan ajje numfashi gami da lumshe idanunsa.

"Wankin ƙoda kuma Affan?" Umma ta faɗa tana buɗe ido sosai. Cikin kwantar da murya yace

"Ki kwantar da hankalinki Ummeey.." ya yi maganar yana kallanta. Girgiza kai Ummeey ta yi ba tare da tace komai ba, se komawa da ta yi ta zauna a kujerar da ta tashi daga kanta tana ji kamar ta yi kuka. A yanzu dai a yanayin da suke ciki samun kuɗin da za a dinga yiwa Abeeyn wankin ƙoda se dai idan Allah ne ze kawo musu wata hanyar.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ummeey ta faɗa sanda ta ke kai hannunta kan fuskarta cike da tausayin kansu. Kusa da ita Gwani ya zauna, ya sake ƙasa da murya cikin rarrashi yace

"Ummeey ka da ki É—aga hankalinki. In Sha Allah kuÉ—in nan za su samu."

"Allah ya yadda." Ummeeyn ta faÉ—a ba dan tana da tabbacin za su samu É—in ba, se dan sunan Allah da ya ambata.

.. Bin ta da kallo Ammi ta yi sanda take ƙoƙarin ɗaura niqab cike da ƙarfin hali. Cikin tausayawa Ammi tace

"Afrah ajje niqab ɗin nan, da lafiya ake yin komai. Saboda haka ki bari idan kika warke se ki je.." Ammin ta faɗa saboda yadda ta lura da Didin kawai ƙarfin hali take yi amma ba ta da lafiya. Duk da haka kuma ba ta haƙura ba take shirin tafiya. Se da Lulu ta tura baki gaba, dan ta san idan da ita ce cewa za a yi ta tafi ta warke a can, dan kowa ya san halinta, abu kaɗan ne ze sanya tace ba za ta je makarantar ba, ko da kuwa lafiyarta ƙalau. Saɓanin Didin da koda yaushe cikin son zuwa makaranta take ko da kuwa ba ta jin daɗi.

"Didi fa baki da lafiya.. kawai ki bari se gobe idan Allah ya kai mu." Itama Lulu ta faɗa tana kallan Didin da har ta koma ta zauna. Se kawai ta koma ta kwanta a kan gadon tana jin wani irin sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Ɗaukar katon blanket Lulu ta yi ta ɗora mata a kai sannan ta kalli Ammi tace

"Ammi mun tafi."

"Toh Allah ya kiyaye."

"Ammi mun tafi." Little ma ya faÉ—a yana yin gaba. Shi ma da addu'ar ta bi shi da ita tana murmushi.

Ko da suka je makarantar yau Gwani be zo ba, dan haka wani malamin ne ya shigar musu ajin. Hakan ne ya sa yau É—in da wuri aka tashe su. Dan haka ana tashin nasu Lulu ta kama hannun Little suka fito daga makarantar tare da Masoyiya.

"Aou Fatima da tafiya za ki yi ki bar ni?" Abida ta faɗa sanda ta ƙaraso inda suke.

"Eyyah a'ah fa. Kin ga mun tafin ne?" Fatima ta faÉ—a.

"Toh don Allah idan ba zaku samu damuwa ba ku É—an raka ni wani gida mana?"

"Gida kuma?" Fatima ta tambaya.

"Ehh pls ka da ku ce a'ah.."

"Masoyiya ni fa tafiya zan yi, kin san Didi ba lafiya.." Lulu ta faÉ—a tana kallan Fatiman.

"Wani gida fa kawai za ku raka ni.." Fatiman ta sake faÉ—a se dai yanzun Lulu take kalla.

"Pls mu rakata É—in.." Fatima ta faÉ—a tana kallan Lulu. Da sauri Lulu ta girgiza kai sannan tace

"A'ah ku yi haƙuri pls.."

"Pls mana." Fatima ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. Se da ta jefa mata harara sannan tace

"Mu yi sauri don Allah.." Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Abidar. Se ta soma takawa tana tunanin yanda za ta yi su rabu da Fatima a yanzun. Cigaba da tafiya suka yi jefi_jefi suna ɗan taɓa hira kaɗan. Little kuma na ƙarawa tafiyar tasu armashi ta hanyar surutansa wasu na hankali, wasu na shirme. Dakatawa Fatima ta yi tana ɗan yamutse fuska sannan tace

"Ina ganin fa baƙon watana ne wallahi.." ta yi maganar tana ɗan riƙe cikinta. Kallanta dukansu suka yi. Lulu tace

"Toh mu koma gida kenan?"

"A'ah mu ƙarasa gidan mana, ae za a samu pad." Abida ta yi ƙundunbalan faɗin hakan, cike da fatan ka da Fatiman tace "Toh" Aikuwa addu'arta ta karɓu dan kuwa buɗar bakin Fatima se cewa ta yi

"A'ah Abida. Kin ganni fa a gida, gwara na tafi gobe ma haɗe, ki yi haƙuri.."

"Babu komai ai, tunda ga Afaaf za ta raka ni."

"Waye Afaaf?" Lulu ta faÉ—a tana kallan Abidar.

"Ke mana, ko ba za ki raka ni ba dan Masoyiyarki ta tafi? Don Allah Fatima ki ce ka da ta ƙi raka ni. Ni kaɗai zan je kamar wata mayya." Ta ƙare kamar me neman taimako. Cikin rarrashi Fatima ta kalli Lulu tace

"Pls ki rakata mana." Ba dan ta so ba, se dan kawai dai ka da Abidar tace ta wulaƙanta ta ne ya sanyata faɗin

"Na ji.." ta faɗa tana sake kama hannun Little suka cigaba da tafiya. Dan farin ciki Abida ji ta yi kamar ta tsaya ta taka rawa. A haka suka cigaba da tafiya, har suka ɓillo wani bakin titi. Cike da ƙosawa da tafiyar, dama kuma abinka da ba ta yi niyya ba, Lulu tace

"Ni fa gaskiya am tired. Har yanzu ba a zo ba?" Murmushi Abida ta yi kana tace

"Mu na tsallaka titi gidan ya ke.."

"Ah toh.." Lulu ta faɗa. Daidai lokacin da suka tsallaka titin ya yi daidai da lokacin da Gwani ya ke saukowa daga cikin Napep tare da wani ɗalibin Abeey. Shi ya soma sauka sannan Gwani ya sauka, ya miƙawa me Napep ɗin kuɗinsa. Yayin da ɗalibin Abeey ɗin me suna 'Abbati' ya ɗan miƙe hannunsa kamar wanda suka yi tafiyar awanni ya gaji. Daidai sanda ya ɗan juya yayi daidai da lokacin da su Lulu suke ƙoƙarin shiga gidan hannunta riƙe da Little. A haka sam ba zaka gane ma gida ba ne, saboda yanda wajen ya ke kamar ba ƙofar gida ba, sannan kuma shaguna da yawa sun yi ƙoƙari wajen kare gidan, dan idan dai har baka san da zaman gidan a wajen ba, toh ba za ka gane akwai gida a wajen ba. A kan Lulun kuwa idanunsa suka sauka sanda ta ida shigewa cikin gidan. Tsaki Abbati ya ja yana girgiza kai, cike da takaicin wannan abu da ke faruwa. Ya kasa shiru har se da ya kalli Gwani da ke ƙoƙarin sake tare musu wani Napep ɗin saboda wannan ɗin tayarsa ce ta samu matsala.

"Wallahi ya kamata a saka ido a kan gidan nan sosai. Iyaye ma kuma yana da kyau su sake saka idanunsu a kan 'ya'yansu. Wallahi Malam yanzu ba ka ga wata yarinya da na gani ba dududu a shekaru ba zata wuce a ƙirga su ba, amma ta shiga gidan nan. Ban san me yasa kamar hukuma na tsoron gidan nan ba ne." Girgiza kai kawai Gwani ya yi sannan yace a nutse

"Allah ya kyauta, ya kuma shirya.." ya yi maganar sanda ya ke hawa cikin Napep É—in da ya tare musu.

A É—an mamakance Lulu ta dinga bin gidan da kallo, dan gaba É—aya ta rasa a wane muhalli za ta aje gidan. Ta kasa gane me ake yi a gidan, suna ake yi ko biki ake yi? Duk ta kasa ganewa.

"Wai biki a ke?" Little ya faÉ—a yana bin wani waje da a ke kiÉ—a da kallo.

"Ehh" ta faÉ—a, dan itama a yanzun ta gane bikin a ke yi, saboda yanda ta ga taron mata ne a ko ina, se jefi_jefin maza kaÉ—an kaÉ—an.

"Kar ki damu Afaaf, ai mun zo." Abida ta faɗa tana jin ita kam yau burinta ya gama cika, tunda har ta iya ɗauko Lulun ta kawota gidan nan, ai komai ya ƙare kuma. Har cikin wani parlour suka isa, ita dai Lulu ta gama ƙuluwa, ta gama fusata dan har ta riga ta ƙudura a ranta cewar, ko me Abidan za ta yi ba za ta sake rakata wani wajen ba, se dai ta ji haushi ta dena kulata. Ita kaɗai ce a cikin ɗakin sanye cikin wasu riga da wando waɗanɗa suka bi lafiyar jikinta suka zauna sosai. Siririya ce se dai ba can ba, amma da ke tana da diri ya sanya a kallo ɗaya ba zaka kirata da siririya ba. Kanta babu ɗan kwali se tulin attach ɗin da ke zaune a kanta kamar ba ɗorawa a ka yi ba, saboda yanda suka zauna sosai.

"Yallaɓiya saukar alkhairi.." Abida ta faɗa tana murmushi gami da ƙarasawa kusa da matar. Da sauri Ladi ta juyo tana kallan Abida kafin ta maida kanta kan Lulu da har lokacin take tsaye a bakin ƙofar, ta daɗe da ƙaguwa a kan Abidar ta fito su tafi. Lumshe idanunta Ladi ta yi kafin ta koma kan kujera ta zauna yaɓar har lokacin idanunta a kan Lulu. Se ta nuna wa Lulu kujera tana faɗin

"Ki zauna mana Baby.." Ladin ta faɗa tana wani maƙe muryarta da tafi kama da ta wani ƙaton gardin. Ita sam Lulu ba ta kawo komai ba, dan ba ma ta ji sunan da Ladin ta kirata da shi ba. Haka zalika shigar jikinta ma bata damu da ita ba, dan tafi tunanin me aure ce, kuma yamma ta yi shi ya sa ta yi wa mijinta kwalliya. Se ta ɗan zauna kaɗan tana sake riƙe hannun Little fuskarta a haɗe saboda yanda ta riga ta ƙulu da Abida.
Chapter 19 · 0% Book details