← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar mai neman ba'asi ta t'saya bata k'ar6a
ba.

"Ajiya na kawo kimin zuwa gobe ne,ba wani abun
ba naga kina tsoro.

Murmushi tai kan ta amsa tana k'allon Ummi
zata wuce,koh ci kanku bata ce ba ta shige gida.

D'uk sai Salman taji wani iri,Ummi sam taki jinin
Ja'afar ta rasa dalili.

Ba jimawa yai mata sallama dan ya rasa abin
fad'i shima.

Dama da Garba ne yau kam da zai iya fad'in
komai ga Salma.
***
Tunda daga lokacin Ja'afar ke zuwa gun Salma
jefi-jefi,d'uk da har yanzun bai furta mata so
ba,amma ita a ganinta d'uk acikin so ne.

A k'wan a tashi gashi har ta kammala secondary,
wannan itace tafiya mafi tsawo da Salma tai bata
ga Ja'afar ba,kusan wata bakwai.

Tun tana damuwa har ta hakura ta rungumi
karatun ta na fita.

Gasu yau sune a gida,d'uk an rame anyi baki.

By
Feenat Ja'afar.
[7/21, 10:10 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
10_Babban tunaninta bai wuce d'uk t'sawan
lokacin nan da aka diba ba Ja'afar ba labarin shi
ba,tasan yakan je mata ziyara makaranta koh a
t'satt'saye ne,ga ita ba waya ba balle ta neme
shi koh lafiya?

K'wana biyu da dawo wa yau d'ai ta kudiri niyar
fita jin ba'asi,koh Garba in ta gani.

Hijab d'in _mss_ d'inta har kasa ta sa harda
nikaf.

Sai d'ai har ta gama zagayen layin ba wanda ta
gani ciki,kawai burinta ganin Ja'afar ne.

Iyanzu kam tasan tai nisa kan sonshi ba kad'an
ba,sai d'ai ita yanzu ta fara tantama.

Har zata juya ta tuna da shago,d'uk da tasan
yanzu ba kasafai yake zama ba tunda ya samu
g'urbin koyarwa.

Sai dai tai chan d'uk bata tunanin ganin nashi.

Daga d'an nesa ta t'saya kusa da wata bishiya ta
d'an kare ba mai ganinta, da sauri ta juya tare da
dafe kirji,zuciyar ta sai bugawa take da k'arfi.

Yanzu ta samo amsarta da kuma kokwantan ta
da ya zama gaskiya...

Bata aune ba sai jin
hawaye tai na bin kuncinta cikin nikaf d'in.

A hankali ta fito daga bayan bishiyar tare da kara
k'allo shagon.

Murmushi yake harda darawa, ita kuma budurwar
sai washe mai baki take tana ta mai zuba,rike
yake da hannun wata y'ar k'yak'yawar yarinya
fara kamar yayarta.

Ji tai wani abu ya tokare mata kirji,da sauri tasa
hannu ta dafe gun,ga hawaye yaki ya d'aina
malala.

Lalle tai wautar kin kula kowa sai Ya Ja'afar da
bai furta mata so ba.

Ido ta rint'se ganin ya d'akko mata wani
had'adan net purple yana bata,wato har kalar da
yasha sanar mata yana so ya bata?

Tai imani mai irin wannan zankadediyar budurwar
fara ba abinda zai da ita Salma baka.

Hannu tasa ta cikin nikaf d'in tana goge hawayen
dake zuba mata.

K'allo sun da zatai taga Ja'afar ya zuba ma inda
take ido,har budurwar na k'allo itama,da sauri ta
juya gabanta na fad'uwa, kar dai ace ya gane ta?

Tab,da k'wa ta bada kanta wallahi.

Juyo wa ta kara,sai karaf suka kara had'a ido da
Ja'afar.

Ba shiri ta tare mai adaidaita ta
shige,tana k'allo ya bi napep d'in da k'allo yana
girgiza ma budurwar kai.

Kawai sai ta sa kuka mara sauti tare da cire
nikaf d'in.

Lalle tai wautar zurmuwa ga soyayyar Ja'afar,
soyayyar da ba'a ma bayyana mata ita ba...

Ya
Ilahii.
**************************
"Oh!

Man Ja'afar, dama kana k'allon mata har
haka?

Bafa koh kiftawa?

Murmushi yai mata tare da girgiza kai, "Hala tai
kama da Salma ne?

Danma da hijab ga kuma
nikaf..

"Kusan hakan ne, jikina ya bani kamar Salman ce
kam..amma nasan ba ita ba ce ma.

Dariya ta danyi har hakorinta farare suka
baiyana,kan tace "sannu _Romeo_ toh, ni
sallameni kan Amal ta fara neman mamanta,
amma ina mamakin yadda ka iya zaben kaya da
color, halama kana son _purple_?

Murmushi
kawai yai mata,kan ya k'ada mata kai halamar
eh.

Ita kam Salma tana zuwa gida ta taho da yaro a
kofa ya kaima mai Napep kud'in shi.

Allah yaso ba kowa t'sakar gidan mama na d'aki.

A katifa kawai ta zube ta sau kuka,sai da tai mai
isarta tai shiru tana maida numfashi.

Chan kuma kamar wacce aka t'sikara ta mike
zaune.

Tabbas Ja'afar bai ta6a nuna yana sonta ba
kam,d'uk zuciya ke yaudarar ta.

Asalima da "K'anwata" yake kiranta, kila hakan
ne tun da,ita kad'ai ke kidanta, gaba d'aya ta
gama kore masu sonta ita a dole ta riki Ja'afar.

Hawaye ne ya kara zubo mata tunawa da yadda
yake washe ma budurwar nan baki.

Tasan yadda Ja'afar yake a gaban mata baya
wargi,baya sake fuska ma bare har yai musu irin
wannan tad'in.

"Tabbas budurwar sa ce,nai wauta ni Salma...

"Lafiyar ki kuwa kike maganganu ke kad'ai ya
sabuwar kamu?

Kai ta dago jin batun Ummi tana wannan y'atsine
matan.

Sai dai ganin irin yadda idon salman yadda yai
ja,ga kuma hawaye yasa ta mat'so
"Mey ya faru kike kuka haka?..

Ai kamar mai jira
a ta6ota ta kara sa wani kukan mai sauti.

Tuni kuma sai Ummin ta zauna tana lallashi da
fad'in lafiya?

Ita de sai kukanta take baji ba gani.

Tashi Ummin tayi,"bari na fad'o ki da mama
toh,kila k'ya fad'a mata ita...

Da sauri ta rike
mata riga, "ni ba komai..

Marata ke ciwo da
bayana kawai.

T'saki Ummin tayi, "Allah kina da aiki a gaban ki
Salma,kukan jinya sai kace wata yarinya.

Ita dai tana jinta ta karaci kardinta tai waje,a
hankali ta zame ta k'wanta,sai sauke ajiyar
zuciya take.
*By*
*Feenat Ja'afar*
庐*NWA*
[7/22, 12:02 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
11_Kan safiya har ta gama tunanin abin da zai
fisshe ta.

Hakan yasa t'saf ta tashi kamar ba ita taci kukan
nan ba.

Aunty A'i yau za'a kaima wuni,tun (12)
suka fice ita da Ummi.

Chan suka yini har dare,a kafa ta ratso ita kad'ai
sakamakon Ummi da ta biya kar6an _style_.

Tunda tazo layin su Ja'afar d'in taji gabanta na
fad'uwa, duk da bata koh k'alli hanyar gidan ba.

"Abokina ina ka tafi ne daga lissafi kai shiru?

"Ba kaga kamar Salma ba waccan mey tafiyar?

Ido Garba ya k'wara, da mutum,amma a duhun
nan bazai tantance ba,kawai sai ya k'ada mishi
kai,
"A cikin duhun daren nan ne har zaka gane wake
tafi....

Shiru yai ganin Ja'afar d'in yai gaba,da
sauri yace "wai mey ke damunka ne?

Ina za
ka?..

Binshi yake shi kuma yana bin mai tafiya a
duhun.

"Salma"...

Chak!

Ta t'saya dan jin kamar an kira
ta,a hankali ta juya,da dan tazara a tsakanin su
kad'an, amma hakan bazai sa ta kasa gane ya
Ja'afar ba koh a cikin dubu,hakan yasa cikin
sauri ta juya ta chigaba da tafiya,har dan gudu-
gudu sauri-sauri take.

"Mey zai fad'a min kuma?

Ta fad'a cikin ranta.

Har kusan layinsu ya bita, tsammanin shi koh
tsorata tayi,amma tabbas wannan Salma
ce,kawai sai ya t'saya a dai-dai layin nasu yadda
bazata ganshi ba,da hasken inji a layin, yana gani
ta t'saya ta waiga,kan da sauri ta shige gida.

"Amma fa baka aiki sam Jaa, wai har nan ka
biyota kage ma koh aljana ce a daren nan?

Juyawa yai yana girgiza mishi kai,"Allah Salma
ce,toh yaushe ta dawo?..

Baki sake Garba yace
"hadda rantsuwa?

In Aljana ce fa mai siffar ta?.

Harara ya sakar mishi kan ya juya suka tafi.

Ita kam tana zuwa gida Abba da Mama suna
t'sakar gida ta shigo sai haki,tuni k'wa Abba
fad'a ya karu, kan mey yasa sukai dare?

Tuni tai zuru zuru,fad'a sosai tasha,saura
Ummi,d'uk da laifin Ummin har sukai daren.

Washegari kusan yamma sai ga nan yaro kan ana
kiran Ummi da Salma inji su isma'il.

Harara Salman ta k'wada ma Ummi, kan tace
"yanzu sai da kika fad'i ma mutanan gidan mu
kika huta koh?

Allah ban san yayi6e ni.

Hararar itama Ummin tai mata,"arziki na binki
kina guduwa,kowa yazo kice bai miki ba,ki mayi
karatun ta nut'su wallahi,dan aure zanyi ni ba
jira..

"Keai Kowanne dan chaburos ma yazo Ummi a
shirye kike, toh ba dani ba.

Yankan farcen Ummin ta bari tai hanyar d'aki
tana fad'in"sai kiyi ta zama kar kiyi aure,har
mahadi ya baiyana.

Cikin kuluwa zatai magana sai ga Mama ta fito a
d'aki, ashe d'uk tana jin su, "toh k'wa maza ki
wuce ki je tun kan na sa6a miki,daga yau na
d'aina zuba miki ido ba fus bare ass Salma...

Yarinya sai taurin kai,ace koh kishin yadda y'ar
uwarki take shiga take fita da y'an k'wabai ba
kiyi?

Toh na gaji da gafara sa dan ban hangi
kaho ba...

Maza ki shiga daga ciki ki g'yara ki
wuce...

Kai kasa Salma tace "toh..

Ita kam tana
mamakin halin Mama har kullum akan su,sai dai
tana tuna Ja'afar tuni taji tana da muradin
fita,tunda wanda take danshi bai ma san tana yi
ba.

G'walo Ummi tai mata,kan tai waje tana sai ta
fito.

Bata aune ba taji mama a d'akin nasu, bani waje
ki ga,da kaina sai na g'yara ki...

Baki sake take k'allon Maman,aikwa ta zage ta
hau cha6a ma Salma k'walliya irin wacce bata
ma san mama ta iya ba.

Fad'i take "na rasa gane wace iri ce ke
Salma,arziki na binmu kina zura da gudu,d'uk
wani buri da na sa kanki kin rushe shi, in banda
haka a jiya kad'ai kina ga irin bajintar da Ummi ta
shigo dashi daga gun isma'il yake ko wa?

"Haba k'alle ki a madubi man,san kowa kin
wanda ya rasa...

Tana yi tana g'yara mata
d'aurin dank'wali.

"Maza ki fita kan Abban ku ya dawo ya hana
ruwa gudu..

Kai ta daga zata d'au hijabi,da sauri Mama ta
warce, "g'yale zaki sa matar Malam,koh a
Shari'ar a haka ake son a ganki,ta ina za'a yaba
in kin maka hijabin?

Toh ba walima nace kije ba..

Kai ta k'ada, ta zama tamkar rakumi da akala,sai
yadda mama tace.

"A'a, ko ke fa,k'alli kanki a madubi ki ga man,ai
da banbanci, maza je ki...

Kai ta kara k'ada
mata, har zatai waje da sauri Mama ta kara
kiranta.

Turare ta fesa mata,kamar tace ba k'yau
mama,sai dai taja tai shiru.

"Ki murmusa man Salma,haba..murmushi ma ado
ne ga fuskar Y'a mace...
Chapter 4 · 0% Book details