← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 29

Sashe 3

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da
Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar
d'inta.

Ganin haka yasa yai mata sallama tai
gida..

A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa
wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar
d'inta yau.

Sai murmushi take saka cike da
kunya ita kad'ai kamar yana ganinta.

A haka har
Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata
gami da had'a rai.

"Yanzu Ummi kinyi dai dai
kenan?

A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale,
"da nai miki mey?

Iya jaraba..

Kai Salma ta k'ada
kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar
yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari
muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma
koda wasa baki fad'an ba?

Allah kin ban haushi..

"Mtsww..

T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni
Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma
K'anwar ta.

"Na zata wani abin kirkin ne wallahi,
toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken
shi?..

Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh..

A
tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji
Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan
koh?

Yara kamar masu ganin hanjin junansu?

Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin
tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da
kunya sam wallahi..

A y'atsine Ummi ta harare
ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan
uban d'acin ran kike wannan kumfar
bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama
abga in dai Ja'afar ne....

"Ke Ummi...

Bana son
fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki
ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki..

Maza bata hakuri.

Tana chunno baki ciki ciki ta
bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen
bak'in ciki.

"Toh fito ki biyoni..

Mama ta nuna ma
ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar*
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 20
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
7_Washegari ma ta fito zata makaranta sai gashi
shi da abokinshi Garba suna tafiya.

Ido ya kura
mata ganin tai kasa da kai tana murmushi.

Sai
ya k'ada kai suka karasa,cikin sanyin murya ta
gaida su,Garba kad'ai ya amsa,shikam Ja'afar
k'allonta kawai yake yana murmushi, kamar mai
son sai sun had'a ido.

"Malama Salma fa kar tai
latti a mata bulala abokina..

Kasa ta kara da kai
tana dan dariya, shikam gogan sai binta yake
kawai da k'allo,kan ya nuna mata hanya kan wai
su rakata hanya.

Ba musu ta wuce suka
jera,Garba sai shakiyanci yake zuba
musu,murmushi kad'ai ne nasu har suka zo bakin
_gate_ d'in islamiyar.

Ka'ro na farko suka k'alli
juna cikin ido,da sauri ta K'awar da kanta tana
murmushi, shikam harda k'ada kai, tuni Garba ya
harbo jirgin nasu,sai ya hau shafa ha6a yana
k'allonsu,musamman abokinshi da yace bai san
so ba..

Hannu Ja'afar ya kai aljihu yana lalube,ita
kam sai ta hau satar k'allon shi ganin mey zai yi.

Da mamakinta k'wa sai gashi ya fito da naira
ashirin yana mika mata.

K'alloshi tai tana kunshe
dariya,sai ta k'ada mishi kai, "Kud'in tara ne fa
Salma, ki k'ar6a ki sai hambididi...

Dariya Garba
ya fara harda rike ciki,itama wacce take rikewa
ta fito fili, sai ta sa hannu a baki dan rufe sautin
ta..

Shikam Ja'afar kawai sai ya hard'e hannu
yana K'allonsu, musamman Garba yadda yake
k'yak'yata dariya.

Shikam ba kasafai ya iya
dariyar keta ba irin ta Garba,shi yasa wataran
yakan kularshi a abu.

"La Malam Ja'afar......

Gaba d'ayan su suka juya k'allon mey magana.

Ja'afar take k'allo tana murmushi halamar jin
dad'in ganin shi, shikam tuni ya had'e rai yana
k'allon ina ma ya santa.

Kamar tasan mey yake
tunani tace *"Bintu*(Na Rufaida Omar) ce,dalibar
ka a day...

Salma ya k'alla wacce itama ke kallon
Bintu,kan ya k'ada kai, "toh Bintu..

Salma Bintun
ta k'alla jiki a sanyaye ganin ko in kulan da
Ja'afar ya mata,"shiga za kiyi ne Salma? kai ta
kada mata, jiki a sanyaye tai gaba Salma ta daga
musu hannu halamar sai anjima tana murmushi.

Da k'allo ya bita cikin wani yanayi, da ko shi
kanshi bazai iya fassara wa ba.

Kai ya k'ada kan
ya k'allo Garba wanda k'wachokam ya maida
K'allonshi kan abokin yana dariya kasa-kasa.

Harara ya maka mishi kan ya juya,sai k'wa
Garban ya kara sa dariya yabi bayanshi.

"An
fad'a tarko makal ana hura mana hanci,sai anyi
magana kace wani "mey nene so?

Ni ban sanshi
ba..

Karyan kawai,koh makaho ya laluba yaji ka
afka so ai yanzu kam.

Chak!

Ja'afar ya t'saya
tare da juyo wa gun Garba.

"Mey kenan haka ke
nufi?..

Harara Garban ya k'wada mishi kan
yace"kar ka maida ni yaro fa malam,kana nufin
baka san kana son Salma ba ko mey?..

K'allonshi
kawai Ja'afar ke yi cike da mamaki,a hankali ya
furta *"SO"*?...

Hararar shi Ja'afar ya kara,gani
yake kamar ya raina mishi hankali ne.

"Kaga
Malam kawai kai saranda haka,tuni tun yadda ka
ke ta yawan fad'in Salma nasan a rina,ka bar
wani k'wane-k'wane.

Shi dai Ja'afar ya
t'sunduma tunani maganar Garba,wai So?

Salma
kuma?. *By* *Feenat Ja'afar* 庐NWA.
9/29/16, 8:56 AM - Queen Safiyyert馃憫: [7/21, 12:28 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
8-Har Ja'afar yazo k'wanciya yana tunanin
kalaman Garba,tabbas biri yaso kama da mutum,
dan yana jin sauyi tun ranar farko da ya dora
idonshi a Salma bayan dawowar shi.

"So"...

Ya furta a hankali, murmushi yai kan ya
k'ada kai,dan yana da aiki a gaba,dan bai san
kom ba game da lamarin.

Tun daga ranar ya zamto kusan kullum da
yamma yakan raka Salma islamiya,koh da yana
shago zai zo ya ganta kawai,hakan na sashi
nishad'i, yau da gobe har ta fara sakin jiki dashi
a karo na biyu.

Sai ya zamana itama in bata ga Ya Ja'afar a
ranar ba batajin dad'i sam,haka zata k'wana
sukuku.

Shirye-shiryen bikin Aunty A'i suke,duk sun shiga
_busy_.

Da yamma sun fito bak'in shagunan su Abba
siyayyan kayan fitar biki, tasan kuma d'uk layin
ba inda ya kai shagon su Ya Ja'afar kawo kayan
k'yali, amma da tayi magana Ummi sai ta tanka.

Kai duk'e yana duba takaddu,kamar
_papers_,chak ya t'saya da abinda ya yake yana
murmushi kai duk'e, ajikinshi ya ji kamar Salma
na kusan shi,itama dai satar k'allon shi take,tana
ganin zai dago tai sauri ta juyar da kai tana
murmushi.

Fara'ar shi ta karu dan hango Salman.

A hankali ta dan kara K'alloshi,sai k'wa suka
had'a ido,da azama tai kasa da kai tana
murmushi har suka karaso.

Tuni Ummi ta had'e rai ganin Ja'afar a shagon,a
takaice ta dan harari Salman ganin sai wani
munafukin murmushi suke sakar ma juna,baki ta
ta6e kan a ciki ta gaidashi tai cikin shago ta
barsu nan.
_"My_ kanwa,..

Kai ta kara duk'ar wa tana
gaidashi,sai ya k'ada kai,ya rasa irin kunyar
Salma gare shi yanzu,abu kad'an duk'ar da kai.

"Biki ya karato ba?

Kai ta daga mishi tana dan
k'allon _net_ d'in gefenshi da murmushi.

Tashi yai zuwa gun inda take k'alla ya fara
saukar mata dasu.

A hankali ta tako gun dan zabi,d'uk sun mata
k'yau.

Sai ta dan kallo shi, "malam Garba fa?

Murmushi
yai yana k'allonta, "yaje inda aka tura shi
_service_ nashi yaga gun,gobe zaki ganshi.

Kai ta k'ada, d'uk sai taji ta kasa za6a ganinshi
kusa da ita.

Kamar ya sani ya kara s'akko mata da wasu.

"Bari na tayaki za6a.

Kai kawai ta k'ada mishi tana k'allon kayan,kan
wani _purple_ idonta ya kai,a hankali ta kai
hannu zata ja shima ya kai zai d'akko shi yana
fad'in
_"purple_ zai miki k'y...

Shiru yai ganin itama shi
ta rike,ya rike rabi ta rike rabi.

D'uk sai suka k'alli juna ba koh kiftawa da wani
yanayi...

Tamkar wanda aka lika _poster_ a gun haka suka
kame da k'allon juna.

Ummi ce ta kat'se su da fad'in
"Ga nan wasu materials y'an leda Salma masu
kaman _lace_....

Shiru tai ganin wani ikon Allah,baki sake take
k'allon su,tuni Salman ta sakar mishi tai baya
tana sunke kai da murmushi tare da amsar kayan
hannun Ummin tana sunyi k'yau ba dan ta gani
ba.

Murmushi ya sakar mata shima,har yanzu yana
rike da _net_,ya rasa mey ke damun
K'wak'walwar shi akan Salma.
*By*
*Feenat Ja'afar*
[7/21, 8:05 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
9_Baki ta dan ta6e,kan a y'atsine tace ma Jafaar
d'in "mun zabi wannan, zamu nuna ma Baba sai
ya bada kud'in.

Murmushi yai yana k'allon gun Salma,itama
idonta na kusan hannunshi.

"Koh na tafi ne Salma?

K'allo Ummin tai,kan ta
k'ada kan suka yi hanyar fita a shagon,a hankali
ta dago mishi hannu halamar _bye_.

Kai ya k'ada mata shima ya dago mata nashi.

Tai k'walli da Ja'afar ta ji dad'i,har aka je gida
bata umm ba um um,sai Ummi ke ta zuba kamar
kanya, yadda zata zuba wanka a bikin Aunty A'i
har ta kule.

Da dare sai ga yaro wai ana kiran Salma.

Rai had'e ta k'allo yaron, "je kace bana nan...

Shiru tai ganin yadda mama ke mako mata
harara, "anya yarinyar nan kalau kike kuwa?

Wato
sai dai ai ta min asarar hoda da kazal a banza
ina tufka kina min warwara koh?

"Farin jini Allah ya bayar kina ma kanki bak'in
ciki?

Haka zan ta barar miki ni baki ban bare na
maida g'urbin abinda na fitar Salma?..

Maman ta k'allo da mamaki,toh rokon samari
mama take so ta fara komai?

Allah yaga ta t'sani
fita zance.

Amma ganin yadda mama ke wanke ta yasa ba
shiri tace ma yaron "yace ma waye?..

Kai ya
daga mata,"wai ince inji
"Ja'afar in kin tambaya...

Ai koh karasa wa nai
ba ta mike,tuni murmushi ya maye g'urbin 6acin
rai, da k'allo mama ta bita, kamar ba ita ce
yanzu ba.

Yau kam ga su Salma harda mit'sika hoda da
_lips stick_ har ta d'au hijab ta kara k'allon
madubi,kawai sai ta janyi g'yalen Ummi tai waje.

Shine kuwa yana jingine da gidan,wani murmushi
ta saka na farin cikin kara ganinshi a daren.

Da sallama ta karasa d'uk da ba wani haske gun
sosai,amma sai dan sinke kai take kamar rana.

Bayan sun gaisa kowa yai shiru kamar basu abin
fad'a.

Chan dai ya nisa ya miko mata ledar hannunshi.
Chapter 3 · 0% Book details