← Book details Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hidaya rasa ina zata saka ran'ta tayi kawai sai ta kashe wayar neman mafita, ta shiga yi bata kaunar taga amrah tayi nisa da ita dole ta wargaza auren nan idan har tana so taci gaba da kwanciyar hankali kafin hawan jini da ciwon zuciya su kama ta tashi tsaye tayi ta shiga kai kawo a cikin parlour zuciyar ta , tana yi mata wani irin bugu kamar zata faso kirjin ta , ta fito...

Wannan kenan...

N.N.D.C QUARTER.

ana idar da salla ya dawo afrah bata dena kuka ba tana ganin sa sai ta tawo gurin sa rungume ta yayi yana cewa hi shiru gani nan na dawo.

shiru tayi ta kwanta a jikin sa , tana sauke ajiyar zuciya.

HAJIYA tace '' ka samu wacce kake so ne ? .''

ɗago kan'sa yayi yace '' eh so nake na fadawa abba ya je ya tambayo min gidan su.''

ikon Allah a ina take daman iyayen ta basu san ka bane ko yaya naji kana maganar tambaya...?.''

Ajiyar zuciya ya sauke yace '' yar nan tudun bala ce so nake na fara neman izinin mahaifan ta.''

Hajiya jin jina kai tayi tace '' wane mahaifin ta ?.''

abinci ken da nayi ance min direba ne suna zaune a wani gida , gidan ma na haya ne amma ni duk ba shi ne damuwata ba yabon da ake mata shi ne abin da yafi min dad'i.

HAJIYA tace '' kai kuwa saheer be ka gani a jikin yarinyar nan bafa naso ka auro dangin yunwa duk su ɗora maka nauyin da ba naka bane ci da shan iyayen ta ya zamo yana kan ka , kasan talakawa ne ke son mallake miji da yan uwan sa Gaskiya da zan faɗa maka ka dauka sam ba tayi min ba ni nayi zaton auren nan za ka yi na ƙwarya tabi ƙwarya sai kaje ka samo mana yar gidan malam shehu.''

jikin sa ne yayi sanyi, da zai iya faɗa mata da yayi mata bayani auren nan shine rufin asirin sa, zai toshe bakin alhaji nuhu ne musamman ma sharrin da yake kokarin yi mai sharri mafi munu duk da ya fitar da wannan labarin amma wannan maganar ta auren sa ta danne wannan yace '' Hajiya kamar dai yadda kika ce a farko kin amince dan Allah ki amince bana son abin da zan yi ya zamo ba da yardar ki ba.''

Buɗe baki tayi za tayi magana sai ga Alhaji Tahir yayi sallama hamdala tayi me taya ta yaƙi ya zo ta amsa mai sallamar sa tana gaishe da shi amsawa yayi yana zama.

tace '' yauwa gwara da Allah ya kawo ka dan ka yau ya dauko mana abin da yafi karfin mu nan ta faɗa mai komai.''

Alhaji Tahir yace '' a'a ai ba wani abu bane Hajiya ki taya shi da addu'a kiyi mai fatan alkairi saheer yana da kudin da zai iya auren mace hudu har da kwarkwa'ra .''

shiru tayi ya ci gaba da cewa ni wallahi sam matar nan tasa ba tayi min ba , gwara ya auri yarinya kina ga tun da akai bikin nan ya dauke wa kowa ko ni da ina ganin ta a cikin gida na amma yanzu bata zuwa ita nunawa take a yanzu tafi karfin kowa kawai kiyi mai fatan alkairi sau da yawa abin da muke gani duhu ne ba haka bane haske ni talaka da me kuɗi duk ɗaya ne Hajiya.

Ba yadda ta iya haka ta amince yace '' ni yanzu haryar ma zan yi sai na biya bani address din.''

HAJIYA tace '' da sauri haka?.''

to Hajiya shi da ba yaro ba , me kuma za a jira,

HAJIYA tace '' haka ne.''

Saheer sosai yaji daɗin zuwan kahun nasa , bashi address yayi, baba jummai ta kawo mai abin motsa baki faruq zama yayi akan cinyar sa da yake mutum ne me son yara be damu ba.

WANNAN KENAN.

kwanon abincin ta hafsatu, ta dauka tana cewa ke umaimah uban wa yace ki zuba mata kamar haka yafi na kowa...?.''

nimrah ɗaga kan'ta tayi, ta kalle ta buɗe baki tayi, zata yi magana sai ta kalli malam da yake zaune jira take taga wanne mataki zai dauka sai taji yayi shiru.

hmmm idan baku san wata ba to yanzu zaku gane Allah da girma yake ta faɗi haka a cikin zuciyar ta .

tashi tayi, ta fara tafiya sai da taje dai-dai tabarmar da hafsatu take zaune ta zube ta sako wani irin ihu dukkan su tashi tsaye suka yi suna kallon ta.

mimmiƙewa tayi tana cewa shi ne kuke takura mata kuna kuntatawa rayuwar ta akan kun ga bata da gata to mune gatan ta yau za mu toshewa kowa taka shi, shi kuwa malam mun dade muna tara shi yana gani ana hanata abinci amma baya magana saboda yana ganin ba shi bane ya nemo to yau za mu dauke shi mu kai shi duniyar mu, muhukunta shi dole mu hana yin bacci na tsawon shekara arba'in.

salati malam ya saki lokacin da yaji tsassauran hukuncin da aljanun nimrah sukai mai.

Hafsatu tace '' dan girman Allah kuyi hakuri ku sassauta min banyi zaton abin zai bata muku rai ba , yarinyar ce bata da kunya.''

Kan uba lallai yau zamu nuna miki ainihin mu suwa ye , kin ƙara laifi cikin laifi dole mu katsai miki jijiyar idon ki na tsawon shekara dari uku dole mu sakar miki gudawa.''

habawa hafsatu tana jin haka , cikin ta yayi wata iriyar murdawa dafa cikin ta , tayi ta fara matsar kwalla hawaye shar shar yana bin fuskar'ta tace '' dan girman Allah kiyi hakuri.''

Khuce nayi meri zandagi bayya mun gama dake au kai wuyan ka ya isa yanka baka iya bada hakuri ba ko? yau zaka fuskanci hukuba wallahi.

Malam yace '' a'a kai na bisa wuya na kuyi hakuri jira nake ta gama sai ni nayi kar kuce nayi muku kutsai cikin lamarin ku ko kuce na nuna rashin girmama wa kuyi min afuwa.''

Umaimah tace '' malam Ayatul khursihu za kuyi mata sai su tafi.''

Yeeee huuuuuuu Yeee huuu dan bantan uban ki damu jiya aka sauke Kur'ani dole mu tsayar miki da bakiin ki a buɗe mu zubar miki da haƙora sai muga da abin da za kice ayi mana addu'a.

fatima tace '' ni wallahi ba ruwana kuyi hakuri.''

wata uwar atishawa tayi sai kuma jikin ta ya saki , malam yace '' Alhamdulillah ku dauke ta , ku shigar da ita daki idan gobe tayi zan je gurin malam Liman, yayi mata rubutu ni daman gani nake nimrah kamar tana da aljanu .''

mama hawaye ta share tace '' na shiga uku malam gudawa fa Allah ka yaye min.''

Ke ba abin da suka isa suyi miki bara zana ce.

nimrah da take kwace ta saki wata ƙara tace '' yanzu zamu aiwatar da shirin mu tun da kace baraza ce dole mu dauke ka.,,

almajiri ne ya shigo yana sallama cikin tashin hankali fatima ta amsa mai tana ja baya almajirin nan yace '' wai ana sallama da malam.''

da sauri umaimah tace '' karka je malam wata kila sune , sukai basaja.''

malam bece komai ba ya fara tofawa nimrah duk addu'ar da tazo bakin sa , tashi tsaye yayi yace '' muje.''

fara tafiya yayi suka fita kofar gida sai da gaban sa ya fadi Saboda wata ƙatuwar mota da ya gani kasa ƙarasawa yayi ya tsaya yana addu'a domin ko tantama baya yi aljanun nan sune suka zo daukar sa to ayar Ubangiji tafi su.....

yana tsaye yaga an buɗe murfin motar nan shi dai tsayuwa ya ci gaba da yi domin gani yake shikkenan ƙarshen sa ya zo.,,

Assalamu alaikum.

yaji sallama, amsawa yayi mutumin miƙa mai hannu yayi suka gaisa.

Sannan yace '' idan ba damuwa ina so muyi magana da kai.''

kallon kayan jikin mutumin yake turkashi to shi da ba wani attajiri ba , balle yace yana da hadi da wannan attajirin da alama ma tukashi ake yi ,malam yace '' to ba damuwa Allah dai ya saka lafiya wallahi ni nan talaka ni kuma ba ruwana da , shiga sabgar wasu balle nace hadakar kudi ta haɗo ni da wani,

murmushi Alhaji tahir yayi yace '' alkairi ne ke tafe dani ka kwantar da hankalin ka .''

malam yace '' to ina jin ka .''

domin shi har ga Allah, Allah Allah yake ya bar mai kofar gidan sa barin yanzu da duniyar nan bata da gaskiya sai a cutar dashi kuma ba yadda ya iya ba shi da ke rama mishi idan ba Ubangiji ba , kaf dangin su babu wani me sharararen kudin da zai daukar nauyin sa kowa takan sa yake.

murmushi Alhaji tahir yayi yace '' okay ba damuwa na lura tsoro kake ji har yanzu hankalin ka be kwanta dani ba da farko dai sunana Alhaji tahir bashir nazo nemawa ɗana Alhaji saheer dalhat dauren yar ka , nimrah idan ba ayi mata miji ba .''

Ƙwaƙwalwar Malam Umaru ce ta tafi tunani da sauri ya ɗago yace '' saheer dalhat me Company manfetur ko wani ba wannan ba ?.''

Alhaji Tahir yace '' shi.,,

Malam jinjina maganar sa yayi a gaskiya ba zai iya aurawa nimrah kamar saheer ba Saboda a komai ya fisu baya so tayi auren da ba kwanciyar hankali a cikin sa , irin su ma basa so talaka ya rabe su, to shi bashi da wannan son zuciyar a ina ma yaga nimrah anya kuwa daman ance masu kudi suna tsafi ko dai dodon tsafi su ne ya nuna musu NIMRAH duk da kowa yana yi mai kyakkyawan zato musamman ma temakon al'umma, malam Umaru yace '' kayi hakuri NIMRAH ba sa'ar auren sa bace kaga dai a yadda muke ba sai nayi maka bayani ba kai hakuri Allah ya basa dai-dai da shi itama Allah ya bata dai-dai da ita.''

turus Alhaji Tahir yayi mamaki ne ya kama shi daman akwai irin mutane nan har yanzu yace '' kayi dai tunani na baka nan da sati biyu kayi shawara.''
Chapter 7 · 0% Book details