← Book details A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

A Bakin Aurenki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwan
Aunty A'i ne yasa aka dawo mutunci kuma.

Kullum tana gidan Ummi,duk dan gudun magana.

Yau kam Ja'afar yace ta hakura gobe tunda aiki
jibi kuma suna,yau masu g'yaran gida zasu zo.

Ba tace toh ba,haka bata ce a'a ba.

Sai dai duk
ta sauya,tunaninta muddin yau take zuwa gidan
Ummi,toh ba makawa sai sunce chaketa,hakan
ya tabbata kenan ita mai tsoron Ja'afar ce.

Tabbas lokaci yayi da zata nuna musu bata
tsoron Ja'afar.

Hakan yasa da k'warin g'wiwarta
ta tashi ta bishi d'akin waje.

Shiri yake yana son
fita wajen ciciku cikun neman takaddun shi da ya
kone.

Yanayin da ya ganta ta dan kama kai
yasan yau abin ya mot'so.

Kawai sai ya kau da
kai.

Zama tai gefen gado tana k'allon shi ta gefe,
"Haba Ya Ja'afar dan Allah...

Yau daya kar kamin
haka dan Allah, ka barni naje tunda an g'yara
kitchen ga kuma d'aki muna dashi a waje bayan
suna suyi aikin....

Ido kawai ya zuba mata,sai da
ta kai Aya tukun yai magana.

"Ke mey yau din
zata miki in baki fita ba?..

Kullum fa tun
haihuwar nan kina fita Salma,dan yau kad'ai nace
ki hakura sai gobe shine ba zaki iya ba Salma?

Fuska ta y'atsine, kan tace ita dai kawai ya barta
ta fita toh.

K'allonta yake,abu yai sauki yanzu
tana son dawo da hali?

"Son ranki za'a bi yanzu
koh nawa Salma?...

A gida na ban isa nace ga
abinda za ai ba sai ace a'a?..

Meye haka kike
son kawo wa kuma da ya wuce?....

Hawaye ta
fara mishi,tabbas yau in bata fita ba,toh gobe fa
sai dai ta toshe kunne.

Haushi tai bala'in
bashi,akan wannan shine harda kuka?..

Sam bai
son abin da ya wuce a dawo dashi.

Nan ta zaune
mishi tana mishi kukan gardamar sai ya batta.

Haka yanaji yana gani sai shi ya sauke ya barta
yace ta shirya su je.

Da murnarta ta shirya suka
fita ya sauke ta.

Sai dai shi sam baida walwala.

Haka tai ta fita har ran suyar nama,washegari
ma wai zata wanke gida,anan suka hau suka
fad'o..

Ya ja ta ja,harda fad'in dama ance
tsoronshi take ji.

Ya rant'se da in har ta fita,toh
zai maimaita mata abin ranar,wato ta fita a bakin
aurenta.

Tuni ta nut'su ta dawo hankalin ta.

Tuni
ya kashe bakin t'sanya,har ya fice ya barta tana
kuka,harda dariyar mugunta...

Ya k'wa gano lago
ai.

By Feenat Ja'afar.

Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
21_Ranar ta fita a Napep ta layin su Ja'afar taga
wani kamar shi tare da wata, har zasu wuce ta
gane Bintu ce,da sauri tace mai Napep ya t'saya.

Sam a yadda suke ba kace ba masoya bane,dan
sai wani sunne kai take kasa halamar kunya.

Tuni zuciyarta ta hau tafasa,ba shiri tai wajen
gadan-gadan,dai dai suyi sallama harda dago
mishi hannu.

Kan ta karasa har ya juyo itama ta
tafi...

Ganin yanayinta shima ya dan
tsorata,amma sai ya maze.

"A'a, har kin fito?..

Harara ta sakar mishi kan ta k'allo Bintun da har
tai mata nisa.

"Ban sani ba...

Ashe dama zance
ka fito shine kace na hau adaidata koh?..

Kuma
da Bintu?..

Har kana wani yage mata baki...

Hannu ya kai kan bakinshi halamar tai shiru yana
duba layin, "Haba Salma,a titi fa muke,kiyi hakuri
ba abinda ki ke zata bane ba...

Harara ta kara
sakar mishi,kan ta farga har ido ya ciko da
hawaye.

Tabbas yau ya tabo jaraba...

Dan sarai
yasan Bintu kam sonshi take,kuma Salma ta
sani.

Akan kishiya k'wa, yasan sai Salma taki ci
taki sha.

Tuni ya hau lallami harda rantse rantse
kamin ta yarda bayan anje gida.

Wataran yakan
yi tunanin koh Salma na da Aljanu,in ta tashi
sauya hali tafard daya ne,sai dai in ya bud'e
mata wuta su shirya. ~~~~~~~~~~ "Shiru ake
jinki makociya,koh dan ziyarar yamman nan an
daina zuwar mana sai jefi-jefi, koh mutumin har
yau yana nan da kullen?...

Baki ta dan ta6e,kan
ta bawa maman Ummi amsa.

"Ai sai abinda yai
gaba, yanzu tunda akai abinnan na farko abu
kadan sai ya kafan sharad'i kan in na t'sallaka a
bakin aurena, ina gudun rabuwar mu,yanzu ma
minti goma ya ban na dawo.

Baki Maman Ummin
ta ta6e, "lalle kina da aiki in dai mazan nan ne,
saf zasu mayarka marar y'anci in bakai ma
tufkar hanci ba,harda lokaci?

Tab aiki..

Ga gobe
sunan _nurse_ din layin chan (Maman
Nuwaira),ke koh barka baki je ba, ke kinsan za'a
watsa karya kiyi kok'ari ya barki muje.

Kai ta
k'ada, "Ai dole,dan wallahi baza ai bani ba,ko bai
bari ba naje koh minti ashirin ne a wat'sa
warishan nan dani.

Hannu Maman Ummi ta bata
suka tafa harda shewar su,ana haka Ummi tai
sallama,kan tunda ta shiga Jafar yace tana nan
ta fito,wai sai had'a rai yake,shi yasa ta bar
mishi gidan, nan ta daura kan na Maman Ummi,
Zuwa chan Maman ummin tace "Kiyi kok'ari hudu
ki biyo min zuwa 5 dawo.

Da wannan suka baje
har ta wuce ka'idar Ja'afar. *Washegari*.

"Wai
dan Allah Salma na tambaye ki zaki ban amsa?

Y'atsine fuska tai kan tace "ina ji..

"Shin dad'i ki
ke ji in kin t'saya muna musayarya magana
dake?..

"Mey yasa in na ce ki bar abu sai dai nai
son ranki,amma ni ban isa ba?

"Ita maijegon ta
ta6a tako kafarta cikin gidan nan da sunan tazo
gunki?..

Ki ban amsa?

Baki ta saka,kan tace
"oho,kana nufin gyaiyar sod'i zani kenan?..

Tunda
ga areni muje biki koh?..

Kai ya kada, "Ke ki ka
kira kanki haka,ba Ja'afar ba,abu daya na sani,ko
na fita ba jimawa zanyi ba, saboda in ma kin
fita,toh kisan inda dare ya miki...

"Mey ka ke
nufi?

Kana nufin yau ma zaka ce a bakin auren
nawa Ja'afar?..

Da sauri ya kada kai,
"K'warai,tunda abinki naga na yanzu har so yake
yafi na da, in har kam kin fitan,toh kisani,kin fita
*A BAKIN AURENKI*...

Sai ki zabi wanda ya fi
miki, aure?

Koh gidan suna?...

Kofar ya bugo
mata yai waje tare da barinta baki sake.

"Eh lalle
yau zan nuna ma tabbas ba tsoron ka nake ba
Ja'afar...

Wannan kurin bakin wallahi bazai
hanani fita sunan ba,daga yau kalmar nan ta *A
BAKIN AURENKI* tabar bakinka.

Daki tai tana
balbalin masifa ita kadai kamar yana k'allonta.

Kaya ta fito dasu tana duba wanda zata sa,
_lace_ din sunan Ummi ta dakko wani karamin
_swiss_ da aka sashi siyanshi dan dole.

Sunan na
manya ne, dan haka sai da kure adaka.

Ba koh
shakku ta fice, yau tun dazu taji gidan su Maman
Ummi t'sit kamar ruwa ya shanye su,halamar mai
gidan yana nan kenan,amma tunda ta fara jiyo
hayaniya tasan yai waje.

Gidan suna kam ya
kayatu, sun samu abinda ake so tuni aka baje a
faranti ana ci ana kora wa gulmar wata.

Kan ta
farga har 5 da yan mintina.

Haka kawai taji
gabanta na fad'uwa hankalinta yayi gida.

Tashi
tai ana fad'in ta t'saya k'ulli ya kare a k'ulla
mata tana a bawa Maman Ummi.

Sauri take ta
zubawa, dan da y'ar tazara a t'sakanin su.

Adu'ar ta daya,Allah sa Ja'afar bai dawo ganin
koh ta fitan ba.

Ta rasa dalilin da ya sa
hankalinta ya tashi,bayan ita ta zabi hakan.

Lekawar da zatai shine taci ka'ro da Ja'afar suka
had'a ido. *WAIWAYE*... ***************
************** Haka yai ta juyi har kusan k'arfe
biyu.

Washegari haka ta tashi sukuku, ga
fargabar Abba yau zai dawo,ga wani mugun
mak'on Ja'afar da yake taso mata.

Kai in ma ba
wai bata kula bane gani take zazzabi ne a jikinta.

"Salma...

Dagowa tayi ganin mama a kofa,da
mamaki fal fuska ta karaso ciki.

"Wai har yau
kukan nan ki ke Salma?..

Mey yaron nan yai miki
ne haka?..

Hannu ta kai kan fuskrta,sam ba
tasan tana kuka ba, da sauri ta goge tana
k'ak'alo murmushin dole.

"Mama ina k'wana..

Kai
kawai ta kada mata.

"Haba Salma,kar fa ki rako
mata duniyar nan...kar ki zamo mace mai
kulafucin D'a namiji duk k'wa wulakancin da ya
mata man...

Ashe ni ina chan jiya nai baccin
farin ciki da aka rabu lafiya ba rabo bare ya kawo
cikas a zawarci ashe ke kina nan kina kukan an
rabu?

Haba Salma, karan nan ne fa ki ke da
dama ta biyu,tunda har ya sallame ki.

"Maza
goge hawayenki ki biyoni daki yanzu.

Kai ta
kada,a gaskiya ta fara mamakin irin kiyayyar
dasu mama suke ma Ja'afar, wato har ma godiya
ake ta rabu da alakakai?...

Allah yaga tafi jin
haushin kanta sama da haushin Ja'afar, in ma
taji haushin shi toh bai wuce yadda ya k'ulle
mata gida ya kuma tafi koh ajikinshi.

By Feenat
Ja'afar.

Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29
Feenat Ja'afar Novel's
*A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*.
22_"Toh wa ya jawo?...

T'sam tai yayin da zuciya
ta tambaye ta, "Ni ce...

Tabbas ni najawo, amma
ba laifi na bane.

Kuka ta fashe dashi,tabbas anci
k'arfinta,ta ko'ina an mata dabaibayi da huduba
gur6atacciya.

"Gashi na jawo wa kaina saki biyu
ba tare da na samo kan ba(kan Ja'afar)..

"Oh ni
Salma..

Ina tunani na yake da har na aikata
wannan wautar?..

Ina son da nake ikirarin ina ma
Ja'afar?..

Ina ya je...

"Salma...

Mama ce ta
kat'se mata tunanin gaskiya da kira.

Hannu tasa
ta share hawayen ta,ta daga kai tare da fitar da
iska dan daidaita nut'suwar ta.

"Na'am..

Ta amsa
kan ta tashi tai waje.

"Gani mama, Kan gado ta
nuna mata kan tazo ta zauna.

Ba musu ta
karaso.

Kafad'arta ta dafa kan ta numfasa, "Kina
ji koh Salma?

Kai ta daga mata.

"Baban ki yau
nasan zai dawo,tabbas ya rit'saki nasan zai cid'a
ki ne a banza.

"Yanzu abinda nake so kiyi
shine,ki je gidan A'i,dan mijinta baya gari ya tafi
sari,ki barni in na gama lalla6a shi sai ki
dawo,dan karan nan kam sai dai ai wacce za ayi,
amma aure kin gama...

G'wara a chanja
hannu,tunda wannan d'in ba fus, bare ass,sai dan
banzan dacin rai ba koh gidan kai...

Hawaye ne
ya zubo mata,ba da ban suna matukar kama da
Mama ba,da tayi shakkun akan haihuwar ta...
Chapter 11 · 0% Book details