← Book details A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 37

Sashe 27

A Jini Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Lulu ta maimaita tana kallan Abida cike da maɗaukakin mamakinta. Bata taɓa tunanin maganar da za ta sake mata ba kenan, ashe da gasken ba ta da kunya? Ashe ba ta tsoron Allah da gaske?

"Ki kama kanki, ki fita a hanyata. Na ga wa'azi ba ya shiga jikin irinku, saboda haka wallahi zan tona miki asiri kowa ya san wace ce ke. Kin san kuma idan har en makaranta suka sani shi kenan se kowa ya ji a cikin unguwar nan. Shi kenan kuma ta ɓare da ke."

"Toh se me? Kin daÉ—e ba ki tona min asiri ba. Idan ki ka je ki ka faÉ—a ai za su tambayeki yanda aka yi ki ka sani, ko me za ki faÉ—a ba yadda za su yi da ke ba. Saboda haka yanzu ma ba se gobe ba ki je ki tona min asirin."

"Haka ki ka ce?" Lulu ta faɗa tana murmushi, dan ita sam wannan maganar da Abidar ke faɗa ta san kawai faɗa take yi saboda rasa abin faɗa. Ban da haka a irin wannan abun har se ta tsaya ma tunanin idan ta je faɗa za ta ɓare da ita?

"Haka na ce!" Abida ta faÉ—a itama tana kallan Lulun.

"Ohk.. ki tsaya ki yi kallo.." Lulu ta faÉ—a tana juyawa a fusace, tana tuna yadda Didi ta hanata tona mata asiri tun ranar farko, da ta barta tun a ranar ta sanarwa wani daga cikin malaman ta san da tuni yanzu an daÉ—e da korar Abidar daga makarantar..

Me son yin payment yanzu kafin mu gama Free pages, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273.

https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_17

___Ganin da gasken juyawa Lulun ta yi ya sanya Abida saurin riƙota tana faɗin

"Afaaf! Wai kin É—auka da gaske nake? Wallahi da wasa nake miki. Kawai ina so ne na ga za ki iya abin da ki ka faÉ—a É—in? Se kuma na ga ashe za ki iya É—in?"

"Cikani malama. Ashe har yanzu ba ki san wace ce ni ba, ni za ki yi wa gatse?" Lulu ta faɗa fuskarta a haɗe tana kallan hijab ɗinta da Abida ta riƙe. Jin ta ƙi sakinta ne ya sanyata saka hannunta ta fincike hijab ɗinta sannan tace

"Dallah can cikanii!!" Daga haka ta juya. Cikin wani irin sauri Abida ta zo har gaban Lulun tace lokacin da fuskarta ta koma kalar tausayi

"Don girman Allah ki yi haƙuri, wallahi na tuba fa ba zan ƙara ba, kuma ki saka min ido."

"Matsa min hanya." Lulu ta faɗa ba tare da ta kalleta ba. Ganin dai da gasken so take yau ɗin ta tona mata asiri a bainar nasi ya sanyata zubewa a kan gwuiwoyinta sannan tace sanda idanunta suka cika da ƙwallar da ba ta tsoro ba ce, face ta zallar takaicin tsugunawa Lulun, lallai ko me Ladi za ta saka a yi wa Lulu ita me amincewa ce komai muninsa kuwa. Se a lokacin sannan Lulu ta dakata tana huci dan wallahi a yau ɗin ta yi niyyar zuwa wajen wani malamin ne ta sanar da shi abin da ya faru, se dai Abidar kuma ta bata tausayi dan haka ta fasa tafiyar. Kafin tace komai ta sake tsinto muryar Abidar na faɗin

"Nima ba dan komai ba ne ya sanya na dage a kan wannan maganar ba, se dan na san ba a yi wa Jakadiyarmu musu, babu wanda ke ƙaunar ja da abin da tace. Toh amma tunda ke kin ƙi yadda, kin kuma nuna ba ki da tsoro, ba ni da damuwa zan je na sanar da ita yanda muka yi da ke, kuma daga yau ba za ki sake jina na zo miki da wannan maganar ba. Ba ma ke kaɗai ba na riga na tuba nima. Ina kuma me sake baki haƙuri.."

"Ita É—in banza! Wace ce ita? Ku dukanku ma su waye ku? Who the hell do u think u are da har kuke ganin ba za a iya muku musu ba?"

"Ai na ce ki yi haƙuri.." Abida ta sake faɗa kamar da gasken ta yi nadama. Tsaki Lulu ta ja kawai ta shige daga wajen ta barta a durƙushe. Se a lokacin sannan Abida ta bi Lulu da kallo, haushinta da kuma tattaurar zuciya gami da taurin kai irin nata na ƙara fusatata.

"Ki jira haɗuwarku da Ladi.." ta faɗa tana fidda wani huci cike da ɓacin rai. Daga haka ta cigaba da tsugunon tsawon mintuna kamar ba za ta bar wajen ba, se kuma can dai itama ta miƙe ta fita Sallahr rai a ɓace.

.. Gaba ɗaya kwanakin yana busy sosai saboda yanda Daddy ya sakasu a gaba a kan fara kasuwancin da za su soma. Sanye cikin gajeren wando da kuma wata hamshaƙiyar farar riga mara hannu, wadda ta gama bayyana halittar ƙaƙƙarfan damtsen farin hannunsa da baƙar suma ke kwance luff luff kamar ba jiki ba, saboda yanda ta ke jere kuma a kintse kamar wadda ya ke saka hannu da kansa ya ke jerata. Numfashi kaɗan ya ke ɗan saukewa kasancewar ya daɗe yana motsa jikin. Baƙar sumar kansa da gashi ke nan ajje tuli kamar ba ya askewa ta ɗan hargitse ta kuma jiƙe da gumin da za ka iya cewa ruwa ya watsa a kan. Se dai da ya ke shi ɗin ba gwanin gumi ba ne a jiki ko a fuska ya sanya jikin nasa gumin kaɗan ne babu yawa kamar wanda ma be yi wani motsa jiki ba. A hankali ya kai hannunsa ya ɗauki wani farin towel da ke ajje wanda yafi kama da sabo gall, ya ɗan buɗa shi sannan ya kai kansa ya shiga tsane gumin da ke cikin kan nasa. A hankali kuma ya koma ya zauna dan ya ɗan sake jin daidai kafin ya faɗa toilet dan yin wanka. Ɗan fesar da iska ya yi daga bakinsa sanda ya tuna nan ba da jimawa ba Daddy kan iya kiransa su ƙarasa magana. Lokaci ɗaya kuma ya tuna da Hero da ke ta kiransa tun ɗazu be ɗaga ba. A hankali ya kai hannunsa inda wayarsa ke ajje, ya jawota yana ɗan lumshe idanunsa, takurar Daddy ta yi yawa, har ya soma ƙosawa da ita. Tun yanzu kuma haƙurinsa na neman ƙarewa a kan rashin samu ya sha ishashshiyar giya. Dan tun lokacin da ya je joint ɗin nan ya sha ta hannun Hero be sake sha ba, couz he thought gaba ɗaya ta ƙasar nan haka take babu daɗi, ga kuma bugarwa da sakawa a dinga yiwa mutum kallan ɗan ƙwaya. Shi ya sa ya dakata se ya samarwa kansa irin wadda ya saba sha sannan ya yi kodimo son ransa. Se dai a dalilin wannan kasunwancin da za su fara ya sa komai ya dakata masa, ga shi kuma yanzu gaba ɗaya gangar jikinsa ta ƙi aminta da kwana biyun da be sha ba, hatta shi kansa jinsa ya ke yi wani daban. Number Hero ya kamo ya danna masa kira kafin ya saka a kunnensa. Tana shiga kuwa Hero ya ɗaga dan dama a ƙage yake da son ganin kiran Bad Man ɗin.

"Bad..!!"

"Hero." Ya faÉ—a har lokacin idanunsa a lumshe.

"Inata kiranka ba amsa.. Akwai daddaÉ—an labari.."

"Labari?" Bad Man ya faÉ—a. Dariya Hero ya yi kafin yace

"Yeap. maganar harkar nan da na ga ba ta maka daÉ—i ba, na samo maka the most expensive one, am sure u will enjoy it.."

"Really?" Ya faÉ—a yana É—an É—age girarsa gami da buÉ—e idanunsa.

"Offcourse yes!"

"Ohk nawa ne price nata?" Bad Man ya faÉ—a dan sake tabbatar da da gasken me tsadar ce ko kuma dai kawai zuzutawar Hero É—in ne

"Na yi dropping maka message. Check ur DM pls.."

"Alright.. Thanks.."

"Haba haba, ka da ka sa na ji wani iri mana, da girmanka? Ai ko me na maka girmanka ne my Man.." Murmushin gefen baki Bad Man ya yi wanda ya matuƙar ƙawata fuskarsa kafin ya kai hannu ya ɗan shafa kwantacciyar sumar da ke zaune luff a kan fuskarsa wadda kallo ɗaya za ka mata ka san mamallakinta na kula da ita, dan kuwa ba ta da yawa irin wadda ake askewa ce a kai a kai, hakan ne ya sanya kodayaushe ta ke cikin nutsuwa babu hayaniya.

... "My son!!" Aunt Makiyy ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin ta yi hugging nasa cike da kewar ɗan yayarta ta. Ɗan murmushi ya yi kafin ya yi hugging nata back.

"Ba dai daga bacci ka tashi ba?" ÆŠan yamutse fuska ya yi sannan yace

"Nop, na É—an motsa jiki ne."

"Dole ko da yaushe jikinka ya ƙara murɗewa. Kana kallan yanda fatarka take sake yin kyau da sheƙi, gami da sake murjewa kuwa?" Ta yi maganar tana kallan yanda ya yi kyau cikin wasu tsadaddadun ƙananan kaya.

"Aunt.." se ta yi murmushi kafin tace

"Da gaske fa.." Daidai lokacin da Mom ta shigo ɗakin kenan. Da murmushi kan fuskarta ta ƙaraso tana faɗin

"Se yaushe za ku fito ne?"

"Yanzu ma kuwa.." Aunt Makiyy ta ƙare maganar tana kallan Bad Man, sannan ta ɗora da

"Yau da kaina na shirya maka abinci me daÉ—i. Hope dai ba fita za ka yi ba?" Hannu ya kai ya É—an murza goshinsa sannan yace

"Eyyah akwai inda zan je buh idan na dawo zan ɓullo.."

"Ai kaa ji kuma." Aunt Makiyy ta faɗa tana ɓata fuska. Komawa ya yi ya zauna a kan ƙaton haɗaɗɗen gadonsa sannan ya soma saka takalminsa. Se da ya gama kafin ya miƙe yana gyara zaman hular kansa da ta mugun karɓarsa kafin ya kalli Mom da Aunt Makiyy yace

"Zan tafi.." Matsawa kusa da shi Mom ta yi ta gyara masa zaman hular kansa kafin tace

"A haka ka fi kyau My boy.." É—an murmushi kawai ya yi dan ya ga alama Mom É—in ba dena faÉ—ar sunan nan za ta yi ba, saboda yanda ya gama zama a bakinta.

"Wai batun aiki ne?" Mom ta sake tambaya. ÆŠaga kafaÉ—arsa ya yi lokacin da hannunsa É—aya ke cikin aljihun wandonsa.
Chapter 27 · 0% Book details