← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 29

Sashe 21

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hauka kenan wannan, dan
koh a musulunce Salma ta haramta a gare ka..ta
haramta har abada,dan kai kam ka nuna mana
bazaka ta6a iya rike aure ba, saki tamkar wasan
yara?

Itama waccan wai ka mata saki uku?..

Toh
koh aure Salma tayi na fad'a maka ta haramta a
gare ka har abada,kaje kaci zuciya.

Da gudu
Salman ta tashi tai d'aki tana kuka..

"Haba
Alhaji, abin bai kai haka ba,kuskure ne kowa yana
iya tafkawa a rayuwa..

Anji bai k'yauta ba,amma
kar hakan yasa kai mishi baki,kai hakuri.

"Hakuri
shine ya biyo ni yanzun nan..

Wace iriyar
haukace wannan kamar a jahiliya?..

Wani yai
mishi sakin?..

Haka Ja'afar naji na gani yai waje
yana waiwayen dakin da Salma ta shige yana
hawaye.

Tun daga ranar duk suka zama sakwa-
sakwa, barin Ja'afar da baida kuzari,ga Abba ya
sako shi gaba ta ko'ina..

Dan har gida iyaye
Bintu suka zo sukai ma Abba rashin k'yauta wa
akan yadda bayan saki uku sai da aka
kumburawa ya'rsu fuska,harda ikirarin
koto,dak'yar aka basu hakuri kan suka debe
kayanta, ranar Abba yayi takaici har yaji ina ma
da ya barma Umman shi Ja'afar,kila da baici
karo da bacin ranshi ba.

Sai dai yace kayan
Salma koh sama da kasa zasu had'e ba mai diba,
ashe ma in ya bari aka diba sun rabun kenan...

Ja'afar mat'sala.

Anyi ban baki, Abba yayi fad'an
ya dawo lallashin amma Ja'afar ba sauki,kawai
sai Abban Salma yace a rabu dashi,dole in ta
tashi aure zai bari a diba da kanshi.

Kullum ta
Allah yana kan jelar gidan su Salma,a wata guda
har kama ya sauya,ba aski,ba g'yaran fuska,ya
zama tamkar zararre.

Sosai Abba yake tausaya
mishi,Mama kadai ke shafawa idonta toka ta
hana ya ga Salman,sai dai a bashi Miemie, haka
zai gaji har ya tafi,sai dai tai ta ganin text na ban
hakuri,gobe ma zuciya zai dawo. ***************
*************** Rayuwa irin ta kunci kam sun
ganta a wata hudu da ta gabata.

Salma ta
saduda sosai akan Ja'afar,dan har yanzu shi
yana kan bakar shi.

Sam in ka ga Salma ta
sauya,ta dawo shiru shiru sosai,kullum zaka
same ta a daki,koh ta dukufa tunani, koh tana
k'allon Miemie tana hawaye.

"Salma...

Gefe tayi
da sauri da kanta tana goge hawayen jin
maganar Mama akanta.

Dole yau ta kawo
karshen matsalar nan.

Zama tayi a gefen gadon
tana kare mata kallo.

"Rayuwa fa kullum sauyi
take Salma,amma banda taku, ni dai ban ta6a cin
karo da kulafucin D'a namiji irin naki ba, wata
hudu ba kwana hudu bane Salma..

"Lokaci yayi
da za ki cigaba da rayuwarki ki manta da kashin
Ja'afar..

Ki d'auka Rabon Miemie kawai ya had'a
ku,ki manta da rayuwar da,dan ta wuce,ki
fuskanci zahiri a rayuwar gaba Salma..

Fad'a
Mama ke ta mata tana kuka, taya zata mance
Ja'afar?..

Taya zata mance zaman su?..Soyayyar
ta da Ja'afar had'i ne na Allah a ganinta ba wai
wani rabon Miemie ba...

In har Ja'afar na bata
haushi bai wuce yadda ya dankara mata saki ba
ba ji ba gani,amma bacin hakan,tabbas bata da
sama da Ja'afar a zuciyarta kawo iyanzu..

"Nasan da kin gama iddar ki sarai...

Da sauri ta
k'allo Mama da t'sananin mamaki, kai Maman ta
kad'a mata.

"Tunda ki ka zo gidan nan ina
fuskance dake Salma,kin gama iddah tun wata
uku da suka wuce.

Kasa tai da kai tana goge
hawaye,tasan Mama gaskiya ta fad'a, dan
shayarwa bai hanata period ba..

"Nasan ma
hakan ne Salma,yanzu abinda nake so dake
shine, "Dole ki fara fita,dan saki ba takaba bace,
bazai yu kiyi ta zama a gida ba kamar matar
kulle,tun yanzu zaki fara fuskantar cigaban
rayuwa,bana son musu koh taurin kai Salma a
zuwan nan daga gunki, dole komai nace kiyi kiyi,
kina jina koh?.

Shikenan kuma,ta faru ta kare,wai
an ma mai dami daya sata..

Shikenan ta shiga
sahu,yanzu sai jiran bazawari..

Kuka ta sa mai
sauti,yi take ba kakkautawa,har ta kular da
Mama ta bar lallashi ta hau sababi.

Dole kam in
dai ta yadda da K'ADDARA ta maida komai ba
komai bane..

Dole ta daina yaudarar
zuciyarta,tana biya zancen Ja'afar a kullum akan
tashi ce shi kad'ai..

Hannu tasa ta share
hawayenta,kan ta g'yara zama.

"Na shirya bin
umarnin ki Mama matukar bai sa6a shari'a ba..

Baki Maman ta washe, "Koh ke fa,yanzu naji
batu,ko ke fa Salma.

Kasa tai da kai tana
murmushi, sosai taga farin cikin Mama.

Washegari da dare bayan Abba ya dawo taje
gunshi suna zaune da Mama,yai mamakin
sauyawarta faradd daya,shima sai murmushi
yake mata.

"Abba..

Zama ya g'yara da murmushi
ya amsa.

"Abba makaranta nake son shiga
dama...

Da sauri Mama ta kallota, ji zata kwafsa
musu kuma,wai makaranta?

Baki ya washe dan
murna.

"Toh Salma,kinyi tunani mai k'yau, Allah
yasa a shiga a sa'a.

Kai kasa tace "Amin Abba...

"Anjima ina son zan k'waso akwatina na a gidan
Abban Miemie koh da y'ar makota ne..

Kai ya
kad'a mata "A'a,ki bari zan ma shi Ja'afar din
magana zai kawo miki har gida.

Sosai sukai fira
Mama na jinsu bata ce kala ba,tana shiga d'aki
Maman ta bita.

"Ya zaki min haka Salma?..

Wace
makaranta kuma ana zaune lafiya?..

Shiru tai sai
da ta gama kan tace ba abinda karatunta zai
tsare mata,tai hakuri tasan zai mantar ta wasu
abubuwan.

Ba dan taso ba ta yarda.

Ta gama da
Mama, saura Ja'afar.

By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:25 AM - Queen Safiyyert馃憫: A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
33_Washegari Abba da kanshi ya samu Jafar din
a shago,duk da yai jim,daga baya ya tuna da
wannan ne damarshi na ganin Salma a yau dan
tuna mata da alkawarin shi.

Da yamma k'wa
yasa Garba ya k'waso mata akwatinan ta da
sauran sabbin kayanta marar dinki.

Da sallama
ya shigo gidan, ya k'wa taka babbar sa'a Mama
bata nan.

T'saye yayi ganin Salman t'saye a
gaban famfo Miemie na mata kukan kunu tana
dauraye murfin feedern.

"Sam baki da jimirin
yunwa Miemie,kimin hakuri yanzun zan...

Itama
shirun tai dan jin sallamarshi.

Da dan rarrafe da
tafiyar da batayi kwari ba ta nufi gun Abban da
murna.

Ganin Miemien ne yasa shi dawo da
hankalinshi kanta,sama yai da ita kamar kullum
suna dariya.

A hankali ta rufe idonta tanajin
zuciyarta na bugawa da sauri,kusan wata 2
rabonta da ta sashi a idonta,jin takunshi na
kusanto ta yasa ta juya da sauri tare da had'iye
hawayenta.

Ya sauya mata,duk ba g'yara, har
wata kasumba ya had'a ta dole ta rashin g'yara
fuska.

Da t'sananin murnar ganinta ya karaso sai
washe baki yake,da sauri tai baya ganin abinda
yake shirin yi tai gun taburma ta d'akko,sai ya
bita da kallo baki sake, tabbas Salma batai
kewarshi kamar yadda ya mato a kewarta ba..

Koh irin d'aukin nan na ganinshi t'sawan lokaci
haka bata yi.

Dan dukan da Miemie take mishi ne
yasa ya kallo ta,da hannu take nuna mishi kan
feedern dake hannun Salman.

Kan taburmar ya
nufa tare da zama,so yake sai ya fassara
yanayin Salman,shi yasa yake ta k'allonta.

Feedern ta mika wa Miemie tana dan satar
kallonshi kan ta kau da kai tace "Ina wuni..

Shiru
yai mata,sai ta dan kalloshi cikin ido,shima ita
yake kallo,bazata iya kallon kwayar idonshi
ba,zata chaza mata matsala,da sauri ta kara
dauke kai tana maimaita gaisuwar.

"Mey yasa
kwana biyu ba k'ya d'aukan kira na Salma?..

Ba
k'ya ban amsa koh na miki text?..

Gefe ta kara yi
da kanta tana kallon wani waje, kan tace "Ban
gani ba ne..

Da mamaki yake kallon yadda tai
maganar cikin nuna ko'in kula.

"Salma kin daina
so na yanzu koh?..

Yadda yai maganar yasa jin
wani iri da dan tausayinshi,da jihadi ta juyo ido
cike da kwalla.

"Ya Ja'afar, ya dace mu fuskanci
zahiri fa yanzu,mu daina yaudarar kan mu dan
komai ya afku..Dole nai aure ka sani,ban maka
alkawarin zama ba aure ba,bazan maka alkawarin
kin kula wani ba..

Yanzu haka karatu zan
koma,ka d'auka rayuwar da ta shud'e a mafarki
muka yi ta, yanzu mun farka...

Dole akwai cigaba
a rayuwa..

Kai hakuri, amma bani da alaka da
daukan kiran ka yanzu,ka manta Salma dan
Allah,mu fuskanci rayuwar gaba..

Kai ta kautar
tana goge hawaye, shi kam k'allonta kawai yake
ba koh kiftawa.

"Ke nan kina nufin son da nake
miki karya ne?...

Soyayyar mu hasashe ce
Salma?..

Zaman mu da rayuwar auren mu wasa
ne?..

Kina nufin Miemie ma mafarki ce?...

Da
fusata yake tambayarta,kai kawai take girgiza
mishi tana hawaye.

"Ba haka nake nufi ba..

"Toh
mey ki ke nufi?..

Shiru tai tana cigaba da kukan
ta,sai ya kada kai cikin takaici.

"Salma kin d'aina
so na kam..

Girgiza mishi kai tai "Ina sonka Ya
Ja'afar, har karshen rayuwata..

Abu daya nake
son ka gane,yanzu komai ya sauya,alakar Mimi
ce kawai ta rike mu...

Ka cire son zuciya aciki,
dan bazan iya haramtawa abinda Allah ya
halasta min ba..

"Assalam Alaikum, wannan
akwatunan fa a zau...

Tsaye tai ba tare da
karasawa ba, kai kasa ta amsawa Mama
sallama,ciki Maman ta karaso,ya gaida ta kai
kasa,duk shiru sukai ba mai magana, sai muzurai
Mama take ma Salman kan ta shiga daga ciki.

Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga ciki,a hankali ta
sa kanta a kan katifa tana hawaye.

Ba dan yaso
ba ya tashi yai fita,tare da shigo mata da
akwatunan ta.

Har zauren Mama ta bishi ta sa
sakata tana sababi kan tai gun Salman.

"Wai ke
baki da hankali ne Salma?..

Meye had'inki da
wannan da har zai shigo cikin gida ki bashi
taburma, har ki zauna a gabanshi kina wannan
shashancin cin?..

Mey fa rabawa(K'ADDARA) ta
raba ku har abada.

Shiru tayi har Maman ta
gama tana ta kok'arin shanye kukanta, ta sani da
koh tayi bayani Mama bazata gane inda ta dosa
ba.

"Kiyi hakuri bazan sake ba.

Kai ta k'ada tuni
har tai laushi.

"Ina kuje miki yaudara irin ta D'a
namiji ne Salma,gaba in kina mishi haka sai ai
abin kunya.

Shiru tai tanajin wa'azin Maman
kawai.

G'yale ne kusan kala 5 had'add'u,tana
washe baki ta fito dasu daga leda.
Chapter 21 · 0% Book details