← Book details Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 14

Sashe 10

Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jikin nimrah yayi sanyi tabbas mutuwar uwa ɓala'i ce har yanzu mutuwar maman'ta tana taɓa ta uwa gatan ɗan ta , tace '' Allah sarki .''

daga haka taja bakin ta , ta tsuke zama tayi, tana cewa ni wallahi ban ma san ta ina zan fara ba komai fa ya ƙare dan jarin ma da nake dashi wacce mara tsoran Allah ta cinye.

Hafsatu tace '' uhmm Allah ya kyauta.''

nimrah kallon ta , tayi ta ja kwafa sarai taga shan kamshin da take mata.

tashi tayi, ta shiga daki ta kwanta tana so ta je ta dauko takardar ta , to bata san yadda za tayi ba su bata takardun ta ko zata dace ta samu aiki a wani Company.

tana cikin wannan tunanin ne taji sallamar farida kawar mama dogon tsaki taja ta tsani munafukar matar nan tun maman'ta tana da rai bata shiga harkar ta domin idan tazo sun dinga yadawa maman ta habaici.

gyara kwanciyar ta , tayi kwata kwata, ta rasa wanne tunani za tayi ta samawa kan'ta mafita har ga Allah ba zata iya ci gaba da rayuwar nan a haka ba gwara ta nemi mafita.''

Amina alhasan Muhammad opay 1k 8141785374

Special group 1,500

Ku turo da shedar biya ta wannan number 0814185374
ZAMAN KANTA TAKE

Episode 5

NIMRAH nimrah sarai ta jita sai tayi mata ban za domin a yanzu bata da lokacin ta.

Mama ɗaga labule tayi tace '' yanzu NIMRAH kina jina kikai min banza?.''

juya idanuwan'ta tayi ta chanza murya tace '' eh lafiya kike yi mana wannan kira irin na hukuma..?.''

dafa kirji hafsatu tayi ta juya jikin ta na rawa kawar ta , tace '' lafiya kika fito a firgice kina da kamar yarinyar nan ace aikin gida ma sai kin yi shi ni wallahi Allah da ace yar miji na ce wallahi tsinke ba zan daga ba tun da dama taki ba sai a koma wa hagu ba Allah be kawo mata miji aure ba kin ga sai ta zama yar wanke wanke da share share kafin Allah ya daga ta.

tun da ta fara wannan zancen mama take saka hannu a bakin ta , take mata alamar tayi shiru amma kamar kara tun zurata take yi sai da takai aya.

NIMRAH da take ɗaki ta daddage ta zunduma wani irin ihu tare da cewa kin gama ko akwai sauran magana mu barki, ki karasa zancen ki na ƙarshe a duniya.

Farida dafe kirji tayi ta kalli mama tace '' hafsatu wannan kamar ba Muryar mutum nake ji ba?.''

Hafsatu ɗaga mata kai tayi tana daga mata hannu tana sakawa a baki alamar tayi shiru da bakin ta kafin aljanun nimrah su zane ta tas.

da sauri ta dauki mayafin'ta da ta , rataye ta fita da gudu daga cikin gidan.

Nimrah tana daki wani murmushi ta saki ta juya ta kwanta cikin ta na yi mata kugin yunwa.

tashi tayi ta fito daga kan'ta sama tayi a fili ta furta tab wallahi ba zai yiwu ba dole duk yadda za a yi na koma wajen nan.

Hafsatu da take cikin daga a hankali ta ɗaga labule jin abin da take fadi ido hudu suka hada da nimrah tace '' mama kin gama girkin nan ne?.''

Mama tace '' kina ga ko tukunya ban dora ba kike maganar na gama girki.,,

nimrah dafa bango tayi tace "' zan fita idan kinji shiru ki je police station domin wallahi Allah banzan yarda ba sai matar nan taba ni kudi na yo hauka ake yi haka kurum ta cinye min kudina."

Kinga nimrah ki yi hakuri ki dauki kaddara wannan matar da kike gani bata tsoran Allah da ace tana tsoran Allah da baza ta cinye miki kuɗin ki ba.

Cewar mama.

Mama wallahi zuwa zanyi na dauki akuyar ta kaita bakin kasuwa gurin Me Dabba.

NIMRAH ta faɗa tana kallon mama.

Mama tace '' tun da bakya ji sai kin dawo gaki ga hanya nan ke ko ciwon da kika ji a kafa be isa ya saka ki zauna na sai kin fita gantali.''

shiru tayi tana sauraran ta , daukan botiki tayi tana cewa wallahi Allah na ɗebo ruwa wani me dogon hannun ya daukar min sai ransa ya ɓaci ya za ayi kamar gidan nan mu dinga zama babu ruwa.

banza mama tayi mata , fita tayi tana ci gaba da fadan ta.

Wannan kenan.

Gaskiya abin nan ya ban mamaki, anya kuwa hakan baya cikin shirin su?.''

cewar Saddam

Saheer harde hannunwansa yayi a kirji yana juyawa akan kujera yace '' ba mamaki domin wallahi lamarin su Alhaji Nuhu yana daure min kai ko baka ji yadda price din su ya sauko ba ? wato sun bi ta wannan hanyar sun ga ba riba amma ni ina ganin kamar mu ajiye maganar auren nan saboda kaga ni yanzu ba wannan ne a gaba na ba tun da alhamdulillah mun yi maganin wannan matsalar sai mu ajiye ta a gefe.''

baka tunanin za su iya dawo da zancen Saddam ya faɗa yana kallon sa domin shi a yanzu Babban burin sa ne huce ganin ogan nasa yayi aure ba ko dan ya samu farin ciki a cikin gidan sa uwa uwa zargin da da yake wa Hidaya.

Saheer yace '' to shikkenan ta ina kake ganin zamu bi ne ?.''

Saddam yace '' idan tana da yan uwan uba mubi ta hannun su ina ganin wannan hanyar me bullewa ce domin kar su kara dawo da wannan labarin.,,

to shikkenan ya faɗa yana buɗe laptop ɗin sa.

saddam sallama yayi mai kai kurum ya ɗaga mai yaci gaba da aikin da yake gaban sa sosai ya mayar da hankali kan aikin sa wani murmushi yayi ya cije lips ɗin'sa.

bisa dukkan alamu dukkan wani zargin sa , ya fara tabbata hakan da yayi, yayi ne domin ya gane ita wace'ce.

shi ya saka har yanzu ya kasa yarda da ita akwai abin da ya faru shekarun baya ba zai taɓa manta tawa dashi ba tabbas ita ya gani a hotel amma me sai ta nuna ba ita bace bayan da idon sa ya ganta ta riƙe hannun wani namiji shi kuma tare da yake da wani bakon sa da yazo kasar dan kadar Pakistan ne.

ganin tunani na ne man yi mai yawa sai ya yi saurin kawar da wannan tunanin ya ci gaba da aikin sa cikin nutsuwa.

wannan kenan.

Ki bari zuwa gobe sai ki tafi cewar Hidaya.

Bestie tace '' gaskiya gwara na yafi so nake gobe na hau jirgi na koma lagos.''

Hidaya tace '' okay ba damuwa karki manta da ki ƙara yi mata magana.''

Inshallahu , ta faɗa tana tashi tsaye hada kayan ta , tayi Hidaya tana ƙwance tana danna wayar ta.

Bestie gama shiryawa tayi tace '' to sai mun'kara haduwa ni zan tafi.''

tashi tayi ta riƙe mata jaka tace '' muje na raka ki ko...?.''

No da kin zauna naga kina jin dadin kwanciyar da kika yi karna takura miki.

Cewar bestie.

bata rai tayi tace '' wanne takura ana zaune qalau muje na raka ki.''

ta faɗa tana riƙe hannun ta a hankali suka fara tafiya har suka fito harabar gidan Hidaya kallon katon gidan tayi ji tayi kan'ta ya ƙara yin girma duk ita kaɗai ce a cikin wannan gidan kuma ba macen da ta isa ta shigo shi idan ba ita ba.

shi ya saka take tsula tsiyar ta son ranta, a bakin gate ta , tsaya tace '' sai mun yi waya.,,

to shikkenan Allah ya sai an jima.

ta faɗa tana karbar jakar hannun hidaya hidaya juyawa tayi ta fara tafiya, barka da fitowa Hajiya cewar me bawa shukoki ruwa.

ko kallon inda yake ba tayi ba ta dauke kan'ta ta ci gaba da tafiya tana zuwa kofar da zata shiga part din ta sai ta bude da kan'ta shiga tayi tana kallon wajen kamar yau ba'a share shi ba duk furen bishiya ya bushe ga alamun duk kura akan tayar ɗin.

da sauri ta fito tana kwalawa kai kai mai bawa shukokin ruwa zuwa yayi ya ɗurkusa a kasa yace '' ranki ya dade gani.''

Kira min duk wani ma'aikaci da yake cikin gidan nan

da sauri yace '' to an gama ranki ya dade.,,

Ya fadi haka jikin sa yana rawa a guje ya kirawo kowa , dukkan sune suka taru kowa yayi kasa da kansa Hidaya tace '' su wa'yancan raini ne ya saka suka ƙi zuwa ko yaya....?.''

ta faɗa tana nuna sojojin da suke kofar farko ta cikin gidan.

kallon kallo aka shiga baba buzu yace '' ranki ya dade ni aikin gadi nake sauran kuma jami'an tsaro ne shi ya saka kika ga basu zo na basu da alaƙa da wannan maganar.''

What kai na saka kane a ciki da zaka faɗa min haka?.''

Baba buzu yace '' kiyi hakuri.,,

hararar tsohon tayi sosai yake jin jina rashin kunyar Hidaya Alhaji saheer yana girmama shi, a yanzu kawai yana zama ne a cikin gidan yana biyan shi albashi maharazu ɗan sane ke komai shi yana zaune be dena bashi albashin shi ba , ya bashi ya bawa maharazu.

Ran maharazu ne ya ɓaci amma sai danne Hidaya tace '' a cikin ku wa yake yin share share...?''

isa yace '' ni ne hajiya.''

daga yau na kore ka saboda baka san aikin ka ba ya za ayi kabar min waje duk datti saboda baka san darajar kanka ba , so kake cuta ta kama ni na mutu ko saboda kai jahili ne baka lura da abin da ya dace.

HAJIYA Alhaji ne yace min nade na sharewa zai dauko wasu ma'aikatan ni iya kaci na harabar gidan nan sauran matan kuma gyaran bangaren ki da bayan gida.

har akwai wanda zai zartar da hukunci ban sani ba ta faɗa tana kallon su.

Isa yace '' Alhaji ne ya fada min haka.,,

juyawa tayi ta bar gurin ranta duk a ɓace me saheer yake nufi wato ita kenan photo ce a cikin gidan dole ta ƙara jan ɗamara.
Chapter 10 · 0% Book details