Sashe 19
A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakin Bintu ya nufa har yanzu
baida walwala sai ya tabbatar da Salma bata fita
ba,yasan Bintu kat ce,bata t'sallaka doka akan
fita,in yace A'a, toh ta hakura.
Sannu da zuwa tai
mishi tana fara'a, a ranshi yana aiyana da Salma
ce yasan sai ta cika tai fa kan ta mishi sannu da
zuwa duk akan ya hanata unguwa,amma kullum
y'ar uwarta ko ajikinta.
"Yau bayan fita ta Salma
ta fita?..
Kai zata girgiza, sai tai saurin kwa6ar
kanta, dole yadda tasa taga bakin ciki har yau
itama ta gani.
"Eh,bata jima da dawo wa ba
ai,baka sani bane?..
Hannu ya daga mata,cike da
jin haushi yace "ya isa ni,tambaya na miki kawai.
Waje yayi tana binshi da g'walo, yana yin nisa ta
tuntsire da dariyar mugunta.
Kamin cikin sand'a
tai waje jin ya zata kaya.
Ba koh sallama ya
shiga parlourn, ganan takalmin a gefen kofa
wanda ta fitar zata sa dazu.
Tana zaune tana
_feeding_ din Miemie ya shigo yana binta da
kallo,da fara'arta tai mishi sannu da zuwa.
Kekam yayi yana k'allonta ba koh kiftawa, tabbas
Salma ta fita,dan mud'in bata fita ba bazata tare
shi da wannan fara'ar ba haka,yasan kayarshi.
"Wato kin fita hankalinki ya kwanta koh?..
Ban
isa ba ashe har yau halinki yana nan baki sauya
ba koh Salma?..
Baki sake take K'allonshi da
tsananin mamaki,sai d'aure ta yake da jijiyoyinta.
Cikin nut'suwa tace "Ni fa ba inda naje tun fitar
ka,dan Allah ka d'aina tun..
Malama ki amshi laifi
kawai,kinsan nafi t'sanar musu sama da komai,
koh kina nufin Bintu karya zata miki?.
K'allon
mamaki take mishi,a hankali ta maimaita
"Bintu"..
Yaki ma bari tai mishi bayani sai
zazzaga mata yake kan bata maidashi abakin
komai ba.
Kawai sai ta sau mishi kuka,tama rasa
abin fad'i,wai Bintu ce ta fad'a mishi,wato ita ba
abin yarda bace sai kishiyarta indai kan fita ne.
"Haka ki ke ai,da kukan rashin gaskiya
Salma..sam bana son ki dawo mana da hannun
agogo baya,ina ta murna komai ya wuce ashe
albarkar ciki ne yasa ki zaman dole.
Ganin
kukanta na karuwa yasa ya fice ya koma d'akin
Bintu.
Har da bawa kura ajiyar nama,wai duk
randa Salma ta fita dan Allah karta 6oye mishi.
Tun daga ranar ya sauya mata,sam in ya shigo
sai dai ya d'au ya'rshi ya fice,itama daga
gaisuwa shikenan ta gama,dan a ganinta
wulakanci ne wannan babba.
Ga wani fi'ilin
mutunci da Bintu ta koya da kissa,kullum faram
faram take mata,harda gaisuwa in antashi.
Ta
d'au Miemie ta goya a bayanta in Baban ya
d'akko ta.
Ba karamin dad'i kwa Ja'afar din yake
ji ba,dan yana karrama mai son Miemien shi,ita
kam Salma nata ido,sai ta dukufa gun kai
kukanta ga Allah.
Dan tabbas tasan tai saken da
har mijinta yai mata mummunan tambari.
Bintu
kuwa kullum rokon ta Allah duk wani sharrin da
take nemanta dashi Allah ya mayar mata kanta.
By Feenat Ja'afar.
9/29/16, 9:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/2, 2:29 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
30_Sai ya huce kamar sati ana mutunci da ta
tambayi fita unguwa zai kicin-kicin,yace tai son
ranta,haka zata hakura tanaji tana gani,in ya
dawo kuma tasha fad'an da batasan laifi ba.
Kawai Allah ya d'aura mata wani irin hakuri,daga
Ja'afar din har Bintun ido tasa musu kawai.
A haka har Miemie tai wata hudu Salma na
zaman hakuri, musamman ga saurin fushin
Ja'afar gareta,ga tai alkawarin daina kai kara gun
kowa sai gurin Allah.
Ana haka Maman Abba ta haihu.
Ganin yau y'an mutuncin na kanshi yana zaune
ya shagala da yiwa Miemie wasa tana wage
mishi baki tana dariya.
Da fara'arta ta zauna kusa dasu tana k'allonsu.
"Abban Miemie...
K'allota yayi tare fad'in yana jinta,cigaba yayi da
wasan su.
"Inda hali dan Allah zani barkar Maman Abba yau
kwananta hud'u da haihu banje ba.
Kai ya kad'a, "wace Maman Abba?..
Da zumudin zai batta ta sanarshi makociyarta ta
unguwar su ta da.
Abinda yake ya t'sagaita yana k'allonta ba koh
kiftawa.
Tuni ya zata an rufe babin y'an tsohowar
unguwar su a gidan,ashe har yanzu tana makale
dasu.
Bazai manta dasu ba,dan sune ummul aba'isin
wargaza gidanshi.
Kai ya girgiza mata,
"Kiyi hakuri ba halin zuwa..
Baki ta sake tana K'allonshi, a gaskiya bazata
zuba ido tai ta zaman gida na y'anci ba,da takura
gaskiya.
Amma sai ta bishi da lallami.
"Dan Allah ya Ja'afar ka barni naje,nima dana
haihu fa sau biyu tazo min har suna uku,kaga ba
dad'i ace ni koh sau d'aya banje ba barka ba sai
suna.
"Sunan ma ki fidda a ranki,dan inda mu'amular
dana fi tsana,toh mu'amular ki da y'an unguwar
chan ne,kin gane ai?.
Kasa tai da kai,sosai take d'aure irin halin da Ya
Ja'afar ya tsiro mata,yanzu da ta kara tambaya
zai ce tai gaban kanta,hakan yasa tai shiru.
Shi kuma yadda yaga batai gardama ba yasa yai
tunanin zancen bai shige ta ba ne.
Miemie ya ajiye kusa da ita ya bar mata d'akin.
A hankali ta zame ta kwanta,sai ga hawaye ya
zubo mata.
Zaman gidan nan ya fara isar ta,hakurinta ya
fara karewa.
Tana ji yai ma Bintu sallama ya fice,kawai sai ta
sau kuka a hankali marar sauti.
Wato a dake ka a hanaka kuka?.
****
Tun bayan fitarshi bayan ta gama kukanta
Miemie ta fara,kukan har ya wuce kima, komai
tayi taki shiru,kawai sai ta goyata tasa hijab akai
suka fita t'sakar gida dan sanyin magriba.
Bintun na t'sakar gida tana saita abin fad'i kan
Ja'afar ya dawo tambayar Salma koh ta fita,dan
komai a k'unnenta ya wakana.
Jijjiga ta take tana yawo daga t'sakar gida zuwa
zaure da ita,tasan Miemie ba mai rigima bace,
tabbas da abinda ke damunta yau,yawan kukan ji
take kamar itama tasa kukan koh taji sa'ida.
Dak'yar ta samu tai shiru,sai ajiyar zuciya take
halamar tai bacci.
Buta ta d'auka ta shiga band'aki kenan sai gashi
kamar an hulloshi gidan,fatanshi yau ya rit'sata
garin satar fita.
Bintu ya kalla wacce ke murmushin ganinshi,sai
taunar cingam take tana kas-kas,kai da ganinta
da yanayinta kaga na mai shirin kulla wani
sharrin.
"Sannu da zuwa..
Kai ya daga mata, kamar kullum zai tambayi
Salman sai yaji bud'e band'aki.
A fusace ya kallo Bintu, "bayan fita ta Salma ta
fita?..
Ki fad'an t'sakani da Allah.
Kwai tayi kan ta fasa tare da yin kas dashi,
"Eh ta fita,mey ya faru?
Yanzun bud'e dakinta ta
shiga band'aki ka shigo.
Gadan-gadan Salma tayi kanta da butar data cika
zatai alwala anjima,kansu farga ta rot'sa mata
aka tana huci,bai isa ba ta rufeta da duka baji ba
gani,fad'i take
"Sharrin naki ya wuce bayan idona yanzu a
gaban idona ma yi..
Mari ya d'auketa dashi shima yana fad'in ta sake
ta.
A fusace tace bazata saka ba,ita kam tamkar
wawiya ta bari Salman na jibgarta,ganin da gaske
take yasa da sauri ya finciko Bintun tare da kara
mata wani marin.
Kunci ta rike tana K'allonshi, "ki sani na gaji da
halinki a gidan nan, karan nan zan d'au
mummunan mataki akanki wall...
"Ka sallame ni in ka gaji dani Ja'afar..
Dan ni tuni
na gaji da zaman gidan ka, ka sallame ni ka huta
toh..
"Haka ki ka ce?..
A fusace tace "eh haka nace..
Tuni shedan ya shiga cikin zuciyar
kowa,musamman Ja'afar da ya rufe ido tamkar
bashi ba.
"Ki je gida sai na neme ki toh...
Cikin kuka tace
''Ban isa zuwa musu ba sheda ba,dole ka bani
sheda..
Ba tare da jin komai ba mugu(shedan) yasa ya
rufe ido.
"Kije na sake ki toh..
Chak!
Taji kukan ya t'saya sai na Miemie data
tashi dan hayaniya.
Baki sake take k'allonshi fuska wanke da
hawaye.
"Ja'afar ka sakeni kace fa?..
Muryarta na
ka'rkarwa ta tambaya.
Da sauri ya bud'e ido ya dawo hankalinshi kanta.
K'allon-k'allo suke ma juna cikin rashin sanin
abin fad'a, musamman Ja'afar dashi ya furta.
Ido ta rufe a hankali, sai ga hawayen da ya
makale sun zubo.
A hankali ta bud'e idon ta k'alli Bintu.
"Allah ya biya ki da dai-dai abinda ki kamin
Bintu..
Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai
dawo gun maishi..
Jiki a sanyaye ta juya gun Ja'afar.
"Shikenan abin nema ya same mu Ja'afar..
Aure
ya kare a t'sakanin mu..igiya uku ka rusheta
Ja'afar..
Ka rushe su..
Hannu tasa ta share idonta.
"Ba ka da bukatar na t'saya maka bayani yanzu
kam,dan ka zuba katanga a t'sakanin mu.
Cikin nut'suwa tai hanyar waje ba tare da ta koh
waiwayi d'aki ba.
Da k'allo ya bita, ilahirin jikinshi ka'rkarwa
yake,ya kasa tattara kalma daya da zai ambata,
har Salma ta 6ace wa ganinshi.
'By
Feenat Ja'afar.
[8/2, 10:40 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
31_"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un..
Allahumma
Ajurni fi Musibati,wakhluf li khayran minha...
"Salma ki ce min ba gaskiya ki ke fad'a ba
Salma?..
Dan Allah ki ce wasa ki ke..
Murmushi take,wanda da zatai kukan zai fi mata
alkairi, amma ta kasa,tun zuwanta gidan Aunty
A'i ido ya kafe,tunani ya t'saya..
Dabara ta ka
re,sai kallo da ido da murmushi da yafi kuka
ciwo.
Waya Aunty A'in ta d'auka dan kiran Ja'afar,
tayuwu koh shi ya mata bayanin da zata gamsu
tunda Salma ta zama kurma.
"Ja'afar..
"Bashi bane..
Tsam tayi dan tasan Bintu ce ta
d'auka.
Da karfin hali ta tambayi in yana kusa ta bashi
man, t'saki tai mata kamin ta kashewar.
Kasa tai da wayar tana mai tabbatar da kalaman
Salma na aure babu,ya ka re.
A hankali ta sakko ta t'suguna gaban Salman
tare da dafa kafafunta.
"Salma kimin magana ba shiru ba dan Allah..
A
dunkule kika bani, dan Allah kiyi magana, shin da
gaske ya sake ki cikon na ukun?..
K'allon Aunty A'in take cikin ido,tabbas wannan
kalmar ita ta 6acewa tunaninta.
Kan ta ankara ta sau mata wiwi,baji ba gani.
"Bintu ce...
Wallahi itace..
Ban mishi komai
ba..ya raba aurenmu..
Allah banyi komai ba
karan nan Aunty A'i,ki yarda dani dan Allah, koh
su Abba baza su yarda ba...
Kamar karatun yara haka take had'a kalaman
cikin kuka.