← Book details Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmmm Alhaji ke nan gaskiyar nan ɗaya da na faɗa maka ita ce sai dai ban san me Ubangiji zai yi a gaba amma ni in a ra'ayina ne babu chaji.

Alhaji Tahir yace '' Allah ya zaba mana abin da yafi Zama alkairi.

amin ya Allah yace.

sallama yayi mai ya shiga motar sa shi kuma ya shiga gida jikin sa a sanyaye abin da yake fatan samu gashi ya samu amma yafi karfin sa.

ganin NIMRAH yayi a zaune kamar ba ita bace ta gama aljanu yanzu.,,

zama yayi hafsatu tace '' kaga an samu ta farfaɗo.''

dan Allah mama me nayi naga duk kuna kallo na

Malam yace '' hmmmm nimrah kedai ki dinga addu'a Allah ya baki lafiya yau cewa kika yi za'a dauke ni duk irin soyayyar da take tsakanin mu.''

dariya ce ta kusan kubbuce mata ganin yadda malam ya koma abin tausayi tace ''dan Allah malam?.''

hmmm kedai idan ana cin ɓaure ba'a tone tone.

kwanciya tayi tana cewa mama akwai abinci kuwa ...?

mama da sauri tace '' eh sauran nawa umaimai dauko mata , taci.,,

NIMRAH tace '' a'a mama ci naki bazan ci ba .''

NIMRAH ba komai ki ci ai ba wai koshi kikai ba.

Ke dan uban'ki, ba zaki je ki dauko mata ba.''

to ta faɗa tana tashi zuwa tayi ta dauko mata amsa tayi tana cewa ɗebo min ruwa fatima zo kiyi min firfita.

dukkan su da to suka amsa mata.

★★★

Okay eh gurina tazo ku barta ta huce Hidaya ta faɗa tana kashe wayar ta security din gidan ne suka hana bestie shigowa.

tashi tayi ta dauki cake ta fara ci tana kurbar lemo idon ta na kan TV ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tayi.

a kullum kara farin ciki take , saboda ita kan'ta tasan Ubangiji yayi mata ni'ima tana auren salihin miji wanda ba ruwan sa baya takurawa rayuwar sa tun da ta zo gidan bata , taɓa bashi abinci ba bello ta sauke mai wani nauyi nasa bata san ta gyara mai party ɗin sa ba , bata taɓa tambayar sa ba wa yake gyara mai..

Assalamu alaiki.......

da sauri Hidaya ta ɗago tana amsawa bestie ta karaso rungume'ta, tayi tana cewa i love you.

Hidaya sakar mata kiss tayi a kumatu bestie tace '' na fa dade a tsaye mutanen nan suka hanani shigo wa.,,

ba laifin su bane suna akan aikin su.

zama tayi kusa da ita tana yi mata wani irin kallo Hidaya tace '' bismillah.''

no nafi bukatar ki fiye da abinci ta faɗa tana kama hannun ta .,

kallon agogo Hidaya tayi tace '' ki daure ki taɓa ko dan wani abin ne .''

Bestie tace '' ban dade da cin abinci ba .''

Hidaya hannu ta saka akan lips din bestie tace '' shiiiii kin manta yau kwana za muyi muna aiki gwara ki cika cikin ki.,,

Amina alhasan Muhammad opay 8141785374

1k

Special group 1500

ku turo da shedar biya ta wannan number 8141785374
𝐙𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐍°𝐓𝐀 𝐓𝐀𝐊𝐄...

OUMYASMEEN

𝑬𝒑𝒊𝒔𝒐𝒅𝒆 4

Bestie tace '' ciki na a cike yake bana buƙatar cin komai.,,

Hidaya tace '' okay amma dai da kin daure kinci nifa bana so bako ya zo gurina yaƙi cin komai Please dan Allah ci ko ba yawa ne..,,

bestie tace '' tun da kin matsa bara naci ko yaya ne.,,

ina so zan wanke hannu na

Bestie ta ƙara tambayar ta.

Hidaya tace '' a dining room akwai sink.''

to tace ta , tashi tana ƙara jin jina arziki irin na mijin Hidaya gida kamar ba'a kasar nan kake ba babu abin da ta nema ta rasa parlour ta sai kace fadar sarkin Dubai ikon Allah, step ta , taka guda hudu sannan ta hau kan barandar inda dinning din yake nan ma gida guda ne wani irin decoration aka yi wa gurin painting ma shi kan'sa abin kallo ne tana kai hannu inda sink din yake ya kunna kan'sa da yake automatic ne wanke hannun ta , tayi tana gamawa sai ga wata iska ta fara ratsa ta me kamshi nan take hannun ta ya bushe ta fito tana mamakin to ban da tabewar rayuwa matar da take cikin daular nan me za tayi da wannan rayuwa ita , ada ta dauka neman mata ana yin sa ne saboda samun kudi ashe abin ba haka ba ne.

zama tayi a kujerar kusa da ita tace '' ya hakuri..?,,

Hidaya tace '' hakuri kuma mene ya faru?.''

Bestie tace '' auren da mijin ki zai yi.,,

tab ni wallahi Allah ma na manta yarfe ne na social media fa , saheer ba zai taɓa aure ba ni wallahi da naga picture din naci dariya Al fa zata iya kashe aure.

Bestie shiru tayi tana kallon ta , tace '' shi da bakin sane yace miki haka?.''

no bamu yi maganar dashi ba amma wallahi Saheer ba zai taɓa aure ba ke ni bani da lokacin tambayar sa wannan banzan tunanin

cewar Hidaya.

Bestie tace '' da sauki ma tun da kin san halin sa.,,

Wannan kenan.

tun da kahu ya fara yi mai bayani ya kasa cewa komai har ya kai ƙarshen zancen sa yace '' to shikkenan duk hukuncin da suka yanke dai-dai sai mu jira su ,,

shiru yayi domin jin me zai ce mai sai yace '' amin ya Allah.,,

Sannan yayi mai sallama.

HAJIYA tace '' yaje can ne ?.''

saheer yace '' eh yaje amma mahaifin ta yaƙi amincewa wai saboda su basu da kudi, nafi karfin yar'sa.,,

mswww zancen banza kamar gaskiya yayi haka ne domin ya nuna muku kudin ku be dame sa ba sai daga baya ya fara fito da halin sa.

Cewar Hajiya.

Saheer shiru yayi yana jin ta can yace '' Hajiya bara na tafi tun da naga sun yi bacci .''

Hajiya tace '' to ka ajiye su a hankali karsu tashi su hana mu zaman lafiya.''

to yace a hankali ya sauke afrah daga kan cinyar'sa ya kwantar da ita faruq daman yana kusa da shi

kallon su yayi ya kalli Hajiya yace '' sai da safe.''

Allah ya tashe mu Lafiya Ubangiji Allah ya tsare hanya.

Amin ya Allah yace ya ajiye mata kuɗi a kusa da ita sannan yace '' gobe inshallahu za'a kawo kayan nan.''

Albarka ta ƙara saka mai sannan ya fita samun direban sa yayi yana jiran sa da sauri ya fito ya buɗe mai gurin me zaman banza.

shiga yayi ya dauki magazine din da aka ajiye mai dubawa ya fara yi magana ɗaya ce dai akan auren sa ajiyewa yayi yana ciro wayar sa miss Call ya samu duba dayar yayi itama miss Call ce da kuma messages.

dukkan kiran akan kasuwancin sa ne na manfetur da ya fara yi, kafin ya ajiyewa wayar sai ga wani kiran ya shigo da gawa yayi.

ƙara wa yayi a kunne magana suka soma yi akan Company sa da yake ibadan yace '' inshallah acikin satin nan sadam zai zo ni kuma zan huce chaina inshallahu a cikin satin nan.''

sun jima suna waya Sannan yayi mai sallama ya amsa wata wayar har suka isa gida be dena waya ba kashe wayar sa yayi ya dauko jakar sa da ɗaya wayar sa ya fito.

kai tsaye part din'sa ya nufa ajiye jakar sa yayi a kan kujera yana sauke a jiyar zuciya.

duk da dare yayi dole ya gyara wajen kwana biyu da baya nan yayi datti jiya da ya dawo sai da ya share bedroom din'sa sannan ya kwanta baya son yan aiki su gyara mai daki da tuni ya dauki masu aiki suna gyara mai.

zama yayi ya dafa kan'sa ajiyar zuciya ya sauke har yanzu mamaki yake da al'ajabin abinda kahun sa ya faɗa.

ba mamaki yanzu haka , haɗa baki suka yi, amma zai nuna wa alhaji nuhu be isa ba auren yarinyar kamar yayi shi ya gama ne.

knocking yaji da sauri ya kalli kofar tasa , a tunanin sa ko dai kunnuwan'sa ne suka ji mai ba dai-dai ba amma sai ya saurara tabbas knocking din kofar sa ake yi.

tashi yayi ya buɗe Hidaya ce ta ci ƙananan kaya tamkar wacce zata gasar kyau dauke idon sa yayi daga kallon ta ya koma ya zauna ba ko sallama ta zauna a kujerar da take facing din'sa tace '' sannu da dawowa.,,

saheer yace '' sannu dai.''

taunar chingum ɗin da take yi ta dena tace '' amma naji baka kara cewa komai ba akan tafiya America ina so na dan sami hutu kaga anan bana samun wani hutu duk da akwai yan aiki wani abin dole nayi.

Saheer yace '' a'a.,,

da sauri ta kalle sa ji tayi kamar ta shaƙe sa tace '' amma ka yi min adalci kenan kasan fa zaman da nake yi acikin gidan nan, ya kamata ka sakar min yanci na tun da a ka'ida aure be kama ce ka ba , saboda son rufa maka asiri na yarda zan zauna dakai a haka ba wanda ya taɓa jin maganar nan sai dai kowa ya kalle ni bakya haihuwa bakya haihuwa.,,

idon sane ya canza launi wannan kalaman nata sun bugar mai zuciya kallon ta yayi ya cire glass din'sa yace '' okay fine amma dai kin san ban miki dole ba ? kuma ni bana kallon ki a matsayin ba matata ba , da ace yau bani dashi wallahi Hidaya baza ki taɓa rufamin asiri ba amma lokaci yana nan zuwa da zaki sha mamaki.,,

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kenan kallon da kake min me son kudi ko to shikkenan saheer ba damuwa.

ta faɗa tana tashi tsaye buɗe kofa tayi ta fita .

tashi yayi ya gyara ko ina sannan ya shiga toilet cire kayan jikin sa yayi, abubuwa da yawa suna damun ƙwaƙwalwar sa sakarwa kan'sa shower yayi yana rintsai idon'sa ga damuwar kasuwancin sa gashi ya dawo Hidaya bata kwantar mai da hankali ba shi kuma wallahi bata isa ta saka shi a bin da be yi niya ba tsanar ta ce ta ƙara samun matsuguni a cikin zuciyar sa.
Chapter 8 · 0% Book details