← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 29

Sashe 9

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai kinje koh?..

Cikin
fusata tace "eh..

Murmushi yai ya k'ada kai,
"Bazan hanaki ba toh, sai dai wallahi ki sani,
mud'in kika sa kafa kika fita,toh *A BAK'IN
AURENKI*....

Bai jira komai ba yai waje,yana
jiyota tana ai wallahi bazaka sani kaffara ba,fita
kam nayi na gama.

By Feenat Ja'afar. 庐NWA.

Like 路 6 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Ummu Maryam Tahir
Sannu da qoqari 6ter
Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Kareema Wakeeli
Tnx
Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 18
_Kitchen_ kawai ta leka,ta d'aura guntun ruwa a
tukunyar silver a _hot plate_ nata karama nepa
suka d'auke wuta.

Kamar zata kashe,kawai ta
bari,a ganinta ba komai.

Kan su kai gidan
gumama kuwa 5 tayi,fatansu Allah sa ba'a za6e
ba.

Kaya kam gasu masu k'yau, tuni ta fara
daddagawa tana ware na wara.

"NEPA"...

Cewar
yaran gidan, sai dai da halamun su Salma hankali
yayi kan gumama.

Suna nan a gidan har kusan
k'arfe 6,amma basu gama da mai kaya ba.

Kamar ance daga kai sama,sai ga nan dan
hayaki na yin sama halamar daga nesa ana
gobara a wani gu.

"Ina ga wutar dazu tai ma
wasu aiki,hayakin nan gobara ce duk yadda
akayi..

Kai Salma ta k'ada, "koh taya ake konawa
ba...

Sai dai kan su farga ihun gobara har kusan
layin da suke.

Maman Ummi tace suzo su je,in
yaso daga baya sa dawo suyi bayanin.

Da sauri
Salma ta tare, "A'a Manan Ummi,nasan yanzu Ya
Ja'afar na hanya 6 saura.

"Muje dai koh gobe
tunda ta kirga wanda muka d'auka ma dawo ai
sabon lissa...

"Umma!..Umma!!...

Da gudu yaron
mai gumama ya shigo, matar tace "lafiya irin
wannan gudu?

Ince dai ba daga gun gobarar ka
ke ba?

Yana haki yace "a gidan Aunty Salma ne
fa Umma..

Ana ta neman inda za'a shiga a k'ulle,
yanzu aka kira Malam Jaaf...

"Na shiga uku...

Ni
Salman koh wa?..

Kai yaron ya daga,ai ina,da
gudu ta fice ta wat'sar da kayan a nan ta bar
Maman Ummi da kira.

Kamar wata sabuwar
kamu haka ta iso wajen,kofar gidan cike da
jama'a wasu na kok'arin sanya t'sani su haura.

A
ka ta d'aura hannayenta d'uk biyun,tama rasa ihu
zata kurma koh kuka.

Baban Ummi ne yace ina
mukullin gidan?..

Nan ta fara tunanin mukulli?..

Innalillahi, ta barshi shima gidan gumama...

Baya
ta fara yi ganin Ja'afar da Garba sun faka mota a
chan gefe, a gigice suka karaso, "Innalillahi
Wa'ina Ilaihirraji'un"...

Itace kalmar da Jaafar ya
iya fad'i.

Ina kan ta farga sai ga hawaye na zuba
tana girgiza mishi kai,mukulli Garba ya tambaya,
kan cikin azama ya lalubo a aljihu ya bashi.

Salman ya k'allo cikin tausayin kanshi, har yanzu
hannu na ka tana k'ada kai tana kuka.

"Shikenan
kin zaunar mu Salma...

Burin ki ya cika sai ki
zuba ruwa a kasa ki sha....

Tuni ta kara fashewa
da kuka.

Fad'in "A kashe meter...

Ne yasa yai
cikin gidan da sauri.

Ba ka ganin koh ina sai
dusu-dusu dan hayaki.

Da taimakon Maman
Ummi ta bar kofar suka shiga daga cikin gida.

Sai dai har yanzu kuka take baji ba gani.

Yau
tasan ta kad'e har ganyenta.

Motar kashe wuta
ce ta iso,da taimakon dak'yar wuta ta mutu.

Ilahirin kitchen da bedroom ya kone ya laso
parlour ta silin Allah ya t'sayarta.

Fito wa tai
bayan taji komai ya dan lafa ta leka gidan,sai ga
nan Ja'afar din sun fito rike da barbadin
_documents_ nasa a hannu.

Kamar munafuka ta
dan ra6a ta shigo kai duk'e tana jan hanci.

Sai da
yazo dai dai ita ya t'saya.

Kanta kasa tana
sharar hawaye,a hankali ya saki burbudin
takaddun ya fice jiki duk yayi sanyi.
**************************** Zaune suke a bak'in
masallaci shi da Garba bayan komai ya lafa yana
tausarshi,yan unguwa sai jajanta mishi suke suna
tafiya.

"Dan Allah ka'r ka ce zaka d'au
mummunan mataki akan Salma, kai
hakuri,ubangiji ya mayar ma da alkairin da ka
rasa.

Shiru Ja'afar d'in yai,zuciyar shi sai tafasa
take,dan ma yana ta kok'arin neman kariya daga
zugar shedan.

Zuwa chan dai ya nesa, "Babban
ni takaici na Garba Takaddu na ne,tun jiya ake
_verification_ gobe ne namu,ni bana ta
Salma,dan a bakin aurenta ta fita...

"Ni ga nan
d'akin waje zan iya maleji.

Kafad'arshi Garban ya
dafa,lalle kowa da jarabawar shi a rayuwa,shi
kuma abokinshi ta mata Allah ya bashi.

"Yanzu
toh ya za ai?...

Murmushi Ja'afar d'in yai wanda
yafi kuka ciwo...

"Ya k'wa zanyi Garba?..

Kana
sane da gamnatin nan tamu, wa zai k'ar6i uziri
na gobe?..

Shiru yai mishi,dan tabbas yasan bai
da abin fad'a ma abokin.

Gida suka koma,tana
nan inda suka barta a durkushe ta tasa takaddun
a gaba tana shesshekar kuka.

Ja yai ya t'saya
yana k'allonta, muryar ta har ta dashe.

Abin
haushi wai kuma zuciyarshi ta fara tausayinta.

Da sauri ya d'auke kai daga k'allonta dan jin
zuciya na ingiza shi yaje ya lallaso ta, Salma ce
fa...

Dake wa yai ya daure tukun yace "toh meye
ne na kuka kuma Salma?..ki tashi kawai kije gida
dan sharad'in dazu yana kan ki....

Da sauri ta
dago ta k'alleshi, tuni taji kukan ya kafe,sai ido
da ta kafe shi dashi, shaf ta manta wani sharad'i
ne ma?

Tuni ta tafi duniyar tuna abinda ya afku
ka ta fita.

Garba ne ya katse mata tunani da
fad'in "haba dai dan Allah?

Wannan sharad'in bai
k'yautu a gun ka ba Ja'afar..

Aure ya fice wasa
fa..

Ka janye sharad'in nan tun kan kowa ya ji ku
koma auren ku....

Da sauri ta k'allo Garba,duk ta
kasa ta6uka komai, Mey Garba yake nufi da su
koma auren su?

Yaushe Ja'afar ya sake ta?....

Bai furta ba sai dai in yanzu..

Cikin muryar kuka
tana ka'rkarwa tace "bai sake ni ba Garba, auren
mu na nan...

Koh yanzu ya furta?..

Banji ba
Allah...

Ni bai sake ni ba...bai sake ni ba..

Sai ta
karasa tare da fashewa da wani kukan mai ban
tausayi.

Ido kawai suka zuba mata, tamkar
zararriya haka take magana.

Duk sai ta karya
musu zuciya, barin gogan,har bai san ya je
gareta ba,da zummar dago ta yaje ya lallashi
abarshi,sai dai kamar wanda aka t'sayar ya
d'auke hannunshi, baya ya koma yana rint'se
ido...

Tabbas yanzu saki ya gifta a tsakani,bai da
_right_ na ta6ata,tabbas bai dashi.

A hankali ya
furta "Salma kin cuce mu...

Kin fara dasa
katanga a tsakanin mu...

Ban san da abinda na
rage ki ba Salma...ban sani ba, dazu a yadda
nake jin zuciya ta,wallahi dan banzan doka naso
na miki,Allah ya kareni da yin kuskure.

Baya ya
juya mata,kan ya k'allo Garba.

"Dan Allah ka
kaita gida gani nan zuwa...

Waje yai ya barsu
nan,Shikenan ta tabbata,ba makawa Ya Ja'afar
ya sallama ta..

Ai tuni ta kara jiniyar
kuka,dak'yar ta tashi sukai waje da Garban.

Sai
duba Yayan nata take koh zata ganshi.

"Muje
Salma,InshaAllah komai zai daidaita,..

Juyowa tai
ta sadakar da yai nisa...

Yana k'allon su har
suka kule kan ya fito a inda ya 6oye a bayan
bishiya.

Harda goge y'ar k'walarshi...

Salma kinyi
aiki.

By Feenat Ja'afar
9/29/16, 9:06 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
19_"Toh a garin yaya haka ta faru?

Fita kukai?...

Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan
Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima.

Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita
sakin, kuma yaushe ya mata?.

"Salma komai
mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi
adu'ar Allah maida muku alkairi kinji...

Kai ta
dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar,
kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba
cewa yai fa ya sake ni...

Wallahi ba dagangan na
bari haka ta faru ba....

A zabure Mama tace "ya
sake ki?..

Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da
yai shiru yana k'allonta.

"Ni dai banji lokacin da
ya saken ba kuma..

Ta karasa da dan kukanta.

Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar,
"Mey take fad'i ne Ja'afar?...

Sam ban gane inda
ta dosa ba..

Kai ya kara d'ukrawa,kan ya
dago,mama in banda harara ba abinda take sakar
mishi.

Ya sani da dole su Abba suji.

Cikin
nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma
ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama,
kawo yau da abin ya faru..

Tsananin mamaki
Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da
wannan d'anyen aikin?

Chan dai ya numfasa tare
da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un...

Kuma
kin fita d'in Salma?..

Baya ta fara ja tana k'ada
kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba...

Murmushi Abban yai na takaici..

Ya ma rasa mey
zai wa Salma ya ji dad'i..

Duka?

Kai ya k'ada.

"Ni meye nawa?

Ba dai kin fanshi fita sama da
aurenki ba?..

"Wannan shine sakin Salma...

Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN
AURENKI*....

Kai ta dago da sauri..

Saki kuma?

Daga fad'in hakan?...

Kawai sai ta sa musu kuka,
"Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara
ba,Abba kai hakuri...

Cikin t'sawa yace "tashi ki
bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce...

Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai
kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da
haka sai da mummuka mata.

Dak'yar Ja'afar ya
lallaso shi.

"Kin wa kanki toh Salma,dan dole
kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min
ba...

"Haba wai Malam dan Allah..

Waye baya
kuskure a rayu....

"Kimin shiru kema, dan duk
laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take
aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au
mataki..

Jan Salman tai d'aki tana bashi
hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita.

Sai da ya
gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi
hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na
rasa abin yi ne shi yasa nai hakan....

"Ni fa
banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai..

Gaba
nasan bazata kara ba.

Shi dai kawai hakuri yake
bama Abba.

Abba ya tambaye shi kan saki nawa
ne?

Yace daya.

Tashi yai yace ya jira shi,sai
yace bari yaje gida shima ya d'au machine
sannan ya sanar musu.

D'aki Abban ya shiga
bayan Ja'afar din ya fita.

"Amma kin bani
mamaki Allah Rabi...
Chapter 9 · 0% Book details