← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yadda maman take yi bata ma san sanda abin
ya bata dariya ba.

Allah ya gama su da uwa "LASHE MONEY", har
ta fita kuwa tana murmushi, mama sai barta.

Suna t'saye gaban wata jar _CRV_ tare da
Ummi,d'uk dinsu sun zubo mata ido.

Ita kanta tasan tayi ne, fari da manyan ido kawai
budurwar Ja'afar zata fad'a mata tasan.

Doguwa ce ita dai dai misali,farin jinin samarin
zamani,fatarta a goge take mai launin Wankan
Tarwada(black beauty), tana gashi ga gashin
ido,gata fuska doguwa,gata tana da diri dai dai
so,d'uk komai ya ji ba bau ba.

Ya dace kam tai amfani da lokacinta tun yanzun.

Cikin takun da ba irin na Salma ta da ba ta
karasa gun su Ummi,ga murmushin nan dan
_beauty point_ din nan sai lot'sa wa yake.

Tuni ta kara tafiya da imanin Muzammil,har yake
ji kamar ya taro ta kan ta iso.

By
Feenat Ja'afar.
[7/22, 4:57 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN
AURANKI*
*漏 Feenat Ja'afar*.
12_Ita kanta Ummi tai mamakin Salma da
sakewar ta.

Sun gaisa da isma'il saurayin Ummin su kuma
suka zaga dayan bangaren motar,
Kusan kawai d'aurewa take tana mishi yake,
amma ita sam taki jinin saurayi mai shegen
surutun t'siya.

Hakan yasa d'uk taji ta gagu su k'auce, ga tasan
Abba gaf yake da zuwa da magriba tayi.

Kamar ance daga kanki, Ja'afar tagani kusan su
kad'an, tamkar gunki yaja ya t'saya, ga nan
wannan budurwar da ta ta6a ganin su itama tana
k'allo su,sai ta k'alli Ja'afar, kawai sai ta d'auke
kai kamar bata gansu ba.

Harda kara bawa Muzammil wani _attention_ na
daban tana murmushi.

Cikin sanyin jiki ya juya,tana dan satar k'allon
shi,a baya budurwar tabi shi tana waiwayen
Salman,ji tai kamar ta k'wada mai kira,So ba
k'arya bane Salma.

Da k'allo Ummi ta bisu lokacin da suka zago ita
da isma'il, sallama sukayi,suna kokarin jan mota
sai ga wata bakar mota ta _parker_.

Ganin su Garba yasa da sauri Salma ta daga ma
muzammil hannu tana mishi murmushi.

Ja'afar dake k'allonta ta glass din ya rint'se ido
da sauri.

Ganin zata juya yasa Garba fad'in "Salma" da
sauri.

Juyo wa tai lokacin da yake yafito Jafar da
hannu halamar ya fito.

Koh ta kansu Ummi bata bi ba tai gida.

Yake tai mishi lokacin da suke karasowa,sai dai
koh inda Ja'afar yake bata k'alla ba shi da
budurwar shi.

Cikin barkwanci Garba yace "duniya da alkawari
kuwa Malama Salma?..

Murmushi tai mishi iya
le6e, "ashe kin dawo amma koh mu sani..

Karon farko ta k'allo gun Ja'afar, idonshi k'wa a
kanta girrr...ba koh kiftawa.

Da sauri ta d'auke kai daga kanshi.

Gaidasu tayi,budurwar na mata an dawo.

Lafiya?

A ciki ciki ta amsa,Garba yace "yaushe a gari?

An gama lafiya _hope_?

Da mamaki take k'allon shi,yanzu dama da
wanda zai ce bai san y'an makaranta sun dawo
ba?

Kawai dai sai ta maze, "yau kusan satin mu da
dawo wa.

K'allo Ja'afar d'in Garba yayi,kan ya dawo da
K'allonshi ga Salman.

Ba wannan dawowar ba,yau k'wana uku da
zuwan mu K'anwarki tace mana kinyi tafiya...

Da sauri ta dago kai da mamaki,tana k'allo gun
Ja'afar d'in ya d'auke kai.

Garba yaci gaba, "zuwan mutumin kenan daga
Zaria yace sai ya zo ya ganki ya miki murna,ashe
ke har kin ma fice a garin.

Batta bakin magana,dan bata san amsar basu
ba,amma Ummi tana mata daya a rayuwa..wai tai
tafiya?

"Ga nan mutumin jiya har sururu yake yaganki da
dare ina mishi t'siya, ashe ke ce.

Kai ta daga,kan ta kara k'allon Ja'afar, d'anna
wayarshi yake kamar bai wajen.

Cikin wasa Garba yace "toh ni zan gabatar mata
da ita ko mey da kai mikis?..kasan ba kunya zan
ba ni.

Murmushi budurwar tayi kai duk'e, dan sam bata
ga fuska gun Salman ba.

K'allon Ja'afar din take,yayin da yake k'allon
Garba yai shiru.

"Toh,mu bama sanya, sai ya juyo gun Salman,
"Salma ga nan budurwa,kuma matar...

Da sauri
ta rint'se ido,kan ta karasa da "Ja'afar"...

Na
sani Malam Garba...

D'uk ido suka zuba mata har Ja'afar baki sake,jin
shirun yasa ta bud'e ido akansu,yadda suke
k'allonta tasan tai su6ul da baka...

Cije le6e tai,amma ta bada kanta wallahi....

Dariyar keta Garba yasa harda k'yak'yatawa, sai
ta dago tana k'allonshi.

Sai da yai mai isarshi kan ya k'allo Billy,
"Haba,Yanzu na ji batu,ni fa naga kowa yana
sassahan kamshi,ashe-ashe...uhm uhm
_Jealousy_...

"Toh wannan Matar Garba ce bata Ja'afar
ba,sassauto madam.

Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta,har
batasan sanda murmushi ya su6uce mata ba.

A kunya ce ta k'allo Billy,sai ta mat'sa kusan da
ita kan tace "sannu da zuwa...

Dariya suka sa mata banda Ja'afar da ya dan
dara,idonshi kir a kanta,bazai iya fassara mey
hakan yake nufi ba, shin Salma na son sa da
kishin sa ne koh mey?

Ita dey sai dan satar K'allonshi take,amma
bazata iya fassara ina ya dosa ba.

Mota su Billy sukai suka barsu,ga nan magriba ta
gabato,gaidashi ta kara yi itama ciki
ciki,t'sayuwa ya g'yara kan ya amsa,tare da mata
murnar kammala karatu,shiru ba mai cewa
uffan,kowa miskilin kanshi,kawai sai sukai
sallama kan gobe zai zo.

Tana shiga gida dan takaici kasa ma Ummi
magana ta cikin fad'a."yanzu Ummi kina k'yauta
min kenan a rayuwa?

Mey Ya Ja'afar ya t'sare
miki ne ki ka ki jinin shi?

Rai ta had'e, kan tace "oho,kawai bai min bane...

Ga nan sakon daga Muzammil,kinga in da ake
harka ai...

Kai ta k'ada dan takaici tai d'aki batabi koh ta
kayan ba.

Washegari dan kalata sai ga su sun dawo, ana
la'asar, mama ta fita unguwa.

Ado Ummi ta ciwo da tafi na jiya,sakare tai ganin
Salma koh mot'sawa batai ba.

"Koh ba zaki bane Salma?

A tunzure tace "ba zani ba..

Baki Ummin ta ta6e,kan ta daga kafada,
"mat'salar ki ce wannan kuma...

Sai tai waje.

Aiko yaro sau biyu ana yi daga waje daga
Muzammil amma fur taki fita.

A ka'ro na uku ne yaron suka shigo da Mama da
ta dawo daga unguwa.

Dole ta tashi badan rai naso ba,sai dan ganin
Ummi ta shigo ta had'a ta da Mama kan taki
zuwa gun Muzammil.

Tana had'a rai ta fito,sai dai da mamakinta taga
Ya Ja'afar t'saye yana aiken yaro kan tazo.

Da
sauri ta koma cikin zauren kan ya ganta.

Jim tai kad'an bayan fitar yaron kan ta fito,kanta
t'saye tai gun Ya Ja'afar, kan tace ya bata minti
biyu dan Allah.

Kai kawai ya k'ada mata,sai tai gun su Ummi,a
mutunce suka gaisa,kan tace da Muzammil
sakon shi sai gobe..

Bata jira amsa ba tai gaba.

Shi kam Ja'afar k'allonta kawai yake,amma tuni
har yazo wuya.

Tabbas dole ya bayyanawa Salma yau ranshi ba
sai an k'wana ba,dan wannan samarin tsaf sai su
iya kasa shi yana k'allo.

"Bissmillah, muje zaure...

Bai yi musu ba yabi
bayanta.

Har ya dan saki fuska, dan sam ba kaunar zaman
ta a layi yake ba.

Bayan sun gaisa yake bata labarin abinda yasa
bai je mata ba.

"Kinsan Mamana tana a Zaria ne,sun rabu da
Abba tun ina dan shekara biyar,hakan ya zamana
Abba ya k'ar6e ni a dalilin tai aure,nakan kai
mata ziyara haka,sannan dan ita na zabi zuwa
Zaria karatu.

A _time_ d'in da za ai _visiting_ aka aiko bata
lafiya,chan naje har t'sawan wata uku.

"Taji sauki sosai,har tana ta fad'an na koma
bak'in aiki na,ana haka y'arta K'anwata ta dawo
sun gama makaranta,hakan yasa na tuna da
Salma..

Nan nai shiri na dawo,duk dan na
ganki,sai aka samu akasi, Ummi tace kinyi
tafiya...

Shiru yai kai duk'e, itama tai tsam tana
sauraren shi.

"Salma"...kai ta dago ta dan k'alleshi, shima
idonshi a kanta.

"Yanzu kam lokaci yayi da zan
sanar ki wani sirri,sai d'ai ina fatan wani bai
rigani yad'awa ba...

"Salma"...

Cikin wata siga ya fad'i, kan yace "na
jima ina dakon son ki azuciyata,tun ma kan
Salman tasan itace...

K'allonshi take baki sake,shikam ya zage sai
tona sirrin ranshi yake a gare ta ido bud'e..

Dad'i, farin ciki har ya kasa misaltuwa a gun
Salma,So d'aya ne, tasan Ya Ja'afar tai ma.

By
Feenat Ja'afar.
9/29/16, 8:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 13_Har
yai shiru ita kam idonta na kanshi,kan dafa bisani
tai kasa da kai cike da kunya,kawai shima sai ya
zuba mata na mujiya yana murmushi.

Magana
suke jiyo wa kasa-kasa,duk sai suka zuba ma
kofar ido.

"Ba mutunci ace kowa yana wuce wa
yana ganin ku a t'saye a titi, gaba na fad'a miki
ki nemi koh zaure ne koh cikin gid...

Shiru Abban
yai dan ganin Ja'afar a zauren da Salma.

D'ukawa ya danyi kan yai ma Abban sannu da
zuwa.

Cikin sakin fuska Abban ya amsa,Salma
ma ta mai kai duk'e.

Sim-sim Ummi tazo ta
wuce,dan duk iskancin ta tana bala'in tsoron
Abban su sosai.

Yana shiga gida shima yai mata
sallama da alkawarin gobe zai zo dan jin amsar
shi.

Da t'sananin farin ciki ta shiga yau, haka
dashi ta tashi.

Tun jiyan Ummi ke ci mata kunu,
tasan kuma d'uk akan Muzammil ne,shi yasa koh
bi takanta batai ba.

Washegari tun kan Ummi ta
shiga wankan yamman ta na kullum Salma ke
gaban mudubi, sosai take k'yali, yau d'aya ta
bata lokaci dan Ja'afar d'inta.

Ummi da tun dazu
ta fito tana jira ta ta6e baki, ''kiyi kare ni ki ban
waje na zauna Malama...

Juyo wa tai da tana
yage mata baki, "dan Allah Ummi nayi k'yau?..

Bar zancen wasa.

Baki ta ta6e kan ta juyar da
kai gefe, "oho miki ni kar ki daman.

Murmushi tai
kan ta tashi ta bata gu.

Bincike ta fara,a babu
babu Mama kala 5-5 ta musu kayan _candy_ na
ke ce sa'a, ciki masu ruwan _purple_ ne kusan
duk.

Cikin nishad'i ta ciro attamfa wata mai
_purple_ da rat'sin _yellow_ riga da siket,
murmushi tai dan tuna wa da kalar da Ja'afar
yafi so kenan.

Tunda ta zura kayan ta nad'a
d'auri take bin kanta da k'allo a mudubi ta gefen
Ummi.

MashaAllah tai k'yau, gashin da ya fito ta
kasa take turawa cikin dank'wali,ta kai dubenta
ga Ummi wacce sai ko'k'arin fiddo nata take tabi
dank'wali ta kansu.

Murmushi kawai ta
mata,tasan da tace ta mayar su ciki ma a iska.
Chapter 5 · 0% Book details