Sashe 29
A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kafad'a ta mak'e tare da lafewa a
kafad'ar Abbanta.
Mota ya shiga tare da fitowa
da leda cike da shopping na chocolate da ice
cream..
Alawa daya ya fito dashi tare da fad'in
"Zan baki sweet fa,zo mu gaisa mana Miemie..
Salma ta kalla kamar mai jiran umarninta.
Murmushi tai mata tare da daga mata kai,abin
kai sai taje ba musu,yau sai ga Miemie harda ma
Alhaji dariya.
Da zai tafi hannu ta daga mishi
tana mishi bye-bye tana dariya.
Duk sai Alhajin
ya bata tausayi Alhajin,har Ja'afar na daga mata
gira halamar tambaya.
Marairaicewa tayi tare da
shagwa6e fuska.
"Y'arka ta rabani da Alhajina
shikenan kunji dad'i..
Harara ya sakar mata
kamin yace "toh bishi, Allah yai ma y'ata albarka
yarinya mai kishin Abbanta koh?
Kai ta daga
mishi tana dariya,da murna ya shillata sama ya
chafe suna dariya.
Gwalo yai ma Salman,sai
Miemie ma ta hau mata,tuni ta fara chunno
musu baki suna cikin shagwa6a.
By Feenat
Ja'afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 11
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 46_Ba
sauran jira,dan karara suke nuna ma fitsara a
gidan Mama, su Ja'afar abin nema ya samu,ba
guntun fulako,ba shiri ta bama Abba shawarar ayi
a mayar da auren nan.
Wata daya aka sa suka
sha biki kamar ba gobe..
Nan take jin labarin
auren Bintu a gidan mai mata uku,tana chan ta
zama bora.
Su Maman Abba duk sun halarci bikin
nata,nan take tsurkuta mata labarin Maman
Ummi kan ranar ta fita gantali miji ya
dawo,bayan ta dawo yace ta nemi inda dare ya
mata,karshe dai akai saki.
Murmushi tayi,tasan
Allah ba azzalumin sarki bane,dole yadda taga
tasku Maman Ummi tagani itama.
Jingina yayi a
jikin bango yana kare mata kallo,fuska rufe ruf da
g'yale,murmushi yayi dan tunawa da daren
farkonsu a wanchan gidan.
Karasawa yayi tare
da g'yaran murya kad'an yana leka fuskarta.
Zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya.
A hankali
ya kai hannunshi tare da daga mayafin da ta rufe
fuskar.
Tsam yayi yana kallonta ido cikin ido,tuni
ya marairaice mata fuska,kuka fa?..
Hannu yasa
yana share mata wani na zubowa,duka ya hayo
gadon tare da janyota yana shafo bayanta
halamun tai shiru.
Sai da tai shiru kan ya dago
kanta.
Ido suka zuba ma juna ba koh kiftawa.
Chan ya nisa cikin murya kamar mai jin bacci
yace "Kin tuna kalaman da na ta6a turo miki na
karshe cikin text message dina kuwa?..
Tunowa
ta fara,sai yai murmushi tare da zamewa kan
katifa da ita a kafad'arshi.
Ajiyar zuciya suka
sauke tare da kamo y'atsunta.
"Na ce miki _" a
heart dat truly loves never loses hope..but
always believes in d promise of love,no matter
how long d time and how far d distance,at d right
time,love will fine a way".._ "Hope kin yarda da
maganar ba wai soki burutsu Masoyinki bane?.
Kai ta daga mishi halamar ta yadda,tunda ga nan
K'ADDARAR wani zama ya kara had'a su waje
daya.
Yau kam ya gama gasa mata jiki da
d'anyun kalaman da ya tanadesu kawai da
Salmanshi,fatanshi Allah ya kare sa6ani a
tsakani.
Washegari da t'sant'sar farin ciki suka
tashi,suna kitchen had'a break fast sai nannan
yake da ita.
Tashin Miemie suka ji tana kiran
Aunty cikin kuka taga sabon waje.
Ganin iyayen
waje daya ita kanta sai binsu take da kallo,
mot'si kad'an ta kallesu,kamar wacce bata so su
rabu da juna suyi rayuwarsu tare. ********** Yau
ziyara aka fito ta sallah ita dasu Ummi, Sun zaga
duk inda ta tambaya saura gida 1 taga sun
karkata zasu shiga gidan kawunsu wanda jiya
sunje.
Ja tai ta tsaya tare da ce musu su shiga
su fito dan yau bata tambayi nan ba.
Murmushi
Aunty A'i tai tare da kad'a kai,a lalle kullum
Salma hankali na kara zuwar mata.
Tuni Ummi
kam tai gaba tana t'saki.
Tana nan tsaye
kawunsu ya fito a gidan,bayan sun gaisa yace
mata ya bata shiga ba ga y'an uwanta suna ciki?
Kai a kasa tace "Abba ban tambayi nan ba
ne,dan jiya munzo yini.
Murmushi yayi na jin
dad'i, "hakane kinyi tunani mai kyau,Allah ya miki
albarka.
Kai ta kara kasa kamin ta amsa.
Kud'i
ya ciro daga aljihu ya kirga dubu ya bata,dan
sosai Salma tana wa mutane bazata,yana
matukar son mutum mai gyara kuranshi.
"Sannu
da jira uwar y'an ka'ida...
Juyawa tayi daga
kallon wani a mota sun tsaya da Kawunsu da ya
wuce yanzu,sai dai kan ta tantance su Ummi sun
fito.
Murmushi ta mata tare da basar da zancen
suna tafiya.
"Wannan ai wahala ce,ace duk inda
zan shiga sai miji ya ban izinin shiga?..
Kai ta
girgiza, "gaskiya da sake..
Hararar da Aunty A'i
ta mata ne yasa tai shiru.
Kallo Ummin tayi da
murmushi, a irin hudubar nan a baya suka
dilmiyarta,ita kwa yanzu a shirye take da yima
Ja'afar biyayya matukar bazata sa6a Allah ba.
Har akaje gida nan ma Ummin ta hau zaiyyanawa
Mama halin da Salma ta tsiro, tuni Mama tai
mata kacha-kacha,Ummi harda kukan takaici
ranar.
Da dare yazo ya dauke su,sai taga a motar
Garba da kamar ta ganshi dazun.
Taga anje gida
yana kokarin rufe mota da abin rufa sai ta kasa
d'aurewa ta tambayi nan zata kwana?
Murmushi
ya mata tare da bud'e gida.
Sai da akazo
kwanciya yake sanarta ai shine albishir din dazun
da yace sai sun zo gida.
"Ya sai sabuwa ne,sai
mukai cinikin wannan dashi tawan, munyi abin
hawa.
Murna tai ba kadan ba tana k'allon
mukullin motar.
Ido ya zuba mata yana kallo ba
koh kiftawa.
Baki ta kai kan idon tare da hurewa.
"Salma..
Hankalinta ta bashi tana murza
yatsunshi cikin nata.
"Daga yau na yard'e miki
koh ba idona ki taka ko'ina u r free...
"Dazun
naga komai Salma,ina horn bakiji bane,kin sani
farin ciki dazun kinsa naji ni din na isa gun
matata..
Duk inda ta tambaya nan zata jefa
kafarta.
"Sai ganan kuma kawu shima ya labarta
min yadda kuka yi sai murnar wai kin san ya
kamata yake..
"Nagode sosai,yau har kawu
yasan ni mai fad'a aji ne a gidanshi..
Murmushi
tayi tana kara ruk'unk'umo shi.
Ta gode Allah da
yasa ta gyara dabi'ar ta maras kyau ta maye mai
kyau.
Fatanta duk wata mace mai irin halinta ta
daina,dan ita taga misali akanta.
Dan a yanzu
rayuwarta ta fi mata dad'i da kwanciyar hankali,
ta gane yanzu kulle ma wasu matan ke ja ma
kansu, tana fatan kowacce mace ta guji fita a
bisa sharad'in *A BAKIN AURENKI* da suke
yi,dan gudun haifar da saki irin nata mai
gabadaya.
Alhamdulillah..
Nan na kawo karshen
littafin A BAKIN AURENKI..
Ina rokon Allah
kuskuren da nayi ya gafarta min.
Da fatan
darasin ciki ya isar masu halin Salma za kuma su
gyara,Allahu ya datarmu aikin kwarai a
gidajenmu.
Gareku dubin masoyan Feenat
Novel's, na gode kwarai da kaunar ku
gareni,Feenat na son duk mai sonta, dama wanda
bai yinta..
Luv you all.
Sai kun sake jina a sabon
littafi mai sunan... *RABO IN YA RAT'SE*...
Nafisa Bashir Tanko, (Feenat Ja'afar) ke muku
fatan saduwa da alkairi.